Sashe 7
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yanxun kuwa sunyi girma kamar kajin turawa tamakar sun shekra 5. Ishaq yana musu dariya yace ku saketa sultan kada ku kada ta gobe ku rasa mau daukanku, suka saketa suna ta tsallen murna$ Aneesa suka isa suka risina suka gaida Ishaw suka juya wuka gaida ginbiyar tasa, da ta take nade akujera tana karatun Novel da yake Allah ya hada jininta da na Aneesa da fara'ar ta amsa gisuwarsu, har tana tambayarsu Hajiyan zaria. Hajiyan Ishaq kenan haka suke ce mata. Driver ya shigo da kayansu, ya risina yana gaida Ishaq ya dube shi yace sannu da hanya lawal, ya kabaro mini hajiyata? Yace lfy lau take tace a gaishe ku, wlh har da tsaraba ta bani na kaiwa Iyali, nagode Allah ya kara girma, Hajiya sam bata gajiya da dawainyya, mumma ai kana dawainiyar da mu. Allah ya taimake mu gaba dayanmu. Yace ameen, Sannan ya fice abinsa Ishaq ya dubi matarsa yace Safeena ina za su kai kayansu? Ina nufin wani daki cikin 3 din can? Ta dube shi tace, ai na gaya maka masaukinsu. Yayi murmushi saboda ya tuno rigamar da sukayi da ya gaya mata yau su Aneesa za su zo hutu shine tace, Gaskiyya so kake in takura shiysa zaka dauko en mata ka kawo mini cikin gida, babu ma kamar sadiya, tunda Aunty Mami (Yayarsa) ba so na take ba, samini ido zatayi, ni kuma kasan ba zan takura ba saboda zuwansu abinda nakeyi na sakewa a gida na ba zan fasa ba. Yace kema kinsan zuwan yaran nan ba zai takura ki ba , su ba masu surutu bane ko shiga sabgar da bata su ba , wannan hutu da suka zo sada zumunci ne, kuma ina son yarana su san 'ya'yan 'yan uwa na, ba don na takuraki bane. Tace Gaskiyya to su zauna BQ, don wlh zuwansu ba zai hanani jin rayuwata ba, yadda muke bajewa muyi rayuwarmu a falon nan ba abinda zai rage balle in fasa. Ya girgiza kansa yace Haba safeena ai duk abinda zamuyi ma shi bedroom kafin su tafi, kin san ana barin Halas dan kunya, kwana nawa zasu tafi? Tace oho! Kaji takurawar ko? Gaskiyya ba zan iya ba su sauka a BQ kawai. Yace Gaskiyya bazan iya sauke en uwana a Bq ba ba, yadda nake jin su suhail suma haka nake jinsu, ba zan iya ba. 30)Ficewarsa yayi a tym din, Yanxun ma da tace haka bai kuma bi ta kanta ba, yace su dauko kayansu su shigar wancan dakin ya nuna musu da dakin da take saukar kanninta, idan su zo mata hutu. Shi abin ma mamaki yaka bashi Yadda bata son 'yan Uwansa su zo su rabe shi amma ita duk hutun duniya ko hakan nan ma ta kan cika gidan da danginta, kuma bai taba cewa komai ba, ko yace suna takura masu, amma ita zuwan en uwansa yin hutu na farko kenan gidan ta nuna sam bata so, shi da gidansa abin ikonsa. Ya dubesu yace sai kuyi sallah ku kwanta ku huta gajiya idan ma zakuyi wanka ga bayi nan. Sannan duk abinda kuke so a gidan nan gashi nan a kicin ko store babu shamaki kuyi anfani da shi, anjima da yamma sai ku shirya muje shopping ku siyo en abubuwan da zaku bukata, na sanku mata da kwalliyya kila zaku bukaci kayan kwaliyya. Misalin karfe hudu da rabi sai kuyi min magana, yauwa ga abinci can bisa dinning, kuje kuci idan kunyi sallah. Sukace to mungode. Har ya juya ya fita sai ya dawo yace, Yauwa na manta matar gidan nan tana son girma, saboda haka ku dinga bata girmnata a duk tym da ya dace. Ku dauketa tamkar ni, ku girmamata, ke Aneesa na lura kin lakanci Halinta shi ya sa kuke dasawa. Ita ma tana fadin kina girmamata ga shi kina son yaranta, to ke ma sadiya sai ki bi yadda Aneesa ke mata don a zauna lfy, don bana son kanannan zance, idan ka riga kasan halin mutum to sai ka ci maganin zama da shi, kun gane? Suka gyada kai, ya fice ya barsu. Sannan sadiyya ta dubi Aneesa ta sauke ajiyar hrt tace, kinji matsalar matar nan ko? Shi ya sa ba babu mai sha'awar zuwa gidansu, ni banda Uncle da kansa ne ya matsa muzo hutnan wlh da ban zo ba. Ita dai ji take tamkar idan aka rabar mata miji za'a kwance mata shi ne. Ko za araba ta da shi, ki duba ki gani ko zariya zaizo tana makale da shi, idan shi kadai ya zo ta dinga masa waya kenan. Ita kila gani takeyi tafi son shi akan son da Hajiya take masa. Haba mata fitananniya jarababbiya kawai. Aneesa tayi saurin toshe bakin sadiya tace ke! Ki iya bakinki wlh daga zuwanmu kada ki jawo mana jangwam ki dai ji abinda Uncle yace Fakat! 31) Da Yamma sukayi wanka suka shirya Ishaq ya dauke su a motarsa ya kaisu suka sayo abubuwan da suke so. Tym din da suka dawo a kicin suka iske safeena tana hada abincin dare bayan sun kai kayan dakinsu. Suka shigo kicin suka sameta sukayi mata sannu da aiki, sannan Aneesa tace aunty me zamu tayaki? Tace, no ku barshi girkin Captain ne bana bari wani yayi masa, amma ku na baku dama ko da yaushe zaku iya girka abinda kuke so, gobe tsohuwar da take tayani aiki zata dawo sai ku dinga tayata wasu abubuwan. Ita ke girkinsu ita da mai gadi da yaron da ke mana wanki, driver har su suhail a gunta suke cin abinci, nima idan ta dafa abinda nake so ina ci, amma captain nike masa girki. Sadiya ta dubi Aneesa a fakaice ta jinjina kai, Lallai ana ji da Uncle dinta. Tunda suka fahimci basu cikin abincin da takeyi sai suka kunna Gas suka dafa Indomie mai dadi. Bayan sallar isha gaba daya aka zauna a falon agidan don cin abinci. Su aneesa da sarakan kiriniya su Suhai ledar cin abinci suka shimfida bisa carpet din falon suka zauna sun cin nasu. Masu gidan kuma suna can bisa dinning. Can su Aneesa suka lalace da kallon gulma amma a fakaice. Suna kallon soyayyar da ma'auratan ke yi suna ba juna abinci abaki, ita kam safeena kusan kwance take jikin Ishaq shi kam jin kunyar su Aneesa yake shi ya sa ya zauna a kujera da ta ba su baya, Aneesa tayi wa Sadiya Rada, mun takura su Yaya. Sadiya muje mu kwanta, ta tabe baki, kinsan Allah babu inda zanje, idan sun matsu da yin luv din su koma daki, ki lura shi Uncle kunya yake ji amma ita wai gata baturiya. Sai wani kwanciya take ajikinsa, me zata nuna mana? Muma mun iya soyayyar fiye ma da ta ta, jira mukeyi ayi mana auran mu bude namu shafi Sadiya ta dubi Aneesa ta sauke ajiya hrt tace, wadannan yara en gata ne, don Allah dubi aljannar duniyar da aka shirya musu kamar ba gobe. Aneesa tace to meye anfanin kana da shi danka bai more ban yayi ma wasu ma balle yaransa, yadda yake ji da twins nan nasa gasu yara ne masu shiga ran mutane. Suka kwantar da yaran suka lullube su, sun juya zasu fita Suhail ya diro daga gadon ya biyo su, yana cewa Anty ni ba zan kwan anan dakin ba, gurinku zan kwana, momi bata kaimu dakinta. Ya kankame Aneesa, Hayaniyarsu ta tashi dan uwansa, shima yace ba zai kwana adakin ba. Ishaq yana ganin sun fito. Tare da yaran yayi dariya yace, haka sunki kwanciya? Aneesa tace har mun kwanatar da su suhail ya fara tashi, wai su dakinmu zasu kwana. Yace to Allah ya bamu alkhairi, amma ku kaisu suyi fitsari, idan sukayi ba su tashi, yawanci suhail ne ma ke tashi yayi cikin dare, saboda yana shan ruwa da yawa. Su Aneesa suka dubi safeena sukace aunty sai da safe. Tace Allah ya tashe mu lfy. Amma wadda ta kwanta da suhail zata sha naushi. Yadda yake sarkin boxing a farke a bacci ma haka yake. Duk sukayi dariya. Hutun su Aneesa a buja sunji dadinsa kwarai don yadda suke zaton safeena zata takura su batayi ba, ko da yake sun bi shawarar Ishaq girma suke bata harda na sayarwa. Ga yaranta da suke mata dawainyya da su kuma, ba sa zama mata a falo. Kamar sun san tayi korafin za su takura mata. A wata safiya Ishaq ya leko dakinsu suna bacci saboda idan sukayi sallar subahi ba sa tashi sai wajen 10am, tunda sun san babu abinda zasuyi, ya bubbuga kofar Aneesa ce ta bude ta sauka su sultan ne yake ranar asabar ne ba sch. Tana ganin Ishaq ta risina ta gaida shi, yace ina sadiya ne? Tace gata can tana bacci yace to ki taso ta ku hada mana break fast. Yau safeena bata da lfy. Tun dare da ciwon ciki bamuyi sleep ba, zamuje asibiti ne. Allah ya sauwake tace, bari in taso ta. Ya koma ita kuma taje ta tashi sadiya ta gaya mata. Kafin su shiga kicin din sai suka shiga har dakinta suka yi mata sannu, tana kudundune cikin bargo. 34) Ishaq ne gefenta a azaune, ya duka daidai face dinta yace, me kike so ayi miki brkfast, don ya kamata kici wani abu kafin muje asibitin? Tayi magana da kyar kuma ashagwabe, na gaya maka bana jin dadin abinci ba zan iya ci ba, gara ma ko ruwan tea ko kunun gyada. Ya dubi Aneesa yace ku dafa ruwan tea mai kayan kamshi, sannan da kunun gyada, ku kuna iya yin duk abinda kuke so. Tace, to yace wadannan en rigimar basu tashi ba, sadiya tace tunda suka tashi da asuba mukayi sallah basu tashi ba, yace yauwa gara kuyi ku gama kafin su tashi su hargitsa gidan. Lafiyyayen kunun gyada Aneesa tayi, suka zuba a flask, suka dafa tea wanda ya sha kayan kamshi da ganyen lifton din saudiya, suka zuba a flask sannan suka kai dakin Safeena. Suka Isketa zaune tayi wanka Ishaq yana shafa mata mai, yayi musu sannu da aiki, sannan suka fita. Da kansa ya soma zuba kunun gyadan yana bata tana shi. Har ta kusa shnayewa sai ta soma amai ba