← Book details Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 51

Sashe 27

Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

damuwa ce ke damunki, haka kurum akan da namiji zaki ja ma kanki ciwo. GRa driver ya kaisu asibitin ALMADINAH likita ya dubata sosai kamar yadda Hajiya ta bukata, akayi mata test babu komai tare da ita sai damuwa da rashin abincin har jininta wai yayi kasa abin da ba'aso. Sai da tasha ledar ruwa3 sannan suka dawo gida. Hajiya ta yi ta kiran no din Ishaq duka wayoyinsa a kulle suke dole ta hkr. Da daddare Aneesa na kwance a daki ita kadai sai ta soma gwada numbers dinsa ko zata samu, cikin ikon Allah sai ta sami layinsa na MTN, bugu daya taji an dauka amma ba'ayi magana ba, dama yawancin tym idan ta kirashi indai ta samu bai cika yin ba sai yaji ta gaji sai kawai yace. Kiyi hkr kin ji Aneesa zanzo ne ba da dadewa ba. Ko da yaushe idan tayi sa'a samunsa a waya to kalamansa kenan na ban hkr. Yauma ta dauka shine sai ta fara cewa Ya ishaq ya ayyuka? Munyi ta kiranka a waya duk a rufe dama Hajiya zata gaya maka bani da lfy ne har munke asibiti anyi min karin ruwa, wlh ina cikin damuwa da kewar rashinka. Me yasa sai da ka fara koyar dani yadda zan so ka na soma shakuwa da wasu al'amuranka sannan zaka tafi ka barni na tsayin tym? Don Allah ya Ishaq ka ce min wani abu ko naji sanyi araina plssss.... Ji tayi an kece da dariya irin dariyar nan ta rainin wayau sannan akace, ayya! Ba yayan naki bane, tauraruwarsa ce, ai damuwa yanzun kika soma shigar ta tunda har kinyi damarar zama da mijin wata, MIJIN ARO! 30) Wlh yanzun Ishaq ya fi karfinki yayi miki nisa ta yadda ganinsa zaiyi miki wuya. Ke da Hajiya kun ci amanata shi yasa na sha alwashin da sa muku bakin ciki a ruyuwarku, tun farko bansan ana son hada ki aure da miji na ba ne da ban taba barinki ki zo gidana ba, ki zauna ba kin gama yi min CID kin gama ganin sirrin yadda nake zama da mijina, kika yi ta yaudaraea kina son 'ya'ya na ashe son Inna kike min son cuta, shi ya sa zanyi miki ramuwar gayya, mijina da kika aura ba ki auri mijin da zakijin dadin rayuwarki ba, MIJIN ARO, ne da zan dinga ara miki shi kila bayan wata3 ko kuma shekara sau 2 zan yarda masa ya zo ya ganki, yanzu ma zan ara miki shi ya zo ya ganki cikin wannan satin, yini kadai zan ba ku shi, saboda naji kina cewar zumar da ya fara lasa miki ya tafi ya barki da kewa, to idan ya zo kada kisa ran lasar wata zumar, tawa ce ni kadai kin amince ko? Kashe wayar Aneesa tayi tare da zirarowar hawaye a kuncinta, haka Hajiya ta shigo ta sameta, ta dauki zafin zazzabin ya sakata hawaye, ta shiga lallashinta. Da aneesa ta zo taki gaya wa Hajiya yadda sukayi da safeena saboda kada Hajiya tace kiran mijinta take, to amma don ta san cewa bayin Ishaq din bane rashin zuwansa da sa hannun matarsa duk da dai duk dangi ma sun san da hakan. Ta zayyane wa Hajiya duk abinda Safeena ta gaya mata kalilan ta rage, saboda wanu maganganun masu nauyin fadi ne. Hajiya tace muna sauraron zuwan nasa idan ta ba shi, mu kuma idan ya zo ai ba zamu barshi haka ba, addu'a ce dai ba fashi dare da rana, Allah ai baya bacci, yana sane da kaidinta, kuma zaiyi mana maganinta Insha Allahu. Kwana 1-2-3 har dai 7 suna sa idanun ganin Ishaq a hanya amma shiru. Katsam ranar asabar bayan sallar Azhar Ishaq ya iso gida, don ko da Hajiya taji numfashin isowar mota irin tasa bata kawo shi ba ne ta dauka baki tayi, kawai sai ga su Imrana da she baki har kunne suna ta shigowa da kaya, Imrana yace Hajiya yallabai ne yau a garin, Allah ya amshi addu'armu wlh jiya kwana nayi ina addu'a akan rashin zuwansa ashe yau yana hanya. 31) Ita kawai Hamdala ga Allah a zuciyarta tayi. Yana shigiwaa falon ya zo gabanta ya sisina abin da bata saba gani a fuskarsa ba shi ta gani, hawaye sirara wani na bin wani. Tausayinsa ya kamata ya danyi rama a fuskarsa tayi duhu, tabbas ko acan da kana ganinsa kasaan hankalinsa ba kwance yake ba da ganinsa. Tace tashi ka zauna bari ladidi ta kawo maka abinci da abinsa ni bana fushi da kai kada ka damu kanka. Yace ina aneesa fa? Tace tana daki kwana 2 bata da lfy munje asibiti har karin ruwa akayi mata. Yace subhannallahi mai ya sameta? Tace to gata nan dai sun ce damuwa ce da rashin cin abinci, sun bata magunguna yau ta tashi jikin da sauki sosai. Ya mike ahanzarce yanufi dakin Hajiyan, a kwance ya ganta bisa carpet tayi matshi da dan karamin filo tana bacci. Ya zo ya zauna gabanta ya kai fuskarsa dai2 tata ya sumbaci labbanta, ya kura mata ido tayi fari tas fuskarta sawai ba kwalliya. Nufashin mutum taji yana sauka a fuskarta shiyasa tayi saurin bude idanu sai kawai taga wanda bata zata ba, tayi saurin tashi zaune tana masa kallon mamaki, yace nine Ishaq Yayanki, Hajiya tace baki da lfy ya jikin naki? Tace jiki alhmdlh na sami sauaki ya hanya? Yace lfy lau bakuyi fushi dani ba ko? Kiyi hkr nima ba'a son raina bane na dade banzo ba. Tace ba komai muna murna da zuwanka, ya su suhail da mamansu? Kunya ca yaji ta kamashi na yadda a kullum ita Aneesa mai kaunar iyalansa ce, amma ita safeena a can yanzu bata da abin aibatawa irin Aneesa tunda ta aurar mata miji. Yace suna nan lfy ba su san na taho ba an kaisu sch tym din da nataho, da sunyi rikici su ma zasuzo. Sun danyi shi can yace, zaki iya zuwa kicin ki kawo mini abu mai sanyi? Idan akwai fura ki taho min da ita, tace bari in duba nan firij din akwai lemuka, furar ma akwai. MIJIN ARO 2***4 32) Duk ta aje masa agabansa ruwa da furar kawai ya sha, yana janta da hira, har akayi la"asar sannan ya barta ya zo ya tafi mosque. Da yadawo nan falon hajiya ya zauna sukayi ta hira da Hajiyar, aneesa na gefe idan ya kama tasa baki ta kansa, abin mamaki nan da nan har ta saki ranta ta soma walwala, hakan yasa hajiya taji dadi sosai. Da dare ma nan falon ya zauna yaci abinci tuwon semo miyar danyar kubewa da ayayo, ta sha man shanu. Aneesa na gefe tana kallon Ishaq yana ta zira loma tamkar ya shekra rabon da yaci tuwo, ko kuma dadin miyar ne ya dinga jansa, don ita da kanta ta zauna ta shirya masa miyar har kusan shadaya na dare yana falon suna hira. Hajiya na barin falon ya dubi Aneesa yace ni zanje na kwanta ko zamuje ki tayani kwanane? Ta make kafada tace, ni babu ruwana ka tashi ka tafi. Yace nasan dai Hajiya kike jin kunya tunda yanzu gidan ba mutane bari ta fito in tambayeta nasan ba zata hana mata taya mijinta kwana ba. Ta marairaice fuska tace, don Allah ka rufa min asiri ni kaga har yanzu gaban iyayena nake basu kaini gidanka ba, kayi hkr har tym da suka kai maka ni, ba zaka ga ina maka musu ba. Ya mike yana murmushi yace matsoraciya na dai kusa raba ki da Hajiya, don na lura ita nan nan da ke bata son a kwantali fatarki ko kadan. Ita dai lallabashi ta dinga yi har ya samu yayi sallama da Hajiya ya tafi makwancinsa don tasan yana iya cewa Hajiya zata je ta yashi kwana, tsoronta kada hajiya ta bata umarni, ita kuma kunya takeji, duk abinda zai faru tsakaninsu bata son faruwarsa nan gidan tafi son su yi komai agidansu cike da rufin asiri. Washegari da safe ya shigo sanye da riga wando na barci, bayan sun gaisa da Hajiya sai yake gaya mata zuwana na safe yana son yake kd. Har zai fita falon sai ya dawo yace, Hajiya tunda naga yarki taji sauki o zaki bani aronta tayi min rakiya? Tace kai da matarka ya za'ayi in hana tayi maka rakiya, sai idan zaka kwana ne bazan bari ba, wannan sai ta tare a gidanka. Yace ba kwana zanyi ba yau zan dawo Insha Allah. 33) Da kyar Hajiya ta lallaba Aneesa ta shirya saboda nadewa tayi tace bata jin dadin jikinta, don ita kam, bata son kabewarsu ta gaji, abubuwa yake koyar da ita wanda yake tafiya yake barinta da wahalarsa, gara kawai su dinga nesa da juna har zuwa ranar da Allah zai sa su kasance inuwa daya. Tuni yayi sallama da hajiya yana mota yana zaman jiranta, ita kuma sai nawa takeyi tana jan aji. Hon yadinga dannawa sannan ta dauki gyale ja ta yafa shine kalar manyan flowers din jikin fara super wax din da ta saka. Sai takalmi fari da jaka er karama fara tasa, ta sallami Hajiya ta ratso falon sai wani ni'imataccen kamshi take yi, tayiwa ladidi dake goge2 sallama, ladidi sakin baki tayi tabi Aneesa da kallon don ya karshen haduwa ta hade tamkar wata aljana haka tayi kyau. Ladidi ta jinjina kai a ranta tace, kai wadannan yara wlh kun dace da juna wato kyau na dukan kyau. Allah ya kawo mana en jikoki kyawawa a gidan nan musha goyo, har hajiya nasan sai ta goya jikokinku duk da tana ciwon kafa. Ita kadai take zancenta a zuci. Ishaq ya hango Aneesa ta fito ya daki sitiyarin motarsa yace, ya salam! Tsarki ya tabbata ga sarkin hallita da ya tsara kyanki da surarki. Shin yarinyar nan kuwa tasa kuwa komanta mai kyau ne? Fuskarta, tafiyarta, kallonta, maganarta, surarta, dariyarta, fushinta kai komai nata mai kyau ne, komai tayi burge shi takeyi da duk bai lura da hakan ba sai yanzun. Tana bude murfin motar tayi sallama, sannan ta shiga ta zauna, kamshin turarenta ya gauraye masa hanci, nan da na jikinsa ya mace ya soma duburburcewa yayi saurin kano hanunta, yace Aneesa! Ya kira sunanta can kasan
Chapter 27 · 0% Book details