Sashe 44
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shi ya shigo yce mata, “Hajiya hala yallabanmu bai da lafiya ne, naga ya shiga mota gashi can ya fi minti talatin bai tada ta ya tafi ba.” Tace, “Lafiya kalau yake.” Aneesa kam tausayinsa ne taji ya kamata. Ya dade sannan ya tada motar ya tafi. ************* ************************ ************************* Tun daga ranar da Ishaq ya tafi dama Aneesa t agama shan maganinta, kuma sun koma gurin malam Balarabe yace asirin jikinta duk sun karye da izinin Allah, sai addu’o’I day a bata a rubuce yace ta je ta lamince yinsu In Shaa Allahu zata gagri Sihiri duk wani mutum da aljani,kullum ta tashi da safe sa tayi wannan addu’ar bayan ta idar da Sallah Subuhi, haka da dare bayan Sallar Isha’i. Ga addu’ar (ALLAHUMMA ANTA RABBI LA’ILAHA ILLA ANTA ALAIHI TAWAKKALTU, WA ANTA RABBUL ARSHIL AZEEM, MAASHA ALLAHU KANA WAMA LAM YASHAA LAM YAKUN LA’HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAHIL ALIYYUL AZEEM. A’ALAMU ANNA LAHA ALA KULLI SHAI’IN KADIR, WA ANNA LAHA KAD A HADA BI KULLI SHA’IN ILMA. ALLAHUMMA INNI A’UZU BIKA MIN SHARRI NAFSI WAMIN KULLI SHARRI DABATIN AKHIZU BI NASIYATIHA WA INNA, WA INNA RABBI ALAA SIRADIN MUSTAKIM.) In Shaa Allahu duk wanda yayi 110) wannan addu’ar babu wani abu mummuna da zai same shi, shi da iyalansa har ma da dukiyarsa inji Annabi (S.A.W). Bayan addu’o’in da take yi kuma Hajiya tad au damarar gyara diyarta don kullum, * Da dare sai tayi mata farfesu ko na kifi ko na naman rago, mai wadataccen room, ko ta soya mata kwai wanda yaji manyan tumatir da manyan farar albasa, a soya shi sama-sama shi bai soyu ba kuma ba danye ba, haka take tasata sai ta cinye, yana kara ni’ima sosai. * Da rana kuma ta fi yin mata abu mai ruwa-ruwa balle ansan zage- zagi da shan fate ko shima hadin da take mata mai saukar da ni’ima ne, a cikin fasuten a sa tantakwashi a yanyanka tumatir da albasa da cucumber isasshe a sa ganye ya ji kabewa, wannan hadin yana karawa mace ni’ima sosai, ko ta gasa mata nama gashi mai ruwa-ruwa, a sa albasa a gashin kada su gasu idan an juye a kwano a yanke tumatir a ci, shima yana da kyau, ko ta dafa mata wake ya dahu lugub sai a sa maid a dafaffen kwai a yanka tumatir da cucumber a ci haka, shima yana da kyau. * Da safe ga hadin da take bata, tayi hadin aya da gyadar da aka soya suma sama-sama, sai jikakken waken suya a jika shi tare da alkama da danyar shinkafa, a bare dabino a zuba, (za’a iya sa kowanne gwangwani bibbiyu) sai a kai a nuka a tace idan ya kwanta kullum da safe shi take dama mata shat a kan zuba mata madarar ruwa ta peak da zuma madadin suga. Da dare kuma lipton take dafa mata da kaninfari, ba’a cika kaninfari ana son rowan lipton din yayi dan kauri, da duminshi za’a fasa kwai a bayan an zuba rowan lipton din rabin dan karamin kofi a zuba danyen kwai daya sai a sa zuma cokali biyu karami ko babban cokali daya sai a kada shi o Ko Kauna? MIJIN ARO 2***12 111) sosai har sai ya tsinke sai tasha, wannan hadin cikin mintuna kalilan mace zata ji alamuma a jikinta, don ko zama tayi zata ji damshi, shi yasa an fi shan wannan hadin da yamma sosai ko dare. * Sai kuma wanda na fada a littafina na girki (SIRRIN GIRKE-GIRKE) Za’a sami rowan cikin kwakwa ne a juye a kofi sai a zuba zuma cokali uku a juya sannan ayi wannan addu’ar da izinin Allah ni’ima zata dawwama a jikin mace mara yankewa, (BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. ALAHUMMA YA MUKALLABIL KULUBBI KABLAL KALBI ALA (ISHAQ) BI MUHIBBATTI DAU’DAN WA KARHAN SIRRAN WA JAHRAN, LAILAN WA NAHARAN HATTA LAA YA SABBIT ALAA SAA’ATI YA ALLAH, YA ALLAH, YA ALLAH.) Sau ukku ko biyar. To In Shaa Allah ni’ima zata sauka sannan soyayyar mace ba zata taba gushe wa a zuciyar mijinta ba, zakiyi zaman dirshan a zuciyarsa fiye da tunaninki, idan aka zo wajen da na ambaci Ishaq sunan mijinki zaki san a kawo misali da Ishaq ne kawai. * Sannan wannan kuma kankana zaki samu mai ja da zaki,sai ki yanke saman kiyi mata murfi, ta nan zaki caccaka cikin kankanar yayi ruwa sai ki zuba zuma cokali ukku ko 5, sai a karanta wannan addu’ar (ni’imal maula wa ni’imal nasir) sau 313, idan kin gama addu’ar sai ki rufe kankanar da murfin sai ta kwana sannan ki zuba kankanar a kofi ki shanye, to In Shaa Allahu idan kina yin wannan hadin lokaci zuwa lokaci ba yadda za’ayi mijinki ya jiki ba yadda yake so ba, ku duba littafi na na (SIRRIN GIRKE-GIRKE). Juice na musamman a shafi 36,38,40, dama wasu juice din iri-iri masu kara ni’ima ne. 112) Tun kafin dawowar Ishaq Aneesa ta soma tausayin kanta saboda tasan ta tsumu, saboda ance mace mai yawan ni'ima idan tana tunanin mikinta zataji kawai babu abinda take so sai kasancewa da shi, to ita kam haka take ji, abin ne zata ji ya namata yawo a cikin jinin jikinta, idan kuwa yayi mata waya da daddare to kwana takeyi cikin kewarsa tana juye juye, ita tana ganinma Hajiya ta dagota. Ranar juma'a da yamma Ishaq ya iso zaria, Aneesa tamkar ba ita bace mai tsananin kewarsa din nan sai ta shiga wani ja masa aji konai zatayi masa amma a yangace tamakar bata yi farin ciki da zuwansa, alhalin zuciyarta kal take har tafi auduga fari. Tym din da yazo Hajiya bata nan an tafi kaita asibitin ABU na shika zata dubo mijin kawarta da yayi hatsarin mota, gidan daga aneesa sai ladidi. Ishaq juice din guava da lemon tsami da abarba da aka hada su kawai ya sha, yanayi yana kallon Aneesa da ta wani takure a agefe kamar taga dodo, kunyar ladidi na gidan kawai yakeyi da ya kwanta a cinyar matarsa ya dan rage gajiyarsa. Can dai ya dubeta yace, duba min saman wardrobe din Hajiya ki bani kwalbar zuma in sha. Ta mike cike da yauki da yanga ta wuce ya bi bayanta da kallo, har wata er kiba ta kara yi tayi kyau abinta kirjinta nan da mazaunanta ma'abita cika da yalwa tamkar zasu yi magana, gashi tasa kaya da suka kamata suka fidda shape dinta, ga kamshi tana zubawa, ya hadiye miyau kuut! Tare da lumshe idanunsa, tamkar an tsikare shi sai ya tashi yabi bayanta tana duba kwalbar zuma ya taho da sanda ya sakle hannunsa ya rike kutirinta ya makaleta a kirjinsa ya tura bakinsa wuyanta yana sinsinarta, nan da nan ta sona dauke wuta tayi magana da kyar pls Ya Ishaq kayi hkr nan da dakin Hajiya ne, so kake ta dawo ta ganmu? Yace zanso ta ganmu tunda har yau kila bata yarda ina tsananin bukata diyarta ba, to kinga idan ta gamun ra'ayal ainun zatayi gaggawar bani ke mu tafi, in kuna ba haka ba in tasa ta gaba ina mata kuka kila taji tausayina ta bani ke. tace nifa ban yarda da wannan rawar jikin da kosawr naka ba ni da banj da dandanon dadi dan Allah ko na koma amfanin me zan maka matarka ai ta isa ta gamsar da kai ya sake kwakubeta yace ni ban fadi haka ba dan Allah ki dena wannan zancen bana so...tace ko baka fada ba ai ka nuna mun tunda ka hadamun zuma da zamzam da kayan fruits in da bansan amfaninsu ba ai yanzu na sani tunda da ka bani har yoyo na dinga yi kai kuma ka hau murna zaka zo ka kwashi gara...yace aneesa na roke ki bar wannan zancen ina rokon alfarmar ki shafe abinda ya faru baya cikin zuciyarki nayi miki alkawarin in kika koma gidana zaki ga canji abinda ya faru a baya ba zai.maimatu ba da yardar Allah....ta banbare daga jikinsa tace naji na yarda Allah ya tabbatar da alheri muje falo bana son hajia tazo ta iske mu.anan...yace wai dan Allah ni va mijinkine ba da ake mun jurilla a kanki sai kaf kaf hajia take dake kaman zan gutsiri wani sassa na jikinki yadda ta bani ke gudarki ko mun shekara cikin daki haka zata ganki a gudarki to mene abun damuwa...tace duk munsan da haka ni dai muje.......kwana 2 da ishaq yai a zaria cikin zullumi da dar dar yake dan baiji hajia tai masa maganar komawar aneesa ba kuma bai ga tana wani shirye shiryen komawa va shi kuma yana tsoron yai magana ya ballo liki sai ya zubawa sarautar Allah idanu ba bai san hajia a sirrance take shirin komawar sirikarta ba komai ta kammala nata shi na tfy jiransa kawai take su tafi amma sai ta gara shi kadan yadda gobe ba zai kuma mata laigin da zaisa su taho gida ba ranar lahadi yayi wanka ya shirya yasa ubansu ghanilla shada kalar ruwan zuma sai maiko da sheki take ga kamshin turare na tashi tunda ya shigo dakin hajia aneesa kallo daya tai masa ta dauke ido saboda wani abu da ya tsirga mata dangane da mijin nata. dan idan ta cigaba da kallonsa zai ganota sun gaisa da haj ita ma ta gaishe shi sannan tacigaba da shiryawa hajia kayanta a wardrobe ya dubi haj a raunane yace haj yau nake son komawa amma dan Allah kimun alfarmar na tafi da aneesa yara na can na ta kewarta kullum sai sunyi kuka tace meyasa baka zo da su sun ganta ba aneesa ba yau zata komaba kana iya zuwa dasu wani satin su ganta ya sake marairai cewa yace haj fa nima rashinta yana sani kewa a gidan dan Allah kimun afwa bazan sake cutar diyarki ba balle na bari a cutar da ita.........tace ai na riga naji tubanka kuma na yafe amma bazan baka yata ba dan bangama shiryata ba kuma bazan laminta akuma wulakantaat ba nan gaba..yace ni ko baki shirya mata komai ba ki bani ita haka na miki alkawarin zama da ita da zucia daya tsakani da Allah ba cuta ba cutarwa...tace shikenan tashi ka tafi sai zuwa wani satin...ya tallabe goshinsa sai ga hawaye na zirara yana faman girgiza