Sashe 8
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ji ba gani, duk ya bi ya rude, su Aneesa ma jin aman da takeyi yasa suka shiga dakin sunayi mata sannu, sai da la lafa mata sannan ya dauketa ta cak ya shiga bayi da ita iya sake mata wanka. Aneesa da sadiya suka tsabtace wurin. Suna fitowa daga bayin ya taimaka mata ta sa kaya sannan suka nufi asibiti. Abinda likita ya gaya musu bayan yayi mata gwaje2 bai yi mata dadi ba, har mamaki ta dinga yi wai, za ace tana dauke da ciki a halin tanayi allurar hana daukan ciki duk 2mnth. Likitan Ibra ne kuma musulmi ya dubeta yace ikon Allah kenan. Ya nuna muku mutum bai isa ya hana shi yin ikonsa ba, saboda haka sai ku barwa Allah lamarinsa, kiyi fatan Allah ya baki lfy. Ta dubi Ishaq wanda bata tantance a wane yanayi yake ne don fuskarsa ba yabo ba fallasa ita anata hasashenma, tana iya cewa murna ce. HAUSA Novels BOOK MIJIN ARO 1**7 35) Ta hana shi magana don kuwa Allah yayi mai son yara ne. Tun tym din da ta sami cikin su suhail tamkar ya maida ta cikinsa haka yakeji. Balle tym din da akayi scanning akace en 2 ne duk boys. Sai ya ninka kulawar da yake mata da ko yaya ta yi mosti sai yayi mata sannu da tace uhum zai ce menene ko me kike so? Haka da aka haife su sun sha gata iri2. Ta dube shi tace, Captain yanzun meye abinyi? Yace meye ko abinyi illa mu godewa Allah da kyautar da yayi mana. Ta gintse fuska gaskiyya ba zan iya wannan wahalar laulayin ba. Ga shi na irin na su Suhail ne tym din babu wuyar da ban sha ba. Su 2 ina kwanciya asibiti duka2 shekarunsu 3 ne fa, ina laifin ma su sami shekara 5 zuwa 6. Ni kam gaskiyya ba zan juri wahaka ba gara tun wuri musan abinyi. Ya daure face tamkar ba taba dariya ba. Ba yace me kike nufi? In zubda gudan jinina yabi kwararo? Sam ba zai yiwu ba. Haihuwa da kika ce ba zaki sake ba sai su Suhail sun shekara 5. Kika ce zakiyi plannin wannan kin matsa mini ne na uarda da yake Allah ba ayi masa wayo ko dabara kuma ba ayi masa dole kinga gashi baki cika shekarun da kike so ba ya baki cikin. Maganar cire shi kam babu ita ba da yawuna ba. Kuma ko da wasa kada kiyi gangancin cire mini ciki wlh zan dauki mummunan mataki a kan hakan. Likitan ya shiga bashi baki. Pls captain be a man, kada kayi fushi kasan halin mata su tunaninsu karami ne. Ka bari kuje gida sai ka lallasheta. Kowa zuciyarsa a kuba suka dawo. Safeena kam tun asali ma bata so sukayi haihuwar fari ba da wuri ba, saboda bata son hayaniyar yara, sai gashi Allah ya hada da en 2, har cewa tayi daga kansu ta gama haihuwa, shi kuma yace haihuwa yanzu ya fara bayan su wasu en biyun na nan zata kara tace. Ba dai ita ba sai dai ya auro wata tayi ta haifa masa yaran, sai yace ai kuwa dai auro duk sai ta hada da su sultan ta rike duk zai bata kyautar su. Sai cewa tayi wlh babu wata er iskar da zata shigo mata gida..... 36) Tace wlh babu wata er iska nace da zaka auro ta rike mini yara, dama niyyar aurenka kake yi shi ya sa zaka fake da son 'ya'ya tunda ni nace 2 sun isheni to ka auro matan duniyan nan wlh nafi karfinsu. Daga wasa sai ta maida zancen fada, saboda tsananin kishi dole ya fice ya bar mata gidan. Magungunan da likitan ya basu kin shansu tayi shi yasa aranar ciwo yayi mata dirar mikiya ga hayaniyar yara, suka zo suka dameta, ai kuwa haushin dadyn su sai ta huce akansu, yana falo yaji ihunsu, yayi sauri ya shiga dakin ya kamo hannunsu yana tambyar menen? Suhail ya nunata yace, mom ce ta yi mana bulala wai mu fita a dakinta. Suje duk inda za su amma bazai yiyu ina ji da kaina su zo su dameni ba, da wanne zanji? Ya fice da su yana cewa, ai ba su suka kar zoman ba ratayar ma ba abasu ba, ba zaki sake ganin su ba. Ya sami su Aneesa a kicin yace, aneesa gasu nan kada ku barsu su shiga gurin mamansu, suna damunta, ko me suke so kuyi musu, komansu yana dakinsu. Kwanan safeena uku bata zuwa ko'ina saboda tana karatu a university din Abuja, aranar wata kawarta tazo dubata, tym din ita da aneesa na dakin baccinta tana tayata gyaran dakin. Ta bar Aneesa a dakin ta fito falo gurin bakuwarta. Da jin hirar su kasan aminan juna ne. Safeena ta shiga zayyana mata cewa ciki gareta, kuma ita wlh so take ta cire shi don ba zata iya wahalar laulayi ba, ga karatu ga su Suhail sannan nan da en watanni ace ta haihu. Kawar dariya tayi tace, ai hkr zakiyi ki barshi tunda mai abin na son abinsa, kina dai ji yace zai dauki mummunan mataki idan kika cire masa ciki. Ke a tunaninki wane mataki zai dauka? Iyaka dai yayi fadansa idan ya gama ya koma fushi daga nan ba zai kai ko ina ba zai saulo, dan nasan hushinsa ba ya kai ko ina duk iya laifin da nayi masa. Kawar mai suna Aina'u tace, tace kinsan fa ya taba ce miki idan ke ba kya son yaran shi yana so kuma zai auro wata tayi ta haifa masa, ba kya ganin zai iya auri watan? 37) Dariya Safeena tayi tace, aure! Ai ina jin Ishaq shi da aure a duniya dai ya gama shi sai da ko a lahira, don idan yace zai aure nima zan dau mataki, mummunan mataki akan haka, zan yi adawa da auren babba ma kuwa, yara kam bani da ra'ayin tara su, kamar akuya, dole ya hkr da tsari na. Aina'u ta murmusa tace. In kuma Allah ya rubuta masa 'ya'ya da yawa ya zakiyi? Kinga dole kiyi hkr ki zazzage masa adadin su. In kuma baki so wata ta zo ta amshe ki. Ta tabe baki tace, kin fa san yadda bana son kishiya, ko sunanta bana son ji. Ni fa ko wata naga za ayiwa kishiya jin zafi nakeyi, ina jin ma na fi ta jin kishin abin. Balle ace ni kuma, kinsan Allah da ya kawo min wata gidan nan amatsayin kishiya gara ya aje macen banza a waje (kuji banza mtsssw) wannan bata dameni ba. Akan kishi kuma a gidana. In ma rabon yaran ne can ahaifa masa su awaje, da dai akawon gida. Kai! Ina ba zai yiwu ba ma, ai gara in mutu da in ga wata mace Captain ya kawo a matsayin kishiya. Kinsan Allah da shi da ni da ita zan iya halaka mu. Gara mu mutu gabada a huta don ba ma zan yarda in mutu ni kadai in barsu su ci gaba soyayya ba gara a yi mutuwar kasko. Ke aina"u kin ma san yadda nake son Captain kuwa? Ni fa ina jin ko uwar sa ba zata fini sonsa ba, ita dai ta haifamini shi, shi ya sa ma idan naga tana wani nan-nan da shi har haushi nake ji, sai in ga kamar zata raba mu ne, Aina'u tayi ajiyar hrt tace, safeena kenan lamarinki sai ke. Ni dai shawarata ki bar cikin nan baki san irin albarkar da yake tattare da shi ba. Aneesa na ckin dakin baccin safeena tayi zuru tana jin wannan zance mai kama da shirin film. Ita kam duk yadda take tunanin safeena ashe ta wuce nan, lallai duk wadda Allah ya hada kishi tare da ita ta shiga3. Ko da yake ma Ishaq baya da ra'ayin kara aure don basu taba jin ya furta ba. Tana dakin har kawar ta tafi safeena ta zo ta suka cigaba da gyaran dakin. Ita a tunanin safeena Aneesa bata jiyo hirarsu ba, kuma ko da ta ji ba abu ne da ya shefta ba, tunda ta san Aneesa babu ruwanta da abinda bai shafeta ba. 38) Ranar litinin Hajiya tayiwa Ishaq waya cewa Mamansu Aneesa ta haihu, amma yaron bai zo da rai ba. Sai dai lafiyarta lau. Da yake ma hajiya na gidansu Aneesa ne sai ta ba maman wayar suka gaisa da Ishaw yayi mata sannu da jiki. Da ya dawo gida da yamma ne ya kira Aneesa da sadiya yake gaya nusu. Aneesa duk sai ta rude ta soma sharar kwalla wai ita gobe gida zata tafi. Yace bayan na gaya miki maman lfiyarta lau, munyi ma magana da ita, baki yarda ba kenan? Tace ni so nake in ganta shi ya sa, yace zaki ganta amma ba gobe ba, saboda nine zan maida ki gida. Ina son zuwa nima amma sai ranar asabar, saboda gabadaya wannan satin ina da tafiye2 kuma ba ma kasar nan bane. Ki bari idan natafi gobe sai friday zan dawo sai mu tafi. Ba don san ran Aneesa ba ta hkr. Tunda babu yadda zatayi$ Ranar da zasu tafi kayayyaki sosai Ishaq din ya saya musu na kashin kansu, don a tafiye2 da yayi naa jigilar fasinja kasashe, acan ma ya siyo masu tsarabar abayoyi da takalma da jakunkuna masu kyau. Don har mama da Hajiya ya sayo masu takal wasu en india masu kyau. Ita ma safeena tayi masu dinkuna irin nasu na en gayu en jami"a don tare ma ta dauke su a motarta suka je gurin tailor ya gansu ya babbance awonsu, saboda sadiya tafi Aneesa jiki, ita Aneesa falen2 ce ajiki, kirjinta ne ke da cika da hips dinta. Suna hanyar dawowa Aneesa tace, Aunty naji kince siket za'ayi mana kala3, duka ne dubu biyar? Tace, a'a ko wani set ne dubu biyar, mu dinki a abuja akwai kyau, amma da tsada. Aneesa tace aunty mu a zariya ba zai wuce dubu daya daya ba, gashi telolinmu sun iya dinki sosai.. Babu wani babbanci dana abujan. Ko zamu amso ne mu bada a can zarian? Tace ku barshi kawai, kinsan mu nan Abuja akwai tsadar rauyuwa komai na abuja mai tsada ne. Shi yasa