Sashe 10
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Allah ya kyauta. Sai Hanne tace, bari in koma gida dama na leko ne in ga jikin naki na dauka har yanzu kina kwance ne, ashe kin mike na dole kina bautar girki, ita da 'ya'yanta sun fice abinsu tunda sunga kin juri wahala ko ba girkinki ba dole kiyi, idan kina son zaman gidansu. Gwiwa ba kwari Hanne ta fita, tunda sam ba sami yadda take so ba, duk yadda ta dawo tsegumin Fatima da 'ya'yanta amarya Basira bai shiga kunnenta ba, amma duk da haka ta sha alwashin yau da gobe sai tayi nasara. Hakan ne kuwa ta kasance, don kuwa yawan shigiwan da Hanne takeyi a boye da wanda 'ya'yanta keyi sun wa Basira hudubar tsiya, ya soma tasiri a zuciyarta, saboda yanzu ta kai ga ranar da ba garkinta ba, bata taya Fatima ko tsinke balle idan Fatima tana uzurin fita, cewa tayi ba zatayi ba, duk mai girkin idan zai fita yayi abinsa kafin ya fita, kuma dole mutum ya dawo da wuri ya dora na dare, amma ita Basira daga baya Hanne ta zuga ta akan idan tana da girki anguwa ta kamata kada ma ta tsaya bata tym dinta wajen yi musu girki, tayi tafiyarta dole Fatiman tayi ko don cikinta dana yaranta, in dan gudar diyarta ne ta dinga tafiya da abarta, hakan kuwa akayi, ita dai Mamansu Aneesa ba tace komai ba idanu ta kawo ta zuba ma Basira tunda ta san zugata akeyi. Ga kara da take yawan kaiwa Abbansu Aneesa tace Fatima tayi mata abu kaza ba ya bincike sai ya hau kai ya zauna ya dinga fada, idan kuwa su Aneesa ne ranar sai jikinsu ya gaya musu, aysha ce kawai bata kai kararta saboda ta lura ita er gaban goshin ubance, kuma kota kai kararta ba ya daukar mataki, shi ya sa ta hkr Hanne tace ta daina, ta taya shi som Aysha zasu fi daidaitawa. Ranar wata monday su Aneesa sun dawo sch kenan ko abinci ba su ci ba, Basira ta fito ta dubi aneesa tace, Garin tuwonmu ya kare ga masara can a buhun bagco ki dauka ki kai mini sirfe da nika. 46) Aneesa tace, ina Iliya almajiri fa? Tunda safe da kin bashi da yanzun anyi nikan, tace banda dama baa uwar iyayi, ke kadai nake jira ki dawo ki kai mini, shi ai ba bawan gidanku bane da komai za'a ce sai shi. Kamar tace ga Aysha nan ai itace kasa da ita, sai dai tayi shiru saboda ganin Mama ta fito ranta a bace ta dubi Aneesa, tace ke karama! Basira sa'arki ce zaki fada ta fada? Ko ko shi Iliyan bawanki ne, to maza kiyi sallah ki ci abinci kije ki kai bana son rainin arziki. Allah ya sa Aneesa ma tayi sallah shi yasa tana tube kayan ta ta kewaya bayi ta wanke jikinta ta gyara kanta sannan ta fito ta danci abinci kadan, sai ta dauki ba buhun tana fitowa zauren gidansu suka yi kicibis da sagir ya dubeta, ya dubi buhun hannunta yace, Aneesa ina zuwa haka ne daga dawowarku sch? Tace wlh an aike ni ne, daga ina haka yace makaranta, na sauka anan dan kawai in ganki inji sanyi gashi kuma fita zakiyi. Tace, to ba gani ka ganni ba, ai kaji sanyin ko? Yace sosai ma, amma kuma ai ba ganinki kadai zanyi ba, hira nazo yi. Tace, sai ka jirani in dawo ai ba zan dade ba. Ya leka buhun hannunta ya ga tsabar masara yace, ba dai kace mai kai nika ba? Yace Haba haba, wlh kin wuce kaiwa tunda kina da kanne, kuma kuna da almajirai a gidan nan ni bani in kai. Amma gaskiyya ba zan yada kije bin layin nika ba. Yana kici-kicin amsar buhun ita kuma ta hana shi suna haka sai ga daya daga cikin yaran Hanne zai wuce cikin gida, ya tsaya yace k. Sagir ina wuni? Yace lfy lau, zo nan ina zaka? Ba ko ina, yauwa ta amshi buhun hannun yayarka kaje ka kai mata nika da sirfe yanzun nan ka dawo ina jiranka anan. Ya amsa jiki na rawa sagir ya ciro naira dari a aljihunsa ya mika masa ta fi, ita dai Aneesa tana tsaye tana kallon ikon Allah, ita kam tasan in baya ga 'ya'yan Hanne na tson sagir babu yadda za'ayi salisu ya kai nikan nan, ko da kuwa uwarsa ce ta aike shi, sai ta bashi lada yake zuwa, in ma bai gama ba ko ta bashi ladan ta bishi da lallashi ba zai je ba, idan kuma ya amsa to yana fita zai aiko yara da aiken ya gudu abinsa, idan abin da za ayi anfani da shi gurin girki ne, har sai wani ya siyo ta hirka bai dawo gidan ba don sangarta, to ana gama abincin zata sa aje anemo shi, wai ya zo ya ci abinci, ko ita da kanta ta dauka gyale ta tafi nemansa. 47) Suna nan a zauren suna hirarsu ta masoya, su Haulata suka fito za su fita. Yayi daidai da dawowar Salisu daga kai nika, agabn idonsu ya mikawa Aneesa nikan sannan ya ba sagir sauran chanjin. Suka gaida kawunsu suka fita, ba su dade ba sai ga su sun dawo. Aneesa na ganinsu ta san tsugudidi ya dawo da su, tym din da suka fito za su sake fita suke ce mamanmu tace in ka gama ka shiga zata baka sako can gida. Ya daure fuska yace, daman kun dawo ne ku gaya mata na zo gidan ban shiga ba gurinta ba? Ku dai ba kwa rabo da tsegumi, Haula tace mu bamu gaya mata ba dama tana neman salisu ne, daya shiga yanzun shine yace ba yawo yaje ba, kainme ka aike shi idan karyane ta tambayemu. Shine ta atambayemu, muka ce eh zaka zo kana zure. Ya gayara fuskarsa yace, to naji kun kyauta, shima salisun daga yawonsa ya dawo na aikeshi, shine zai fake da cewa ni na aike shi, ita kan Aneesa ta san wannan kai mata nika da salisu yayi sai ya janyo jidali tsakaninta da Hanne har da mamansu. Bayan sun fita ta dubi sagir tace, bari inje in kai nikan cikin gida, kaima kaje gurin kiran da aka maka. Ai kuwa yana shiga yayarsa tayi kicin2 dai rai tace, meye dalilin da za a aiki Aneesa dan ita shaffafiya da mai ce zaka amsa ka ba dana don shi bawa ne, ita kuma tafi karfin a aiketa dole ita ga budurwa, in banda kinibibi ina kanneta da ba a ba su ba sai nawa yaran. To wlh ahir dinka kada ka kuma yi mini haka, in hutu kake nema mata ai da kaine ya ya kamata ka zo ka dinga zuwa mata aiken, tunda ka zama sullutu. Yayi murmushi da yake shi mai barkwanci ne, kuma ba shi da surin fushi, yace ni ba don zakice na zama karai ba ai, da na dawo gidan nan ko don in dinga tayata ayyukan da naga take sha kullum. Taja Uban tsaki, au abin ma wasa ka maida shi? Tunda ka maisheni abokiyar wasanka, to ni zan gamu da Aneesan gobe idan aka aiketa ba zata kai ba, yarana ba, sanin halin yayarsa tasa yasa ake barkwancinsa gefe ya soma magana ta fahimta da fadin gaskiyya da ya ba mata akan zumuncinsu da ta riga ta tarwatsa. 48) Allah ya hanne a bar maganar wasa, Aneesa ko ba soyayya tsakanina da ita ai er uwar salisu ce, ta jini ko ni kawunsa bance yaje mata aike ba zai iya zuwa mata ba, idan tace yace gaskiyya in ma da wani abu tsakaninsu da iyaye bai kamata ku dinga saka 'ya'yanku a ciki ba, saboda zumuncinsu kuke ruguzawa tunda idan ki ba zu kuyi ba tsakaninku, su dole ne suyi zumunci da juna tunda alakar jini ta hada su, kuma alakar jini wlh ta tafi gaban wasa, xumunci dole suyi shi tunda Allah ne da kansa yayi maganar zumunci dole suyi shi tunda Allah ne da kansa yayi maganar zumunci kuma duk wanda baiyi shi a duniya ba, dole zai yi shi alahira, to ba gara ayi shi tun a duniya ba cikin dadin rai da kaunar juna. Tunda rayuwar duniyar 'yar kadan ce ta lahira tafi ta duniya tsayi nesa ba akusa ba, itace mara iyaka. Tayi murmushin da bai kai ciki ba, tace sagir kenan, in dai wa'azinka akansu Aneesa ne na riga na saba jinsa da dai akan wani abu ne kila zan dauka, amma banda wadancan gara ma ka kyayeni, tun kafin namu zumunci ya baci ni da kai. Yayi murmushi a ransa yace, in dai zumunci ne da ke ai da tuntuni ya lalace da ace ina daka ta taki, in banda ni cikin en uwa wa yake jurar halinki, har vewa ake yi ba ni da zuciya inji en dakinmu. Yace ai ni da ke zumuncimu babu mai raba shi, tunda ko alahira sai munyi shi, wannan zumuncin yaran nan nake son ki kule musu shi gam2 tinda dai kece babba a gidan nan. Inbanda Goggo ita kam ba a sata alissafi, tunda mara lfy ce amma Allah yanxun kece uwar gidan nan. Ko shawara za ayi dole a ce kece kan gaba. Ta tabe baki, naji nasiharka yaya sagir, ka tashi ka tafi. Yayi dariya ya kwanta bisa doguwar kujerarta yace, ni ba yanzun zan tafi ba sai naci tuwon dare. 49). Tsarin zaman gidansu Aneesa yanzu ya chanza kwata2, babu wani kwanciyar hankali, saboda Basira yau gobe yasa ta dauki zugar Hanne dadin munafuncinma, yaran hanne yanxun dakin Basira suke wuni en matan. Duk ranar girkinta ba yin abinci yadda za'a koshi, in ma miya ce ta kara kana cin abinci to baka isa ta kara maka ba, sai dai ka ci gaya ko ka hkr da abincin, mama da ta lura da gayya Basira keyin hakan sai tana dafa musu wani idan basu koshi ba, nan ma Basira ta gaya ma maigidan, yace sam bai yadda akara yi masa girki 2 ba. Idan mutum bai koshi ba ya hkr, wai sharri ne kawai za ace a gidan sa ba adafa abincin isasshe. Sai mama tanayin miya ta ajiye idan basu koshi ba sai su siyo