← Book details Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 51

Sashe 18

Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da zasuyi yana neman sirri da nutsuwa. Ta dube shi ya nutsu agefen gadonta akasa bisa wani tum tum mai taushi tace, ba wani abu yasa nace ka zo ba illa ina neman alfarma da nake son kayi mini, kuma ina ganin babu wanda zai yi mini wannan alfarma inji sanyi a raina inji bana kokwanto sai kai, ina fatan zaka share min hawayena. Baki ya bude yana mamaki, Hajiyata yanzun don kina neman alfarmar wani abu a gurina har sai kinyi kokwanto, ai ni kin fice neman alfarma a gurina sai dai ki bani umarni take in bi umarnin indai ba ya sabi Allah bane, kada kiyi kokwanto a kaina, fadi ko menene kike so in dai bai fi karfin arzikina ba zaanyi miki. Ta gyara zama tace, ba wata alfarma nake nema cikin arzikinka ba, saboda ni babu abinda baka yi mini ba, kai dan halas ne na gasken gaske, Allah yayi maka albarka ya albarkaci zuri'arka ya biyaka da aljanna. Ta danyi shiru tana jinjina lamarin, shi kuma yayi shiru cike da ladabi, umarninta kawai yake jira ya cika idan kuma bukata ce yayi gaggawa biya mata ita, don kuwa ji yake ko da fansar ransa ne ta umarta zai iya badawa. 86) Can tace, kasan nayi maka waya dangane da maganar auren Aneesa ka riga kasan komai. Yace kwarai kuma zancenta aurenta na raina don kuwa har na fara shirye2 na jira kawai nake inji ansa takamaimain tym sai in sanar da ke tsarin da nayi, don bana son kowa ya wahalar da kansa daga ke har abbanta da sauran en uwa, nine zan dauki ragamar yin komai, a yadda nake kaunar Mama da zuri'arta wlh babu abinda bazanyi musu ba. Hajiya ta numfasa saboda zancen da zata dauko ba wannan bane, ya sha bambam da duk wani shiri da yake yi a auren na Aneesa, tace ai maganar shirye2 ma ka aje ta agafe saboda a halin yanzun an fasa auran Aneesan, Ya juyo anfasa? Me ya faru? Tace mu dai takamaimai bamu san me ya faru ba daga can ba, amma mahaifin yaron ya zo ya bada hkr yayi kalamai na fahimta, cewa dan uwansa ne ya ba shi diyarsa shi kuma babu yadda zaiyi, shiyasa ya umarci sagir din ya amsa. Idanun Ishaq suka yi ja, ransa ya baci yace, amma wannan wulakanci ne, yarinyar nan bata kula kowa sai dansa nima har ina gargadinta tunda shi take so, kada ta kuskura ta kula wasu tarkacen samari, ashe zai yaudareta ne, ni ban yarda an bashi wata ba dama can mayaudari ne, Hajiya tace kada ka ji zafin yaron nan, shi sam bashi da laifi, tunda har nan ya zo yayi mini gamsashen bayani, kuma na yarda da bayaninsa, kawai mu dauka ba matarsa bace, shi yasa hakan ta kasance, ni dai yanzun burina, Allah ya bata miji na gari wanda ma ya fishi. Yace Insha Allahu Aneesa zata sami miji mafiyinsa, akwai wani abokina dan zariyan nan da muka taba zuwa gidan nan da shi ya ganta, yayi ta damuna da zancenta sai na gaya masa ta tsaida miji, tunda hakan ta kasance zance masa ya zo su daidaita. 87) Hajiya tace, kabar maganar wani abokinka, dama ni tun asali bana son Aneesa tayi aure inda dangin miji zasu dinga tsagwamarta, to gaskiyya dama en uwansa ba wani son auren suke ba, musamman Hanne da kanneta, iyayensu ne ke so, shi ya sa da haka ta kasance ai banji ciwo sosai ba, shine yanzun nake son kayi mini alfarma a matsayina na mahaifiyaka wadda nasan na isa da kai, ka auri Aneesa don kai ne nake ganin zaka rike mani ita da zuciya daya. Ishaq ya dubi Hajiya duba na ya zanyi da wannan lamarin, yace ni in auri Aneesa Hajiy? Kina ganin ba zata shiga cikin matsala ba tsakaninta da Safeena, saboda safeena wayayya ce ta fita wayewa da wayau, sanna abin dubawa kuma safeena sam bata kaunar kishiya, ni kaina ina tunanin irin matsalar da zan fuskanta da ita duk ranar da nace zan kara aure, tunanai na ko da zan kara aure zan auro dai2 da ita ne wayayya ba wadda zata sha wahalarta ba, amma aneesa ba zata iya kishi da safeena ba. Hajiya ta girgiza kai tace, amma ka bani kunya tunda har kake tunanin ba zaka iya sarrafa matarka ba da gidanka, ina ce safeena karkashin ka take? Kaine zaka juyata ba ita bace zata juya ka ba, to ni mahaifiyarka nayi maka Umarnin auren Aneesa, wanda ina fatan alheri na kulla, don kuwa ina hangi wannan alherin tare da zamanku, idan kuma ba zaka iya ba saboda kada ran matarka ya baci tunda bata son kishiya sai in nema mata wani nagartaccen mijin cikin en uwana, wanda nasan ba za su watsa mini kasa a ido ba, za su share min hawayena. Ishaq yayi shiru yana jinjina irin wannan kauna da Hajiya ke wa Aneesa wanda har bata kaunar yarinayar ta shallake zuri'arta. Hakika yarinyar natsatsiya ce mai hkr da hankali ga shi son addinin ya ratsata kwarai mutum zai so ta zamo uwar 'ya'yansa don samun tarbiyya ta gari a gidansa. Shi kam! Yana kaunar yarinyar irin kaunar da zaiyiwa duk wanda jininsa ya gauraya da nasa, jin yarinyar yake tamkar Hajiyarsa ta haifeta, a matsayin autar Hajiya yake ganinta, sai dai bai taba jin ko so ko tunanin wai shi Ishaq zai auri Aneesa ba, illa dai wannan kaunar. 88) Ya dago idanunsa cike da danuwa ya dubi Hajiyarsa yace, Allah ya huci zuciyarki Hajiya, ni idan ban share miki hawayenki ba, waye zai share miki? Wlh ko da ba Aneesa da nake jinta araina ba, zan iya aurar duk yarinyar da kika yi mini umarnin in aura balle Aneesa da ta rayu tare da mu, tarbiyarmu ke gareta, komanta irin namu ne haihuwarta ne kawai bakiyi ba, amma kinfi kowa sannin cikinta da bayanta. Ki kwantar da hankalinki, na anshi auren er lelenki, ina fatan zaki taya mu da addu'a Allah ya tabbatar da alheri a tsakaninmu, ya bamu hkr zama da juna tunda kinsan babu wata soyayya a tsakaninmu. Murmushi Hajiya tayi irin murmushi nan mai bayyanar da farin ciki, ta dubi Ishaq tace, ni kam ka gama min komai a duniyar nan tunda ka amince zaka dasa daga inda na tsaya, wajen tallafawa rayuwar Aneesa, kwarai bana son rayuwarta tayi nisa da cikin zuri'ata. A kullum addu'a ta kenan, ashe Allah ya ga zuciyata da alherin da ke cikinta shi ya sa ya canza lamarin ayren nan har gashi ya dawo cikin zuri'ata. Zanyi muku addu ba zan gushe ba har karshen rayuwata, tunda kun ginu akan kaunar juna to na tabbata kauanarku zata rikide ta zamo soyayya da izinin Allah, aneesa yarinya ce mai shekarun da ba su haura sha takwas ba, kai kuwa ka haura shekaru talatin, kai namiji ne mai ilimi mai wayau fiye nata, kaine zaka koya mata yadda zata soka ba sai na gaya maka ba, kasan kuma a irin sigar ladabi da biyayyar da zata shiga gidanka da shi da kyakkyawar tarbiyar da take da shi, da su zata samo soyayyarka a gareka. Allah yayi muku albarka ya albarkaci wannan auren da za'ayi yasa alheri muka kulla. Dukkansu shiru sukayi na kusan mintuna 2, kowa da inda zuciyarsa ta nufa, ya dubi Hajiya yace, kin sanar da Aneesa wannan maganar? Tace ban sanar da ko ba daga ni sai kai sai Allah dake tare da mu kawai ne muka sani, yanzun nake son in kirata a gabanka in gaya mata. 89) Yayi saurin duban Hajiya yace, ki barta sai na tafi kinsan akwai nauyin juna a tsakaninmu. Tace ai na so ne tun yanzun ku fara fahimtar juna, amma tunda ka ce haka shikenan. Sai ka saya mata waya ku dinga yin magana. Yace zanyi ma Ali waya sai kawo mata su kyau ta zabi wadda take so. Tace, yauwa kafin ka wuce kaje ka sami babanka Alh. Sani da dan uwansa kayi musu bayani, sai su kai gaisuwa gidansu Aneesa. Ka turo da isassun kudin gaishuwar in ma sun bukaci sadaki, sai a bada tunda bai fi wata 2 ne zata kare karatun ba, da ta gama ne yace zai aurar da ita, kaga shikenan ayi a ahuta. Ishaq yace yanzun dai suje su yi maganar neman auren, komai zai iya biyo baya daga baya, ke naga duk kin matsu ayi abin da gaggawa ne. Tace eh dole in damu ayi saboda ubanta hutsumin mutum ne, yadda idan bata kawo masa miji ba, zai daura mata aure da wanda rabonsa ya rantse ai kaga ba zanyi yayi mata auren wulakanci ba, yarinyar da gatanta da komai a dauketa a aurar ga ko wane irin miji, in dai ina raye ba zan bari duk da ba iko na bace. A falo ya iske Aneesa zaune tana cin abinci, ladidi na kicin tana goge2. Aneesa na ganinsa tace Ya Ishaq ba dai har zaka tafi ba? Yace zanje uguwan juma ne yanzu zan dawo in wuce. Tace yaya ni yau banji kace girkin da nayi maka yayi dadi ba, kada ka sa Hajiya da Ladidi su yi mini dariya. Yace yanzun nan dama zance girkin ki yayi dadi, ya ma fi na kullum ga tukwicinki nan, Ina ladidi ta amshi na na taya ki da tayi. Ya kwalawa ladidi kira ta fito daga kicin din tana amsawa, ya mika mata en dubu guda 2 tayi ta godiya ta koma bakin aikinta. Aneesa kuma dubu biyar ya bata, ta amsa tayi godiya ya fice. Asalain Family house na su yaje a unguwan Juma, gidan mahaifin Alhajinsa wanda a yanzu kannen mahaifinsa ke zama da iyalensu. 90) A zauren gidan ya same su su duka biyun bisa manyan tabarme dake shimfide a zauren. Yayi sallama ya shiga Zauren Alh. Sani ya dube shi yana murmushi yace, a'a kaga direban jirgi ne da ranan nan, sannu da zuwa. Suka gaiggaisa suma dattijan kawari ne irin Alhajinsa shi ya sa ko da mahaifinsu ya rasu sune suka maye masa gurbinsa. Saboda dattakonsa da rikon zumuncinsu, ba irin zumuncin yanzu ba da ba'a abu domin Allah sai don ganin idon iyayenka idan suna raye, idan basa raye sai ayi wa
Chapter 18 · 0% Book details