← Book details Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 51

Sashe 32

Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bukata a gurin wata diya mace, an shiga an fita an mantar da shi hakkin wata na kansa banda na safeena, shi gani yake tunda bata rasa ci da sha ba muhalli mai kyau to mai zai takurata. Itama Aneesa sai take ganin bata da wata matsala tunda zata ci duk abinda taga dama, ta sha duk abinda ranta ke so, matsalat dai kenan ace miji bai bata hakkin aure ba, wanda ita a wautarta hakan ma tafi nono fari tunda dai bai nemeta ba hanashi kanta balle tashiga fushin Ubangiji. Duk tyn da hajiya tayo mata waya ta tambayeta yaya yanayin zaman babu matsala ko? Sai ta nuna wa Hajiya bata da matsala suna zaune lfy. To idan ma tace da matsala zata iya gayawa hajiya ne ai abu ne mai nauyi ta gaya mata har ya Ishaq bai taba leko dakinta ba. Itama bata taba leka nasa ba. Ita dai Hajiya jin Aneesa kawai take yi tasan ba son ta fadi wani abu ne, da zai tada hankali, amma a yadda ta san safeena tasan halinta zaiyi wuya ta barsu yi zaman aure irin yadda takeyi. Amma koma menen zata turi wani yazo ya gane mata irin zaman da 'yar tata takeyi, balle gashi tafi kusan wata guda kenan shima Ishaq baije zarian ba, ko dayke ko ya zo bazata ji komi abakinsa ba kamar yadda bata ji daga bakin aneesa ba. Yau tun wayewar garin Aneesa ta tashi da matsanancin ciwon kai irin nagefe din nan, wanda masana sun nuna irin wannan ciwon kan alamomi ne na karancin magnesium. Tana nan kwance har mutan gidan duk suka fice gurin aiki bata iya tashi ta fita sun gaisa ba, shi kuma maigidan baya tunanin tunda bai ganta ta fito gaishe shi ba, bari ya duba yaga lfy take, wanka ma kansa kasa tashi tayi, har sai wajen zuwan Baba mai aiki ita kanta baban tayi mamaki da bataga Aneesa ta fito ba kamar yadda ta saba, har taga aikace2 tayi girkin rana ta gama sai tayi sallama tare da bubbuga dakin Aneesa, Allah yasa tana falonta bisa kujera, ta nade cikin bargo saboda zazzabin da takeji, ga sanyi na kadata. Ta amsa sallamar baba sannan tayi mata izinin shigowa, ta karaso kusa da kujerar da Aneesa ke kwance suka gaisa tace, lfy kike ko? Gani nayi yau baki fito ba yadda kika saba shi yasa nace bari in duba ki in gani, aneesa ta dafe kanta tace, wlh ciwon kai yau na tashi da zazzabi shi yasa ban iya fitowa ba, tace Allah sarki sannu Allah ya sauwake, ai tunda naji ki shiru nasan kila ba lfy ba. To ko in kawo miki abinci ne? Kila ma baki samu kin karya ba, don naga abin karyawanki bisa table. Tace ban fita ba amma na sha ruwan tea da na dafa tym din da nasha magani da safe, tace bari in kawo miki abincin. Taje ta kawo mata tuwon shinkafa miyar wake, da kyar ta matsa mata ta danci kadan sannan ta bar dakin. A ranta tana tausayawa wannan yarinyar tunda Allah ya hada ta kishi da irinsu safeena, ga ta dai ba wata babbar mace ba, amma kisisinarta da kissarta yafi na iyayen mata, ita dai a yadda take ganin zaman da sukeyi kamar an zaluntar yarinyar nan anayi mata gashin kuma aboye, to me zata ce sai dai ta taya yarinyar da addu'a, akan Allah ya kareta ya fissheta ga kisisinar wannan matar. Koda masu gidan suka dawo Baba bata gaya musu halin rashin lfyar Aneesa ba saboda a tunaninta kila ai sun sani. Tunda ciwon tun safe ne dashi ta waye gari. Har dare Aneesa bata fito ba Ishaq abin ya dame shi, har ya aje sallar magriba da Ishai ya dawo bai ga ta fito ba tayi masa sannu da dawowa ba kamar yadda ta saba, gashi dama tun safe haka ya fita bai ganta ba. Sun zauna cin abin idanunsa na kan koridon hanyar zuwa dakinta, duk ya kosa ya ga ta fito, da yaji shiru sai ya dubi safeena yace, wai yarinyar can lfy take kuwa yau? Naga ban ganta ba safe ba, yanzun ma gashi tunda na dawo banji motsinta ba? Cike da kissa da kisisina tace, lah ai mun hadu da safe kasan yau ka rigani fita, yanzun ma dakaje sallaha ta fito, kasan ta da son zaman daki gata da bacci kamar mai yaron ciki, ko dai ka bata tsarava ne daga zuwanta? Kallon mamaki kawai ya bita da shi, wato abin har zolaya ya koma tunda ta san ta tsare gaba ta tsare baya, ta hana su rawar gaban hantsi shine zata ce haka, kawai sai ya kada kai yace, au haka zakice? Bayan kin tsare gaba kin tsare baya, kema kinsan ke kadaice mai iyawa dani, ita kam ba zata iya ba da sauranta. Tayi dariyar cin nasara, kwarai ta san duka mace ke iyawa da in garman namiji irin mijinta ba, ta sanma ko ta barshi da ita ba zata iya masa balle ga yadda ta lura da yarinyar wata lange2 gata dagani akwaita da limbo. Ya dubi Suhail yace kai suhail ke ka duba antyn me takeyi a daki, kace ta zo. Yaron ya ruga da gudu sabida kko ba komai yanzun zai sami damar tashinta daga baccin da ya shiga sau ba adadi yaga tanayi, don tunda suka dawo yake shiga sai ya isketa a kwance idanunta a rufe, bai san duk shigiwar da yake tana jinsa ba ta son ya dameta da surutunsa shi yasa taki bude idonta. 58)Ya na shiga ya ganta yadda ya barta ya haye gadon ya leka fuskarta sai yaga idanunta a rufe amma ga hawaye yana fita yayi sauri bai fadi sakon daddynsa ba ya koma da gudu ya rike hannun Ihsaq yace, daddy zo muje kaga Auntyn kuka takeyi, jikinta kuma taba akwai zafi. Ishaq ya dubi safeena yace to ko bata da lfy ne? Tace ina zan sani tunda muna cikin gidan bata gayawa kowa ba, bari inje in dubata. Ta mike tanufi dakin, shima sai ya ga ba zai iya hkr ba dole yaje yaga halin da yarinyar mutane take ciki, karo na farko kenan da kafarsa zata taka dakin matar tasa, anya kuwa akwai adalci a zaman nasu, haka zuciyarsa ta dinga kissima masa har ya shiga dakin ya iske babi kowa a falon sai ya zarce dakin baccin Aneesa. Aneesa na kwance daga ita sai shimi ta daura zani, kanta babu dan kwali kalba ne tayi wa kanta en kanana sun kwanta bisa filon da tada kanta. Safeena ta tsaya tana tambayarta abinda ke damunta, ta dafe kai tace ciwon kai ne da zazzabi. Ya matsa daf da gadon yace ya akayi kina ciwo ba zaki gayawa kowa ba. Ki kwanta a daki haka akeyi? Ita dai shiru tayi saboda ta san da ya damu da ita shine mutum na farko da fara sanin tabata da lfy, amma tunda ya bagarar da ita bata ganasa ba dole bane yasan lafiyarta da rashinta. Ji tayi hawaye sun zubo mata saboda tausayin kanta, shin meye laifinta don bata gaya musu bata lfy ba? A ina ta gansu balle ta gaya musu? Yace to meye abin kuka, ko jikin ke damunki sosai ne muje asibiti? Ita dai girgiza kai tayi ta nuna alamun a'a. Safeena kuwa takaici ya isjeta yau Allah ya hada mijinta da shagwababbiyar yarinya, lallai idan ta sakewa yarinyar nan ko da irin wannan shagwabar zata iya samun shiga zuciyar mijinta don shi Allah yayi shi mai son shwagbar ne, shi ya sa yake son Yasmin cikin yaransa saboda shagwabarta, to yau ga wadda ta zata maye hali irin na Yasmin. 59) Ya dubi safeena yace taimaka mata tasa kaya muje likita ya dubata. Ta dubi Aneesa tace tashi bari in dubo miki kaya ki sa. Ta juya gurin akwatunan Aneesan zata dauko mata kaya, ita kuma Aneesa ta mike kenan jiri ya kwasheta ta tafi luu! Zata fadi Ishaq yayi saurin tarota ta fadi bisa kirjinsa, zanin jikinta ya silale kasa tai saura daga shimin jikinta sai wani wando skin tie dan gajera. Ya dubi cinyoyinta da kallo zuwa kirjinta nan da nan matsananciyar sha'awarta ya kamashi, sai ya sake mannata a kirjinsa, ji yayi wani abu na masa yawo a ilahirin jikinsa. Gaskiyya in bayan safeena na dakin nan da yarage radadin abinda ya taso mata. Karaf! Safeena ta juyo da kaya a hanninta sai tayi ganin da ya fadar mata gaba mijinta rungume da yarinyar da rainawa wayau, hada idanunsa yasa ya shiga taitayinsa yayi saurin zaunara da Aneesa agefen gadon yana cewa tana mikewa jiri ya debeta saura kadan ta fadi na tare ta,safeena tace ai gara da ka tareta, ko in barku kasa mata kayan ne? Ya girgiza kai no ki bata tasa ai zata iya, bari inje mota ki taimaka mata idan ta gama sai ki kawota mota mu tafi. Tace to ko zamu tafi tare ne, naga jikin bata da karfi? Yace haba ki kyaleta zata iya, kuma wa zamu barwa yaran gida ba kowa? Tace sai mu tafi da su, yace ya zamuje asibiti da yara su ba ciwo suke ba haka kawai su kwasuo kwayoyin cuta acan, ki bar min yarana a gida muma asibitin dole zamuje. Duk inda ta bullo sai ya kawo mata hujja, ita kuma kishi yadda za'ayi ta bar mijinta ya fita da wata mace su biyu takeji, balle wannan shagwabbiyar yarinyar manne masa a jiki zata dinga yi, kuma ya sami abinda yake so biye mata zai tayi tunda. Yasan matarsa ce, ta so ne ta bisu don idan yana ganin. Idanunta ba zai dinga biye wa yarinyar ba. A mota ta same shi har ya juya kan motar ta nufi bayan motar zata bude ita nufinta Aneesa ta zauna abayan sai yace, ki bude mata nan, tace wai nufi na sai ta kwanta naga tafi son kwanciyar, yace a'a kyaleta ta dinga zaman yawan kwanciya ma yana karaea mutum ciwo. Babu yadda zata iya dole ya budewa Aneesa gaban mota suka shiga suka tafi. 60) Rabin hankalin Ishaw yana kan aneesa rabi kuma tukin da yakeyi, ya lalubo hannunta dake gefensa ya rintse a nasa yace, aneesa wai me
Chapter 32 · 0% Book details