← Book details Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 51

Sashe 30

Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kira sikin sa,a ta same shi,ya soma gaida hajiyan tare da ban hkr sa ya saba a duk lkcn da wani ya kira shi a waya,ta shaida masa gasu nan bisa hanya,bai nuna damuwa ba yace Allah ya kawosu lfy.sha daya da kusan rabi na safe suka isa gidan ishaq a abuja,duk ga motocin ishaq din nan guda biyu a gida.itama safeena ga tata motar nan tabbacin kowa na gida kenan 44/sha daya da kusan rabi na safe suka isa gidan ishaq a abuja. Ga motocin ishaq din nan guda biyu agida itama safeena ga tata motar nan tabbacin kowa na gida kenan suna hutun karshen mako. Sunyi ta sallama a falo gidan tsit! Tamkar babu jama,a acikinsa,sai daga can ishaq ne ya fito faga dakinsa yana ganinsu ya soma musu maraba yayi saurin amsar jakar hannun hajiya yana cewa hajiyata sannunku ashe da wuri zaku iso,ku karaso falo su, suhail na ganin aneesa da hajiya ya makalkale su yana tsallen murna,su yusra duk da ba wani sabo sukayi da hajiya ba,suma sun haye jikinta.babu wani bacin rai a tattare da safeena tamkar ba ita bace mai tsananin kishin nan,haka ta dinga yin nan nan da hajiya da aneesa ta kawo musu flas babba na ruwan zafi da gwangwanayen kayan tea dasy bread,ta wuce kicin ta soya musu kwai da ayaba (plantain) duk ta jere a gaban su tace su karya kafin ta dora abincin rana.shi kam!ishaq sai dari-dari yakeyi ya kasa sakin jikinsa da hajiya tunda ya san shi mai babban laifi ne.da yamma bayan sallar la,asar ishaq ya shigo dakin bakin da aka sauki hajiya yace mata zai fita anguwa, tace yazo zatayi mgn dashi ya nemi guri ya zauna.tace to dama matarka ce gata nan na kawo maka ita,don rashin adalcin naka yayi yawa,in ma ajiyarta ka bar mini to ga ajiyarka nan na kawo maka,ina son yanzun ka nuna mini dakinta don ni gobe zan koma za,a zo a gyara mata dakin agobe insha allahu,yace nan yayi mata?kinga falo ne da dakin bacci daya sai bayi,sai tayi manaji kafin in gama gini dana fara wancan babban guri ne kowa da bangarenta,hajiya ta juya ta dudduba dakin yayi ba makusa ta dube shi.shike nan yayi,gobe za,a taho da kayanta za,a gayara mata dakin,ga dai yata nan amana kada kaci amanarta kuma kada ka bari aci amanarta,ka san dai yarinyar nan amana ce a hannuna,to gata nan nima na damkata a hannunka amana,in tayi maka ba dai dai ba ka kirata cikin lumana kai da ita ka gyara mata.don idan mutum yayi laifi ba,ayi masa fada cikin jama,a tozarci ne, .:............. .....:.................mijin aro 45/gara a kira shi a kebance ayi masa fada yafi saurin jin faadan ya karbi nasihar da akayi masa, abu na karshe ko dayake na fada kari zanyi,kayi adalci,ka kwatanta adalci a tsakanainsu, ka tsayar da adalci a gidanka idan kayi haka zakaa sami nasara da kwanccciyar hankali tsakaninka da iyalanka:Allah yayi muku albarka ya shirya iyali ya dai daita tsakaninku;yasa ku gama lfy 46/dama su hanne har an kishingide babu niyyar komawa zaria a yau.duk wani abu da safeena zatayi ya nuna tana adawa da auren nan sam bata yishi ba sbd irin yadda ta amshi hajiya da yayyin mijinta har mada iyayen aneesa,duk sai abin yabasu mamaki musamman ma su yaya hannatu da lamarin nata ya daure musu kai.washe gari dazasu tafi aneesa kuka ta dingayi, tun da garin Allah ya waye.ita gani take yi tamkar idan sun tafi zata rabu da walwala da halin farin ciki datake ciki ne domin ita kanta lamarin safeena ya daure maya kai so sai,ita dai fatanta Allah yasa wannan karban datayi musu hannu bibbiyu ya dore bana ganin ido tayi ba. Sha tara na arziki ishaq yayi musu.don kyautar manyan kudi yayiwa yan uwansa,su hanne da basira dubu goma goma yaba kowaccen su da tirmin atamfa super england,ya basu shadda mai tsada a ledarta yadi goma da dubu ashirin yace akaiwa abban aneesa,su babban sasa ma kowa da nasa abin alkhairin.su hanne sai washe baki akeyi anga abin arziki,amma fa a zuciyarta cewa takeyi inama su haula ne Allah ya kawo a wannan matsayin ba aneesa ba,gani takeyi sune sukafi aneesa cancanta da wannan kyakkyawan matsayin.. Tunda suka tafi aneesa tana daki tayi kukanta ya isheta,ta hkr ta tashi ta shiga bayin dakinta tayo alwala tazo tayi sallar azahar,ta dade bisa sallaya tana rokon Allah yabasu zaman lfy da fahimtar junansu,bacci ya fara dibarta bisa abin sallar ne taji an fara kwankwasa kofar dakinta tar da yin sallama,ta amsa sallamar sannan tayi saurin fitowa falonta tana yiwa mai sallamar izinin shigowa mai aikin gidan ce yar dattijuwa wadda dama sun san juna ita da neesa tunda tana zuwa gidan. 47/kuloli ne ta jero a tire ta risina ta ajiye bata dago daga durkuson ba tace ga abincinki nan,in kuma kina bukatar wani abun sai kiyi mini mgn in dafa miki.aneesa tace,don Allah baba tashi daga durkuson nan,ai nice diyarki ni yakamata in girmamaki in durkusa miki,to ballema Allah yace SHI KADAI NE ZAMU SURKUSAWA WAJEN YIMASA BAUTA KADA MU KAMANTA SHI DA KOWA.sannu da aiki,kome kika dafa zanci ba sai kin sake wani ba,kuma daga yanzun idan kin gama abincin ki barshi a kicin din zanzo in dauko ba damuwa. Baba mai aiki ta mike tana cewa Allah yayi miki albarka,yan nan ya baku zaman lfy ya kawo zuri,a mai albarka,ta juya ta tafi,ba wata tsohuwa bace amma dai ta manyanta yadda aneesa ke ganin tilas ne ta girmamata a matsayinta na babba sa,ar mahaifiyarta,ta bude abinci kuskus ne da miyar kayan lambu,ta debi dan kadan taci sannan ta sake gyara dakin fes.tasa turaren daki sannan ta haye doguwar kujerar falonta ta kwanta. Bata farka ba sai wajen hudu da kwata tayi saurin shiga bayi tayo alwala tayi sallah ta dan gyara fuskarta sannan ta fito ta nufi kicin anan ne taji motsikila safeena ne suke hada abincin dare.tayi sallama kicin din suka amsa sannan ta shiga tana cewa sannunku da aiki aunty.ai da kin aiko in tayaku, wlh bacci ne ya daukeni sai yanzun na tashi nayi sallah abin mamaki ta dauka zataga sakin fuska kamar yadda tayi musu ta amshe su hannu bibbiyu sai taga sabanin haka,ta dan yatsina fuska tace ki barshi kawai mun kammala,kije ki kwanta abinki aike yanzun sai hutu,ina amaryaa ina shiga kicin.aneesa tace haba aunty wace ni da hutu,ai shiga kicin ya kamani dole sunyi shr dukkansu sai aneesa take tambayar ina yaran ne taji gidan shr,safeena ta amsa,an kaisu islamiyya.da dai ta lura safeena ba zata barta ta tayasu aikin ba sai ta koma daki,ta soma harhada kayan kallonta,ta dauko kaset din walimar aurensu tasa a DVD ta kwanta tana kallo don ya rage mata kewar gida 48.data idar da sallar magrib bata fita ba tana dakinta amma tana jiyo hayaniyar yaran tare da babansu tabbacin ya dawo kenan,da taga shr nai leko inda take ba sai ta dan yafa karamin gyale ta fito falon don tayi masa sannu da dawowa,a kishingide a kafet din tsakiyar dfalon ta ganshi su yasmin sun dane jikinsa yana ta wasa dasu,ta karasa ta dauki yusra tace yan islamiyya ashe kun dawo tana dubanshi tace yaya ishaq sannu da dawowa,yace yauwa ya kuke?ta rufe fuskarta tana dariya yace sunyo mini waya sun isa gida lfy,sun kira ki? Tace eh yaya hannatu ta kira ni, hajiya ma ta kirani.safeena na fitowa ta wani kalle su ta wuce dinning abinta,nan da nan ishaq yq shiga taitayinsa, yar hirar daya soma da amaryarsa ya kawo karshenta yayi dif. Tamkar an dauke wuta,da aneesa ta lura da haka sai ta dauki yusra ta kama hannun yasmin suka wuce dakinta.a falo suka zauna da yaran suna ta mata surutu,sai taji tamkar ma abar mata yaran don sun isa su debe mata kewar komai.can suhail ya kwankwasa kofa yana sallama tace shigo, aneesa tayi tayi yaran su tafi cin abinci suka ki wai su sun koshi,data matsa musu wai su a kawo musu nan. Su anan zasu kwana,sai da suka gata yafa gyale ta kama hannunsu tace suje tare sannan suka yarda,tana kawo su falon taga sun tafi sai ta dawo daki,tun da ba,a ce tazo cin abincin ba, ita garama haka bata son shiga tsakanin mata da miji tunda ta lura matarsa bata son ko da hira ne taga ya shiga tsakanin su,tsananin kishin fana nan.tea ta hada tasha tare da cake,tayi shafa,i da wuturi tayi addu,ointa na kwanciya ta kwanta abinta. 49/tunda ta tashi tayi sallar subhi bati addu,oi sannan tayi karatun qur,qni har sai da gari ya soma haske sannan ta kai karshen surar da take karantawa tayi addu,a sannan ta shige cikin bargo ta soma bacci. Bata farkaba sai wajen goma saura na safe ,bayi tayi saurin shiga dama ta kanna hiter bayin tayi wanka tazo ta shrya cikin atamfa mai ruwan kasa da manyan fulawa jajaye,sai ta yafa karamin gyale da a madadin dan kwali sbd yawancin bata daura dankwali in dai agida take sai dai ta gyara gashinta ta yafa karamin gyale,ta bi jikinta duk ta shafe shi da turarukan kamshi kawai ke tashi. Ta saka flat shoe. Ja sannan ta nufi falon gidan don ta gaida masu gida duk da dai bataji motsin kowa ba kicin ta fara biyawa ta iske baba har ta iso tana wanke wanke aneesa da fara,arta ta gaida baba sannan tace ,jama,ar gidan nan sun tashi kuwa? Tace ai gaba daya ba kowa gidan nan kin san yau ranar aiki ce iayaen sun tafi gurin aiki yaran kuma duk an kaisu makaranta,shr kawai aneesa tayi,shin ita dasu wa keda laifi? Ita da bacci takeyi bata san zasu gurin aiki ba,ai kamata yayi ko kowa bai nemeta ba ishaq yaje ya dubata yaga ya ta kwana a matsayinta ma bakuwar zuwa gidan,sannan duk baccin da takeyi ai ya kamata ya tasheta ya gaya mata zasu fita,amma sai suka kyaleta suka fita abinsu,to da ba baba mai aiki haka nan zasu fice su barta ita kadai acikin gidan tana aikin bacci. Baba tace ga abin karyawa can bisa wancan babban teburin,in kina son wani abu sai kiyi mgn in dafa miki yanzun.tace wanda suka bari ma ya isheni, ngd baba.ta juya ta koma ta hau teburin ta zauna
Chapter 30 · 0% Book details