Sashe 14
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ma sai a tym dine ake tuna su, dama haka ake so ko bayan baka a fadi alherinka, mama kam ta sami yabo daga bakin jama'a na kuda ita da na nesa. Hajiya ta tambayi en uwan mama da suka cika dakin inda Aneesa take, suka ce tana cikin dakin baccin maman akwance. Ta mike ta shigo dakin ta zauna gefen Aneesa itama sai tashi daga kwance suna kallon juna suka soma kuka, dole Hajiya itace mai karfin halin da ta dinga lallashin Aneesa tare da gaya mata maganganu masu sanyaya rai da karfafa zuciya. Da kika rasa Fatima ba wai kin rasa jin dadi da gata gaba daya bane, ni din nan insha Allah zan maye miki gurbinta, zan zame miki uwa da uba, duk wata damuwarki ki gayan min, insha Allah zan share miki hawayenka. 65 IS A BLANK PAGE 66) A falon Mama ta same shi, shi kadai ne a falon yana sanye da wani yadi mai dan karen kyau, kalarsa dark blue, shi ya sa ya fito da zallar kyan Ishaq da yake fari ne har yafi Aneesa haske, ko da yake kalar jikinsa na en hutu ne, luf luf kamar jikin mace haka yake, ga gashi nan en kanana kwance a jikinsa, gaskiyya Ishaq mai kyau ne ga tsafta koda yaushe tas2 zaka ganshi, kamar farar takarda, lallai dole matarsa tayi kishin abinda don ta san mijinta mai kyau ne, kuma irin mazan nan ne a tsaye masu shegen kwarjini a duk inda suka shiga, ita kanta tasan yana da farin jini don a tarihin soyayyarsu tayi gwagwar maya da en matansa da suke rububin sonsa, balle shi dama tun asali rayuwarsa dan baiwa ne ta bangaren karatunsa, a aviation har zuwa fita kasar turai da yayi karatu, zuwa aikinsa a Nnamdi Azikwe international airport a abuja. Tayi sallama ta shigo, ya amsa sallamarta sannan ya nuna mata kujerar da ke fuskantarshi yace ta zauna, kafin ta zauna sai ta tambayeshi Hajiya yace, yanxun ta shiga daki je ki gaisheta ki dawo. Taje ta gaida Hajiya sannan ta dawo gurinsa ta zauna ta gaishe shi tace, ina su suhail da mamansu? Yace yanzu drive ya kaita gidansu wata kawarta da sukayi karatu tare a jami'ar abuja, za su dameni na tarkata mata su ya hada mata da su da mai rainon su Yusra. Sun danyi shiru ya soma mata dangane da karatuna ta gaya masa komai, yace to akwai kudi zan dinga turowa ta account din Hajiya na hidamarku ke da kanneki, don bana son in kuna cikin matsa ko yaya take, duk sati hajiya zata dinga baku kudin da za kuyi anfani da su, larurar shc kuma komai ya taso kije ki gaya mata, bana son zurfin ciki irin naki, sannan wayar mama da take hannunki ki ba Abbanku, bana so ki rike waya, saboda ina son ki fito da sakamon sch ma kyau ta yadda ko da kinsa mi mijin mun aurar da ke zaki cigaba da karatun jami'a a gidansa, Hajiya ta taba gaya min akwai yaron da ke son auranki dan gida ne, ina fatan kina sonsa ko? Ta sinne fuskarta hakan ya bashi tabbacin tana son yaron. 67) To tunda kina sonsa sai ki tsaida shi banda jajibe2 kinsan yawancin samarin yanzun mayaudara ne, kada ki biye dadin bakin wasunsu basu da kirki, kina jina? Ta gyada kai. Ya saka hannu a aljihu ya dauko kudi dubu biyar ya mika mata yace, ga wannan ki rike a hannunki ko da wani abu zai taso muku, mu yau zamu wuce insha Allahu, amma nxt wk idan na sami tym zanzo, ki ci gaba da hkr, ki kula da kannenki sosai kisa ido a karatunsu kada ki bari suna fashi sai da kwakwaran dalili kinji? Tace Insha Allahu zan kula, mun gode Allah ya kaiku gida lfy, yace ameen. Tana gidan har su safeena suka dawo da yake basu dade ba, suna dawowa sukayi shirin wucewa, su sultan suka rike Aneesa wai saai an tafi da ita. Ishaq yace tana yin jarabawa ku bari idan ta gama sai ta zo can ta sameku, suka ce to su zasu zauna gurin Hajiya su jirata ta gama jarabawar, yace to ku kuma naku karatun wa zaiyi muku? Da kyar dai aka lallaba su suka tafi. Bayan tafiyarsu ta dawo cikin gida tare da Hajiya, haka kurum taji Hajiya taji tana dada jin tsananin tausayin Aneesa fiye da sauran yaran. Saboda tafi shakuwa da maman sannan yanzun duk wani nauyin kula da yaran zai koma kanta, da ma can ita ce ta jibanci yawancin al'amuransu. Hajiya ma haka ta tasa Aneesa gaba da nasihohi da en shawarwari akan yadda zaman gidan su, da ita kanta yadda zata kame mutuncinta tunda yanzun babu mai kulawa da tarbiyarsu a gidan sai wanda Allah ya so...... 68) ******************************************** A halin yaanzu Aneesa ta shiga ajinta na karshe kenan na secondary, Iyayen sagir sun zo sunyi maganar neman masa aurenta, saboda yanzun har ya sami ya so mayi. Shi ya sa ya ji ya matsu ayi bikin nasu. Baban sasa da yake shine waliyyunsu sai yace ya ba shi, suka kawo kudin gaisuwa, aka saka ranar biki idan ta kammala karatunta, amma ba'a tsayar da ranar ba sai ta kammala tukunna. Hajiya ita ce uwar biki, shi yasa duk wasu sayayya da uwa keyi idan zata aurar da diyarta ta dauki Aneesa sun shiga kasuwa sun sayi waasu abubuwan, da suka je Ummara ma ta siyo wasu. Ranar wata juma'a Aneesa ta shirya tsaf cikin atampa kalar atamafar ya amshi jikinta, to dora bakar riga ta yane kanta da gyalen ta sa pin ta matse. Basira ce ta aiketa wani gida a gwarbai, ta fito kofar gida rike da sakon a irin babbar ledar nan, a kofar gida taga wani mutum tsaye, ta tsaya ta dan risina ta gaisheshi, duk da bata san shi ba, yace dan Allah Alh Ali ya dawo kuwa? Tace bai dawo ba, amma nasan yana kan hanya. Yace ko ke diyarsa ce? Tace eh, yace yauwa dama wani muhimmin sako ne, tunda na ganki natsatsiya bari in baki, don Allah idan ya dawo ki bashi, zan kira shi a waya in yi masa karin bayani. Ya dauko wani file a bayan motarsa ya mika mata tare da cewa, don Allah ki adana sosai kafin ya dawo, nagode sai anjima. Ya shiga motarsa ya wuce. Har ta juya zata koma cikin gidan sai tayi tunanin bari kawai ta wuce da shi don bata sani ba ko abinda ke ciki sirri ne. Ko wasu muhimman takardu kada taje ta ajiye tsautsayi ya same su ta shiga uku, ko kuma basira tana iya bin sahu ta dauke ta boye don kawai Abbansu ya wulakantata. Idan ko ta boyen kanneta zata lakabawa ko ta yaga tace sune, tunda haka take musu binciki da ance sunyi kaza zai kama su da duka kamar Allah ya aiko shi, shi ya sa take taka tsantsan bata son laifin da za'a ce kanneta ne suka yi, tafi son ace idan ma dukan ne gara ya doketa, ko da yake yanzun ta girma da wuya ne zata yi laifi ya bugeta, sai dai idan Basira tace tayi mata abu kaza daga ranar ya daina amsa gaisuwarta. Idan tace abu kaza nasu ya kare ta aiko kanneta ba zai saya musu ba, sai ya ga dama... 69) Ita kuma Aneesa duk kudin idan Ishaw ya zo ya bata ko Hajiya ta bata boyewa take yi saboda Basira ta fara kulla mata sharrin wai yawonta take xuwa tana samo kudi gurin maza, ranar da ta kulla mata wannan sharrin tayi kuka tamkar ranta zai fita. Shi kuma Abbansu ya hau kai ya zauna tamkat bai san Ishaq ke musu hidimomi ba, alhalin wani tym din ma agaban shi yake bata kudin, ya ba Abban ita ma basira idan tana nan ya bata, idan kuma bata nan zai bayar yace a jiye mata, amma don sharri sai ta bage da yi maya sharri shi kuma Uban ya yarda har yana tirketa wai ta gaya masa gidan uban take xuwa idan baya nan ta samo kudi. Tai masa rantsuwa babu inda take zuwa duk bai yarda ba tana kuka taje ta dauko alkurani izifi sittin kuma cikakke ta zo gabansa ta dafa alquranin zata ranste ya kwace yana fada wai zata janyo masa masifa waya gaya mata ana rantsu da Alkurani, balle ita da baya da tabbacin tana da gaskiyya, akan abinda zata rantse din. Tace gara ya barta ta rantse ko da ajalinta ne zai sauka gara ya sauka ta huta akan kazafin da akayi mata. Da ya hanata haka tayi ta kuka, kusan sati tana kuka tare da ciwo mai tsanani da ya kamata, har sai da Hajiya ta zo gidan da kanta ta dauketa suka je asibiti, aka bata magunguna da allurai. Ta saka file din cikin ledat nan taga gara ta tafi da shi idan ta dawo ta san tym din ya dawo sai ta bashi bakinta kanin kafarta. Ta isa gidan da zata kai sako, ta tarar matar bata nan amma yanzun akace zata dawo ta jirata, gashi bata son tayi dare, saboda yamma ta gabato sosai, ta so ta bar sakon sai ta tuna Basira tace tabata ne hannu da hannu kada ta ba kowa. Kusan magriba sannan ta dawo ta bata sakon sannan ta riko file dina nan ta taho gida. 70) Mashin tayi tunanin hawa saboda shine zai kaita gida akan lokaci, don kuwa idan tace mota zata hau sai ta fito bakin titi ta shigo ta kuma kafin ta fita lungun nan sai ta dade. Tana dan tafiya tana waigen mashin. Kawai sai taji tafiyar mutum abayanta, ta soma taku da sauri saboda tsabar tsoro, can sai taji an ja gefen Hijab dinta, ta waigo da zafin tsiwarta zata yayyafawa ko waye masifa, kawai sai tayi ido hudu da sagir, ta sauke ajiyar hrt tace, Amma wlh ka bani tsoro daga sama ko kasa? Yace daga ina kike ke da magriban nan. Kin zo unguwarmu ko ki neme ni, dama ko sabon gidan mu baki taba zuwa ba. Tayi murmushi tace haka kurum sai in zo gidanku, da dai ina zuwa idan ana sha'ani da su haulat to