← Book details Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 51

Sashe 20

Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai a daureni har igiya tayi rara ke kuma sai ki zuba ruwa kasa ki sha, munafuka ai fa ke yanzun nan zaki tare 'yarku zatayi aure gidan masu kudi, lallai kam! Muna nan muna sa ido zamu ga yin auren, auren cin amana. Ita dai Halima tunda ta riga ta gama gaya masa gaskiyya daki ta shige ta barta tana babatu wanda ta san idan ta ci gaba da kulata yau haka za su wani sun musanyar yawu. Aneesa kam! Kasa sukuni tayi tunda wannan lamari ya zamo haka, gidan Hajiya ma da take wuni a can kullum yanzun sai ta soma ragewa, saboda nauyin Hajiyan take ji yanzu, har sai da Hajiyan ta sa aka kirata tayi mata fada sosai akan wannan matakinda ta daukarwa kanta, sannan ne fa ta saki jikinta, wanda Inshaq yace zauyi wa waya kawo mata waya ya zo ya kawo mata ta zabi Nokia mai tsada har da kayi da kudi ya sa mata, sau daya Ishaq ya kirata shima gaisawa sukayi. *************** *************** ************95) Ishaq tunda ya bar zariya a mita yake ta sake saken wannan al'amarin yadda ya kasance. Da ya koma gida kasa sukuni yayi sai da ya zauna yayi shiru yana tunanin hanyar da zai sanar da Safeena zancen wanna auren bai san yaya zai yi mata bayani ta fahimta ba, saboda ita baudaddiya ce, duk yadda ka so ka fahimtar da ita abu bata yarda tafi aminta da abinda zuciyarta ta kitsa mata, balle yanzu. Da ta zama ma'akaciya dabi'unta gaba daya ta canza su, sau da yawa su kan sami sabanin ra'ayi a zamantakewarsu shi ya rasa dalili, to balle yanzu idan yake mata da wannan mafi munin zancen a gurinta. Da dare yayi lokacin kwanciyarsu yayi taje ta aki yaranta dakinsu ta janyo musu kofa ta nufi dakinsa, a bakin gadon ta same shi zaune ya tallabi kuncinsa da hannu 2, ta zo ta dan taba shi sannan ya dubeta yace, kin kwantar da su Yasmin ne? Tace, eh duk sunyi barci, na jika shiru ne a daki lfy dai kake kwana biyun nan ko? Yace lfy lau me kika gani? Lfy ta kalau, ta girgiza kai tace, ba lfy kake ba tunda ba haka na saba ganinka ba, inkuwa lfy jikinka yake to ba lfy zuciyarka take ba, akwai wata mummunar damuwa a tare da kai..... 96) Ya fuskance ta sosai, yace zauna muyi maganar tabbas, zuciyata akwai abinda ke damunta, na rasa ta yadda zan gaya miki ne ki fahimta shi yasa abinke damuna a zuciya yana mini ciwo, kin yarda in gaya miki ba za ki bani matsala ba? Tunda taji haka sai jikinta yayi sanyi ta san cewa akwai wani abu da zai faru da ita na bakin ciki, kuma kila daga zaria abin ya samo tushe, sai dai ba ta fatan abinda zuciyarta ke ayyana mata ya kasance gaskiyya. Ta zauna suka fuskanci juna sosai sannan tace, bana fatan abin da zaka gaya mini ya kawo matsala a tsakaninmu sai dai in dama lamarin mai matsala ne to kaga ba daga gareni bane. Ya janyo hannuwanta ya makale su cikin nata ya soma murza su a hankali ta sauke ajiyar zuciya, ta tsura masa idanu tana sauraronsa. Yace, safeena kiyi hkr nasan abin da zan gaya miki zaiyi miki ciwo, aure aka bani a zaria, kuma babu yadda zanyi in kaucewa auren dole na amsa. Hannuwanta ta fizge cikin nasa tamkar wadda ta rike rushin wuta, ta mike tana huci ta nuna shi da dan yatsanta sannan tace, daman na san za'a rina, wannan sintiri da kakeyi a zaria ai yayi yawa, tuni zuciyata ta soma ayyana mini wannan mugun lamarin ina yakice shi, ashe zai tabbata akaina ne da gaske. Yanzu kai kamar ka da Iliminka da kudinka da wayewarka, za'a baka aure baka so ka amsa, sai dai in dama can kana so ne amma ba zan yarda baka akayi ba, gara ka fito barao2 kace min ka nemo aure a zaria har an baka zan fi yarda. Yace, ni wlh ba ni na nema ba, bani akayi, kuma duk kudina da ilimi na da wayewata ban isa in ki bin umarnin na gaba da ni ba, har duniya ta nade su ne sama dani dole inyi musu biyayya, nafi son farin cikin su da nawa, nafi gudun bacin ransu akan nawa, shi yasa da suka bani auren na amsa tare da godiya don nasan ba dan su cutar da ni ne suka bani auren nan ba, alheri ne suka kulla. 97) Dama ai ba za su cutar da kai ba tunda abin alheri suka kulla maka, nice dai suka cuta zasu kulla min abinda ba alheri ba. Kaiko a family dinku waye ya baka wannan auren ka amsa? Yace ba wata bace sai wadda ta isa dani, wato hajiyata. Auren kuma da Aneesa ne za'ayi. Ta ware idanu tace, Hajiya ta baka auren Aneesa!!! Yanzu kai a wayewarka me zaka yi da wannan yarinyar? Yace shi yasa nima nake ganin idan kika kwantar da hankalinki zaki juya yarinyar nan duk yadda kika so, tunda ita ba mai hayaniya bace, ba zaki sami matsalat zama da ita ba. Ta dakatar da shi tace, Ya isa! Ya isa!! Tun yanzu har ka zo gaba na kana yabonta, tun bata zo gidan nan ba, to bari kaji in gaya maka aure ko kaje kayi Allah ya bada sa'a, amma tsakanin ni da kai babu sauran zaman lfy, balle ita kanta idan ta zo gidan zata gwammace gara agidan yari da gidan nan ban,don ba za taji dadi da ma'aurata keji a gidan aure ba, ai duk macen da tace zata auri mijin wata to (MIJIN ARO) zai zame mata, saboda haka ina nan ina jiran zuwanta. Ta dauki saman rigar baccinta da ta cire ta aje bisa gadonsa ta fice daga dakin, yana kiranta ko sauraronsa bata yi ba ta nufi dakinta, ta murza key ta rufe kofarta, don ma kada ya shigo ya dameta. Kwana tayi kuka da sake2 abinyi, amma har gari ya waye bata samo wa kanta mafita ba, na yadda zata wargaza auren. Da sassafe ko sauraronsa bata yi ba, ta tuta masa sako ta wayarsa, cewa zata fita anguwa, bata jira mai zaice ba ta fice, su Yusra gida ta barsu gurin mai kula da su. Gidan aminiyarta ta nufa, guri daya suke aiki, ta girmeta da shekaru akalla biyar. Haj. Nuratu manyan mata kenan masu juya naira saboda ba aikin kadai takeyi ba, tana safara zuwa Dubai, sannan shi ma mijinta juya shi takeyi tamkar karamin yaro duk da yake babban mutum ne amma macece ke jan ragamarsa. Tana ganin safeena ido kode ya jeme da kuka, ta riko ta suka shiga dakin barcinta, tana tsokanarta. Ho! 'Yar lelel Captain me kuma ya faru ne? Na dai san ba Captain bane tunda shi baya laifi kullum cikin faranta miki yakeyi, kece ma in 'yan tsiyarki ya tashi kike gara shi, bawan Allah inji ki, ni kam namiji ban dauke shi abin tausayi ba, sai da kawai ya bauta mini ni kuma in juya shi yadda raina ke so. 98) Safeena ta zauna tana sauke ajiyar zuciya tace, yau Captain ya tabo ni na daina yabonsa har abada in dai baya janye Alkaba'in da ya dauko mini ba. Haj. Nuratu ta kyalkyale da dariya tace, hala aure zaiyi, don nasan tatsuniyar maza bata wuce aure in dai sunji su lafiyyayu, ba sa son bin matar waje to yanzu za suce aure don ba su cika son cin tuwo daya kullum ba. Murmushin takaici Safeena tayi tace, wlh kamar kin sani aure zaiyi wai Hajiyarsa ce ta ba shi yarinyar a can zaria, kinma san yarinyar wadda zaki ga hajiyan nan- nan da ita tamkar wata autarta, wata fara sirirya, shegiya sai nono da duwawu ( Hahahaha kunji fah, ita ina nata) kilama shi Captain din ya gani suka tsole masa idanu, dan na san halin kayana. Haj. Nuratu ta saka dariya tace, ai tuni nake gaya miki namiji ba abin yarda bane, tun kafin ya saki kuka gara kiyi maganinsa ta yadda kina ganin sai yadda kikayi da shi, to ai ga irinta nan ya dauko auren er garinsu, en zariya masu shegen asiri, su kansu iyayen ba haka suke barin 'ya'yansu ba, yanzu ai kinga zama bai gammu ba, sai ki tashi mu san abinyi. Safeena ta tashi daga kishingidan da tayi tace, to hajiyarmu yanzun meye abinyi? Tace tashi zaki yi mu kama hanya dole mu hana auren, wani kauye zamuje nan kusa da birnin gwari, zaki ga aiki da cikwa. Sun hau motar Haj. Nuratu ne sukai ta sharara gudu awa daya da rabi sannan suka isa kauyen. Haj. Nuratu ta zayyanewa bokan abinda ke tafe su, yayi dariya yace, ku sha kuruminku daga auren har zarian ba zai kara yin maganarsu ba, ku tashi ku tafi. Suka aje masa kudi masu yawa suka baro kurgurmin dajin 99) Tun daga ranar Ishaq bai sakeyi wa safeena maganar aurensu ba, ta sa idanu taga ko zaije zaria nan ma shiru, tun daga tym din ta soma murna a ranta, asirinta ya kamshi, tunda har ta raba shi da auren da ya rakito ta nisanta shi da mahaifarsa. Hajiya kuma taji shiru ba zuwa ba waya, abin ya bata mamaki, abinda Ishaq bai taba yi ba don ba ya sati biyu bai zo ba mahaifarsa ba, in kuwa bai zo ba to baya kasar ne, to zai ta yiwa Hajiya waya yana bata hkr tare da jin lfiyarta, sai ga shi yanzu har yayi wata guda cur! Rabosa da zaria kuma ko yi mata waya, sai ita ne wani tym ta kan kira shi, amma ba ko yaushe take samunsa ba sai tayi sa'a, sau biyu idan ta kita safeena na dauka tace wai baya garin wayarce ke gida. Tun daga tym din Hajiya ta sha jinin jikinta, ta tashi tsaye da rokon Allah akansa sam, bata bacci dama ita, kauwama ce ( mai yawan tsayuwar dare) Kuma sauwama ce ( mai yawan azumin nafila ce). Har malamai nagartattu masu sani tasa suka dinga taya da rokon Allah. Gabatowar bikinsu da aksa ya zo ne tare da samun nasarar rokon Allah din da akayi masa,
Chapter 20 · 0% Book details