← Book details Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 51

Sashe 22

Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bai auky tsakaninsu ba da bai san yadda zai yi ya iya fuskantar aneesa ba balle kuma mahaifuyarsa datavdanka masa amanarta yana shiga dakin ya ganta zaune a bakun gado ta tallafi kuncinta hannu bibbiyu tana ganinsa sai ta kura masa idanu , shi kansa ya fahimci so take ta tuno wani abu amma da yake ya fita wayau sau ya jinkirtar mata da tunaninta yace "ke ashe yar kauyece ban sani ba , daga shan lemu sai ki bingure tamkar mai mayemaye! ta dan yamutsa fuska tace lemu! wani irin lemy ka bani haka har wani irin mugun mafarki nayi sai inajin duniyar na juyawa dani? yace "ba wani lemu bane mai sa maye, ina ganin don baki taba shansa bane ya bugar dake. yanzu dai tashi kiga kayayyakin ta riga ta fidda mana masu kyau , sun fita da maigidan kina nan lemu ya bugar dake" ta mike tayi saurin duban jikinta ba kamar yadda taga an cire mata hijabi da riga ba , komai nata yana jikinta, ganun hakan ya ya dada tabbatar mata da mafarki tayi, tayi saurin yin hamdala ga allajallah da munmunan al'amari bai faru da ita ba. Da kyar ta dinga daga kafa saboda nauyi da kasalar da jikinta keyi. a wani dakin ya nuna mata wasu kayayyaki masu kyau, kama daga leshi material xuwa shaddoji yace ta duba ta gani duk wanda baiyi mata ba sai ya cire, ita dai duk wanda sai tace yai mata, ita dai ta kosa ne su koma gida saboda jikinta sam babu dadi ya kira mai gadi ya kwashe kayan duka, bayan an zubasu acikin wassu akwatuna na fata, ya zubasu a kujerun bayan motar sannan yace ta sjigashiga su tafi...ya duba wayarsa yaga yana da missed calz dauawa amma na haj sunfi yawa, ya danyi murmushi ya dubi aneesa yace kinga na bar wayata a mota haj tai ta kira bana tare da wayar, tace " nima anan na bar tawa wayar ga msd calz dinta nan har goma" yace bari in kirata, yana kiran jaj bugu daya ta daga dama kiransa kawai take tsimayi. yace "haj kiyi hakuri a mota muka bar wayoyinmu sai yanzu naga kirankikiranki, gamu nan a hanya kiyi mana afuwa" fadan da taso tayi sai ta fasa tunda taji lfy suke sai tace sai kun iso, amma kasan dare yayi ko? yace yi hkr haj gamunan bisa hanya. Ya dubi ameesa yace bativmu dan shiga TULIPS in saya miki ice cream tace "zaka koma damu baya kenan ai da ka barshi kawai " bai saurareta ba kaeaivya karya kan motar suka shiga layin queen elizabeth. A tulips din bata shiga ba shine ya sjiga ya jidp mata abubuwan sha da ci don ledojin gurin manya guda biyu ya shaqo da kayan qwalama da makulashe iri2, sannan suka hau titin skt rd sula dauki hanya. Haj na ganinsu ta saukar da ajiyar xuciya tace haba ishaq! kun tashi hankalina da yawa, na kira wayarku sau ba adadi dula ba'a dauka ba, xuciyata da sake2 babu mugun abinda nata saqa mini ba, ni bama kai nake ji ba yar amanar Allah nakeji, da darennan ka matsa sai taje wani duba kaya gsky anyi na end, yayi murmushi " ni dama na san sabida ita xaki damu amma tunda tana hannu na ai baxata bata ba gata nan yadda na daukar miki ita lfy haka na daeo da ita lfy ba' gutsira ko farcenta ba " tayi dariya kawai tana duban aneesa wadda smyl din karfin hali kawai take yi don ita kam har yanxu jikinta bai dawo mata dai2 ba, bakinta ma ji tayi yayi mata nauyi, ta gefen haj kawai ta zauna.. ishaq ya tashi ya fita can suka dawo da yan samarin da ke zama gidan sun debo akwatunannan har cikin dakin haj suja shiga dasu. Ya bude mata yace ta duba ta gani, ita kam haj murnace ta cika mata ciki ganin yadda ya dauki komai da muhimmanci, gashi ya gama duk wassu muhimman abubuwa na neman aure tunda har sadaki ya biya ranar daurin aure kawai ake jira 7) Ishaq ya fita can suka dawo da en samarin da ke zama a gidan sun debo akwatunan nan har cikin dakin Hajiya suka shiga da su. Ya bude mata yace ta duba ta gani, ita kam Hajiya murna ce ta cika cikinta ganin yadda daga zuwansa ya maida Hankali akan zancen aure nan. Ya dauki komai da muhimmanci abubuwa na neman auren tunda har sadaki ya biya ranar daurin aure kawai yanzu ake jira. Ya dubi Hajiya yace gobe kiyi wa su Yaya Hannatu waya su zo su duba kayan nasan da akwai abubuwan da za'a kara sai in basu kudi su saya su kara, nima a wannan satin zanyi doguwar tafiya daga can sai kara wasu abin. Aneesa ta mike tace, Hajiya zan wuce gida naga dare yayi. Tace ai nayi ma Abban naku waya nace masa yau na rikeki anan zaki taya ni kwana, mai aikina bata nan. Tace, shikenan bari inyi sallah isha'I banyi ba muka fita. Ta shiga bayin dakin, Hajiya ta bi bayanta da kallo saboda taga ta canza bata da kuzari kamar yadda suka fita, to wani abin ne, ko gaya mata wata magana mara dadi ne har ya zamo bata da walwala? Haka wadannan tambayoyin suka yi ta zaga kwakwalwarta, ta rasa gano dalili. Ishaq ya shigo da ledojin nan na Tulips ya aje gaban Hajiya yace, ga tsarabar er ki nan, ni na tafi sai da safe, tace Allah ya tashe mu lfy. Hajiya ta dubi Aneesat tym da ta idar da sallah, tace na ganki wani iri ne ba walwala, me ya faru? Ko wani abin yayi miki na bacin rai? Tayi saurin girgiza kai tace, babu abinda ya faru, ganin mun dade a can gidan ne nayi wani iri, duk sai na damu na kosa mu dawo, balle da naga msd call dinki nasan zaki yi fadan dadewarmu, ni kauna agije nake barci nakeji yau banyi na rana ba. Tace ko zanyi fada ai shi zanyiwa, tunda nasan shine zai sa ku dade ba ruwanki, ai ba zan sake yarda da wannan fitar ba sai an daura aure can kuje ku karaci yawon anguwarku amma yanzu an gama. 8) Washegari Ishaq zai tafi cikin dabara hajiya ta nuna masa kar ya dinga zancen auren sa gaba Safeena. Saboda bata son hankalinta ya tashi, dan va ko wace mace bace ke son kishiya sai dole. Yace ai, rigima sosai mukayi da ita don ko yanzu ba wani dasawa muke yi ba, duk da dai bana yi mata maganar auren, ita ma bata yi min, balle tunda taga nayi sati 4 banzo zaria ba kila zata dauka an fasa yi ne. Hajiya tace, Yauwa hakan yayi ka bari sai tym din ya gabato sai sake sanar mata, kuma duk wani abu da akeyi wa uwargida na ban hkr kamar akwati da gyaran daki, zuwa kudade duk kayi mata don bana son kayi mata abu ba daidai ba. Yace Insha Allahu komai zanyi mata. Ana sauran sati2 daura aure, Ishaq yasa akayi fentin gidansu na Abuja aka canza komai na falonsu, safeena ma yace ta fadi irin abubuwan da take so na gyaran dakinta, sai ya bata kudi ta saya. Ta dube shi shekeke tace wannan gyare2 na menene do baka yi min bayani ba? Yace bana komai bane, hakan nan dai nake son in gyra gidan. Tace tuna bana komai bane bana so. Ta rike kwankwaso hannu2 tace, Kai Ishaq bari kaji duk nagano wannan rawar jikin da kakeyi ba akan komai bane sai akan wannan kucakar yarinyar wadda bata gama wayewa ba, don an baka sadakarta shine zaka so ka isheni da rawar jiki, kasan dai ko er jami'a zaka dauko bata isheni kishi ba balle wannan yar ficikar yar sakandire, to ka taka a sannu, in ba haka wlh sai nayi maganinta har kai. Yayi murmushi yana kada kai yace, Kinga tun farko ma shi yasa na gaya miki kada ki tashi hankalinki akan zuwan ta, tunda ni nasan bata kamo kafarki a komai ba, in banda abinki kishin me zakiyi tsaya yi da ita. Iyakarta dake a gidan nan ladabi da biyayya sai nayi bari na bari, balle ita da banyi tsammanin tasan wani kishi ba, ta lafe shi da idanu tace, wace bata san kishi ba? Don Allah malam kada ka maida ni yarinya, ai ina jin ko yaron goye yasan abin da ake kira kishi, tunda ko en 2 gasu nan kana da su idan aka ba daya abu daya kishi yake shima sai an bashi, balle diya mace kace bata san kishi ba. 9) Kuma tun yanzun bari na gaya maka ko kayi auren ka ba dai kawo min yarinyar gidan nan ba. Don ba zai yiwu ta raina ni ba, data gane gadon baccin mijina shikenan na zama hoto, balle kai idan ta gama sanin sirrinka ciki da waje, saboda haka kasan inda zaka aje ta kasan bana son raini. Ya raunana murya, haba feena ke ba jin dadinki bane in kawo mai taimaka miki agidan nan, dama gashi baki cika son er aiki ba, shikenan kin sami mai taya ki aikace2. Tace, to in baka sani ba wlh gara er aiki sau dubu da ita, tunda er aiki ba ta da wani matsayi a gidan nan da ya wuce na ita er aiki ce, ita fa? Ina ji ina gani zan ganta a dakinka kuna kwana tare ban gama tantancewa ba za'a wayi gari in ganta dauke da cikinka, ka gane banbancinta da er aiki ko? Yace to za'ayi wannan kun ai na Allah ne idan hakan ta faru. Tace, yauwa kaji ba to shi yasa bani son ganin haka a nan gidan ka barta can ma a zaria zai fi maka kwanciyar hankali, amma nan kam bata da daki. Ishaq duk ya gama gyare2 yadda yayi wa Aneesa akwatuna shida irinsu sak, yayi wa safeena ya zuba mata zannuwa har sun fi na Aneesa tsada. Saboda yasan halinta shi yasa yayi abin dai birgeta. Ba sai sakar kuturwa yake yi na baya na warwarewa. Da dare yayi ta danna kararrawar kiranta amma ta ki zuwa. Ya kira ta waya da kyar ta
Chapter 22 · 0% Book details