← Book details Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 51

Sashe 4

Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tsaki tace, Amman ai naji haushi har chocolate din nan da nayi ma su Shuhail alkawari saida na tsaya na siyo musu, ni na dauka kwana za suyi, Umman ce na iske sunje dubiya shi yasa na dade. ta mikawa Hajiya ledar tace, ga ajiya nan duk ranar da suka dawo ko da bana nan ki basu. Ko idan daddyn su ya zo shi kadai ki bashi ya kai musu. tana amsa tana cewa, oh wadannan yara da a garin nan suke da sun san suna da uwa mai ji da su. Tayi dariya ta mike tace, Hajiya bari in karasa gida, zan dawo da yamma zanyi miki wani haddadden girki da aka koya mini. tace Yau laraba kada tayi girkin gidan nan da kenan? tace, to shikenan. zo ga sakonkinki inji yayanki. Tace daga kushin din can ki dauko kudi, Ta mika mata tace wannan yace ki sayi books din sch da kukayi magana, wannan kuma ki sayi kayan makeup. Ta amsa tayi godiya ta kara cewa, kai yayana da tsokana yake ni yaushe yaga ina kwaliyya? Daga vaselin sai hoda nake shafawa ai. Mama fada ta kama yi mata da ta isa gida akan ta dade da yawa, tace wlh mama Umman ce bata nan sunje dubiya, shine na jirata. ga sakon tace in gaisheki da jikin. idan da wata matsala ki yi mata waya$ tace kinga ma kudi nan dubu biyar Ishaq ya gaisheni ya bani, Ya dade muna hira yana jiranki, Hajiya tace masa kin shiga baya nan ko kun hadu? Tace sun tafi nima da zan tafi gidan Umma ne naga motarsa shine na shiga gidan, kafin in dawo har sun tafi, nima kinga kudaden da ya bani har da books din da na fadan masa, shine yace na fada masa sunan ya sayo min ko zai aiko min da kudin in siya. Mama tace Allah ya saka masa alkhairi, ya karamasa budi, nikam Ishaq babu abinda da zance masa don ko bai zo ba garin nan in dai zai turo ma Hajiya kudi sai kinga nawa kason. washegari Maman da sassafe tayi wanka tayi shirin zuwa asibiti, tunda abbansu Aneesa ya ga tana shiri ya soma hade rai, saboda ya san zata tambaye shi kudin hoto, da ta ga haka sai bishi dakinsa tayi sallama a ciki2 ya amsa, sannan daga baya ko kallonta baiyi ba ya ci gaba da gyara wasu takardu, ta nemi gefensa ta zauna sannan ta sake gaida shi , ta dan dube shi tace, daman yaune zan koma sibiti kuma zanyi hoto daga nan, yace amma ain naga ya miki bani da kudi. abar maganar hoton sai karshen wata ko? Koko dole ne sai anyi hoto a haihu lfy? Ya kar maganar a hasake idanunsa kyam a kanta, Ta risinar da idanu kasa tace, nima da na hkr din sai jiya Ishaq ya shigo ya bani 5k shine zanje inyi hoto sauran kidin sai in sayi sauran kayan haihuwar da bamu syab. MIJIN ARO 1**5 Ya dan tabe baki yace, shikenan Allah ya taimakeki tunda dama kin matsu kiyi hoton, sai kije a dawo lfy. Ta mike gwiuwa a sabule saboda wannan halin ko'in kula da yake bata wanda tun asalin aurensu ba haka. ta saba gani ba, ita anata hasashen idan zama yayi zama yau da gobe ne Ma'aurata ke fuskantar canji a tsarin zamantakewarsu ta fil*zal, koko ta gundure shi ne yake mata haka? Ita kam ta rasa dalili, kila kuma wani abu take masa baya so, to in wannan ne ai ta sha tambayarsa sai yace shi batayi masa komai ba. wani tym din idan ya kuntuka mata wani abin yaga tana zubda hawaye sai duk ya damu yayi ta lallshinta da bata hkr wai shima ya rasa dalilin da yasa yake yawan bata mata rai. Ta taba gayawa hajiyan Ishaq sai tace ta dinga yawaita nafilar dare da tsananin addu'a insha allahu komai zai daidaita, shi ya sa ta kae kaiwa Allah kukanta, ta rungumi shawarar Hajiya shine fa wani tym ta kan ga sauyi. kafin ya sake botsare mata, Haka dai zaman yake yau fari gobe tsumma. sannan gashi ya sa duk abinda aka ce kta ko Aneesa sunyi a gidan nan yake saurin hawa kai ya zauna, ya zama Gabar wadda bata juri zunguwa ba. tana shiga daki ta iske Aneesa da kofin shayi tana fifitawa, ta dubi Uwar tace, Mama ga tea din naki baki karya ba zaki tafi? Naga kina ta sauri. Ta mikawa Aneesa hannu tace bani to insha bana so in makara kinsan asiboitin daga can wuce gurin hoto gara tafi da uwri. Ta zauna ta soma kurban tea din, Naeesa ta dubi Maman tace, Mama kiyiwa Aisha magana tayiwa Yara wanka ni sai inji da abin karin shirya su, tunda ni Abba ya hanani zuwa sch idan suka tafi sain gyara. gidan inyi wanke2 Ta aje kofin tea din tace taso mini ita tunda tayi sallar asuba ta bi ta nade a gado tamkar tare da shi aka halliceta. ai dole ta tashi ta taya ki wankansu. kema ai ba zamanki kenan ba agida, ranar mon dole kije sch in kuma ya hana sai in gaya ma Yayan sasa, gaba ai da gabanta. Taje ta taso Aysha sai zumboro baki takeyi, tazo gefen Maman Ta zauna, Maman ta dube ta tace, ba zama zaki ba tashi zaki yi ki yiwa Yara wanka don ni asibiti zanje ita kuma karama aiki zai yi mata yawa saura na dawo tace min bakiyi musu ba. Haka aysha ta sirka ruwan wakan da zafin gaske tana shekwa Yaran suna tsala ihu, suna zabura saboda zafi. don taga Mama ta fita, kuma tayi hak ne don Aneesa tayi magana su yi fada tana jin haushin ta tasheta abarcinta, dan ta san babu abinda Aneesa ta tsana. irin kukan 'yan kanneta, ita kuma ta san abinda aysha ke nufi sai kawai ta ahsreta ta cigaba da aikin gabanta. Tana durkushe tana wanke2 bayan ta shirya kanneta suna daki, suna karyawa sai ga Aysha ta fito daga dakin ABban su da Uban kayan Wankinsa a tunanin Aneesa yau Aysha ce zata kai masa gurin mai wanki da guga na layinsu, har tana mamaki. Aysha da ko bokitin ruwa bata iya daukowa awaje wai kunya takeji ita adole ga budurwa, shine yau sai gata da tilin daurin wanki, da mama ce ta aiketa da an sha korafi da zumbura baki. 'w- sai Aneesa taga Aysha ta dire wanki agefenta tace, sako daga Abba yanzun zai fito zakiji bayani. murmushi kawai tayi tasan yau itace mai kai wankin kenan, to meye sabon abu a gurinta, kaya ko yafi wannan zata dauka don ita bata dauki kanta akomai ba, tunda ko ruwa ne idan nasu ya kare kuma ba na famfo zata fita ta debo a makwabt. Abbansu yace tunda kin zama baiwa agogo sarkin aiki, to ga wanki nan daga yau na daina kaiwa gugda ke zaki dinga yi idan sun bushe ki goge su... Ki goge da dutsen gawayi. ya ciro dari 3 ya mika mata yace, Gashi nan ki sayi sabulun da sitati. Ta amsa hannu bibbiyu ba tare da wani bacin rai a fuskarta ba tace, Insha Allahu kafin ka dawo zan wanke in goge. Adawo lfy Allah ya bada sa'a. kafin ya fice ne ta bishi da wannan addu'ar bai amsa ba yayi ficewarsa abinsa. Da yake Allah yayi Aneesa mai zafin Nama kuma sam bata da kasala, ta saba da kazar2 shi ya sa kafin 10am har ta gama wanke2 ta share dakin Mama da Na Abban tare da hada ruwan girki. Ga kayan da yawa 15sets cikin ikon Allah kafin 12pm har wasu sun fara bushewa, Allah ya taimaketa akwai wutar nepa sai kawai ta fara gogewa$ Tana cikin gugar ne taji bugun gidansu ta san kannenta ne suka dawo, tana bude musu suka rungumeta Jafar yace, Aunty yunwa nakeji kin gama abinci? Tace naga jafar ai na sanka chop2 ne. Sai da ta canza musu kaya sannan ta shimfida musu tabarma a inuwa ta xuba musu abinci suka soma ci. ita kuma ta koma aikinta. Can taji ana knockn kofa tace Amira je ki bude kofa kila mama ce$ A madadin Maman taga ashe kanin hanne ne ubansu daya( matar baban sasa) yana zuwa koda yaushe gidan shima ya zama kamar dan gida. Ta gaishe shi yace Ina Aneesa fah? tace tana dakinsu tana guga$ Ya karasa ciki ya iske Aneesa, Ta dube shi tayi murmushi tace, a'a dan uwanmu kana garin nan kuwa? ko hutu ne ya boye ka? Yayai murmushi yace wani hutu ne ga dan makaranta, ke ce ma yar hutu tunda nazo gidan nan sau 2 ana ce mini kina nan bakya zuwa makaranta. kinga ai kce 'yar hutu. Tayi mrmushi, dole ta sa banje sch ba amma ran monday idan ka zo kamar wannan tym in bazaka ganni ba ina sch . Yace gaskiya ki din daina fashi, gaki da brain amma kina son ta dakushe ki ma 'ya'ya na asara. Ki goge da dutsen gawayi. ya ciro dari 3 ya mika mata yace, Gashi nan ki sayi sabulun da sitati. Ta amsa hannu bibbiyu ba tare da wani bacin rai a fuskarta ba tace, Insha Allahu kafin ka dawo zan wanke in goge. Adawo lfy Allah ya bada sa'a. kafin ya fice ne ta bishi da wannan addu'ar bai amsa ba yayi ficewarsa abinsa. Da yake Allah yayi Aneesa mai zafin Nama kuma sam bata da kasala, ta saba da kazar2 shi ya sa kafin 10am har ta gama wanke2 ta share dakin Mama da Na Abban tare da hada ruwan girki. Ga kayan da yawa 15sets cikin ikon Allah kafin 12pm har wasu sun fara bushewa, Allah ya taimaketa akwai wutar nepa sai kawai ta fara gogewa$ Tana cikin gugar ne taji bugun gidansu ta san kannenta ne suka dawo, tana bude musu suka rungumeta Jafar yace, Aunty yunwa nakeji kin gama abinci? Tace naga jafar ai na sanka chop2 ne. Sai da ta canza musu kaya sannan ta shimfida musu tabarma a inuwa ta xuba musu abinci suka soma ci. ita kuma ta koma aikinta. Can taji ana knockn kofa tace Amira je ki bude kofa kila mama ce$ A madadin Maman
Chapter 4 · 0% Book details