← Book details Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 51

Sashe 33

Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yasa kike zama a daki kina takura kanki? Wannan ai zai iya janyo miki wani. Ciwon ko wani abun ke damunki ki gaya min? Girgiza kai kawai tayi ita kam me zata ce masa? Ai ya riga ya yasan komai game da gidansa, shi kanshi rashin kulawar da yake mata kadai ya isa ya dami zuciyarta ya sata ciwo, ita fa gidansa babu abokan hirarta da nishadi,babu inda take samu walwala da fain ciki sai a gurin yaransa sune abokan hirarta, in ka debe su babu mai hira da ita, tsakaninsu da ita sai da gaisuwa shine suke da sanin zamanta a gidan. Idan bata fito babu mai nemanta, wanna wace irin rayuwar aure ce, ki da mijinka bbau halin ka ganshi balle har kuyi hira da juna, idan kana cikin matsala ma ai tanan zai gane ko kuma ka gaya masa, to kiri2 anyi mata shamai da shi ya zame mata MIJIN ARO! Ita kanta suna ne yake mijinta amma a zahiri ba nata bane mijin wata ne, tunda acewar safeena nata ne ita kadai sai in taga dama zai kulata ko yayi hulda da ita, kuma haka dinne tunda gashi a zahiri ita kadaice ya maisheta mace asali komai nasa, ita Aneesa ta zama er kallon yar jiran gidan idan sun tafi aiki, tayi musu girkin rana ita da baba , su dawo suci abinsu babu wanda ya ta nuna mata yasan ita keyin girkin a cikinsu balle yayi mata sannu da aiki kuma tabbas sunsan ita ke tunda sunga canji a girkin amma na aneesa daban ne, in safeena bata son dandanon girkinta ba ai Ishaq ya sani tunda a zariya baya cin girkin kowa sai nata, ita kuma safeena ida tayi nata da dare basa gayyatar ta ko da yake sun gayyaceta, sau daya ta je taga kamar da gayya suka kirata don su nuna mata iyakarta agidan wai su sarakan soyayya wata laila da majnoon ko romeo da juliet. Shi yasa ta yanke hukincin idan an gama zata dinga zuwa kicin din ta diba shima cin abinci daren dole dai ta hkr don bata son ganin wulakancin abubuwan da safeena kewa Ishaqa, ita kam daga yau ma ta daina musu girkin rana sa dinga cin na baba tunda ita ba er aikinsu bace. 61) Ya qara matsar hannunta yace,kinyi shiru sai tunani kike yi,ki gaya mini mana idan da abinda ke damun ki,gaki nan sai faman tunani kike na san ma a daki abinda kike yi kenan. Ta sake girgiza kai,yace maganar ma sangarta kike yi min ko sai na sayi bakinki ne? Nan ma shiru tayi, yace, lallai aneesa to Allah ya baki hakuri tunda na lura ni ma mai laifi ne,ayi mini afuwa. Sun isa wani private hospital kai tsaye ofishin likitan suka nufa kuma akwai sanayya a tsakaninsu,kuma tun a mota kafin su aneesa su fito ya kira shi ya gaya masa zai kawo patient dinsa. Shine a gaba suka shiga tare da sallama,likita na ganinsa yayi dariy yace,ran captain ya dade yau kaine da kanka,waye ba lafia? Ya nuna aneesa yace,gata nan amaryata ce ba lafia,amma cikin ciwon nata har dana shagwaba ko kuna da maganin shagwaba anan asibitin. Daktan ya saki dariya yace,a'a bamu da maganin wannan kai ke da maganin ka bari zan gaya maka. Suka tafa hannu suka gaisa aneesa dai na tsaye tana kallon ikon Allah. Likita yace,sannu amarya zauna ga kujera wannan mijin naki baya da kirki bai ce ki zquna ba,na lura kuma kina tare da jiri. Ishaq yayi sauri ya gyara mata kujera yace oya zauna kada ki fadi yanzu ki fara kuka don na san ki komai kuka kin zama a lallaba,auren zmani. Ta zauna likita ya fara mata tambayoyi tana bashi amsa. Ya dubi ishaq yace,bari in dubata,ya dauko abin awon jini ya auna ta yaga jininta ya soma hawa,yayi duk wasu en gwaje gwaje sannan ya dubi ishaq yace,madam na tattare da damuwa da yawan tunani hakan har yasa jininta ya soma hawa,zan rubuta mata magunguna amma don Allah ka lallashe ta ta gaya maka abinda ke damunta kayi mata maganinsa don in ba haka ba yawan damuwa da tunanin zai iya haifar mata da babbar matsala da tafi wannan,abinda bama fata kenan. Sannan abu na biyu zan auna fitsarinta mu gani ko akwai ciki sbda mu san irin magungunan da suka dace mu bata,likita ya juya da tambayar shi gun aneesa,yaushe rabon da ki ga aladarki? Shiru tayi sbda jin tambayar tayi wani iri,sai likita ya dubi ishaq yace,captain hala dai akwai cikin ka kaima an boye maka? Anyway rabu da ita yay zan fallasa maka ita. Suka yi daria,ishaq ya dubi aneesa suna hada ido ta risinar da idanuwanta qasa tace wa likita,gaskia dr bani da wani ciki,kada ka wahala gurin wani awon fitsari,likita yayi dan murmushi yace,kin tabbata baki da ciki in rubuta miki magunguna daidai da mara ciki? Tace Allah na tabbata,gashi nan zaune ka tambaye shi idan ma da cikin yafi kowa sa ni. MIJIN ARO 2***7 64) Duk sai kunya ta kma ishaq kada dai bakin yarinyar nan yayi subul ta fadi bai taba hada shimfida da ita ba tana a matsayin matarsa,lallai kam ya san bai yi ma yarinyar nan adalci ba ya rabota da iyayenta da en uwanta da mahaifarta ya zo nan ya ajiyeta kamar wata er aiki ko er karo a gidansa,gaskia dole yarinyar ta shiga cikin tunani da damuwa,hakika shine sanadin ciwonta,kai dole ma ya zo ya gyara wannan tsarin zama na su mara adalci,kazntaccen zama ne da ya sabawa sharia,zai yagi zuciyarsa da ke raya masa cewa a duniya babu macen da zata gamsar da buqatarsa irin safeena,itama fa aneesa a duk yadda ya bi da ita zata iya da shi,qila ma ya samu tafi safeena duk wani abu da yake ganin babu irin safeenar ,?kila ma juriya da kulawarta yafi na safeena idan har ya bata dama. 65) Tunda abinda yake so idan bata ga dama ba wata rana sai ta bata masa rai a wajen kwanciyarsu don ta dinga qirqire qirqire sai ya saya mata kaza da kaza shi kuma ransa na baci ace mace ba zata yi abu domin Allah don ta faranta ran mijinta ba sai in zai saya mata abinda ranta ke so. Likita idanuwan shi na kan ishaq yace,are u sure bata da ciki in rubuta magungunan? Ka dan akwai maganin da bai dace mace ta sha idan tana da qaramin ciki ba sbda karfinsa zai iya salwantar da cikin shiyasa dole a tambaya don a rubuta mata daidai da yanayinta. Ishaq yace,eh bata da ciki na tabbata. Likita ya rubuta mata magunguna tare da shawarwari akan ta rage damuwa da tunani. 66) A wani pharmacy masu magunguna masu nagarta ya tsyaa ya sayo mata magunguna,suna da supermrkt a hade suka shiga nan ma yayi masu sayayyar kayan kwalama iri-iri sannan suka tafi.Yayi lallashin duniyar nan a hanya ta gaya masa in akwai abnda ke damunta amma sai tace masa babu komai. Sun zo daf da kwanar da zata kaisu gida ne yayi fakib din motar daga gefen titi ya sauka daga titi sosai ita dai tana kallonsa. Ya juya sosai yana kallonta yace,aneesa nayi - nayi dake ki gaya mini abin da ke damunki ya ke saki tunani kin qi ko? To idan ba zaki gaya mini ba ina roqon alfarma ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa,in ma ina da hannu cikin damuwarki to kiyi hakuri wallahi kina raina zuciyata ce kawai ke raya mini wani abu wanda ni na tabbata karya take kitsa mini ki taya ni addua nima ina nan ina addua ina qoqarin yaqi da zuciyar tawa ta bar kitsa mini abinda ba zai fisshe ni ba,ni kaina ina cikin damuwar kyale ki a sagale da nayi kiyi hakuri kinji? Ta sauke ajiyar zuciya tace,babu komai ni wallahi ba komai ke sa ni tunani ba sai kadaici,in banda shi babu abnda ke damuna. 67) Dadi ya kama aneesa jin cewa zata cigaba da karatu,babban burinta kenan ashe ishaq yana sane bai nuna mata ba.Ta gyada kai tace,ina so nagode.Ya laliba ledat da yayi sayayya ya dauko robar ice cream ya bude yace, bude bakinki in baki ice cream.Ta rufe fuska da gyale tana murmushin kunya duk ya kamata,yasa hannu yana kokarin janye gyalen,ta sake boye fuskarta yace,aneesa ko kin manta ni mijinki ne kike jin kunya ta.Tayi shiru,yasa hannu ya amshe gyalen gaba daya ya aje sannan ya debo ice cream din yace,come on bude bakin ki. Ta bude bakin ya diba ya bata ta sha,ya sake bata sannan ya mika mata cokalin yace ta bashi shima,ta debo xata bashi hannunta sai kyarma yake yi shi abin ma sai ya bashi dariya sbda ganin yadda ta rude,lallai wannan yarinyar danya ce bata san halin en maxa ba da sauran ta,haka ya fadi a ransa. Ya matso da fuskarsa daidai tata yace,matso na goge miki bakin ki ga ice cream nan a lebanki, ta dauka da gaske yake yi sai ta matso,caraf ya manne bakinsa da nata ya shiga lasar labbanta wai yana share mata ice cream din ne,tun tana zamewa har ta hakura ta kyale shi ya gama luguiguita ta iya son ransa,sannan ya kyaleta,shi kanshi a kasalance ya ja motar suka tafi,ita ma tana kwance a gefen cinyarsa jikinta gaba daya a mace yake,shi kanshi ya san daga shi har ita sun kai kololuwa a bukatuwa da juna babu ma kamar shi,amma bai san dalili ba sai tausayin yarinyar na rinjayarsa da kuma ganin ba zata iya masa ba irin safeena,shiyasa a kullum yake jin ba zai iya kai mata bukatarsa ba, 68) Sha daya da minti biyar daidasi suka shiga gida,a falo suka iske safeena ta zubawa kofar falon idanu,tana ganinsu ta sauke ajiyar zuciya tace,haba captain kasa na gaza barci ina nan ina tunanin ina kuka shiga daga zuwa ganin likita,na kira wayarka tana ta ringing baka dauka ba me ya faru ne? Hakika yaji ana ta kiran wayarsa amma a lokacin yana can a duniyar aneesa shiyasa ya share wayar bai ma duba ba balle yasan ko waye ya kira ashe ita ce,lallai da ta san me yake yi a lokacin kila da ya dawo ya tarar ta kusa hadiyar zuciya sbda ya san
Chapter 33 · 0% Book details