← Book details Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 51

Sashe 47

Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

MIJIN ARO 2***13 Wannan fagen ya iya gudanar da soyayyar da zai mantar da mace wani bakin cikin rayuwa. Da zai fita sallar subahi ya tasheta yace, ga ruwa can na hada miki ki gasa jikinki sai kiyi wanka kiyi sallah zanje mosque. Bayan fitarsa ta tashi amma sai bata ji ciwo irin na ranannan ba sai dai tsamin da ciwon da jikinta ke yi, shina da taa gasa jikinta da ruwan zafi sai taji garau, gajiya 2 ce ta tarar mata gata mota sannan ga wannan shi yasa abin yayi mata yawa. Ta idar da sallah tana karanta alkurani ya shigo ya zauna gefenta yana sauraron kira'arta mai dadi tare da fidda tajweed irin ta malaminsu na islamiyya mal. Abdullah Abba. Har ta kai karshen suratul kahf tayi addu'ointa suka shafa tare ta juyo ta gaishe shi yace, ai na manta ina tare da malama ne a gida na, gaskiyya na dora miki alhakin karatun alkuranin yara, ko da yake suhail ya gaya min kina koya musu, yanzu to ya zaki da cigaban karatunki na addini gashi kin baro zaria tushen ilimi. Tace kasan malamin namu ya dawo nan Abuja da aiki dana zance ka neme shi don naji ya bude gurin koyarwa kaga sai ka saka mu ni da Aunty idan ma akwai na yara sai maida su can. Yace good kin kawao shawara mai kyau. Ya kai hannu ya mammatsa jikinta yace ya jikin ya daina ciwo ko? Ta shagwabe fuska tace ya dan daina, amma yanayi, yayi dariya yace wannan wace irin amsa ce, ya daina amma yanayi? Na dauka ya daina oya zo muje ki kwanta kiyi isashen bacci tunda jiya kin hana mu bacci, ashe haka kike? Ta dan harare shi tace, don dai kada in yi maka korafi ne ka canza salon maganat da zanyi, da nasan haka kake da nayi zama na gidan Hajiya yadda idan ka dameni zan kai mata kara ko in gudu gurinta, yanzun fa ko nayi mata korafi kana damuna hkr zata bani, yace to in bata baki hkr ba ya zatayi da danta dole ta baki hkr ki ba dantaa abinda yake so, tayi sauri ta mike ta barshi a gurin ta haye gado taja bargo. Ya biyita yana cewa au har yanzun da sauran kunyar ne, bari nazo in cire rahiwar. Ya haye gadon ya rungumeta a jikinsa ta soma zamewa tana bashi hkr cikin kuka shagwaba, don Allah kayi hkr wlh duk jikina ciwo yakeyi, kasan fa na wwahala da yawa so kake inkasa tashi da safe? Yace to menen idan kin kasa tashi, ba kinyi bautar aure bane, bata son tayi msa gardama saboda kada yaga gazawarta don ance hakan na dakusar da sha'awar mace ga mijinta yawan korafi shi yasa tace, kwarai bautar aure nakeyi, Allah ya bani lada tare da kai. Ya ji dadin kalamanta sosai. Baccci da bai barta tayi kenan ba aka da da dasa wata sabuwar rayuwar mai kunshe da darusa. Jin da yayi Aneesa ba zata taba gundurarsa ba shi yasa yayi wanka ya fice a gidan, amma sai da gaya mata zai fita ta shirya masa bkr fast kafin ya dawo nan da karfe 10am. A cikin wanna satin Ishaq ya soma musu shirye2 tafiya honey moon tunda Aneesa bata taba zuwa wata kasa ba, ta dai taba shiga jirgi sau biyu da suka zo abuja ita da hajiya da zasu koma yaka su a jirgi suka sauka a kd suka kwana gidan Inna binta( kanwar hajiya). Safeena na gani suka abar kasar zuwa kasar england sai da sukayi sati2 suna cin amarcinsu sannan suka dawo a tym en kuma ishaq ya dukufa nemawa Aneesa jami'ar abuja da yake ta zana Jamb taci tayi post ume ma duka ta sami abinda ake so shi yasa babu wata wahala ta sami admission. Duk da a wannan tym din aneesa na dauke da ciki, ita da Ishaq babu wanda ya sani har sai da cikin ya shiga wata4, watarana ita ke da girki cikin dare ta farka da matsanancin zazzabi da ciwon kai, Ishaq ya shiga rudani sosai saboda kukan da Aneesa ke masa, tun da yayo sallah subahi ya dawo ya taya ta tayi wanka suka nufi asibiti. Duk wasu gwaje3 anyi mata har da hoto suka gano tana dauke da typhoid sai abin farin ciki tana dauke da ciki wata 4, kuma a scannin en 2 ke kwance a mahaifar Aneesa. Jin haka Aneesa tayi abu 2 ya kunsar mata farincikin da tsoron wai itace zata haifi en 2 shi kam babu komai bayyane a fuskarsa sai zallan farin ciki, tun tana kwance a gadon scannin din da yake agabansa akayi, ya zagayi gefen kunneta ya rada mata, kin yarda ni dan baiwa ne ko? To ki daga nxt en 3 ne. Kawai sai yaga hawaye na ziraro mata ya rage tsohonsa ya sumbaci labbanta yace, to meye na abin kuka bayan ranat haihuwar ma tare zamuyi nakudar ki haifi daya ni in haifo dayan. Zancensa na karshe ya bata dariya tayi murmushi shima yayi dama so yake yaga afara'arta. Tun a hanya da zasu dawo gida yake lallashinta akan ta kwanta da hankalinta, bayan ance ma haihuwar ba wani wahala, kila ma kina bacci kawai zaki farka kiga kin haifo yaran, ni ne ma zan tasheki.... Hahahahaha Tayita dariya har suka iso gida. Safeena na gidan da yake ba aiki ranar tun a falon ya soma fesa mata, kanwarki fah ciki gareta anyi mata scannin yace en 2 ne shine tun acan take ta kuka, na gaya mata haihuwar ba wani wuya ko? Safeena ta rasa bakin magana, ita ga abin bakin ciki ya gaya mata amma shi murna kawai yakeyi za'a haifa masa en 2, abinmda bata tabaa zata ba, ita gashi ta juyar da tata mahaifar yanzun ya zatayi kenan? Gaskiyya bazata yarda tana kallo wata tazo ta dinga haihuwa da Ishaq ba, ta dau alwashin sai dai a haifo masa da a titi indai yana da rabon sake haihuwa, amma ba dai cikin gidansa ba. Kuma boka yayi mata alkawarin turo aljani ya sace mahaifar, toh amma sai gashi wai tana dauke da cikin en biyu a mahaifar tata. Ta dawo daga tunanin da ta lula, ta dubi Aneesa tace ki daina tada hankalinki, babu wata wahala haihuwarsu gashi kin sami cikin da babu laulayi ai kinyi sa'a. Haka dai ita da Ishaq sukayi ta karfafa mata gwiuwa. Safeena ta bar falon taje daki ta kira aminiyarta Hajiya Nuratu awaya ta gaya mata abin bakincikin da ya faru a gidansu, wai Aneesa na dauke da cikin en 2. Haj. Nuratu ta dafe kirji tace, what??? Ciki? Amma boka bai kyauta mana ba da ya bari bai yi mana aikin nan ba har yarinyar nan tayi ciki, to amma babu matsala ki shirya ki zo mu tafi gurinsa. Safeeena karya tayiwa Ishaq wai za suje gaida Hajiya Nuratu bata da lfy ita da yaranta, bai yi musu ba yace ya barta, saboda yasan kawancenta da haj. Nuratu. Ta shirya yaran tsaf sai Suhail yace shi agida zai zauna tace, za'a kaiku gurin wasa ne fa ku da su saleem ku sha icecream ( karamin yaron haj. Nuratu ne sa'an suhail din). Jin tace haka yasa ya soma murnar tafiyar. A niyyarta ta bar yaran gidan Haj. Nuratu har su je su dawo sai tayi rashin sa'a kaf yaran sun tafi yini gidan iyayen mijin Hajiyan, mai aikinta kuma tayi tafiya shi yasa ma ta aka kai yaran gidan kakaninsu. Dole da su suhail suka tafi birnin gwarin. Sunje lfy a mota suka bar yaran don tasan halin suhail duk abin da ya gani sai ya gayawa daddynsa. Boka ya bata maganin da zata ba Aneesa a abinsa, in dai ta sha to cikin zai zube kuma ita da haihuwa har abada (kunji fah tamkar shine mai bayarwar). Da farin ciki suka baro dajin nan. Suna ta murna duk safeena ta kosa su iso gida ta aiwatar da abin da boka ya bata. Kana nakaa Allah na nasa, sun baro birnin gwarin sosai a dai2 wani kauye sukayi mummunan Hatsari. Shi dai Ishaq yana gida suna falo da Aneesa, jami'an kula da lfyar hanya sune suka kira shi a waya saboda a motar sun sami abubuwa da suka jibance shi suka sanar masa cewa iyalinsa sun sami hatsari, amma gasu nan asibitin Abuja. A gigice ya dinga amsa wayar har aneesa ta gane me ake gaya masa. Yayi yai ta zauna a gida yaje ya gansu takunna amma taki yarda ta zauna, dole tare suka tafi. Ahanya Ishaq mamaki ya dinga yi me ya kai safeena haanyar birnin gwari har ta kwasar masa yara, ya sami ganinsu yusra da yasmin a gurin safeena..... 125)Yusra da yasmin na gurin safeena basu ji wani ciwo ba sai kujewa da sukai a hannu da fusja...amma suhail ne ya samu rauni sosai yana emergency shi da haj Nuratu...safeena na jin shigowar ishaq akin da aka bata gado ta rufe idonta kamar tana bacci don bama ta son hada ido da mijin nata saboda haintarsa da tayi. Ishaq ya bar aneesa anan ya tafi wajen likita dan yaji karin bayani akan dan sa bai ma bi ta kan wata haj nuratu ba ita ma mijinta ya iso yana ta sunturi a energncy din sai bayan sallar ishai ne likitan ya fito yana yarfe zufa yana neman mahaifin suhail a lokacin yana tsaye a kofar dakin dan ya kasa zama ita kuma aneesa na gefensa ta durkusa saboda tace jiri take ji likitan ya mukawa ishaq hannu suka gaisa yace am sorry to say munyi iyaka bakin kokarinmu amma Allah bai bamu nasaraba yaron ya ansa kiran ubangiji ishaq salati ya saka aneesa kuma dafe kirji tayi tana salati ishaq a rude ya tallabo ta sai gata ta zube jikinsa a sume ya firgice ya rike likitan pls doctr ka taimakeni tana da ciki gashi ta firgita kar nayi asarar cikin nan likitan ya kwalawa nurses kira yace zuzo da gadon daukan.mara lafia da gudu suka zo da gado suna daga ta zasu dorata jini ya balle yana zuba...ishaq ya sake rikicewa kaga abinda nakr gudu yanbiyu ne a cikinta doctor yace kaga suma zan rasa su kuma shima yaron nan
Chapter 47 · 0% Book details