← Book details Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 51

Sashe 25

Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dai ji abinda na gaya miki namiji wayau gare shi da dabara, fiye da tunaninki. Kunya duk tabi ta kama Aneesa har Hajiya ta bar kicin din bata bari sun sahada ido ba, wato uwar har tagano me danta ke nufi akanta, ita kanta ta lura tsaba manufarsa, so yakeyi ya sami biyan bukatarsa ya tsallake ya barta sai kuma ta ganshi, tunda yanzun matarsa bata barin ya zo zaria kamar da, tunda zancen auren nan ya bullo ta murda kambunta. 20) A falo suka same shi yana kwance bisa doguwar kujera ya rufe fuskarsa da Jarida da alamun barci yakeyi. Ajiye tiren da sukayi bisa teburin da ke kusa da shi, shine ya farkar da shi ya dube su yace, sannunku banji shigowarki ba, bacci nakeji sosai. Ya tashi ya zauna sadiya ta juya zata fita yace, ina zaki sadiya? Tace Hajiya tace in zo in karbo maka wani abin yanzun zan dawo. Ta fita dama haka yake so. Ya na fitowa ya ci abinda ta soya masa har nikakkiyar hanta. Da albasa da tarugu a suyar dankalin. Ya sha kunan wanda ta zuba madarar gari yayi kauri, ya dinga yaba mata har ya gama. Tana tattare kayan ne ya riko hannunta yace, muga kunshin nan. Gaskiyya yayi kyau kawo kinga na kafar. Ji tayi duk ya takurata da ya rike mata hannu, ya duba kafar yace, Haka kike da tsoro sai kace zaki ne ya rike miki hannun, kinji yadda jikinki ke rawa kuwa? Don Allah ki kwantar da hankalinki kada zuciyarki ta buga akan tsorona, ba gutsurar naman jikinki zanyi ba. Da kyar ta saki ranta suka cigaba da hira, shine ya dinga janta da zance ya tabo nan ya tabo can, shi dai a dole ta saki jiki da shi bai san tsorace take ba da shi ba. Hajiyarsa ta tsoratar da ita wayonsa kada ya lallabata ya gudu ya barta. Duk wata hikima da zaiyi mata yayi amma ko jikinta da nashi taki yarda ya hadu sboda tasirin nasihar Hajiya. Ta san kuma gaskiyya ta gaya mata, ba zata gaya mata abinda zai cuceta ba, tunda duk tsiya tafi son Ishaq a kanta, ko da yake Hajiya a kullum dan waninta shine nata, har gara Ishq shi tana dan ji da shi, tunda shine karamin danta da yayi saura, kannensa uku duk mutuwa sukayi, shiyasa shine auta. 21) Anan ya barta yace tayi sallar la'asar shi kuma yaje mosque yayi tasa ya dawo. Suka cigaba da hira suna kallon dish wani film akeyi a action horrow film ne, duk sai Aneesa ta tsorace, yayi hikma ya dawo kusa da ita ya rabata da jikin shi, tayi lamo a kirjinsa ya soma wasa da gashin kanta, wanda bata taba sa masa mai ba sai ranar bikinta, shi yasa yayi tsayi yayi kyau sosai, ga mayuka masu kamshi da ta shafa ta gyara shi, har sai da ya zame dan kwalinta yaci gaba da wasa da gashin, can rada mata a kunne, tunda kina jin tsoro kawai ki kwanta nan dan ko kinje wannan dodon zaki dinga gani abaccinki, nan ko muna tare ba zaki ganshi ba. Jin ya ambaci kwana yasa ta dawo hayyacinta tsoron ya saketa, har ta gano sunyi nisa a wani yanayi ita da shi, sai tayi saurin mikewa tana daura dankwalinta tace, kaga gari ya soma duhu ana ta kiran magriba bari in shiga gida, hira dai ai na tayaka, sai da safe kuma idan ka shigo. Yace au irin bankwanan da zakiyi mikin a kenan a tsorace, ni bari in gaya miki wanda zanyi miki, manneta yayi da bango ya lalubi bakinta cikin nasa, sai da yayi nisa da ita wata duniyar sannan ya saketa, yana murmushin yaci nasara akanta, ta zuba masa idanunta da suka canza launi ta kasa furta ko kalma daya, kawai sai yaga hawaye yana ziraro mata akunci, ya sa babban ya tsansa ya share mata yace, meye kuma na kuka, so kike idan Hajiya taga idanunki ki tace nayi miki wani abu, naga tana kaf2 dake bansan dalili ba. Aneesa gaba kawai tayi ya biyo bayanta har sai da ya kawota kofar da tahada gurinsa da gidan Hajiya sannan ya koma dakinsa. A gaggauce yayo wanka ya wauce mosque, cike da nishadi, ko ba komai dai wani abu da yake addabarsa game da yarinyar nan yau ya dakushe radadinsa da ke taso masa, ko ya koma Abuja kewarta kadan ne zata dameshi. Tym din da ya shigo da safe har tayi wanka, ta saka under wears farare zata juyo ta dauki skirt dinta na atampa data aje kan gado, kawai sai ta ganshi ya shigo tare da sallama, tayi kokarin kwatar skirt din da ya dauke ta kasa kawai sai ta durkushe ta soma kuka, hawaye yana ta fita, kawai sai ya miko mata abinta yace lallai yarinyar nan shagwabarki ta tym din kuruciya ta dawo, yanzu meye abin kuka, so kike Hajiya ta ganki kina kuka tace ina matsa miki ko? 22) Ni mamaki kike bani ni mijinki kike jin kunya amma bakijin kunyar Hajiya ita da ta zama surukarki, ni me nayi miki ne? Bata ce masa komai ba sai da ta gama saka idanunsa tsaf akanta yana kallonta, sannan tace, ni Hajiya ba surukata bace uwa tace don ko haihuwa nayi babu wanda zaiyi min wanka sai ita. Matsowa kusa da ita yayi yace iyen ba ashe zaki haihu? Amma shine kike tsoron miki kina gudunsa to ki shirya haihuwar en biyu kinsan ni dai gidana bibbiyu ake farawa gaki er falen2 zanso na ganki da cikin twins. Ya kai hannu yana shafar cikinta tayi saurin ture hannunsa tace, nan fa dakin Hajiya ne meye haka. Yace au na manta jiya fa turaka kika je shi yasa aka barni na sakata sosai ba ayi min korafi ba, ina jin ma fasa tafiya yau zanyi sai gobe. Ta dan harare shi tace, Allah gara ma katafi abinka don babu inda zan kuma zuwa, jiya kasa tunda na dawo sai boye kaina nayi a daki, Hajiya kanta kunyarta na dinga ji, don Allah kaje falo zanzo na same ka. Ya nemi kan carpet yayi zamansa ya kishingida a tintin yace, idan kinga na bar dakin nan to mun gama sallama ne dake ne. Hajiya tayi sallama ta shiga ta dan dubi sashin da Aneesa ta takure, ta dube shi tace Amma Ishaq ni ban san haka kake ba sai yanzun. Yayi saurin tarar ta yace Hajiya dama can kinsan ni mai kirki ne mai nayi yanzun? Tace ban san kana da son takurawa mutane ba sai yanzu, cikin kwana 2 nan duk kabi ka takura min yarinya, haka akeyi? Yace Allah Hajiya ni ba takurata fa nake ba, ita take takura kanta da ta ganni kamar dodo, alhalin ni ko farcen mutum ban iya yanka balle namansa, yau idan na tafi sai ta saki jikinta,tunda ba kwa son in zauna. Tace muna murna da zamanka, amma wannan binbinin ne nake son ka dainayi mata, takurata kakeyi kaga bata saba ba. IJIN ARO 2***3 23) Misalin 11am yana kokarin rufe jakar kayansa zai fito ya tafi yaga kiran safeena wadda tun safe yayi ta kiranta tanaki taki dagwa, ya san fushi takeyi har txt ya tura mata bata bashi amsa ba, dole ya hkr ya kyaleta shine yanzun taga dama ta kira shi, ya amsa wayar shi ya faraa gaisheta ya tambayi yara, da kyar ta amsa masa suna lfy sannan cike da tsiwa da masifa da gatsali tace yaushe kayi niyyar dawowa yara sun dameni, ko har yanzu baka gama cin amarcin bane, ka sami yarinya sweet 16 sai ka gama side sweet din nata sannan zaka dawo? Yayi murmushi ya san tsananin kishi ne ke damun safeena shi kuma bai zai biye mata ba, yanzu sai suyi battaciya yace yanzu haka jakata ta na hannuna take nima duk na kosa in zo gareku, wlh ina cikin kewar ku, amarci kuma ba'a tare ba ba ko kin yarda in fara yanzu in shanye amarcin a gidan Hajiya? Haushin maganarsa ta karshe taji wato ita zai mayar yarinyar sai tace, don Allah Ishaq kada ka maida ni diyar cikinka Yasmin ko Yusra, ni dai fatana kalaman soyayyar nan da kake gaya min kullum donb Allah kada ka taba gaya mata irinsu, ka gaya mata nata dai2 da matsayinta. Dariya ce ta kama shi na wannan irin labari na safeena. Amma sai bayi dariyar ba yace, haba! Haba!! Wannan kalaman ai sun fi karfinta don sunyi wa shekaranya girma. Ke din dai kika fi dacewa da su, ina fatan in gaya miki fiye da wadanda kika taba ji a daren yau, in dai kin shirya tarbata kamar yadda kike mini da. Tayi murmushi saboda din dama take jiran dawowarsa ta aiwatar da abubuwan da suka amsa gurin boka, ciki kuwa har da shiri na musamman tayi saduwarsu ta yau, don ta tsumu irin magungunan da ya hada mata hatta gadon baccinsu ya sha surkulle da bargon rufansu dawowarsu kawai ake jira, don kuwa ta dau damarar mantar da shi duk wata mace a duniyar nan ciki kuwa har da uwar da ta tsuguna ta haifeshi.... Wa iyazu Billah Allah ka tsare mu, kasa mu fi karfin zuciyarmu. Ya shigo falon Hajiya anan ya sameta don yayi mata sallama. Imrana yayi sallama ya shigo shine babban yaron gidan Hajiya mai kuwa da komai tun yana karami yake w Hajiya barance. Shine har gashi ya zama saurayi suna tare. Ishaq ya ce sarki fadan Hajiya ya akayi ne? Yace ranka ya dade na sa jakar da sauran kayan a motar, shehu ya gama wankewa ya goge. Akwai dama wasu dattijai ne da suke ce suna son ganinka. Yace to kace su yi hkr gani nan fitowa, sallama nakeyi da jama'ar gida. Yace to yallabai a fito lfy. Ya juya ya fita. Ishaq ya dubi Hajiya, to Hajiya nayi harama zan wuce aci gaba da mana addu'a. Tace Allah ya tsare ya kare mana ku ya bada sa'a, ya kiyaye hanya. Kayi dai kokarin ganin an sami gidan nan don Allah. Yace Insha Allah zanyi, wannan sarkin barcin ba dai ta kwanta ba? Tace, yanzu ta shiga ciki ba mamaki kwanciya tayi. Ya girgiza kai yana murmushi ya kutsa kai
Chapter 25 · 0% Book details