← Book details Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 51

Sashe 1

Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

MIJIN ARO 1**1 4) Bakin daki! shine sunan da Aneesa ta lakaba wa dakin da take takure a cikinsa tana tilawar kuka tun wayewar garin yau... a sakamakon shardadin da mahaifinta ya gindaya mata a wannan rana kafin ya fita zuwa aiki$ idan ta tuno da kalaman nasa takan sake tsinkewa da kuka saboda tsananin tausayin da takewa mahaifiyarta wanda a dalilinta ne komai ke faruwa... shin wai me mahaifiyarta tayi wa babanta ne da har baya tausayinta? shin ko tun asalai dama baya son tana ne lika masa ita akayi shine asalin. wannan wane irin zamn aure ne? ita yadda malamin islmiyarsu ya gaya musu ginshikin auratayya yace farko akawai soyayyaa da tausayi, to ita kam bata gani a gurin mahaifinta, shin meye dalili? ta tashi jiki a mace ta leka ta window ta hango mahaifiyarta a zaune a akan kujera ta tasa bahon kayan kanninta tana wankewa wanda kafin hakan wannan aikin ne da ita Aneesa ta daukarwa kanta, a ko wace safiya da ta idar da sallah subahi da shi take farawa, da ta gama shanyawa zata tafi. rijiyar kofar gidansu ta debo ruwa, in babu ruwan fanfo kenan saboda akwai fanfo gidansu. sai tabi dukkan manyan robobin xuba ruwansu ta cika, sannan ta shiga kitchen ta hada musu abin karyawa in koko ne ta dama ta rufe, idan tea ne ta dafa ruwan zafi ta zua flasks. daga baya tayi sharar tsakar gidan tsa da dakin mama, idan kuma maman taga aneesa tayi leetin zuwa sch sai tace bar wasu ayyunkan tayi ita. wannan kauna da tausayi da ke tsakanin uwa da 'yarta shine mahaifin baya so, shi acewarsa wannan ba aikin yarinya mai karancin shekaru kamar Aanasa bane wadda ko shekaru sha biyar bata gama cikawa ba. a safiyar yau din ne ya ya kirata ita da maman.... 5) Fatima me nagaya miki game da ayyukan da kike jibgama Aneesa a gidan nan? ina ce na hana? idanunsa kyar a kan mahaifiyar Aneesa. Ta risinar da kai kasa tace, yadda kace in daina sa ta na daina kuma ko dama bani ke sata ba, itace take taimka mini, wni tym din kafin in fito zanga ta kama ayyukan, ko dazu da ka dawo masallaci ka iske ta soma wanki ban sata ba, amma kayi hkr ba za asake ba. ya soma sababi, na dai gaya miki ba zai iwu ba Aneesa yace kuma ke kika haifeta, ba baiwa ba ce balle ace duk ayyukan gidan ita ce mai yinsa dubeta yarinya fara kyakkyawa mai garin jiki amma duk ta kekashe ta bushe saboda aikin wahala, tun bata yi aure ba ta iya ayyukan iyaye mata ta horu da wahala. idan kika haihu tamkar ita kika haifawa itace koman su bacci kawai ke hada ki da 'ya'yan, da mai saurin Nonuwa ce da yanxun sun xube sabida goyo, to wlh sam! ba zaiyuwa ba, na kashe wannan ayyukan kwata2. ya juya yana hci idanunsa akan Aneesa yace, ke kuma mai kunnen kashi. idan na hanaki aikin wahala ba kya bari ke a dole ga mai tausayin uwa to zauna anakasa miki rayuwa ki tun baki je gidan naki mijinba, in har zaki cigaba da rayuwar wahala to ba yadda z aayi namiji ya ganki yayi sha'awar ya so ki balle har ya aure ki. jiya duk an gaya min aikin da kika yi bayan dawowar ki makaranta, saboda haka yau zanyi maganinki ba zaki makarantar ba balle ki dawo kiyi bauta kulleki zanyi acan dakin har sai na dawo zan bude ki. ta soma zubda hawaye shar2 tace, Abba don Allah kayi hkr idan ta haihu ta sami lfy sai in daina tayata ayyukan.. Ya nunata fa yatsa, ke! ni kike gayawa ya kamata? to mu zuba ni da ke zanga wanda yasan ya kamata. shine musabbin da ya rufeta a daki yau abinci ma yace ta window za a bata. tana tsaye a window tana kallon maman tasu dake dauke da ciki wata biyar duk jinkinta a kumbere yake. 6) musamman kafafunta a dalilin hawan jinin da likitar dake mata awon ciki tace ya kamata. Aneesa tace mama ki bar wanki komai dare idan Abba ya dawo ya bude ni zanyi miki. Tayi murumshin karfin hali tace. ki kwantar da hankalinki nasan ke mai tasausayi ce da biyayya to kiyi wa mahiafinki biyayya. insha Allahu ba zaki tabe ba, ni kuma zan cigaba da bautar aure duk da larur da ta sameni ba zan ga za ba, in ma hakan ne zaiyi ajalina to alhmdulillah, ina murna da hakan. ranar. Aneesa wuni tayi kuka saboda tana tsaye a window tana kallon Mahaifiyarta yadda ayyuka sukayi mata yawa, ga wanki ga dora girkin rana gashi ice danye saboda tym din damina ne, duk tayi wujiga2 idonta yayi jazur saboda hura wuta ga hayaki. ko dama ta kammala abinci ta kawowa Aneesa kasa ci tayi duk da uwar yunwar da takeji tunda ko kokonta na safe bata sha ba, maman tayi2 ta sha taki, ga abincin rana ma taki ci. sai karfe uku da wani abu baban Aneesa ya dawo sai tym din ya bude ta ya bita da kallo yace. dbek harkiy y farinki ya da sabodaa. ni a rana ba kina aikin. wahalaa ita dai tayi shiru tayi saboda wahalar da yake kira ita a duniya bata ganta ba. saboda a duniya babu abinda da zai yiwa uwa ya biyata irin wahalat dawainyarsa da ta sha tun yana ciki har zuwa nakuwadr haihuwarsa da uwa uba rainonsa. musamman ma diya mace da tarbiyarta ke da wuya, tunda ko bacci takeyi sa kabi. kana gyara mata kwanciya. ya sake duban Aneesa yace, dauko abincin ki muje dakina ki ci don na lura baki ci ba. batayi musu ba don ta san halin babanta dole tayi yadda yace, ta bi bayansa da kwanon abincin, yaceoyazn ki inye abindan so nake ki maida jikinki kyanki ya dawo. haka ta dinga cusa abincin nan tamkar tana cin magani. kwana 2 yrufnesa ai, a kwana n 3 ne ya bar dakin abude yayi mata gargadi da kakkausar murya cewasaura ya dawo yaji tayi aikin da zai maida ta tsohuwa tunda kuruciyarta.. 7). Ita kam abin mamaki yake bata na yadda uba ke son raba 'ya da uwa da karfi da yaji abin da ba zai yiwu ba kenan. saboda ko hira yaki jinin yaga tana yi da Maman sai ya ja Uban tsaki yace, ke dai Fatima Allah ya kyauta miki baki da abokiyar hira ko shawara sai diyarki diyarma ta fari. wai nan kuma kunyarta kike ji har ba kya fadin sunanta$ sai dai kawai tayi murmushi abinka ga hakuarriya ba ita maida masa martani a matsayinsa na mijinta na lalle kuma uban yaranta. Yana tafiya aiki aranar Aneesa tayi saurin fitowa daga bakin dakin da lakabawa suna ta saka hannu ta soma wanke kayan kannenta da suka cire da safe . mama tayi saurin fitowa daga daki tana cewa a'a rufa min asiri ki koma ki zauna ki huta yadda abbanki yake so kada ya dawo kan tsautsauyi ya ganki yace ni na saki. mama ki kyale ni kawai ba zan iya ganinki yace ni na sa ki. mama ki kyale ni kawai ba zan iya ganinki kina wahala ke kadai bani ina zaune to meye amfanin haihuwata da kika yi? ai dole ne da ya jikan mahaifansa, ki kyale Abba da akidarsa ni ban san manufarsa ba ni dai Allah ya sani zanyi masa biyayya in dai bata sabon Allah bace, Amma ba zan iya yi masa biyayya ina kallonki kina wahala ba, ai ba haka addini ma yace ba. Dole mai Mama ta kyale ta taci gaba da wankin ta janyo kujera 'yar tsugune ta zauna tana wankewa tana daurayewa suna hira jefi2. can tace Mama wannan kumburin naki sai dada yawa yakeyi, babu wani magani da za su baki ne agurin awo ya ragu? tayi dan murmushi tace, sunce hawan jini ne ai naga ya miki, sun kuma bani takarda inyi hoto. amma naba Abbanku ya ki maida hankali ayi hoton, tunda bai bani kudin ba, kinsan ni kuma bani da kudi ahannuna, sai in wata ya kare anyi albashi na samu basukan da nake bi na atamfofinda na baya zanj in karbo naje hoton. Aneesa tace to Mama ko gurin Umman tudun wada zanje in amso kudin hoton tunda na san idan nagaya mata abinda za ayi da kudin za ta bayar. ta numfasa.. HAUSA Novels BOOK MIJIN ARO 1**2 8) Karama kenan ( Sunan da take kiran Aneesa da shi kenan a dalilin 'yar fari ce) ni fa koda suke iyayena bana son kullun in yi ta dora musu wwahalar da ba dolensu bane, duk da dai iyaye za su iyayin dawainiya da larurar ciki ce bata shafesu ba, ki bari zan nemi rance a gurin Hajiya. aneesa tace ita ma hajiyan ko kin amsa aka maida mata ba zata amsa ba in dai taji abinda zakiyi da kudin. tace ai ba zan gaya mata ba, ai kokari da taimakon da Hajiya keyi a akaina da ku ko ita takawo ni duniyasai haka. Allah dai ya biyata da gidan aljannah. nace ameen. tana tsaye tana shanya kayan kwatsam sai ganin Abbansu ya shig gidan. ya tsaya yana mata kallon mamaki yace, lallai Aneesa wuyanki ya isa yanka tunda har zan hanaki abu kiki hanuwa, yau kan zaki gane kuskurenki. wuce ki koma dakin tare da zulumin abinda zai biyo baya. ya juya kan Fatima da sababin fadansa inda yake shiga ba nan yake fita ba ita dai shiru tayi tunda ta san halinsa, idan ta bashi hkr ba hkra zaiyi ba, idan kuma tayi masa shirun nan bata tsira ba cewa yake ta maida shi mahaukaci wato yayi tayi kenan. wata lafiyayyar bulala ya dauko daga dakinsa ya shiga dakin da Aneesa take ya shiga lallasa mata jiki tun tana ihu har ta gaza babu mai cetonta, da yake kanneta sun dawo sch sai suka kama kuka su ma, dan babbansu ne ya sulale ya nufi sassan wan babansu ya gaya masa. Allah sa baban can sassan na nan ya garzayo a fusace ya shigo sassan ya tsaya a bakin kofar dakin yace, wlh Ali idan ka sake bugun yarinyar nan sai ranka
Chapter 1 · 0% Book details