← Book details Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 95

Sashe 86

Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daqyar Haj Zainab ta iya bude Baki tana kallon Amal din jiki a matuqar sanyaye ba qarfi murya ma a sanyaye tace,

"Amal ciki ne ajikinki??

Kowa tsit yayi Yana jiran amsar Amal din Banda AQEEL dayace Dr tayo ta Dan Basu guri tana fita ya dawo da kallonsa kan Mamin Kai tsaye cikin nutsuwa yace,

"Mami ki.....daga Masa hannu tayi ta dakatar dashi fuskarta ha walwala ko kadan.

Amal din takuma kalla Kai tsaye tace,

"Ciki ne ajikinki???

Sauke Kai Amal tayi hawaye masu tsananin zafi suna gangaro mata jikinta na wani irin sanyi da mutuwa sbd Bata taba zatan alokaci daya kowa zai gane halinda take cikiba.

AQEEL ne yasake kallon Mamin Kai tsaye ya amsa Mata tambayarta da cewa eh cikine Kuma bayason a daga hankali akai tunda ba laifi bane Kuma sosai yakeson abinsa adduarsu kawai yake buqata ba wani tone tone da tiqewaba....

Amsarsa tasa zuciyar haj Maryamah data umma harma data Zainab din bugawa da qarfi

Haj Maryamah take ta dafe kirjinta dake gazawa tana kallonsa tace,

"AQEEL jinina a jikin Yar Zainab???

Kallon cikin na Amal tayi take idanuwanta suka fara dishi dishi tsaban tashin hankali da baqin ciki da wani irin zafi Mai ciwo da nauyi.

Umma kuwa kuka ta fasa tana kallon Zainab tana binta da kalmar ta cucesu taci amanarsu sai Allah ya saka musu.

Haj Zainab datayi mutuwar tsaye itama sbd takaicin Amal da mamakin tareda kasa yarda da wannan abin dake faruwa sbd wannan cikin Bai nuna na wannan tafiyar bane

Wannan cikin ya Jima da samuwa,

Itama wasu zafafan hawayen takaicine suka gangaro Mata ta share tareda juyawa batareda tace komaiba tabar dakin.

Anty Fareedah da Siddi kuwa gurin Amal data fashe dakuka Mai qarfi sukayi suna rarrashinta.

Haj Maryamah ma kuwa Dole AQEEL ya tarota sbd neman zubewa datakeyi da sauri aka Kira Dr tayo aka Kasheta zuwa wani dakin aka kwantar Ana bude Mata fanka da AC lokaci daya sbd wani irin zufa datake fesowa tako Ina ga numfashinta na neman toshewa sbd hayewar jini.

Sabuwar damuwa AQEEL yashiga ganin halinda mahaifiyarsa tashiga din Dan Haka Dole yabar Amal su Anty Fareedah Suka tafi da ita gida sai shi yaji da Haj Maryamah din da umman Cameroon dataketa kuka tana debewa Zainab da zuriarta sbd duk suka hadu da zainab ko zuriarta sai sun dangana da gadon asibiti ko ita ko yarta,

Wannan masifar tayi musu yawa,

Wace masifa tafi ace yau jininsu je ajikin Yar Zainab,

Zainab dai ta tabbata itace muguwar qaddararsu.

Kukan datakeyi da tsufanta yasa AQEEL yace Al-Amin ya maidata gida sbd sosai ta Shiga nata tashin hankalin Amma dayake ita duk tsananin tashin hankalin yanada wuya ta samu attack ko somewa Dan zuciyarta nada tauri.

Haj Zainab ma Bata tsaya jiran kowaba ta bar asibitin da motar dasuka zo da ita Dan batasan me zata tsayaba Kuma tayi,

Zafi goma da goma ne,

Maganganu marasa Dadi da tsinuwa umma ke jifanta da 'yarta dasu akan wannan lamarin da itama 'yar tata ta rufeta sai alokacin take sani tsabar sun taru itada AQEEL din sun Raina Mata wayo sun maidata Yar Iska.

Tana barin asibitin uncle Lulu ya dauko su Amal din a tasa motar Suka nufo gida har lokacin kuka takeyi ahankali jikinta na sanyi da yanayin yanda mommy ta dauki fushi Mai tsanani.

Daga Anty Fareedah har siddi Babu Wanda yayi Mata wata maganar cikin sbd kada su qara Mata damuwa rarrashinta kawai sukeyi musamman Siddi da wani bangaren na zuciyarta ke tsananin farin ciki da samuwar cikin duk da tana cikin mamaki Mai girma itama na yaushe aka samu cikin bayan dukkaninsu sunsan Babu ko kallon jituwa a tsakanin Amal din da AQEEL ASAD.

Uncle Lulu dai Bai iya cewa komaiba Dan kuwa mamakinsa qalilan ne sbd Daman yayi zargin zargin hakan aduk lokacinda yake haduwa da motar AQEEL ASAD a anguwarsu tunda safe idan yafita jogging,

Da farko Bai kawo AQEEL din bane Saida ya ringa haduwa da motar akai akai a layinsu saiya tabbatarda shi dinne Amma Bai tabbatarda gidansu yake zuwaba da sassafiyar.

To idan Hakan ne yanzu da cikin ya bulla badai a cikin gidan aka samu cikinba.

Suna Isa gida uncle Lulu ne ya saka Amal din gaba da kansa sbd Hana duk wata rigima da fadan da zainab zatayi dan shi kansa kunyar ayita maimaita zancen cikin yakeyi Dan abune dayazo a bazata gaskia.

Tunda aikin Gama ya Gama Dole suyi hakuri su zubawa sarautar Allah Ido.

Suna Shiga palon Amal taja gefe daya ta rakube ta tsaya sbd mommy dake zaune a palon na kasa tana Hana kanta fushi sbd tsananin zafi da ciwon abin datake ji,

Tayaya Amal zatayi ciki tana zaune gida batareda ankai karshen matsaloli anyi tarewaba,

Yaushe ma aka samu cikin?

A Ina aka samesa?

Tsawon wane lokaci cikin yake?

Me take tinani lokacinda ta bari ta dauki ciki,tana tinanin su umma zasu yarda su karbi cikin ne??

Wani sabuwar rigimar ce kawai ta debowa kanta ta debo Mata gashinan tun yanzu umma na debe deben albarkar data saba yimata.

Guri dukkaninsu Suka nema Suka zauna Banda Amal data kasa zama ta tsaya a gefe da ciki tsuru.

Cikin Haj Zainab ta qurawa Ido zuciyarta na nauyi tareda wani irin kunci da baqin cikin hada zuriar da zatayi dasu umma Rana tsaka Babu zato Babu tsammani.

Ita kanta har ga Allah batason hada iri dasu kaman yanda tasan sunfi son balai Akan su hada iri da ita,

Meyasa AQEEL zai Mata Haka Bayan yasan kwata kwata harda tsoron wannan dalilin yasa taqi yarda da tarewar Amal din tun lokacinda aka daura auren.

Meyasa zai Mata Haka?

Uncle Lulu ne yayita Bata hakuri akan daukan kaddarar cikin.

Cikin takaici da kunyar yanda Suka samu kebewa aka samu cikin ta kalli Amal a qule tace,

"Bazaki bude Baki ki gayan cikine ajikintaba kokuwa???

Sanyi jikin Amal yayi tunda Babu tsira Babu dabara saita daga Kai ahankali wasu hawayen nakuma gangaro Mata.

"Wata nawa?" Mommy tasake tambaya bacin ranta da baqin cikinta na qaruwa.

Kasa magana Amal tayi dan bazata iya bude Baki ta fadaba kunyar tariga tayi Mata yawanda fada ma sake cusawa Kai kunya da damuwa ne.

A tsawace mommy tasake tambayar wata nawa ne cikin..

Anty Fareedah ce data karba takardar scanning din Dr tayo lokacinda zasu taho ta basu

Batama budeba sai alokacin ta bude tana cewa,

"Ga takardar scanning din bari a duba.

Budewa tayi tana karantawa taga cikin Kam Yana wata uku cikin koshin lafiyarsa.

Karantowa mommyn tayi

Mommyn tasake yin shiru tana rasa abin fada.

Duk barikinsu da budewar idonsu Allah yasani Bata taba shaawar yayanta su samu ciki tun suna gidaba Koda kuwa na aurene.

Tana Nan tana lissafin Shiri da gyaran da zatayiwa 'yarta ayi bikin alfarma duniya ta sheda ta aurar da sauran dayar 'yarta kaman yanda akai komai na alfarma a auren Siddi na farko Dana biyun Amma Ba wannan Damar itada AQEEL sun wargaza komai da rashin Hakurinsu Wanda batama buqatan sanin yanda sukai abubuwansu.

Amma babban takaicin da mamakin shine Rena Mata wayon da Amal tayi Dan tasan AQEEL tsaf idan tashine bazai boyewa kowa komaiba.

Tana tinanin ko Gama sanin juna basuyiba bare afara Tunanin tarewar Ashe itace Yar wahalar datake tinaninta ita kadai.

Kasa wata magana tayi sai Uncle ne daketa tausasa maganar sbd yanda Amal ke kuka da yanda tashiga wani irin kunya da damuwa sosai.

Miqewa Mommyn tayi kawai ta haye sama ta shige dakinta ta rufe idanuwanta na sauyawa sbd shikenan AQEEL yayi musu daurinda haukarsu su dukan bazata warware alaqarba da ko ita duk da tana tsananin son jika bataso yazo a wannan hanyarba Kuma duk yanda bataso dinba bazata taba yarda ayiwa yarta abortion ba Koda su umma zasu sheganta cikin ne bazaa taba Mata yartaba Amma Kam wlh daga AQEEL din har Amal sunci Amanar yardar datayi musu Dan taji zafin wannan abin sosai,bakuma komai ne yayi Mata zafinba kaman yanda Amal ta boye Mata da ciki ajikinta har tsawon wata uku sai takejin kanta kaman uwar data Gaza da tarbiyar yayanta tunda har akai ciki a gidanta tana sake da Baki Bata saniba.

Siddi ce taja Amal ta rakata har dakinta da Bilkisu tagama gyarawa sbd sanin yau zasu dawo din.

Suna shiga dakin Siddi ta Dan rungumeta ta sake rarrashinta tareda qarfafa Mata gwiwa da nuna farin cikinta sosai akan samuwar cikin tinda ai abin rabone gashinan ita tana nema takasa samu Allah Bai nufaba.

Bayan fitar siddi ruwa Mai Dan sanyi Bilkisu ta kawo Mata tana Mata sannu dan duk abinda aketa yiwa fada a palon tanaji Kuma itama taga cikin itama Kam gaskia tayiwa Amal din murnar samun cikin sbd harga Allah AQEEL ASAD mutumin arzikine.

Kasa Shan ruwan tai ta zauna bakin gado tareda rafka wani irin tagumi tana Shiga tinanin yanda nasa familyn zasu tinkari al'amarin.

*****Umma Al-Amin na Isa harabar gidan Bilkees na fitowa daga sashenta tareda mufeeda suna cikin nishadi da walwala tareda kwanciyar hankali sun samu rayuwarsu yanda sukeso.

Key ne a hannun mufeeda na motar da zasu fita da ita

Suna ganin umman Cameroon Al-Amin na rikota tana fitowa mota duk a yamutse take cikin baqin ciki da tashin hankalin abinda Allah ya hukunta musu.

Mufeeda Yi tayi kaman Bata lura da umman da a keta faman kamowaba ta Isa mota tashige tana cewa rigimar tsohuwar Nan tayi yawa,yanzu Haka wata masifar suka sake janyowa kansu.

Bilkees kuwa cikin kirsa ta nufi umma tana cewa,

"Lafiya kuwa?

Meya sameta?

Cikin motar take sake kalla tana cewa leqawa tace,

"Ina umma?

Ko hawan jinin ya tashi ne?

A kufule da tsananin takaicinta umman ta kalleta tana debewa rayuwar datakeyi a garin Lagos albarka tana cewa,

"Wlh Bilkisu da Aurenki gwara Babu,

Son abin duniyarki yasa bakya ganin komai sai rayuwar qarya gashinan kin ja mana hada iri da mugun abu,

Duk da kema wlh mugun abun ce hada iri dake ko masifa da asara gashinan yarki tana ganina cikin wannan halin tadauke Ido ta shige mota,

Tunda muka hada iri dake ai hada iri da Idon Nera shima ba komai bane tunda dukanku masifar ce.......
Chapter 86 · 0% Book details