← Book details Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 95

Sashe 7

Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon Anty Maryamah tayi kafin ta Dan girgixa Kai ahankali.

Karbo jaririn yayi ya miqa Mata Yana cewa"

Gashi kema ki saka Masa albarka Tunda 'dan ki ne kema.

Karban babyn tayi hannuwanta na Dan rawa ta matso dashi jikinta ahankali ta Kama da kyau Tana kallon fuskarsa cikin wata irin kauna da kulawa....

Kaunarsa ta sanyata murmushinda tun rasuwar mahaifinta batai irinsaba na tsakani da Allah daya fito daga tsakiyar zuciyarta.

Yanda take kallonsa kaunarsa na bayyanuwa a fili fuskarta yasa Maryamah zuba Mata ido a karon farko rayuwarta Tana qare Mata kallon tsaf.

Komai na Zainab din kusan na mahaifinsu ne,

Dashi take kama sosai sabanin ita da mahaifiyarta ta debo sak sai dai hancin mahaifinsu da ido data biyo itama.

Tsakanin itada Zainab din baasan Wanda yafi sahirtaccen kyauba,
Duk kyanta ganin takeyi kaman Zainab zata iya finta idan tasamu rayuwar nutsuwa da Hutu gata yarinya yanzu take cikin budurcinta da 'yan matanci.

Mamakinta na biyu yanda Zainab ta bayyana Tana kaunar abinda ita din ta Haifa Wanda Bata taba tunanin hakan ba.

Dauke idonta tayi daga kan Zainab din ganin zata dago ta kalleta gudun kada taga Tana kallonta,
Amma Kuma yanayin yanda Zainab din ta rungumesa da kyau Tana Masa kallon kauna daukeda murmurshi a fuskarta yasa taji kaman mahaifinsu ne yake bayyanarda kaunarsa ga jinjirinta sbd Zainab ta zama kaman ita kadaice jinin mahaifinta Tunda basuda danginsa dama zai iya tunowa dasu.

Babyn na hannun Zainab Alh Asad ya karbesa yayi Masa huduba tareda kiransa da suna *_MUHAMMAD AQEEL_*

Sunan babyn Zainab ta maimaita a cikin ranta cikeda kaunar yaron tasake cewa Allah ya rayasa"ahankali.

Sai guraren 12 na Rana aka sallamesu suka dungumo suka dawo gida.

Koda suka iso gidan Zainab hidima ta sake ninkuwa Dan kuwa gidan rikicewa yayi da baqi kala kala Yan zuwa barka,

Tun batajin komai har jikinta yafara gaya Mata sbd abinci wani kan wani haka takeyi ga shara kusan so hudu takeyi a wuni sbd yawan jamaar daketa yawon zuwa barka Kuma kusan dukansu dangin Alh Asad ne da jamaarsa sbd mutum ne me jamaa sosai.

Washe gari qanwar umma ta iso wadda itace zataiwa Zainab din zaman jego.

Zuwanta yasa wasu ayyukan suka Dan ragewa Zainab Dan itace me girkin abincin Maryamah Dana Maigidan
Itakuma Tana na baqi da masu Aikin gidan da share share.

Suna saura kwana biyu umma tazo tareda wata matar qaninta.

Zuwan umma ko Maryamah kila batai farin cikin da Zainab tayiba saidai a iya zuciyarta ne Tunda batada kusancin dazata bayyanar Amma dai ita kanta umman taga murnar zuwanta a tattareda Zainab din
Itama Kuma ta yaba da yanda taga Zainab din na hidima sosai da kulawa da gidan Maryamah.

Haka dai ta ringa hidima Bata zaune Bata tsaye har saida akai suna aka watse kowa ya Kama gabansa.

Bayan suna Inna Karima ma tafiyarta tayi sbd ganin yanzu ragamar komai ta Aiki da kula da gidan yakoma hannun Zainab wadda take ganin ta sameta Amma tafita samun matsayi agun Maigidan Dan kuwa ko dunkunan biki Alh Asad zannuwa masu kudi ya siyawa Zainab din duk da Bata wani sakaba sbd aiki da hidimar Kai kawo har aka Gama biki aka watse Bata samu kantaba

Daga qarshema da umma zata koma lace din babba me tsadar da atampar daya ta Bata ita Kuma ta dauki atampar daya Dama kala uku ne.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma

*KI KULANI*🔥
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥
*_IDON NAIRA_*
_Mamuhgee_
_Arewabooks@Mamuhgee_
_ZAFAFA BIYAR 2023_

5
LAST FREE PAGE

*_MAAB LUXURY HOME_*
_ASSALAMU ALAIKUM JAMA’AR KWARAI.. JAMA’AR AMANA… JAMA’AR ZAFAFA… MASOYA KUMA MABIYA MASU ALHERIN SAYAN ZAFAFA A KODA YAUSHE BA GAJIYAWA…GODIA MAI TARIN DIMBIN ALBARKA DA FATAN ALKHAIRI AGARE KU.._

_KUNSAN DUK INDA ABUBUWAN ARZUKA SUKE MUNA SHIGA MU KURDA MU NEMO MUKU SU DOMIN JIN DADIN KU..🥰💕SABODA KU DIN NA GABAN GOSHINAN MU NE._

_TAMKAR KO DA YAUSHE.. YAU MA MUNZO MUKU DA WATA TSARABAR.. TSARABAR DUNIYAR KAYAN KITCHEN, DECORATIONS DA SAURAN SU… KU MARMATSO KU JI…_

*_MAAB LUXURY HOME_*
*_MAAB LUXURY HOME_*
*_MAAB LUXURY HOME_*

_KUN GANI KO? TO INA AMAREN? INA UWAYEN GIDAH INA YAMMATAN DA KE SHIRYE SHIRYEN SHIGA DAGA CIKI? INDA ZAKU JE KU KANKARO MUTUNCI KU DANDALO ARZIKI NA KECE RAINI.. INDA ZAKU WUCE RENI DA GANIN KASKANCI..INA MAZAN DA KE BURIN FARANTAWA MATAN SU DA ‘YAYAN SU DA KANNEN SU? _

_MAAB LUXURY HOME: RIGIJI GABJIN KENAN! WOHOHO WANI KAYA SAI AMALE KAN DAUKA.. MAAB LUXURY HOME : ALJANNAR KAYAN KITCHEN KENAN, INDE AKACE KAT TOH KARSHEN MAGANA TA KARE KENAN.. MAAB LUXURY HOME ; A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY KITCHEN UTENSILS, HOME DECORATIONS AND MUCH MORE_

_ADIRESHIN MU: MUNA KAN TITIN AHMADU BELLO WAY, KANO STATE. ZAKUGA TAMBARIN DA MAAB LUXURY HOME.._

_DAN SAUKAKA MAKU FITA ZUWA SHAGON MU. ZAKU IYA ORDER AKAWO MUKU DUKKANIN INDA KUKE A FADIN NIJERIYA DA KETARE. _

_INSTAGRAM: @maabluxuryhome._

_FACEBOOK: @maabluxuryhome._

_KO KU NEME MU TA LAMBAR TARHON MU: 08034631010_

_KYAU! INGANCI! RAHUSA! ADADE ANA AMFANI DA SHI SAI KAYAN: MAAB LUXURY HOME_

_100% TESTED AND TRUSTED😍☑️_
______

*********""
Ahankali sukaci gaba da renon babyn itada Anty Maryamah din Dan kuwa saidai ace su biyu ke renon.

Wata uku Da haihuwar Maryamah tafara fita Aiki a babban guri Mai kyau da matsayi a kamfanin mijinta Dan haka kusan renon Aqeel da dawainiyarsa yadawo hannun Zainab Dan tsakanin Maryamah da jaririn nata sai dai ta bashi Nono da Yan sauran kauna da kulawar da baa rasaba Amma ko Aiki Bata zuwa dashi sbd Bata wani dadewa take dawowa sbd shayarwan datakeyi.

Zainab ce ta zama uwar renonsa da Dole da qarfi da yaji ta koya komai na kulawa da babys da hidimarsu,

Tun Tana tsoro da fargaba tareda taka tsan tsan akan kada tayiwa 'dansu ba daidaiba harta fara sakewa tana iya Masa wasu abubuwan,

Wanka ne kawai Bata iya Masa sbd shima Tana tsoron abinda zai iya faruwa Tunda har lokacin yarone sosai Amma Bayan wanka itace goyansa,
Basa Madara,
Sauya Pampers da sakasa bacci.

Ayyukanta kokuma ace nauyin dayake kanta saiya Ninku sbd lalurar renon yaro wani sabon aikine Mai wuya da taka tsantsan Amma haka take daurewa tayi dukkanin aikinta Yana bayanta Yana bacci wani lokacin Kuma Yana daki ta kwantar.

Sam batajin damuwa ko gajiyar kulaw da renon Aqeel sbd tsananin kaunar datake Masa har cikin ranta,

Jinsa takeyi kaman itace ta haifesa Kuma wahala ko Wace irice zata iya Masa Dan haka Sam batajin komai akan dawainiyarsa.

Da farko ganin yanda Zainab take shaquwa da kaunar Aqeel yasa Maryamah daukar me Reno Tana zuwa dashi gurin Aiki ta rabasa da Zainab ganin yafara wayo Yana gane Zainab din fiyeda kowa gashi shi Dadynsa ko ajikinsa Dan haka ta rabasu dan kada yayi mugun sabo da Zainab fiyeda ita.

Tashin farko Aqeel din kullum rigima yake musu harsu je Aiki su wuni su dawo baya zama
Bayan rigima Babu abinda yakeyi ko cereals dinsa da nono daqyar yake karba
saidai idan yayi barci ne kawai suke samun sukuni Amma ahakan ta dage taqi maidawa Zainab renonsa duk da ta fahimci rashin Zainab ne ke sakasa wannan rigimar ta tashin hankali.

Ita kanta zainab kusan har qaramin zazzabi tayi da aka rabata da renon nasa Dan kuwa ta shaqu dashi fiyeda komai da kowa data sani rayuwarta Bayan mahaifinta Aqeel shine Dan Adam na biyu datake tsananin ji har cikin ranta.

Mai renonsa Rabi'a tsabar rigimarsa yasa idan Maryamah Bata kusa ubansa takeci  tayita yi Masa tsawa harda marin kumatunsa ko bakinsa duk tanayi tareda zare Masa idanuwa Tana zaginsa duk tabi ta firgitasa Sam ko ganinta yayi sai kuka.

Taurin zuciya Maryamah tayi taqi maidawa Zainab renon nasa duk kuwa da yawan kukan tashin hankalin dayake Mata a gida da office qarshe haka ya shide sai gasu a gadon asibiti.

Hankalin Dadynsa ya tashi sosai sbd baisan abinda yake faruwaba kwata kwata akan hakan Tunda bawani zama yakeyiba koyaushe Aiki
Idan Kuma Yana gida suna harabar gida gurin karatun addini Dan shi din maabocin karatun addini ne Yana kaunar zurfafa iliminsa akan addininsa.

Alh Asad dinne dabai San meyake faruwaba Amma dai yasan akwai shaquwa sosai tsakanin Zainab da Aqeel din Dan kuwa harshi wasu lokutan idan Yana hannun Zainab qyuya yake Masa baya yarda da kowa indai Yana hannun Zainab.

Baisan Maryamah ta rabasu ba da haka yasa driver yakawo Zainab asibiti sai gashi itama Zainab din Tana Jin kaman zatai kuka lokacinda ta ga Aqeel din kwance a gadon na asibiti Yana bacci da Alama har yunwa akwai ataredashi.

Tana zaune gefensa ya farka Yana bude ido da ita yafaracin Karo sai kawai ya fashe da kuka Yana Kiran sunanta cikin rashin iya fadan sunan sosai Dan bai wani dadeba da fara koyan magana.

Dole uwar naqi tasaka Maryamah barwa Zainab din jinyarsa qarshema daga wannan jinyar sai kawai aka yayesa daga nono Daman yayi shekara daya harda watanni goma.

Tun kuma daga ranar bata ƙara ƙorafi akan kulawar da Zainab ke bai wa AQEEL basai ma tafi jin nutsuwar zuciya akan gwarama Zainab ɗin ta dinga rainonsa don ta fahimci ta fi Rabi'a iya bashi kulawa cikin nutsuwa hakama Rabi'a komai nasa aka Ba cinyewa takeyi tace shine yaci Bayan tasan qarya take Masa Dan rigimarsama Bata Bari Yana cin komai.

Zainab kuwa daman ita hakan takeso renon nasa yadawo hannunta Dan haka taci gaba da kulawa dashi da gidan harma da masu gidan Dan yanzu Anty Maryamah din Bata zama sosai itama kullum Tana office sai yamma take dawowa idan ta fita tun safe,
Chapter 7 · 0% Book details