← Book details Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 95

Sashe 60

Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To Amma ba damuwa zataga yanda zatai idan sunje Koda ta wayane likitan suyi magana da Amal din Koda akwai abinda zai iya cewa akan matsalar.

Sallama sukayi itama tana sake Dan shiga sanyin jiki sbd har lokacin tasan Yana cikin quncin abinda yafaru dinne,

Shikadai yasan halinda suka kusa sakasa da zancensu na rashin tinani,

Sun girgiza fiyeda yanda Shi kansa yake tinani Dan Haka ya zabi bawa Kansa da zuciyarsa hutu Akan dukkaninsu kowa da kowa sai gashi hakan na azabtar da kowaccensu Banda Amal da hakan yayi Mata daidai yanda takeso wato fitarsa arayuwarta.

Lokacinda mommyn ta fada musu AQEEL Bai bar tafiyar da Amal ba shiru Amal din tayi batareda tace komaiba zuciyarta na nauyi duk da Daman tasan hakan zata iya faruwa Amma Kuma idan har yayi ne Dan ta rokesa da kanta to ta hakura da tafiyar itama.

Siddi datake mamaki da Jinjina lamarin da ita Bata Saba gani a rayuwar nata aurenba ta kalli Amal dataqi cewa komai kan maganar tace,

"Amal Zaki iya da AQEEL ASAD dinnan kuwa?

Kiga yanda fa yake magana Kai tsaye baya shakka ko tsayawa Dan inda inda,

Gaskia Amal ki kwantar da Kai Kawai ki rokesa yabarki sbd kina buqatan tafiyar Nan fa.

Girgiza Kai Amal tayi tana cigaba da duba wayarta tace,

"Nafasa tafiyar inada abubuwan Yi a school.

Haj Zainab dake jinsu kasa cewa komai tayi sbd damuwar rashin zuwa da Amal din dakuma taurin kanta dazai Hana ta rokesa yabarta duk da tasan koda Amal din ta roka tunda yace aa to bazai canjaba.

Dukkanin Shirin tafiyarsu angama

Su duka gidan zasuyi tafiyar harda uncle Lulu da Anty Fareedah hadda Fahat

Daga ita saisu Bilkisu zaa Bari,

Baqin ciki da bacin Rai ne a cikin zuciyarta Mai tsanani akan rashin tafiyar Amma tadanne ta barshi aranta Dan kadama tabawa zancensa mahummancinda zaayi tunanin ta nemesa.

Tanaji tana gani suka wuce Kuma ko a Daren ranar da zasu wuce din yazo gidan da daddare taqi fitowa Haka shima Bai tambayetaba bare ya nemeta, Maminsa ya bawa kudi masu yawan gaske da zasu buqata komai acan harsu dawo sbd dawowarsa rayuwarsu zuwa yanzu hatta abincin gidan yanzu shine yake kawo komai batareda ya tsaya tambayaba Haka ake kawo abinci duk wata a jera a gidan.

Ranar dasuka wuce a school ta wuni sai yamma sosai ta dawo,

Wanka tai ta fito taci abinci kadan ta koma bedroom dinta Bata sake fitowa ba sai washe gari.

Ranar batajin fita koina Dan Haka very late ta tashi ko wanka batayi ba brushi kawai tayi tafito sanyeda riqa da wandon bacci masu santsi gajeru sai slippers da wayarta a hannunta tana kokarin Kiran su mommyn taji isarsu.

Saukowa tayi palon qasa tacewa Bilkisu takawo Mata abincinta sama.

Juyowa tayi zata koma daidai shigowarsa palon sanye cikin black hoodie fendi Riga da wando masu fadi dasuka fidda hasken fatarsa sosai,

Da alama shima yau din ba fitarda zaiyi sbd kayan dake jikinsa suna nuni daga morning jugging yake.

Ba zato tagansa Dan Haka idanuwanta suka Shiga cikin nasa

Cikin basarwa ta dauke nata Idon tareda nufar hanyar saman zata wuce yakira sunanta kai tsaye fuskarsa a kame.

Daka tawa tayi batareda tasan tayi hakan ba.

Takowa yayi ya qaraso zaiyi magana saiga Bilkisu tafito daga kitchen daukeda breakfast din nata tana ganinsa tayi daurin dakatawa tareda gaidasa cikin girmamawa ta juya kitchen da abincin.

Fasa maganarsa yayi Ana ya Kama hannun Amal din Kai tsaye yajata zuwa sama suna Shiga tsakiyar palon ya saketa tareda kallonta zaiyi magana saiya fasa yayi mata kallo daya ya dauke Kai yace,

"Jeki ki sako wani kayan.

Sai alokacin ta dago itama ta kallesa batareda tayi abinda yace dinba sbd zafinsa datakeji akan rashin tafiyarta gashi kowane lokaci period dinta zai iya zuwa azabarta na hanya tasani.

Ganin taqo motsawa daga inda take yasashi zuba Mata idanuwansa cikin mamaki yasake maimaita abinda ya fada din.

Kujera ta nufa da niyar zaunawa akawo Mata abincinta

Bata qarasa zamaba akai ya riqota gabaki dayanta ya nufi bedroom dinta da ita.

Qwacewa take kokarin Yi daidai lokacinda ya bude dakin nata ya sakata aciki tareda rufe kofar ya tsayar da ita gabansa Yana kallon yanayin kayan nata,

A kirjinta da Babu bra ya tsayar da idanuwansa sbd Kai tsaye shima ya fahimci Babu bra a tareda ita.

Motsawa tai zata janye jikinta daga nasa ya matseta jikin kofar suna fuskantar juna,

Faduwa gabanta yayi Jin kirjinsa daya dafe nata kirjin jikin kofar dashi.

Lokaci daya suka dago suka kalli juna tana kokarin boye tsoronta da faduwar gabanta dake bayyanuwa.

Qamshinsa ya sauya numfashinta dake fita da sauri kirjinta na harbawa ahankali batasan lokacinda takai tafin hannuwanta zata tufesa daga jikintaba cikin rashin sani hannuwan nata suka sauka a fatar cikinsa da rigarsa ta Dan janye sbd hannuwansa dake sama gurin Mata runfa.

Sanyi da taushin hannuwanta suka sanyashi rintse idanuwansa tareda zura hannunsa daya ya sake matsewa da ita Yana bude idanuwansa akan fuskarta datai saurin janye hannunta..

Qamshin jikinta ya shiga hancinsa ya sake bude idanuwansa akanta Yana kallon yanda take kokarin turesa daga jikinta.

Fuskarsa ya goga Mata a cikin wuyanta ahankali

Take jikinta ya dauki rawa ta rintse Ido cikin sauri batasan lokacinda ta bude bakiba tace,

"Me kakeyi???

Bakinta da yayi maganar ya dago ya kalla kafin yakai bakinsa kan kunnenta ahankali yace,

"Kina magana Ashe??

Na dauka kurma nake aure.

Turesa tayi da karfi sbd takaicin maganarsa da wani irin shock da dumin numfashin maganarsa ta sakar Mata a kunnen.

Tana turesa da sauri ta qarasa toilet tashige tareda fincike kayan jikinta tana wurgi dasu sbd qamshinsa dasuka Kama ba Bata lokaci.

Bai kalli kofar toilet dinba shima ya fice dakin yabar gidan gabaki daya Yana Dan saita Kansa kamar Babu abinda ya faru.

Wanka tayo tafito ta shirya cikin doguwar Riga ta fito taci abinci ta Kira Ahmed duk da batayi niyar fitaba taji tanason fitar kawai.

Ahmed na zuwa suka fita zuwa makaranta Dama tanada lecture daya kawai dai batayi niyar zuwa bane sbd Bai cika zuwaba lecturer din.

Bata baro school dinba sai yamma bayan sun biya ta siyo maganinta sbd ciwon mararta daya fara zuwa kadan kadan

Daman tasani lokacin yayi.

Koda ta dawo gida a sanyaye tadawo sbd jikin nata Dan Haka ko abinci bataciba wanka kawai tayi ya Dan sha magani ta kwanta tana Jin ciwon na fara qaruwa kadan kadan.

Tea Mara shuga Bilkisu ta dafo Mata takawo Mata daqyar ta iya Shan kadan ta ajiye Takoma ta kwanta.

Da daddare ma sake dafo mata tea din Bilkisu tayi takawo shima kadan Tasha cikin azaba ta jiye takoma ta kwanta.

Ahankali ahankali yafara yawa tanata Dan daurewa har tasamu gari ya waye suka Kira Dr saidai Bata gari.

Sake Shan magani tayi tayi wanka da qyar tana fitowa takasa shiryawa ta kwanta a qasan dakin nata tana juye juye tareda kuka sosai sbd tsananin azaban ciwon da Marar keyi Mata.

Sanye cikin navy blue plain luxury yadi yashigo palon dayayi tsit Babu kowa,

Ahmed ya sanar Masa da Bata fitaba tana gidan Dan Haka Kai tsaye ya wuce saman Yana shigowa Bilkisu na fitowa daga dakinta daukeda tray din abincinda Amal din takasaci..

Tana ganinsa tayi qasa da Kai cikin damuwa da tsoron rashin abinyi da Amal din.

Yanayinta yasashi kallon kofar dakin Amal din inda ya jiyo kukanta na fitowa ahankali.

Kofar bedroom din ya nufa Bilkisu Kuma tayi saurin yin qasa.

Kwance take a kasa daga ita sai towel din wankanta fuskarta tayi jajir tana dafe da cikinta.

Mamaki yasashi qarasowa Yana kallonta.

Yanayinta yasashi daukanta gabaki daya ya Dora akan gado Yana tayata dafe towel dinta da bazaiso ya kunce ba shima Dan bazai iya gani ba.

Kuka takeyi sosai ahankali tana dafe cikinta..

Wayarsa ya fidda ya Kira Maminsa da Bai Dade da Gama waya da itaba.,

Tana dauka ya tamyeta yanayin na Amal.

Damuwa tashiga ta Masa bayanin hakan takeyi daman Akira Dr kawai.

Kashe wayar yayi Yana kallon agogon hannunsa sbd tafiyar da zaiyi Nan da awanni uku shima.

Yanayinta ya kalla yaji zuciyarsa na nauyi da yanayin nata,

Al'amin yakira yace aturo Masa likita mace yanzu a Idon Nera Rs.

Yana kashe wayar ya kalli fuskarta datayi ja ya dagota ahankali tareda shigar da ita jikinsa ya rungume hannu daya Yana dafe Mata towel dinta da hannun daya.

Kasa kwace kanta tayi itama sbd bada lafiya bare qarfin Dan Haka ta samu ta Dan dafe towel dinta shima ya tayata dafewar.

Cikin qaguwa yaketa duba agogonsa akan zuwan likatan Amma har lokacin shiru.

Zafi Kansa ke neman dauka da rashin zuwan likatan dakuma jikin nata ga tafiyarsa dolece Amma bazai iya tafiya yabarta a gidanba ita kadai.

Al-Amin yasake Kira Yana dauka yace,

"Kasake siyan ticket daya da sunanta.

"Ok sir.

Yana kashe wayar ya janyeta jikinsa ahankali tareda miqewa tsaye ya fito ya turo Bilkisu ta shiryata kawai.

Time yake Kallo din bayan seconds sbd hankalinsa daya rabu biyu.

Doguwar jallabiya Bilkisu ta sako Mata da tunanin asibiti zaa tafi da Amal din.

Ana Gama shiryata handbag dinta kawai aka daukar mata ya daukota da Kansa suka fito Bilkisu na sauke Kai qasa.

Su malam Rabiu ma hango fitowarsa da ita a jikinsa sauke kan sukayi Saida ya shiga motar.

Yana Shiga malam Rabiu yashigo yatada Kai tsaye airport suka wuce inda al'amin ke jiransu.

Suna Isa acan taga wani likitan gaggawa yayi Mata allurai take bacci ya dauketa ajikinsa batareda tasaniba har suka daga zuwa portharcourt.

Har suka Isa bacci takeyi sosai

Saida suka Isa ta farka a hankali jikinta Babu qwari sai alokacin tasan tareda wa take.

Tashi tayi daga jikinsa tana Dan Bata fuska saidai bazata iya maganaba.

Ganin akwai mutane manya a inda suke din yasata yin shiru har suka fito jirgin suna Shiga mota tace a maidata gida.

Bai kulataba yacewa Al-Amin su tafi kawai Ana jiransa bayason Bata time.

Kai tsaye gurinda zaiyi meeting dinsa Al-Amin yafara ajiyesa da driver kafin ita ya wuce da ita masaukinsu kafin AQEEL ASAD din yazo daga baya.

##MAMUH#

#HOTLOVE#ROMANCE#

#AMAL IDON NERA.

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥

Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥

Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥

Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥

Safiya huguma

*KI KULANI*🔥

Miss xoxo
Chapter 60 · 0% Book details