← Book details Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 95

Sashe 14

Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zainab ta sauya sosai kamar ba itaba,
Tayi kyan gani matuka tareda samun kwanciyar hankali da nutsuwa harma da Jin dadi daidai gwargwado duk da kusan komai na malam din yadan tsaya sbd manyan dayakewa karatu acan gidajensu basa iya zuwa gidansa sai kawai da yawansu suka sauya malamai da Wainda zasu ringa zuwa gida suyi musu karatun shikuma daga Hakan kusan duk jamaarsa suka tafi sai yakoma yanzu Bayan Aqeel da wasu Yan tsirarraku Babu masu daukan karatu agurinsa.

Zainab tayi jiki sosai tayi fresh abinta Dan yanzu duk sati take kitso 
Lalle ma duk bayan sati uku ko hudu takeyi sai Takoma kamar wata Yar budurwa sabon tashe gashi Daman kyakkyawan ce nutsuwa da gyara ne Bata samuba da kwanciyar hankali.

Bata taba saka ran zuciyarta zata San wani so da soyayyaba sai yanzu data samu abokin rayuwarta mijinta abin alfaharinta malam Umar sanda.,

Soyayyarsu suke Mai dadi da kwanciyar hankali tareda tattali Dan kuwa tattalin dayake Mata yasa aduk lokacinda ta kallesa mahaifinta take tunawa Dan kuwa su biyun Hadi da 'danta Aqeel sune kadai masu tsananin so da kaunarta da kulawa da ita,
Ta rasa mahaifinta Amma tanada su biyun a yanzu 
Tana Kuma fatar su dore a Hakan har lokacinda mutuwa zata rabasu.

A yanzu datake cikin wannan rayuwar ta yanci burinta daya ne taga tafiyar Aqeel karatu sbd kusan ayanzu tafi haj Maryamah son tafiyar tasa Dan haka kullum cikin tambayarsa tafiyar tasa take.

Shi Kansa yanzu tafiyar yafiso fiyeda komai sbd yasamu Maminsa yanzu Tana hannu na gari Dan haka yasan koda ya tafi hankalinsa a kwance yake da inda yasan yabarta zai dawo ya sameta.

****Cikin ikon Allah da rabo daga garesa wani babban al'amarin farin ciki ya samesu na samun rabon ciki daga Zainab..

Sunyi murna sun godewa Allah musamman malam Sanda sbd yariga ya tsufa baida 'dan Kansa 

Lamarin da kwata kwata bai saka raiba badan ya cire Rai daga rahamar ubangijinsa ba.

Zainab kuwa kunyar kanta ta ringa ji musamman da cikin yafara girma Aqeel ya gane.

Shi Kansa Aqeel din yaji nauyin Amma farin cikin daya shiga yafi na nauyin Dan haka sai ya zama shine yake kulawa da ita sosai.

Da Kansa yakaita asibiti akai Mata komai na ganin likita duk Bayan sati biyu.

Duk ranar zuwa ganin likita shine yake kaita ya dawo daita..

Babbar damuwarsa da rashin Jin dadinsa shine baya qasar Maminsa zata haifar Masa 'dan uwansa ko 'yar uwarsa Wanda ya tabbatarda kafin su hadu ya daukesu cikin hannuwansa ya rungumesu sai sun girma Tunda ba kusa zai dawoba,

Saidai su gansa a hoto shima ya gansu a hoto.

Labarin cikin Zainab ya samu Haj maryamah da umma Amma har lokacin Babu Wanda ya iya daukar kirantaba.

Komai na alaqarta da Yar uwarta Haj maryamah da umma yagama lalacewa sbd sun tabbatar Mata da Basu ba ita din har abada kamar yanda suka Bata zabi.

Cikinta yakai wata bakwai ta zama wata yar lukuta da ita,

Babu kalar kulawa da tattalinda Bata samu daga malam Sanda da Aqeel Wanda kejin kamar ya Ciro babyn dake cikin ya ganta kafin ya tafi Amma ba Hali Dan haka saidai yake kulawa da Mamin tasa kadai.

Ba qananun kudi yake kashewa Mamin ba da Kuma kayan baby komai order yakeyi online yasiyo yakawowa Mamin wadda takejin kamar ma Aqeel din yafita zakwadin babyn.

Haj maryamah dakeda bayanin komai daga PA dinta akan yanda Aqeel ke kashewa babyn da Zainab zata Haifa kudi ranta ya sake baci takirasa tayi Masa tas karshe hadda umma saida taji zancen ita Kuma takira Zainab din da rabon dasuyi magana tun aurenta Amma yau da kanta takirata tayi Mata kaca kaca da fada har saida baiwar Allah tayita kuka karshe duka abinda Aqeel yabata tace ya maida inda ya siyo ya karbo kudadensa.

Bai karba ba Kuma ransa ya sosu matuqa da abinda itama Mamin tayi Masa Dan haka kwana biyu saiya dauke Kansa ga kowa ya maida hankali kan tafiyarsa da batafi sati biyu ba.

Kwana biyu da baya zuwa gidan sai itama Bata nemesa ba sbd malam Sanda dake fama da ciwon ciki Dana Kai a kwanakin sosai shiyasama koda akai rigimar harma da Kiran da umma tayi Mata tana fada duk bai iya saka bakiba sbd sosai ciwon cikin ke damunsa ko bacci baya samu sosai a kwanakin.

Aqeel baisan da halinda suke ciki ba Dan sbd shima tafiyarsa tazo ga Haj maryamah tadawo sbd tafiya tasa Dan haka ya maida hankali sosai gurin shiryawa da mahaifiyarsa,

Bayason ya tafi Tana Mai fushi dashi Dan haka ya tattara lokacinsa gabaki daya ya Bata gashi itama Tana fama da nata rashin isashiyar lafiyar hawan jini ya sakota gaba.

Jikin malam Sanda ya Dan tsananta Dan sunkai a kwance yake yanzu.

Taso Kiran Aqeel yazo sukai malam din asibiti saiga Kiran umma kamar tasani ta gargadeta akan kada ta sake Shiga tsakanin maryamah da 'danta tabari su rabu lafiya cikin kauna da kulawa Tunda Aqeel din tafiya zaiyi yabarta.

Jin Yana tareda mahaifiyarsa sunata daidatawa da begen juna kafin ya wuce yasa ta fasa nemansa ta kame kanta Dan gudun sabuwar matsala Tunda ansamu sun daidata din.

Itada malam din sukaje asibiti yaga likita Amma Basu samu wani cikakkiyar bayani akan abinda yake damunsa ba andai rubuta musu test da hoto harma da wasu Yan magani tukuna kafin result din yafuto.

A hanya suka siyo maganin suka dawo gida daqyar yasha ruwan zafi da abinci kadan yasha maganin yayi sallah ya kwanta.

Sai data ga bacci ya daukesa tukuna ta fito tayi alwala jiki a mace tayi sallar la'asar Dan tun safe suna asibitin suna fama sai qarfe uku suka baro.
Itama abincin taci kadan sbd Jin duk batajin dadin jikinta da yayi sanyi da ciwon nasa Dan abune da Bata taba ganiba.

Da daddare jikinsa ya matsa sosai Allah yasa Basu kwantaba Dan haka ta rasa yanda zatai Dole takira Aqeel suna gaisawa cikin kewar juna taji Yana tareda mahaifiyarsa Dan haka saita fasa fada Masa kawai sukai sallama ta kashe ta ajiye wayar.

Magani tasake basa ya Sha sai ciwon cikin ya Dan lafa.

Ruwan zafi yasa takawo Masa yayi alwala acikin babbar roba ya zauna Yana nafilu.

Itama kasa komawa baccin tayi Dan haka tayo tata alwalar tsakar gida tadawo ta shimfida daddumar sallah a bayansa ta fara Jero nafilar itama.

Har kusan qarfe ukun dare tukuna yakoma ya kwanta take bacci ya Dan daukesa.

Da asuba ma jikin nasa tashi yayi sosai
 ciwon cikin Mai tsanani ya dawo Dan haka Dole tasamo abun Hawa suka Kuma komawa asibitin saidai Basu samu ganin likitaba haka suka dawo sbd kamar kada su nufa asibiti ciwon cikin yakoma ya kwanta.

Suna dawowa itama zazzabin takeji sbd yanayinta na juna biyu ga damuwa da tashin hankalin ciwon mijinta.

Ganin Yana ciwon ciki yasata dama kunun tsamiya ta zuba a flask saita dafa farar shinkafa kawai da Mai da Dan yaji sbd ita kanta batada wani apatite na cin abinci.

Haka ya wuni a kwance Yana bacci Mai nauyi sosai sai yamma ciwon yakuma tadashi daqyar yayi sallolinsa yasha kunun kadan Amma Sam bai zauna a cikinba ya amayar duka take qarfinsa yayi qasa sosai.

Duk inda hankalin Zainab yake ya tashi Dan haka ta zauna gabansa bayan kuka Mara sauti Babu abinda takeyi sbd Babu wata mafita.

Batasan me zatayiba Kuma,
Aqeel ne gatanta harma Dana malam din Amma Kuma batason lalata Masa komai tsakaninsa da mahaifiyarsa,

Idan takirasa komaima faruwa zaiyi Dan haka saita zauna tanaci gaba da kukanta sbd duka maganin da aka rubuto Babu Wanda Basu sayaba hakama babu Wanda bayasha 
Gashi sunkoma asibitin Amma Basu samu ganin likitaba ance sai emergency patient kawai zaa iya gani,
Su ankasa yarda da emergency dinne.

A wunin azabar ciwon yafi na kullum Dan haka take malam din gabaki dayansa ya sauya lokaci daya kamaninnsa duk suka sauya.

Tsananin tsoron dake zuciyar Zainab yasa kukan natama ya tsaya qarfe itama zabgewa Tai lokaci daya.

Dare nayi jikinsa yayi tsananin da bazata iya kasa Kiran Aqeel ba sai gashi Tana Kira wayar tasa a kashe 

Take jikinta ya dauki rawa Tana fashewa da wani irin kuka.

Shi Kansa malam din jikinsa yayi nauyinsa bazai iya ko bude Baki yayi magana ba......

Bugun kofar gidansu taji guraren goma saura.

Bata tsaya tambayar wayeba ta nufi kofar ta bude idanuwanta ko gani basayi sosai.

Aqeel ne,.

Kallonta yakeyi kamar yanda itama take kallonsa Tana fashewa da qaramin kukan qunci ahankali.
Cikin mamaki da dan firgici yace,

"Mami lafiya?

Meya sameki?

Jikin ne?

Ina baba Malam??

Ahankali ta takaita kukanta tareda share fuskarta Tana bawa kanta hakuri da qarfin zuciya tace"

Malam dinne ba lafiya sosai tun shekaran jiya.....

What????

Mami meyasa Baki sanar daniba?

Ya Salam....

Ciki suka qarasa da sauri saidai Koda suka Isa malam din yayi nisa....

Kansa yayi da sauri Yana ambatar,

"Innalillahi wainna IlayhirRajiun

Haka jikin yayi tsanani Mami?

Innalillahi.

Kokarin kamasa yakeyi Yana cewa"

Mami asibiti zamu kaisa yanzu.

Da Kansa ya kamashi Mamin tasa ta Kama Masa suka kaisa mota yaja motar suka nufi Babbar private asibin kakarsa Haj Kaka.

Suna Isa asibiti aka karbesa da gaggawa sbd yafara nisa sosai.

Waje aka koro Aqeel din da Maminsa suka zauna kowannensu hankali tashe 
Bayan fata da adduar samun saukinsa Babu abinda kowannensu yake kitsawa cikin ransa.

Zainab gabaki daya jikinta yagama saki da komai,
Zuciyarta ta riga tayi nauyi Jin take kamar kirjinta bazai dauki nauyin zuciyar ba.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥

Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥

Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥

Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥

Safiya huguma

*KI KULANI*🔥

Miss xoxo

Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171

Maryam sani

Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*🔥

*_Arewabooks@Mamuhgee_*
12
Zainab Tunda ta zaunar da duwawunta kan gurin zama ta sunkuyar da kanta Bata sake motsiba bare iya magana.
Chapter 14 · 0% Book details