← Book details Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 95

Sashe 24

Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maigadin na ganin hakan yasan wasa ya 'baci Dan Haka ya miqe da sauri zai nufota
A haukace tadauki sandarsa ta gora ta ringa dukansa ta koina tana musu ihu tana Kiran jamaa

Kafin kace me gidan yacika da mutane
Ta rufe Ido tanata ihu da neman daukin sun lalata Mata yarinya...

Dayake DS ya Jima da barin gidan 'dan nasa ne kawai aciki Yana aikata Barnarsa kala kala da Yan Mata da shaye shaye
Shikuma DS din da matarsa da sauran yaransa Mata da wancan Dan nasa daya da Lulu ya illata sun koma babban makeken gidansa dayafi wannan din so da Dama,

Kuma Daman sbd ya ringa lura dame basa barazana wato Lulu yasa ya zauna a anguwar
To yanzu daya Gama da matsalar lulun saiya tashi daga anguwar Dama ba mutuncinsa bane zama anan din.

Wani irin mummunan duka zainab tayiwa maigadin dashi Kansa Suraj Wanda yasa Dole akai Kiran hukuma tazo ta kwashesu
Itama tayi hakan ne Dan case din ya zama babba.

Ana zuwa gurin hukuma babu Bata lokaci yan anguwa suka bada shaidar abinda zainab ta fada
Aka Kai yarinyar asibiti aka duba bai Kai ga yimata fyaden ba Amma dai hukunci yahau kansu dagashi har maigadi gashi dukansu suna asibitin sbd Shi maigadi har haqorinsa hudu ya rasa dan harda Yan anguwar aka taru aka rufar musu da shegen duka Mai muni.

Zance yanata yaduwa a duniya da social media take hankalin DS ya tashi yayi duk yanda zaiyi Amma zancen yariga ya yadu mutane idanma baayi adalciba zainab a shirye take da Kai zancen sama inda komai zai sake lalace masa..

Matar DS ta samu zainab har gidanta ta fada Mata maganganu masu daci da tozarci,

Takirata da karuwa,
Mai 'yaya shegu Dan Haka kome akai musu ai ba fyade bane tunda sanaar uwarsu ce,
Ta kirata da Mara asali Kuma zuriar Yan daudu...

Tayi kukan data manta Yaya akeyin kukan ma sai aranar, saidai Kuma aikine ya tashi Dan kuwa qudurinta akansu ma sauyawa yayi,

Ds yayita nemanta a sirrance akan tajanye case din taqi sai shima ya bullo Mata da maganar aure Dan yayi amfani da damar su janye case din sbd yazama babba lamarin.

Kamar yanda ko yanzu tasan cewan auren manufa ne zaiyi da ita itama saita sakawa ranta hukuntasu da manufar tasa.

Amincewa aurensa tayi sai gashi cikin qanqanin lokaci akayi auren
Aka Kuma yada cewan sbd karamcinsa ya aure matarda 'dansa ya lalatawa 'ya shine abinda zaiyi ya kare mutuncin yarinyar da aka so lalatawar.

Hakan yasa mutuncinsa ya ringa qaruwa a idon mutane sai hakan ya ringa Masa Dadi musamman da zainab din ta fito ta nunawa duniya irin kulawa da kaunar dayake Mata itada 'yayanta...

Aikuwa hakan datake nunawa yasa DS sake mutuwa akanta da yayanta,

Matarsa Haj sadiya hankalinta mummunan tashi yayi ganin DS gabaki daya ya koma wani iri agun zainab,
Ga Suraj din har lokacin Yana gidan yari zainab taqi ma yarda DS ya tasa zancen,
Cikin salon daukar hankali ta nuna Masa abar Suraj din acan sai bayan zabe sai a fiddosa gudun yadawo ya lalata Masa komai tunda yanajin haushin an aureta din.

Aikuwa hakan akayi ds yabar maganar Suraj din akan sai angama zabe....

Sabuwar rayuwa zainab ta bude a gidan uban siddi batareda kowa yasan siddin DS ne ubantaba,

Kudi da Jin dadin rayuwa suke ja tako Ina hakama duk wani tattalin arzikinsa tanata janyewa tana tanadarwa 'yarta siddi Dan kuwa tayi alqawarin duk sai sunbiya abinda sukaiwa Lulu da marigayya siddi.

Koda aurenta da Ds yayi watanni Tara tagama tarwatsa gidansa Dan kuwa hatta matarsa Saida sukayi rabuwar kotu inda tun anan mutunsa yafara zubewa mutane,

Dan kuwa Haj sadiya cikin bacin Rai tonan asiri tai Masa Wanda zainab tayi amfani da hakan aka tada case din Lulu.

Tada case din Lulu yasa hankalin ds tashi haka zainab tasa ya ringa sakin kudi koina yanaso a sake rufe case din Amma baisaniba hakan yasake badashi da kuwa duka kudaden dayake badawa a banza suke tafiya....

Qanqanin lokaci rayuwarsa da iyalinsa tagama wargajewa
Akai zaben Kuma bai ci aikuwa qaramar hauka ta taso Masa gadan gadan.....

Bai qarasa Aron haukaba sai ranarda zainab tayi winning case din Lulu akansa sai gashi Lulu ya fito.....

Qarar qarshe data kusan buga zuciyar DS itace qarar yayiwa siddi fyade hartasamu cikin yarta ta rasu gurin haihuwa.....

Binciken asibiti da kotu ta bayar ya tabbatarda siddi yarsa ce Dan Haka aka yanke Masa hukuncin bin dansa gidan yari shima.

Dukiya Mai tarin yawa tasamu daga da aurensa Dan Haka fitowar Lulu ta sauya musu rayuwa gabaki daya...

Lulu yai kukan ganinta tare dana mutuwar siddi,

Daga Shi har ita zaman anguwar data garin fita kansu yayi gabaki daya sbd a rayuwa bayan Rashi da baqin ciki Basu San komaiba....

Amma a yanzu dasuke da 'yaya gabansu bazasu sake barin quncin kowa ya illata rayuwarsu data 'yayansuba.

Qaton gidan DS dayake kusa dasu tuni ya mallaka Mata Shi da Ana zaman Dadi kafin ta fara tarwatsashi Dan Haka gidan Mahaifinta ya dawo Mata.

Da gidan da gidan Lulu suka hade tareda maidasa wani irin babban gida da shaguna a waje suka zuba yan haya....

Mutuwar aurenta da Ds babu abinda yaja Mata sa suna da farin jinin manya Dan Haka cikin qanqanin lokacin takuma wani auren sadai shima baifi watanni huduba suka rabu Wanda Shi yamafi ds din arzki Wanda ta aura daga bayan..

Yawan aurace auracenta yasa Ake Mata kirari da IDON NERA,

sunan yafara binta ne tun anan kafin suka tattara sukabar garin sanadiyar wani Mai kudin data aura ya kaita Lagos...

Zuwansu Lagos da wata shida shima auren ya lalace daganan sai Bata dawoba Lulu ya sameta acan suka bude babin wata baudaddiyar rayuwar zaman Kai da budewar ido....

Kamar yanda akace zaman gidan yari qarin course,,,to hakan ne ga Lulu sbd yanzu daya fitone yake asalin hamshaqin tantirin Kansa bare sun dawo Lagos sun sake zama fitsararru..

Gidan kansu ne dasu na masaukin duk wata Yar barikin data rasa gurin zama to suna tallafa Mata sbd sabo da zama da karuwai da sukai tun acan dasuma gararin dasukai anan karuwan ne suka karbesu da mutunci sai basa iya ganinsu Acikin garari....

Da farko Suma Lagos din sunsha tsananin wuya da garari kafin suka gane kanta suka fara gwagwarmaya da Fadi tashi Dan duk arzikinsu da zainab ta Tara Saida ya qare musu a yawon Haya da wahalhalu a garin kafin da Lulu yaga ta kwabe masu suna neman wulaqanta kudin cin abinci ma na neman gagarsu ya tsunduma harkar dillanci Mata da alhazai shine fa suka fara daidaita...

A wani babba gidan karuwai suke zaune wanda ya hada mutane sama da 40,

A gidan kowa karuwanci sukeyi shine sanaarsu,
Ita Kuma zainab auren masu kudi shine nata,
Suna nan suna karuwancin Basu Tara komaiba ita Kuma a aure biyu ta Tara wani irin arziki suka tattara suka koma sabon gidansu itada Lulu dasu Amal sai sabuwar Mai aikin datayi....

Sunan IDON NERA yayi sunane a aure auren manyan data ringa Yi a garin Wanda yaja Mata attention din mutane sbd zuwa lokacin manyan gaske take aura,

Asalinta da kowa ya sani shine karuwanci Wanda har lokacin Bata taba jin shaawa ko tunanin tsayawa ko so daya tace ita ba karuwar bace,
Duk Wanda yaji ya fahimta ita karuwa ce to aje hakan Dan kuwa tai Nisan da saidai a fada a iya inda kake badai a fili ba.

Business sukeyi sosai Wanda shima ya karbu Kuma sunanta yasake habbaka sunan kasuwancin nasu,

Ta goge,
Ta sauya,
Takoma kamar ba uwar Yan Matan dasuka fara girma ba a gabanta,

Ta rufe idonta batajin komai Bata gane kowane yare saina NERA,

Shi kansa lulu baka ganesa Dan kuwa yakoma hamshaqin Dan daudunsa mai hulda da manya
Dan kuwa shine asalin wanda yake kutsawa ya shiga ya fita ya samo Masu rumbun nerar da zainab ke aurewa.

Babbar kaunar dake tsakaninsu da karuwai baya sauyaba tana Nan dan haka gida garesu na musamman dasuke bawa karuwanda basuda mafita gurin zama wasu Kuma sune suke zama gatansu
Ire iren wainda karuwancin bai Gama shigarsuba kenan...
##MAMUH#
#HOTLOVE/AMAL IDON NERA
#AQEEL ASAD

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma

*KI KULANI*🔥
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥

*_Arewabooks@Mamuhgee_*
20
Rayuwarsu a Lagos da gwagwarmaya da wahala suka Kai matsayinda suke a yanzu,

Mutane babu ruwansu da wahalarka,.da zufanka, da gwagwarmayarka, da dararrakun baqin cikinka Amma daga ranar da aka gano kuskure daya atareda Kai zaa fassaraka,zaa bika da zantukan gaskia da sabaninsu,hakam zaa bika da tsinuwa da kalamai maka mantansu,....

Daga ranar da aka haifi siddi ta gano hakan Kuma taji hakan daga gurin  'yar uwarta, jininta Dan Haka duk abinda duniya zata kirata dashi kokuma ake kiranta dashi Bata damuba sbd ko tace aa babu me shedarta......

Kowa Yana aikata kalar nasa laifi ko sabo tsakaninsa da ubangijinsa ne
Dan Haka itama wannan shine nata laifin,

Ta zabi aurarrakin datakeyi ne akan karuwanci Wanda mutane suka kasa rabasa da karuwancin sbd abinda takeyi din karuwan ma sunason samun damar Yi Amma Basu samu ba Dan basuda kamar hajiya Lulu Wanda shine sanin manyan gwamnati na gida Dana waje....

'yayanta tuni akai musu tambari da sunan shegu basuda uba Dan babu wadda akasan ubanta acikinsu,

Taji ta gani takuma dauka saidai Kuma nerarta na sake zaunuwa Ana mantawa da yayanta shegu ne kamar yanda ake fada...

Ta badawa yaranta gata da Jin dadin da duk wani Mai uwa da uba zai nema,.

Rayuwar yayan hutu da gata sukeyi tareda abinda ransu yakeso sbd mahaifiyarsu da yayar mahaifiyar tasu Haj Lulu sun tsaya musu yanda ransu yakeso...

Karuwai mutanensu ne haryanxu akwai Amana tsakaninsu dasu Dan kuwa sune mutanen dasuka karbeta alokacinda batada kowa batada komai batada gurin zuwa,
Chapter 24 · 0% Book details