← Book details Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 95

Sashe 41

Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta bangare daya Kuma kamar Ana nuni da tsafatataccen AQEEL ASAD yazo gurin wainda tsarkinsa ya qazanta,

Wayeshi dazai shigo rayuwarsu Yana neman lalata musu suna cikin sanyi...

Me mommy take tunani dazata Bari aci gaba da cin mutuncin IDON NERA's akan AQEEL ASAD wadda Rana tsaka ya shigo rayuwarsu.

Kiran Hayat ne yasake shigowa wayarta ta jefarda wayar gefenta tana sakin qaramin saki sbd Hayat din Yana qara Mata ciwon kai da Kiran wayarsa dayaketa yimata tin safe.

Bude idanuwanta tayi akan hotunansu dake kan jaridar ranta na qara soyuwa da kalmar da Yan jaridar sukai amfani da ita Wai uwar ko 'yar.

Jan motarta tayi Kai tsaye ta nufi office din mommynta Dan gwara ta yanke alaqarta da AQEEL ASAD da wuri batason alaqarsu kawai.
##MAMUH#
#LOVE/HOTLOVE/AQEEL ASAD/AMAL SANDA
#IDON NERA

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma

*KI KULANI*🔥
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
32
Tunda safiyar ranar shikuma Hayat gidansa aka tashi da fitina Mai qarfi tsakaninsa da Nafee wadda itace kadaice tasan da yasaka a bibiya AQEEL ASAD akan tabbatarda shine yake zuwa IDON NERA's,

Tajisa alokacinda yake maganarsa dakuma lokacinda aka tabbatar Masa da AQEEL ASAD dinne,

Batareda tunanin Aminyarta ba kokuma mutuncin AQEEL ASAD da kusancinsu ta fidda labarin Wanda Daman neman tabbacin jita jitar Media keyi Dan Haka tun a Daren ta fitarda labarin Tunanin nata Mijin ya fita tarkonsu.

Yana cin karo da jaridar yasan Nafeen ce Dan Haka ya tinkareta Kai tsaye ta tabbatar Masa da itace.

Fada da tashin hankali sukai sosai Wanda yasa yace tabar gidansa Takoma gidansu sai tayi hankali Kuma kada ta yarda ta fadawa kowa itace tafidda zancen.

Kukan tashin hankali da Dana sani taringa Yi gashi ita kanta tana tsoron Bilkees taga labarin Bare hartasan itace ta fidda zancen,

Sanin wacece Bilkees da tsananin zafin kishinta yasa tashiga sabon tashin hankali karshe ta Dole saidata Kira Bilkees din tana kuka ta sanar Mata Hayat ya koreta akan IDON NERA..

ba shiru Bilkees din ta iso gidan tana yiwa Idon Nera adduar dibar albarka da fatan su hadu da nasu masifar datafi Wanda suka saka Aminyarta.

Koda ta Isa Haka suka zauna suna jajanta lamarin Bilkees cikeda tausayin Aminyarta ta baro bayan ta rarrashin Amrah dataketa kukan rabuwa da mahaifiyarta.

A hanyarta ta komawa gida Traffic light ya tsaidasu cikin lafiyayyar motarta da ake tuqata,

A cikin Dan qaramin cunkoson holdup din dasuke tafara qosawa da jiran ta Dan dago kanta tana kallon wajen motar cikin mummunan tsautsayi idanuwanta suka sauka kan hoton kyakkyawan mijinta a shafin farka na jaridar da wani me siyarda jaridu yaketa dagawa Dan a siya.

Ajiyar zuciya me sanyi ta sauke tana jin son AQEEL ASAD dinta me tsananin girma na sake mamayeta musamman tunaninta na koda yaushe akan nata dinne ita kadai.

Take tausayin Nafee da aurenta yabi duk ya wargaje sbd masifa ya dawo ranta.

Murmushin farin ciki ta sake tana sake kallon fuskarsa a jaridar tareda saka hannu handbag dinta tana lalubo wayarta Dan kiransa taji murmuyarsa.......

Dakatawa tayi daga dauko wayar cikin Jakarta tana Dan tsayar da idanuwanta akan jaridar lokacinda me jaridun ya matso har gaban gilashin motarsu Yana sake tallata sanaar tasa.....

Ras ta bude ido da kyau ta karanta bayanin dake rubuce baro baro gameda mijin nata da hotonsa yake Kai,

Duk tsananin ilimin addinin datake dashi Kuma a matsayinta na matar wadda yakeda sani a addnini sosai bata iya kamo salatiba a bakinta sbd mummunan faduwa da rawar da kirjinta yayi,
cikin tashin hankali da tsoro hannuwanta na rawa tace"

Wayyo Allah na
Nashiga uku,
Meye wanna nake gani?

Murya na Yar rawa ta kalli drivernta tana cewa,

"Habibu karantamun abinda yake jikin jaridar Nan Dan Allah
Kaga nakasa gane mena karanta...

Me jarida kuwa yana ganin hankalinta sosai akan jaridarsa ya sake matsowa sosai Yana sake Nuno mata jaridar Yana cewa,

"Jaridar yau ce Haj.

Ahankali habibu ya bude idanuwansa akan jaridar ya karanta abinda yake rubuce a gurin hoton maigidansu.

*_DR sheykh MUHAMMAD AQEEL ASAD Former COA, HN Spk/MADAME IDON NERA._*
*_Work(aiki) Or busness(kasuwanci)????_*
*_Mother(uwa) Madame haj zainab IDON NERA or Daughter ('ya) AMAL Sanda IDON NERA???_*

Sake karantawa yayi dakyau ya tabbatarda dai Maigidansu ake nufi wato Dr Aqeel sheykh..
To meya hada sunan dr sheykh da wannan hamshaqiyar matar data bawa karuwai cikakken yanci da gata???

Me ake nufi da uwa ko 'ya?.....

Cikin Yar shaqewar murya bilkees tace"

Habibu fassaramun dakyau nagane Mana
Ka karanta kayimun shiru kabarni Ina jiran bayani.

Shiru yayi yana Dan kaucewa kallon jaridar a natse yace"

Hajia shirme ne da neman lalata suna irin na Yan jarida fa Amma bakomai ban.....

A rikice ta zaro kudin da batama San nawa bane daga Jakarta ta sake glass din motar ta miqawa me jaridar ta karba da qarfi tana sake ware idonta sosai akai tana sake karantawa.....

Innalillahi,kenan dai abinda ta karanta dinne da farko ba kuren karatun bane...

Innalillahi na shiga uku na lalace,
Kodai sunan SSG zasu saka suka saka na Sheykh sbd a iya saninta babbar masifar data tarwatsa farin ciki da gidan SSG a yanzu ba kowa bace face IDON NERA,
Saidai bata saniba Yar ce ko uwar ake magana yanzu akan AQEEL ASAD dinta..

Mezai hada mijinta me tsananin qyanqyamin sunan zina ma bare karuwan dake aikata zinar har a hada sunansu a jarida.....

Zuciyarta taji tana doka wani irin tsalle da rawar firgici,

Nashiga uku bana gane komai wlh,
IDON NERA kuma?
Dr shaykh Dina Kuma??

Zufane yaketa karyo mata tako Ina cikin doguwar jallabiyar dake jikinta,

Ahankali numfashinta yafara yin sama sama sbd tsananin firgici da abinda takeji a zuciyarta,

Zuciyarta wata irin zafaffiyar zuciyace akan mijinta,
Tanada wani irin mugun rauni agurin kishi sbd abu kadan ne yake sakata shiga masifaffen hali sbd kishin Mijinta Wanda ya kasance abin so ga Mata da yawa,

Me ake nufi?
Taje ta kaso rigimar gidan Nafee shine masifar zata bullo akanta...
Cabdijam,
Wllh gwara da wurwuri masifar Takoma inda ta fito wato gurin Hayat din Amma baa kan AQEEL ASAD dintaba..

kishinta rinjayar iliminta yakeyi sosai aduk lokacinda ta hararo mace a rayuwar Mijinta shiyasa take wahala sosai da zuciyarta gameda Mijin nata,

Wani gumi take sake fesowa tana Jin zuciyarta na tsalle,

Ganin mawuyacin halinda tashiga yasa habibu qarawa motarsu gudu suka iso gida a rikice sbd ganin kamar zata shide bata hayyacinta.

Yana parking ko Jakarta a juye ta daukota tana tafe Yan wasu abubuwa ciki suna zubewa batareda ta ankaraba.

Kai tsaye hayar shashen umma ta nufa idanuwan ko gani basayi sosai sbd rikici.

Daqyar da wahala ta iya Dan seta kanta kadan sbd sanin doka da halin ummar na rashin son rawar jiki da tashin hankali da rashin nutsuwa.

A Palo ta taddata zaune kan doguwar kujera tana karanta sako a waya,

Kasa riqe kanta bilkees din tayi sbd gab take da Dora hannu akai tayita birgima tana qwala ihu da wannan mummunan abin datake neman me yimata budadden bayani akan ba gaskia bane abinda aka rubuta din.

Hannunta na wata irin rawa ta miqawa haj maryamah jaridar hannunta tana sako wasu irin hawayen tashin hankali da shiga uku...

Kafin tayi magana Hameeda ce tashigo palon itama hankalinta atashe riqeda jaridar ko gabanta bata gani sosai itama tana cewa"

Umme B menene yake faruwa zaa lalatawa daddyna suna?

Wannan IDON NERA fa ake magana akai,

Meya hada sunan daddyna da suna hamshaqan karuwai dasuke lalata zaman lafiyar gidaje?

Meya hadata da daddynah?

Meya hada sunansu guri daya?

Wace tambayace suka rubuta anan din????

Wurgi tayi da jaridar tana sakin hawaye itama Dan wlh bazata iya muguwar tsanar datayiwa AMAL IDON NERA ba,
Ta tsaneta Haka kawai tsana Mai tsanani sbd ta lalata rayuwar gidan uncle SSG.

Haj Maryamah kuwa da aduk duniya idan akwai kalmar datafi tsana a fada gabanta to itace kalmar karuwanci,

Ta tsani kalmar sunan tsana mafi muni da qyama Wanda kusan kowa yasan hakan shiyasa shima Dr shaykh Aqeel ya tsani kalmar sunan a baya batareda yasan dalilinta na tsananta tsana da tsananta qyamar sunanba,

Ajiye wayarta tayi agefe tareda kallonsu daya bayan daya gabanta na Dan nauyi ganin yanda hankalinsu yayi masifar tashi gashi suna ambatar wannan munanniyar kalmar hadeda sunan AQEEL dinta.

Hannu takai a sanyaye ta dauki jairidar ta saukar da idonta akai tana kokarin nutsar da kanta ta karanta.

Jimmm tayi tana sake maimaita karanta kalmomin daya bayan daya bugun kirjinta na Dan sauyawa ahankali.

Sake kallon hotonsa dake kan jaridar tayi ta tabbatarda AQEEL ASAD dinne 'danta qwalli daya ake magana,

Komawa yayi tasake karanto zancen dalla dallah kusan so hudu...

Ahankali ta saukar da idonta akan lafiyayyan hoton Zainab dake gefe da 'yarta inda aka rubutasu da sunansu da manyan baqi.

Innalillahi wainna ilayhi rajiun
Innalillahi wainna ilayhi rajiun

Balkees na ganin haka tasake shiga mummunan tashin hankali tafara nanata sunan IDON NERA a bakinta cikin rikicewa tana cewa"

Wayyo Ni Allah wace ranace wannan??
Innalillahi wainna ilayhi rajiun..

Miqewa Haj Maryamah tayi zata bar gurin sbd zuciyarta dake bugawa ba daidaiba Amma tana tsayuwa qafafunta suka kasa riqeta ta sulale zuciyarta na daukan wani irin nauyi da harbawa take BP dinta ya haye sama.

Kanta sukayo cikin tashin hankali da tsoro suna Kiran sunanta hankali tashe.

A office duk yanda yaso samun damar fitowa hakan Bai samuba saima wani babban abin daya taso Masa Dole zai tafi Abuja da yamman tareda baqin nasa.

Dole ya hakura da zuwa gidan Maminsa Amma gabaki daya hankalinsa nakan AMAL dayake buqatan gani Ido rufe sbd ya tabbatarda itace little MARYAMAH.

Labarin jaridar tuni ya yadu kamar wutar daji da kuwa tunda ya fito koina labaran akeyi,

Wayoyinsa Dole ya kashe sbd masu kiransa danjin idan bacin sunane a dauki mataki,
Chapter 41 · 0% Book details