← Book details Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 95

Sashe 73

Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abubuwan dayake Mata yasata fara kuka tun Bai nufi babban aikinba
Tanajin yafara kokarin sake kusantarta taqarawa kukanta karfi tana janyewa Amma Sam yakasa tsayar da Kansa baya Kiran sunanta babu abinda yakeyi.

Sosai yau dinma ta gurzu a hannunsa kafin yabarta daurin hannunta ma duk sun gama yamutsa sun warware bandage dinma.

Sabuwa jinyar tata tadawo sbd kusan kadan ne azabar yau din batakai ta jiyan ba Amma itama taji azabar sbd yau din yafi samun guri da kyau.

Kuka da Kiran mommynta Babu Wanda batayiba Haka ya lallaba yasake gasata da Kansa sosai suna fitowa yabata magani Harma da grilled chicken da aka kawo cikin abincin dinner dinsu da Basu ciba da qyar ya iya dumamata kadan a oven
Sbd Bai iya komai na girki ba yakawo yabata abaki Bata wani iya ciba zazzabi da bacci Haka yasamu yasake lallabata tasamu bacci.

Bata farka ba sai karfe goman safe tayi sallah jiki a mace tasake wanka daqyar ta iya yin breakfast tasake Shan magani ta daga Masa hankali da rigima zuwa gida sbd su mommynta dasuke hanya.

Sai data sake warwarewa zuwa Rana kafin ya nufi asibiti da ita aka sake dubata da hannun kafin ya wuce da ita gida.

Ahankali take tafiya Amma ba kaman jiyan ba ya rakata har cikin bedroom dinta ya tayata sauya Kaya da Kansa kafin ya kwantar da ita yayi kissing bakinta sosai kafin ya fito.

Yana ficewa gidan takira Bilkisu a waya ta gargadeta akan fadawa Kowa kwana biyu Bata gidan.

Bilkisu na fitowa dakinta bacci Mai nauyin gaske ya dauketa Kuma alokacin Anty Fareedah tashigo harabar gidan tareda Siddi data dauko da airport sbd tayita Kiran Amal Amma Bata daukaba.

Suna shigowa suka taddata tana bacci Mai qarfi Dan Haka suka qyaleta batareda sun tadataba.

Guraren karfe hudu harta gota su Haj Zainab Suma Suka iso Siddi ce taje da motar Amal wadda tana bacci Ahmed yakawo gidan ta daukosu.

Suna dawowa Amal din na farkawa batama San sun dawoba Saida Tai wanka tasake gaso kanta jikinta ya sake sakewa sosai ta shirya cikin doguwar Rigar Atampa army green Mai kyau tayi sallah ta shafa liner cikin idonta sbd kodewan dasukai kada agano tayi kuka kwana biyun.

Ahankali ta fito dakin cikin nutsuwa ta nufi palon qasa datake jiyo hayaniyarsu tana kokarin sake fuskarta da murnar ganinsu gabaki daya.

Kallonta sukeyi ganin yanda take sanyi Haka fuskarta ta Dan sauya
Cikin kulawa Haj Zainab da siddi suna hada Baki gurin tambayarta ko lafiyanta kalau.

Dan fuskewa tayi tana qarasowa ta zauna jikik mommyn tana cewa,

"Mommy nayi kewanku Dan Allah kada ku sake tafiya kusa.

Jin jikinta da Dan dumi yasa mommyn sake tambayarta lafiya.

Hannunta dake Dan kumbure ta nuna Mata tana cewa,

Buguwa nayi naji ciwo a hannu shiyasa nake Dan zazzabi tun jiyan.

Cikin kulawa dukkaninsu sukai Mata sannu Anty Fareedah na cewa taga likita akan hakan?

Ahankali ya gyada Kai tana cewa eh.

Sannu suka qara yimata suna fadawa wani zancen gabaki dayansu harda ita datake kokarin bawa kanta qarfin halin rashin kuzarin datake tattare dashi.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma

*KI KULANI*🔥
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥

*_Arewabooks@Mamuhgee_*
59
Zuwa magrib jikinta yaqara zafi sosai tana Jin zazzabinta na dawowa Amma Haka ta daure Bata Bari kowa ya rabeta ba bare aji jikin nata da zafi Sosai harma agane batada lfy din.

Haka ta daure ta cijewarta har sukai dinner shima abincin da dauriya tacisa sbd batason kowane attention dinsu ya dawo kanta dasunga alaman rashin lafiya a tareda ita.

Itace tafara gamawa ta miqe ta baro dining room din ta nufi kitchen tace Bilkisu takai Mata tea me zafi dakinta.

Tana fitowa kitchen taji qamshinsa Dan Haka Bata tsaya tabbatarda idan shi dinne ba ta nufi hanyar saka batareda ta waiwayo ba.

Su Maminsa ya gaisa dasu Cikin nutsuwa kafin yace suci abincin zai jira Mamin a sama idan ta Gama.

Dayake gyada Masa Kai tayi Dan Bata Jima ita da fara cin abincinba.

Saman ya wuce hankali kwance cikin nutsuwa Yana shiga Kai tsaye ya nufi bedroom dinta sbd yaga wucewarta saman.

Tura kofar dakin yayi Kai tsaye ya shigo hankali kwance ba tsoro ko fargaban wani ya gansa cikin nutsuwa yake kaman yanda ya Saba komai basa a natsen.

Tana toilet batasan dashiba ta fito toilet din tareda nufo tsakiyar dakin ahankali take tafiyarta har lokacin.

Sai data fito sosai tagansa kawai zaune akan kujera Yana duba sako a wayarsa hankali kwance.

Tsayawa cak tayi daga inda take tareda yimasa kallo daya ta sauke Kai tana gyara zaman rigar baccinta data cirewa bra tana shigowa dakin.

Ajiye wayarsa yayi ahankali ya juyo ya zuba Mata idanuwansa yana kallon yanda ta tsaya a narke.

Tasowa yayi ya qaraso gurinta tareda riqo hannunta ya qarasa da ita bakin gadonta ya zaunar tareda shafa goshinta zuwa wuyanta yaji jikin da zafi.

Numfashi ya sauke ahankali tareda kallonta yace,

"Kinsha maganinki da yamma?

Girgiza Kai tayi tana kasa dagowa takallesa.

Wani numfashin Yakuma saukewa ahankali baice komaiba ya nufi drawer din gaban mirror daya ajiye Mata maganin ya bude ya dauko yadawo saiga shigowar Bilkisu.

Tana ganinsa tayi saurin juyawa zata fice yace takawo kawai.

Juyowa tayi Kai a qasa takawo tray din ta ajiye ta juya ta fice.

Maganin yabata a bakinta Tasha ya miqa Mata tea din ta girgiza Kai sbd Jin Bata buqatan shansa Kuma.

Kwantar da ita yayi ya rankwafo ahankali ya Dora bakinsa kan nata ya Dan tsotsa lips dinta ya kalli cikin idanuwanta murya a tausashe yace,

"Sleep well Amaryata kinji¿
Da safe ki tabbata kinsha maganinki Kuma gobe ba zuwa school ki huta sbd bakida lfy bakya buqatan wani wahalan fita.

Rufeta yayi da bargo yasake kissing lips nata kafin ya kashe Mata wuta yajuya ya fito tareda rufo dakin.

Har lokacin Mami Bata hawo ba sai kawai ya sauko
Yana qarasowa palon qasan zata hawo.

Kallonsa tayi tana cewa,

Sorry AQEEL na tsaya magana ne a waya inata saurin nagama din Kuma fa.
Tafiya zakayi ne?

Dan kallon agogon hannunsa yayi yace,

Yes Mami,
Gobe Zan dawo kema yanzu kina buqatan hutawa sbd kinyi tafiya.

Cikin nuna tata kulawar itama tace,

"Ok Saida safe,ka kula kaima.

Juyawa yayi ya fice a haraba Suka sake haduwa da uncle Lulu suka Dan sake magana sukai saida safe ya wuce.

Itama Mamin tana Hawa Saida ta leqa dakin Amal taga harta kashe wuta tayi bacci dan Haka ta sake janyo Mata kofar tanufi dakin siddi wadda take wanka a toilet sai kawai Bata tsayaba ta wuce nata dakin.

Washe gari ma tajima tana bacci sai latti sosai ta tashi dayake tayi sallarta ta asuba tun subahi.

Jikinta ya sake sakewa sosai sai dai sanyi da tayi kawai,
Brush da wanka tayo ta shirya cikin Riga da skirt na atampa ta fito daukeda wayarta da batama San ya kashe mataba kafin ya fita jiyan.

Kunnawa tayi alokacinda take fitowa
Text dinsa ne yafara shigowa tana karantawa ta da rintse idanuwanta sbd abinda ya rubuto din Jin tayi kamar ta fashe da kuka sbd kunya.

Siddi ta tadda a Palo zatayi breakfast sbd itama Bata jima da tashiba,
Zaunawa tayi aka kawo musu breakfast din tare taci Takoma dakinta Tasha maganinta a boye kafin tadawo sukai sashen Anty Fareedah sbd mommy ta Riga ta fita.

Acan sashen Anty Fareedah dinma sune suketa surutansu ita Bata wani saka Baki tana lafe a kujera tana saurarensu.

Haka ta wuni sukuku Bata wani doguwar motsi ko son magana dayake sunsan Haka halinta yake sai Basu wani gane sanyin nata ya qaru ba.

Da Rana ma bayan taci abinci Haka Takoma dakinta Tasha maganinta shima sbd text din Shan maganin da yayi Mata.

Sai yamma mommy ta dawo zuwa lokacin Amal tasake kokartawa kanta sakewa sosai.

Da daddare ma Koda yazo suna Palo Baki dayansu gidan dan Haka baisamu Daman ganinta ita kadaiba Haka yaringa binta da mayen kallonsa tanata kaucewa cikin Shiga faduwar gaba da tsoron abinda zai iyayi.

Daqyar ta ga yayi sallama da Maminsa ya tafi
Ta sauke ajiyar zuciya a boye zuciyarta naci gaba da bugawa da sauri.

Washe gari tana tashi da text dinsa tasake cin Karo tafiya ta kamasa da safen ta kwana biyu.

Ajiyar zuciya tasake saukewa bayan karanta text din kafin ta sauko gadonta taje toilet tayo brush ta fito sanyeda kayan baccinta ta Dora qatuwar jacket Mai girma da tsayi akan kayan ta fito.

Abinci sukaci Mommy tace ta shirya suje asibiti akan hannunta daya Dan kumbura.

Asibiti sukaje aka sake duba hannun aka Bata wani maganin na shafawa Mai Dan zafi Haka Suka dawo.

**Kwana biyu tayi tana jinyar kanta batareda sanin kowaba harta warke sosai Takoma daidai taci gaba da zuwa makarantarta hankali kwance.

Kusan sati guda yayi a tafiyar Kuma kullum da text dinsa take tashi hakama idan zata kwanta,

Zata karanta ta ajiye Amma Bata taba yimasa reply ba baikuma damu da hakanba,

Makaranta ta dawo da wuri sosai yau din
Ahmed na ajiyeta ya juya ya wuce tana shigowa gida siddi da Anty Fareedah sun fita mommy ma Bata dawoba tana can office tareda uncle.

Kitchen tafara tsayawa ta tadda Bilkisu na yanka fruits zaa hada da tareda abincin office da ake kaiwa su mommy yawancin lokuta.

Kallon fresh fruits din tai tareda tsaida idonta akan water melon din data fasa babba
ahankali tace ta yanka Mata ta zuba Mata Madara dakuma condensed milk ta kawo Mata sama Dan kusan shine favourite dinta inda a fruits ne.

Saman ta wuce ta nufi bedroom dinta ta tube tashiga wanka,

Tana cikin toilet din Bilkisu ta kawo Mata abinda tace ta ajiye Mata akan ta bedside ta juya ta fice.
Chapter 73 · 0% Book details