← Book details Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 95

Sashe 57

Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyar zuciya ya sauke ahankali Jin yanayin nata Dan Haka ya katse wayar kawai tareda nufar bedroom dinta abinda bayayi sbd itace Mai zuwa can sama gurinsa.

Kai tsaye bude dakin yashigo Yana kallonta tana zaune tana cin lafiyayyan breakfast da aka kawo Mata aka jera Mata Akan center table...

Bai kalli abincin ba ita yafara kalla kafin ya kalli abincin ya fahimci lafiyarta kalau kenan,

Juyawa yayi kawai ya wucewarsa sbd bazai iya Bata lokacinsaba gurin tambayarta lafiyar tata tunda alamun sun nuna

Kawai raayintane da ganin damarta na rashin zuwa garesa sbd kishinta.

Bangarensu umma ya nufa acan dinma Babu wata Fuskar ko kadan sbd gabaki daya sun dauke Masa wuta musamman ummansa dako ganinsa batason Yi.

Cikin nutsuwa ya sanar da ita tafiyar da zaiyi

batareda ta kallesaba tace Allah ya tsare ta miqe tabar Masa palon.

Umman Cameroon ce ta kallesa bayan barin Haj Maryamah palon itama Bayan ta danne zuciyarta ne ta iya cewa,

"AQEEL matuqar kana kaunar mahaifiyarka da farin cikinta tareda son gamawa lafiya da ita to dolenka wlh ka yanke aurenka da 'yar Zainab Dan Nima har abada bazan karbi wannan auren naka ba bare mahaifiyarka da kayiwa wannan cin mutuncin da tozarcinda har abada bazata Dena kukansa ba matuqar ba yanke alaqar ka dasu Zainab zakayi ba,

Meya baka shaawa a auren wainda Basu dauki auren a bakin komaiba?

Meye abin albarka atattare dasu?

Me zaka samu agurinsu Banda barnar suna da 'bacin suna Mara amfani kanada mutumcinka.....

Ahankali ya furta,

"Nagode umma Zan wuce time din tafiyana yakusa.

Miqewa yayi yanufi kofar palon ya fice yabarta da sauran maganganu a bakinta suna qona Ransa da cin Ranta Kamar zata bi hanya tana ihun Kiran Zainab da tsinewa zuriarta.

Haj Maryamah datake jinsu Yana ficewa taji zafi da ciwon zuciyarta na qaruwa sbd hakan na nufin baida niyar sakin auren kenan?

Wane babban balai Zainab ta aikata akan AQEEL dinne da duk duniya idan ba itaba bayaji baya ganin kowa??

To kodai shayar Mata da 'da tayi a wancan lokacin batareda sun saniba Dan kuwa wannan balain daga gani yasha Nononta ne.

Fitowa tayi gabanta na harbawa da karfi da tashin hankali da sabon radadi a ranta tace,

"Umma Zainab ta shayar mun da 'da Nononta......

Wani shock ne ya Shiga umma datake neman zamewa daga zaune ta fito da idanuwanta cikin mafi tsananin tashin hankali tace,

"Ta basa Nononta kikace?

Tabbas Nima wlh na yarda da hakan yanzu sbd nono ne kawai yakeda wannan qarfin daya kasa ganin kowa sai ita...

Innalillahi wainna ilayhi rajiun

Mun shiga uku da wannan sabon tashin hankalin,.

Zainab ta cucemu taci amanarmu taci Amanar Alh Asad daya yarda da ita tun wancan lokacin,

Me nakeji¿

Zainab nono Kika bawa AQEEL?

Wannan masifar wace irice¿

Rayuwar AQEEL ta lalace tun Yana qaraminsa sbd Zainab,

Ta shayar da Isa nonon karuwanci,

Ta Bata tsakaninsa da mahaifiyarsa,

Ta rabasa da mutuncinsa a Idon jamaa ta hanyar aura Masa karuwar 'yarta,

Yanzu me duniya zataji idan akaji nonon Idon Nera AQEEL ASAD yasha??

Uwa uba nono daya yasha da wadda aka yaudaresa aka daura masa.

Neman zarewa umma da Haj Maryamah din sukai da wannan mummunan tashin hankalin dasuka sakowa kansu,

Bilkees data shigo Bayan wucewar AQEEL ta taddasu Acikin wannan taradda din Jin tayi wani masifaffen Dadi Mai tsananin gaske ya rufeta musamman dataga suna shakka sai kawai ta daka tsalle ta tabbatar musu da ya taba fadar Kamar hakan Amma sirrinsa ne da Haj Zainab din.

Jinin umma Hawa yake kokarin Yi cikin tashin hankali saidai Bilkees din ta Kamata tana tausarta sbd ganin tasamu gabar datafi komai a cikin sauki.

Umma kuwa kuka tafara Yi tana sake debewa zuriar uwar Zainab dinma albarka da suka barta da ita bayan mutuwar malam da Basu zo sun dauketa sun rabata da rayuwarsu ba gashi duka ta zama jarabawansu itada 'yarta Haj Maryamah da jikanta AQEEL.

Haj Maryamah kasa danne zuciyarta tayi tacewa umma wlh tana buqatan sake ganin Zainab Dole saita fada Mata yanda tayi ta shayar Mata da danta,

Me Tasha tasamu nonon data basa¿

Me takeso a rayuwarta

Ko duka abinda ta mallaka zata Bata ta fita daga rayuwarsu itada yarta subar qasar su koma inda bazai sake ganinsu tunda su kudine burinsu da kwadayinsu.

Ita kanta umma tana son fuskantar Zainab din tabbas sbd wannan gabar komai ya wuce tinaninsu

Basu dauka balain nata yakai can ba.

Umman Cameroon kallon Bilkees tayi duk da tana cikin tashin hankali da damuwa

Cikin baqin cikin ganinta itama tace,

"Wallahi tallahi naji zancen Nan ya fita a bakin Aurenki Dan kingama auren jikana kenan sbd kema kin nuna ba 'yar arzikin bace,

Albarkacin mufeeda kikace da tun wancan lokacin Zaki koma inda Kika fito Dan hada zuriar dake kema baida amfani tunda bakisan rufa asirin iyayen Mijinki ba.

Shiru Bilkees tayi tanajin umman Amma zuciyarta batajin komai sbd bullowar wannan maganar yasata Jin kamar an yaye Mata duk nauyin dake kan zuciyarta,

Qarshe dai ansamu abinda zai raba AQEEL ASAD dinta da Amal Idon Nera wadda takejin ma yanzu ko lokacin damun kanta akan auren batada tunda gashi kwadayinsu yasa anyi auren Amma AQEEL din ya barta Dan baya buqatarta.

Abu daya ya rage Mata shine yanda labarin zai fita batareda ansan itace ta fiddasaba sbd Dole sai zancen na ya fita duniya tasani a sheda aurensa da Amal Idon Nera ya haramta shikenan ta fita wannan masifar mai suna IDON NERA a rayuwarta.

*****AQEEL ASAD kuwa Kai tsaye airport aka wuce dashi baisamu ya biya gidan Mamin ba sbd yayi latti saidai sukai magana a waya,

Yauma driver yazo kaita school Amma taqi tafiya,

Washe gari ma haka driver Yakuma zuwa taqi,

Haka driver ya ringa yawo da zaman jira wuni a banza Amma taqi ma sake bi takansu,

Dawowar uncle Lulu ne daga tafiya ya tadda abinda yake faruwa ya Kira AQEEL ASAD din da Kansa ya rokesa akan ko shine yabari zai ringa kaita tunda batason driver din.

Kai tsaye ya sanarwa uncle Lulun Idan bazata bi drivern ba ta zauna Babu Wanda zai ringa kaita.

ganin tanason zuwa school din dakuma wasu guraren shiyasa uncle Lulu dasu mommyn suka rarrasheta daqyar ta yarda tafara bin driver din Wanda sai ranar yafara ganinta.

Daga ranar kullum tunda safe yake zuwa ya zauna jiranta har lokacinda zata fito yakaita makaranta yakuma jira ko yaushe zata kai tagama ya dawo da ita gida.

Sauran gurarenma datakeson zuwa duk shine yake kaita daga school batareda tadawoba sbd idan tadawo mommy Bata barinta fita sbd iya school ake nufin yabarta aringa kaita.

Su umma kuwa yau suka nufo gidan Haj Zainab badan sunsoba Saida sukai kwanaki suna tausar zuciyarsu akan zuwan sbd Dole suzo su funkaceta akan maganar idan ta shayar dashi ta fada musu kokuma su makata kotu su nuna Mata iyakarta.

#MAMUH#

#LOVE/ROMANCE

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥

Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥

Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥

Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥

Safiya huguma

*KI KULANI*🔥

Miss xoxo

Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171

Maryam sani

Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*🔥
46

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

46

Yau sai kusan yamma ta Gama abinda takeyi a cikin makaranta Dan Haka tana fitowa daga lectures Kai tsaye mota ta nufa a Dan gajiye.

Doguwar A shape ce ajikinta na atampa navy blue wadda tayi Mata kyau sosai sai qaramin Chantilly veil da bvlgari handbag,

Fuskarta ba kwalliyar komai akai

Ta nufo motar tana kalla batareda tayi mamakin sauya motar da Ahmed yayi ba numbern motocin gidansa yasa take ganewa duk lokacinda Ahmed ya sauyo motar daukarta.

Kai tsaye ta qaraso motar

Ahmed ya fito da sauri ya bude Mata kamar yanda ya Saba

A natse ta shiga ba zato tagansa a Bayan zaune cikin milk Yadi Mai taushi da tsadan gaske,

Gabaki daya sanyayyan qamshinsa ya Gama rikita motar

Ba zato ta kallesa da idanuwanta dasuka Dan matse

Bai juyo ya kalleta ba waya yake amsawa ahankali cikin nutsuwa.

Jan motar Ahmed yayi suka bar cikin makarantar

dauke idanuwanta tayi gabaki daya tareda maidawa kan hanya fuskarta ba sakewa ko kadan.

Gama wayarsa yayi ya ajiye ahankali tareda waiwayowa kadan ya kalli gefenta idanuwansa akan qaramin gyalenta dayake gefe daya kawai.

Jin idanuwansa na yawo ajikinta yasata kasa motsi tana Jin zafi na saukar Mata.,

Maida idanuwansa yayi kan farar fatar wuyanta dake bayyane.

Ahankali ya dauke idonsa akai ya bude Baki a natse yace,

Meye wannan din da Kika yafo??

Shiru tayi Masa batareda ta juyoba ko amsawa.

Sake maimaita tambayarsa yayi Nan ma takuma yimasa shiru.

Maida kallonsa kadan yai kan Ahmed Kai tsaye yace,

"Mu wuce gidan Karatu.

Juyowa tayi ahankali Jin abinda yafada taqi kallon fuskarsa dake sake sakar Mata zafi ahankali itama tace,

"Ku ajiye Ni Zan hau drp na qarasa.

Bakinta da yayi maganar ya kalla itama Jin baice komaiba yasata juyowa ta kalli fuskarsa idanuwansu suka hadu a fuske ta Dan janye nata Idon tana kokarin sake magan ya katseta da cewa,

"Meye wannan ajikinki nace??

Jikin nata ta kalla a sace taga gyalenta yake kalla dan Haka saita qi cewa komai.

Ahmed tuni ya kama hanyar gidan Karatu ganin baida niyar sake magana shima saita sake juyowa ta kallesa tana son magana Amma izzarta na hanata Dan Haka tai shiru tareda dauke kanta itama.

Babban gate din gidan Ahmed shige da motar bayan an wangale musu kofar gate din.

Danne zuciyarta tayi yaqi juyowa ta kallesa

Dan jiran takeyi ya fita motar Ahmed ya wuce da ita gida.

Ahmed na parking ya bude motar ya fice Dan Basu guri.

Fitar Ahmed yasata juyowa ta kalli gaban motar zatayi magana ya zuba Mata fararen idanuwansa takasa cewa komai cikin mamakin abinda ya tsaya jira a motar ta Dan kalli gefensa zatayi magana ya katseta ta hanyar bude motar ya fice ba tsammani taji ya bude ta gefenda take cikin kulawa.
Chapter 57 · 0% Book details