← Book details Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 95

Sashe 77

Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shima ranar Bai samu shigowaba sbd wani daurin aure Mai mahummanci da aka gayyacesa Wanda yayi haduwarsa da Amininsa da sai satin ya dawo Nigeria tareda matarsa data tattara ta bisa can suka daidaito tunda tasamu ta rabu da masifar rayuwarta wato Amal Idon Nera.

Da farko SSG yaso nuna bacin Rai da fushinsa akan AQEEL ASAD din Amma Sam AQEEL ASAD Baima bada Fuskar da zaayi maganar iyalinsa da waniba Dan bazai iya bada fuskarda Hayat din zai alaqanta Kansa da matarsaba Koda a gurin bada bayani ne Dan Haka kwata kwata yaqi nuna akwai wani Abu daban bayan asalin alaqarsu da amintarsu Wanda yasa Hayat duk yanda yaso ayi dawo da bayani Dole ya hakura yabar maganar sbd AQEEL dabai nuna akwai wani abinba bayan Abotarsu.

Da Haka ya hakura yabarwa Allah tunda ya shirya da matarsa Amma Kuma bayajin ya fasa qara auren tunda yayi niya zai samu tasa shima Mai Kamar Amal din.

Baisamu kansaba sai dare shima dan Haka ta waya yayi magana da Maminsa kawai sai Kuma mutuniyar itama dayake yasan bata Masa magana kota waya Dan Haka text yayi Mata kaman yanda ya Saba.

Washe gari yazo da safe kafin ya wuce wani taron Musulinci da aka gayyace a ranar Amma Bata tashiba tana bacci Dan Haka ko ranar Basu haduba saida aka kwana biyu duk basa haduwa saidai ta waya safe Rana dare dayake Jin lafiyanta da kewanta.

A kwana biyun ta Dan sauya sbd hutawar datakeyi sosai daga bacci sai cin abinci.

Ranar Thursday Bayan tadawo makaranta da yamma sai datayi bacci ta huta tayi wanka da sallar magrib ta fito sun zauna cin abincin dare tana zama sai gashi yashigo palon sanyeda wando da hoodie Balenciaga sweatshirt milk.

Qamshine ya yadu a palon ita tafara Ankara da zuwan nasa sbd qamshin, ta dago ahankali ta kalli hanyar palon saiga idanuwansu ya Hadu ahankali.

Idanuwansa daya zuba Mata Yana binta dasu yasa jikinta neman mutuwa tana Dan dauke idonta daga nasa tana Jin abincin na kasa shiga ci kawai takeyi Bata wani ganewa.

Bai qarasoba a Palo yayi zamansa Dan baya buqatan dinner a koshensa yake Dan azumi ma yayi ranar.

Jin tayi ta koshi Amma Kuma takasa tashi sbd Babu Wanda ya Gama.

Ganin tagama Haj Zainab ta kalleta tace,

"Amal ki kawomin ruwa Wanda beyi sanyin wannan ba tunda kin gama,

Wannan yayi sanyi Bilkisu taqi Dena bamu ruwan sanyi sosai haryanxu.

Rintse Ido tayi sbd tsoron Isa palon ba kowa acan sbd Idan ba ita datake saiti da kofar palon ba babuma Wanda yasan yazo sai sun Gama sun fito zasusan ya zo.

Miqewa tayi ahankali ta fita ta shige kitchen ta dauko ruwan ta fito

Ga mamakinta Bai taso daga inda yakeba harta wuce takaiwa mommy ruwan

Idanuwansa kawai yake binta dasu tanajinsu ajikinta kamar zata harde ta Fadi.

Sallama tayi musu Dan yanzu da wuri take Shigewa ta fice ta nufi hanyar hayewa sama Amma ko Isa stairs din batayiba ya Kira asalin sunanta daya sata tsayawa cak zuciyarta na harbawa da qarfi aduk lokacinda zai kirata asalin MARYAMAH dinta Wanda bayanshi duk duniya Babu Mai kiranta hakan,

Sunanma idan bada ya bayyana rayuwarsuba batasan tanada wani asalin sunanba.

Ahankali ya Kama hannunta ya jata zuwa saman dakansa har cikin dakinta suka shige ya turo kofar Yana shinshinata yace,

"Ganina yasa Kika kasa cin abincin?

Bata fuska tayi tana cewa ah ah batareda tasan tafada dinba.

Ruwan dake gefen gadonta ya dauka ya bude ya Dora Mata abaki tafara Sha babu musu sbd ya lura da Natasha ruwaba bayan Gama cin Dan abincin datayi.

Ruwan takesha ahankali Yana Bata Yana kallon yasa take hadiye ruwan cikin sanyi da nutsuwa komai nata sanyinsa da narkewarta na sake hargitsa zuciyarsa.

Tana Gama Sha ya rufe ya ajiye yasaka hannu Yana goge Mata Wanda suka zubar Mata har cikin kirjinta.

Kallonta yakeyi yanajin kewarta sbd kusan kwana biyar kenan Basu ga junaba.

Hijabinta ya saka Mata tareda janta cikin nutsuwa Suka fito ba tsoro ba shakka ya jata har qasa suka fice batareda kowa yagansuba bare sanin ficewar tasu.

Daman shine ya kawo kansa Dan Haka yajasu Suka bar gidan.

Ita kanta yau Bata tsaya wahalarda Kansa musawa ba sbd idanma Basu bar gidanba tasan zai iyayin abinda zai sata kunyar familynta a gidan.

Suna Isa gidan Karatu a palonsa suka yada zango Saida yagama rikitasu suka gama tarwatsa pillows din west Elm sofa set dake palon kafin suka qarasa dakinsa acanma Saida suka Gama yamutsa gadon kafin komai ya lafa.

Wannan karon itace wani bacci Mai nauyin gaske ya dauketa batareda tasaniba.

Ganin tayi bacci saiya kyaleta Bai tadataba yaje yayi wanka yayi Shirin baccinsa ya rufe koina yazo yashige jikinta take bacci Mai nauyi shima ya daukesa.

Da asuba gigice ta tashi ganin inda take take tafara hawaye ya samu ya rarrasheta tayi sallah gari nafara haske kadan ta daga Masa hankali ya maidata gida Bata Bari yashigo gate da motarsaba a waje yayi parking suka shigo da qafa securities na Masa barka da asuba ya amsa Kai tsaye Yana wucewa ciki raka matarsa.

A bakin kofar palo tace yakoma

Saida ya Kuma kissing bakinta ahankali kafin ya saketa ya juya takira Bilkisu a waya ta bude Mata kofar ta wuce sama da sauri tana zuwa tashige dakinta ta kwanta sai bacci.

Washe gari Babu Wanda Koda Wasa ya fahimci baa gidan ta kwanaba bayan Bilkisu dake ganin ikon Allah abinda yafi karfinta.

Ranarma hakance da daddare yazo ya fice da ita bayan mommy ta shige siddi Kuma tana kicin tareda Bilkisu data saka aikin gasa Mata cake.

Kaman yanda ya dawo da ita jiyan Haka ya dawo da ita a yau Amma yauma harsunyi latti kadan ya rage Basu hadu da Uncle Lulu daya fita yau din tunda safeba.

A kwanakin komawa yayi Yana raba kwana a tsakaninta da Bilkees batareda Bilkees din Tama tsaya ta fahimci duk Bayan kwana biyu baya kwana a gidaba hakama Amal data manta gabaki daya da yanada wata Matar.

Ana cikin hakan yayi tafiyar dazata daukesa kusan sati biyu ko uku ma.

Ranar dazai tafi acan suka kwana dagacan school ya ajiyeta Koda kowa ya farka Bata gida Bilkisu tace musu ta wuce school tunda safe dayake exams Sukeyi.

Yana ajiyeta airport suka wuce shida Al-Amin Ahmed yakaisu yakoma makaranta jiranta.

Karfe uku ta fito makarantar Suka dawo gida wanka kawai tayi taci abinci ta kwanta sbd Dan zazzabin datakeji tun shekaran jiya sama sama.

Koda maraice yayi jikinta yayi zafi Sosai Haka ta Dan daure aka Bata magana tasha,

Hankalin mommy tashi yayi sbd lurada wata yaqare ciwon marartane na period zaizo wannan karonma kaman ta gota harda kusan sati daya,

Mamakin lamarin mommy tayi Amma dai ganin tafara zazzabin Mai zafi saita San ciwon ne zaizo.

A sukwane ta wuni kwance hakama washe gari ta tashi da zazzabin dayake sun Saba da ciwon nata sai akaci gaba da Bata maganin datakesha hakan saiya fara sata ciwon Mara ahankali batareda itama tayi wani tunaninba ta dauka period dinne zaizo dan harta manta da ciwon nata dataga lokaci ya wuce batai period dinmaba kwata kwata.

****Haka kawai Bilkees ta zowa su umma a wuya ta tsaya sbd gabaki daya ta tattara zancen lamarin Mijinta da aurensa ta watsar tamaida hankali gurin rayuwar Matan manya dasukeyi itada qawayenta su Nafee data dawo Suka sake dinkewa abinsu ganin kowa ya watsar da kwallon mangwaro ya huta da quda,

Ita Nafee tana sane da AQEEL ASAD Yana tareda aurensa da Amal Bai rabuba Amma taqi fadawa Bilkees din sbd kada tayi rigima auren ya mutu tasan Amal na rabuwa da aure wallahi Allah ne kawai zai Hana Mijinta aurenta Dan Haka ta zabi yin shiru tana sake Dora Bilkees din a hanyoyin da bama zatasan akwai aurenba bare tayi wani yunqurin.

Umma Babu safiyar da Bata debewa bilkees akan wawanci da haukata gashi Suma yanzu sunaji suna gani AQEEL yake qin kwana a gida wasu lokutan Wanda sune kadai sukasan inda ake gashi ba damar magana saidai Ido da guni a zuci Wanda yafi komai ciwo.

Haj Maryamah kuwa ganin da gaske suna zaune zasu iya samun mugun labarin sabuwar hadin zuria da Zainab da Haka tafara dagawa Bilkees hankali akan sake haihuwa sbd Daman can Dan ana Zaune kalau ne bata maganar asake Amma har cikin ranta 'yaya takeson AQEEL ya Haifa musu masu yawa tunda ita Shi kadaine, itama ita kadaice agun ummanta gwara shi ya hayayyafo da yawa tunda akwai arziki Mai yalwanda ko 'yayansu bazasuyi talauciba da yardar Allah hakama Shi kansa tasa yanada masifan son yara tunda sungani tun haihuwar Zainab datai ta Amal dn yabi ya rikice.

Bilkees ganin masifar dasuka bullo Mata da ita ta maganar haihuwa ba arziki Ido a rufe gabaki daya sun sauya Mata Dan ita umma harda maganar Daren farkon Nan tana ranta takasa cirewa ace matar dasuka kawo Masa Babu Wani motsi salin alin Amma 'yar karuwa anzo Anata neman madinka da likitoci hardasu gashe gashe Dan Haka akwai zance a qasa tsakaninta da uwar Bilkees idan Takoma Cameroon bata yarda dasuba rufa rufa sukai Mata aka bata ta aurawa jikanta.

Bilkees da mufeeda dataji abinda sukewa mahaifiyarta binsu suka ringa Yi da magana

Bilkees Babu ranarda Bata debewa tsufan umman Cameroon albarka tana fatan ta tattara Takoma Cameroon sbd itace mahadin komai.

##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥

Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥

Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥

Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥

Safiya huguma

*KI KULANI*🔥

Miss xoxo

Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171

Maryam sani

Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*🔥

Mamugee
63
Chapter 77 · 0% Book details