← Book details Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 95

Sashe 78

Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

•Abu na farko daya sake biyowa bayan zazzabinta shine yawan baccinta,
Ga zazzabi koyaushe Mai karfi ga yawan baccin saikuma Dan ciwon marar gashi period din yaqi zuwa,
Hankalin Haj Zainab fara tashi yayi akan ciwon duk da hankali ko tinaninta Bai taba zuwa kan wani tunanin wani Abu Mai Kama da wani abinba Amal zata iya alkatawa.
Ita kanta Amal din gain lamarin na neman ja Mata attention din mommyn sosai sbd abinda tafara magana shine meyasa wanna Karon Babu wannan ciwon marar kwata kwata sbd Dan wannan datakeyi bama ciwo bane akan Wanda ta Saba.
Tashin hankali tashiga sbd sanin meyasa batai ciwon marar ba kaman vanda vafada Mata ai bazata garaba ayanzu sbd….....kasa qarasa tunanin tayi sai ta aro qarfin halin gaske ta dorawa kanta qarfin danne ciwon.Asibiti mommy tace zasuje a washe gari Dan Haka cikin mummunan yanayin tsoro da tashin hankali da kunar suie asibitin ace any wani abin da itane shiyasa ta Dena ciwon Mara.
Da wane Ido zata kalli mommynta da familynta musamman idan sukaji Wanda yayi wani abun da ita.
Kasa daukanta bacci yayi duk yanda kuwa take da tsananin bacci a kwanakin.
Da kanta ya cake cikin tashin hankali da fargabar wayewar gari kuka ta fashe dashi tana rufe idanuwanta Dan Bata taba tunanin akwai dalili akusaba Wanda zaisa a iya ganewa.,
•Fatanta Allah yakawo dalilin dazai hanasu zuwa asibiti har aje aji wani abin tayi idanma ance tabbas zatayi denying Kai tsaye sbd bazata yarda da wanna zancenba.
Sai guraren asuba bacci ya dauketa da ciwon kai Mai
Dan tsanani.
Batafi awa biyu tana baccinba ta farka tana duba agogo taga 8 saura Dan Haka ta tashi ta sauko gadon kanta na sake tsananta Mata ciwo ta nufi toilet.
Brush da wanka tayo tana fitowa ta shirya cikin doguwar Abaya blue da simple gyaran data saba ta fito wayarta da hanbag dinta a hannunta ta fice gidan kowama Bai tashiba Daman takira Ahmed tana fitowa
Suka wuce makaranta sbd tunda Suka kammala exam har aka guntun hutun aka dawo batajeba tana fama da kanta.
Yanzune aka dawo Dan Haka ba waima angama dawowa hutun bane gabaki daya Dan Haka Babu Wani karutu sosai ko mutane sosai Sosai dasuka dawo ita kanta Bata fara zuwa da wuri Idan aka dawo
Amma yanzu ba yanda ta ivane tana cikin tsananin
Hali na damuwa da tashin hankalin mommy da zasu asibiti a yau din shiyasa ta gudo.
A mota tayi zamanta tunda Suka iso makarantar ahakan bacci ya dauketa
Ahmed saiya fita motar yabar Mata ita a kunne sbd
AC Tasha baccinta tsawon lokaci kafin Kiran mommy ya farkar da ita dakuma yunwa da zazzabi Mai garfi daya sake sauko Mata,
Cikin fada sosai mommy ke tambayarta tana inane?
Dan daidaita muryarta tayi ta sanar Mata tana school kiranta akai akan akwai lecture din da zasuyi Mai mahummanci da safen.
Rasa abin fada Mommyn tayi sbd takaici sai kawai ta kashe wayar tana cewa,"Neman lafiyar takima sai an ringa binki Ana rarrashi.
Ajiyar zuciya Amal ta sake jikinta na sanyi sbd duk abinda mommynta tace tayi shi takeyi Basa tsallake maganarta duk freedom da rayuwar yancin dasukeyi ba takura ba saka Ido to sunada tarbiyar data Basu shine basada rashin kunya ko gadara tareda reni ga wainda sukasan manyansu ne musamman ita datake mahaifiyarsi,
Amma ita yau gata a tsaka me wuya na wanna yanayi daya sameta,
WIh batasan tayaya zata iya kallo ko Shiga gidansuba idan akasan me tai ta Dena ciwon Mara din.,
Me ma zatace Akan AQEEL ASAD din Wanda ko gaisawa baa San sunayiba bare kalion juna har irin wannan abin yashiga,WIh musawa zatayi duk likata ta bada tabbacin cewa
tagano kila tayi sex ne ta dena.
Fitowa makaranta sukai tace suje talindo steak house.
Suna zuwa shine ya Shiga yayo Mata order na
abincinsu da AQEEL ASAD ya koya Mataci sbd acan
kawai ake siyo musu abinci.
Brown spaghetti sauce dinsu takeso sosai kaman maita kusan duk suna tare sai ansiyo Mata duk da
Bata taba fadaba Amma yanda take cinta yanayinta
Yana nuna yanda takejin dadin cin nata yasa ya
fahimci tana tsananin sonta Dan Haka duk zaa kawo
musu abinci sai anhado da ita Kuma Idan so nawa
zataji saita lumshe Ido cikin Jin dadinta.
Suna barowa Kai tsaye school Suka koma acan taci
abincin ko gamawa batayiba vau din sai amai ya biyo
baya sbd ba ahaka ta Saba cintaba,Yawanci a zaune kan gafafunsa yake zaunar da ita a dining ya ringa Bata abaki tanaci atmosphere din bama daya Dana makaranta ba aikuwa take cikinta yakasa amsa ta ringa amai Mai qarfi da galabaitarwa.
Hankalin Ahmed tashi yay ya rasa ya zaiyi Kuma waye zai Kira gashi ba Daman tabata,
Bottle water guda uku ya siyo Mata masu Dan sanyi yakawo ta karba da gyar ta iya wanke fuskarta da bakinta wani mummunan jiri na dibanta ta dawo mota tana shiga jikinta ya ringa kakkarwa.
Sake shiga damuwa Ahmed yay Yana Tunanin kaita gida Amma Kuma ya lura kaman yau tsoron zuwa gidan takeyi baisan meyake faruwaba kada yakaita ya lalata Mata shiri ko wani abinda takeda niyar Yi Dan
Haka saiya sake shiga damuwa.
Wayar AQEEL ASAD yafara Kira Amma sam baya dauka bd tana silent Yana meeting da mutane Kuma tana kife ne a gefensa so bazaiga ko hasken kiranba.
Kira kusan biyar yay masa Bai dagaba Dan Haka ya lalubo numbern Al-Amin ya saka kiransa.
Na farko Bai dagaba shima bd meeting din Amma ganin Ahmed ya sake Kiran yasan maganace data shafi Amal da ogansa tunda Shi duk kiransa Akan abinda ya shafa Amal ne bd Dan ita kawai aka daukesa aikin.
Ahankali Al-Amin din ya miqe ya fito daga office na meeting din ya Dan Yi gaba kadan kafin ya daga Yana cewa,
"Yes, Ahmed lafiya dai ko??
Ajiyar zuciya Ahmed ya sauke cikin damuwa Mai tsananin gaske ya sanar dashi Ms Amal ce batada lafiya sosai.
Dan juyawa Al-Amin yayi ya kalli kofar daya fito kafin mamaki da kulawa yace,
"Baa kaita asibiti bane?
Tana inane?
Bayani yayi Masa a tagaice cewan kaman batasan zuwa gida Kuma ga ciwon sosai Yana damunta shi baisan ya zeyi bane shiyasa yakira Sir AQEEL yafada
Masa sai ya sanarda yanda zaayi idan ya kaita gidane kokuma asibiti.
Sake Shiga mamaki da Dan abinda zaayi din Dan shima anan din Kam baisan mezaice ba sbd maganar ivalin AQEEL ASAD din ake magana Kuma ko Dan tsakanin Nan yanzu yafi kowa sanin Amal ba garamin matsayi take dashiba a zuciyar Sir AQEEL din Dan
Haka shima bazai zage ya Fadi komai Dan Haka sai Sake Shiga mamaki da Dan abinda zaayi din Dan shima anan din Kam baisan mezaice ba sbd maganar ivalin AQEEL ASAD din ake magana Kuma ko Dan tsakanin Nan yanzu yafi kowa sanin Amal ba garamin matsayi take dashiba a zuciar Sir AQEEL din Dan
Haka shima bazai zage ya Fadi komai Dan Haka sai kawai yace Ahmed din yakaita gidan karatun zaa turo likita yanzu idan ya fadawa AQEEL ASAD din.
Ciki ya dawo ya qaraso gurin AQEEL ahankali tareda
Dan ranqwafowa cikin tausasa murya qasa gasa yace,
"Sir Ms Amal ce ba lafiya sosai inji Ahmed,
Nace yakaita gidan Karatu Dr tayo na zuwa insha
Allah.
Shiru yayi ya dauke wuta gaba daya kaman Wanda Bai fahimta hausar ba kafin ya juyo ahankali ya kalli
Al-Amin din Yana zuba Masa idanuwansa ya bude
Baki yace, "MARYAMAH??
gyada Kai Al-Amin yayi ahankali Yana saka Kiran Dr tayo ya juya ya fice cikin gaggawa yace taje ta duba
Amal din.
Yana dawowa Kai tsaye AQEEL yace ya siya musu tickets zasubi jirgin yamma idan akwai.
Amal kuwa gidan Karatu suka Isa suna Isa ta fito ta lallaba tashiga ciki sbd itama bazaso zuwa gidaba a wanna yanayin zai sake dagawa mommy hankali da zuwansu asibiti.
Kai tsaye bedroom dinsa ta nufa ta shiga ta zube gasa ta kwanta tana maida wani irin numfashi Mai
Dan wahala
Tun tana juye juye hartasamu bacci Mai garfi ya dauketa cikeda azabar zafin ciwon zazzabi.
Tana grin tana bacci saiga Dr tayo wadda da Bata gantaba a koina ta iso dakin tayi knocking daqyar
Amal din ta farka ta jita ta rarrafo tazo tabude kofar ko tsayuwa Bata iya yi.
Kamata Dr tayo tayi Suka koma dayan bedroom din sbd Nan master bedroom dinsane ko wancan lokacin sbd yanayin jikin natane yasa Suka shigo.
Zaunar da ita tayi bakin gadon dayan bedroom din tana kallon yanayinta gabaki daya ta rasa karfin jikinta da kuzari.
Fara taba jikinta tayi taji zafinsa ta kwantar da ita tareda duba plse dinta take tagane tanada ciki ajikinta saidai tana bugatan sake tabbatarwa Amma kafin Nan abubuwa ta rubutawa Ahmed yaje asibitin ta yakarbo Mata a pharmacy yana kawowa drip tafara daura Mata ta zauna tana jiran yaqare jikinta ya Dan sake suje asibiti a can akwai abinda take buqatan dubawa.
Sai guraren 3 drip din yaqare Kuma tasamu karfin jikinta Sosai harma da isashen bacci
Wanka tayi jikinta ya sake sakewa tayi sallah Tasha yoghurt Mai sanyi sosai a fridge.
Har lokacin Dr tayo ce take tareda ita sbd AQEEL din daya bugaci hakan ita batama San yasan meyake faruwaba.
Fitowa sukayi tareda Dr tayo Suka nufi asibitin Dan itama tanason sanin matsalar Bata Saba ciwo Mai kashe jiki irin wannan dinba.
A motar Dr tayo din Suka tafi tabar Ahmed anan akan daga can Dr zata ajiyeta gida ta yanda mommy zatasan taje asibiti bama sai takaitaba any wani bude buden zance.Isarsu asibitin Kai tsaye dr tayo scanning Tai Mata
Dan tafison tagani Kai tsaye din.
Dr tayo na cewa scanning zatayi Mata taji gabanta yayi wani faduwanda yasata dakatawa daga Hawa gadon scanning din ta kalleta da idanuwanta dasukai ciki tsaban firgita ahankali tace,
"Scanning name zaayi??
Qarasa zaunar da ita akai Dr tayo tayi tana cewa,
"Naga alaman kinda ciki ne inason tabbatarwa.
Shiru tayi tana kokarin fahimatar zancen dakyau a bude bd qwaqwalwanta daya kasa daukan zancan lokaci daya,
"Ciki as in ciki na haihuwan baby??
Gyada Mata Kai Dr tayi tana Dan kallonta da mamaki tace,
"Kina mamaki ne?
Qasa riqeta gafafunta sukai ta silale zata zame Dr tayo tayi saurin rigota tana cewa,
"Ki kula fa karki illata kanki da babynki.
Tunda mommynta ta haifeta tayi wayo tasan kanta tun tana Yar Qarama harta kawo yanzu Bata taba kukan wayyo ita Allah ba sai alokacin.
Ihun kuka Mai garfi ta fashe dashi tana Hawa gadon dukkanin jikinta na rawa tace a duba din idan da da akwaisa Amma dai fatarta Allah ubangiji yasa Babu cikin Dan kuwa batajin a rayuwarta zata shiga masifar datafi ace cikine a jikinta.
Innalillahi wanna ilayhi rajiun" ta ringa maimaitawa dukkanin jikinta na rawa gabaki daya ciwon zazzabinta bacewa yay take tajita Ras sbd tsananin tashin hankali da firgici.
Yanda tashiga tashin hankali da firgici yasa Dr tayo
Jin firgicin itama tana mamakin meyene abin daga hankali a ciki musamman irin wanna da zaace
AQEEL ASAD ne ubansa ita sai take ganin kaman sa'ar IDON NERA's dinne atlast dai zasu hada jini da
AQEEL ASAD irin masu kudin dasukeso ace sunada alaga dasu,
Kuma garshe dai gashi sun samu jikan da suketa so daga Siddi Dan ko ita tayita duba siddin akan nema haihuwa.
Chapter 78 · 0% Book details