← Book details Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 95

Sashe 55

Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata ajiyar zuciya ta sauke tana da sake murmushin da batasan lokacinda yake saukowa fuskartaba.

Kallonta yakeyi har lokacin ganin yanda amincewar tasa tayi Mata Dadi.

Dauke idonsa yayi akanta ya maida kan hanyar dakin Amal yace,

"Bazata sake fitaba batareda saniba

Idan ta taka wannan dokar zata koma can gidan a ranar Mami.

Ajiyar zuciya Haj Zainab din ta sauke tareda kallonsa tace,

"Karatun nata fa?

Zanyi maganarsa daga baya yafada Yana kallon agogon hannunsa zaiyi magana Amal ta fito daga dakinta sanyeda doguwar Riga Mara hannu tana kawowa tsakiyar palon ta dauke Kai ta sauka qasa Kai tsaye ta nufi dining.

Bilkisu ce takawo abincin da mommyn tace ta hado takawo sama anan AQEEL zaiyi dinner tareda ita.

Siddi da Amal ne kawai sukaci abinci a dining suna gamawa suka koma sama suka shige dakin Amal din dan anan siddi zatayi fira tunda Mommy na tareda AQEEL ASAD a palon.

Tunda Amal ta shige bata Kuma fitowaba har yabar gidan Bata fitoba

Tayi kwanciyar ta adaki har Siddi tagama surutunta akan AQEEL ASAD din da charisma dinsa tabar dakin Bata kulata sbd ciwon kaima surutun ya sakar Mata.

*****Daga gidan asibiti yasake komawa sbd duba ummansa da kusan so uku kenan Yana komawa asibitin a ranar.

Zaune ya taddata Jamila Mai aikinta ta shekaru tana harhada sauran Yan kayansu an sallameta zasu wuce gida da ita.

Yasan da sallamar shiyasa yazo daukan nata da Kansa.

Ko kallonsa batayiba ya Kamata ta dakatar dashi Akan zata iya da kanta.

Tashi tayi ahankali ta nufi kofa duk suka biyo bayanta zuwa mota.

Saida tashiga motarsa ya rufe Mata ya zagaya ya Shiga yaja suka bar asibitin,

Jamila kuwa saidai tabi driver da dayar motar.

Har suka Isa Babu Wanda yayi magana acikinsu sbd ya lurada ko fuskarsa taqi kalla da alama Bata son ganinsa saita sauko shiyasa bazai iya takurata ba.

Suna Isa gida har palonta ya rakata

Tana shiga ta wuce dakinta Kai tsaye tabarsa tsaye.

Bai damuba ya juya a natse yabar sashen tareda nufar part dinsa Kai tsaye,

Nanma tunda Bilkees da mufeeda sukaji dawowarsa suka shige suka qi fitowa sbd son su daga Masa hankali yarasa gane komai har sai ummansa tadawo daga asibiti tukuna zata tada zancen a gaya Mata cikakkiyar gaskiyar abinda yake faruwa.

Babu Wanda yanema acikinsu sbd yasan kome sukeyi suna sane Dan Haka Kai tsaye ya wuce bedroom dinsa yayi Shirin baccinsa ya kwanta batareda damuwan kowaba a ransa sbd kowaccensu shine yakeda iko da ita hakama Babu wadda fushinta zai Jima yasani zasu nemesa ne da kansu daga umman harsu Bilkees da mufeeda...harma da ita Amal din.

Washe gari Kai tsaye Bai tsaya batawa Kansa time ba ya shirya cikin ash Armani's ya fito cikeda kwarjini da kyansa Mai sanyi da nutsuwa.

Mufeeda yafara gani a Palo tana jiran fitowarsa itama school zata takeson ya ajiyeta sbd Bata fara driving ba da kanta.

Gaidasa tayi batareda ta kallesa ba.

Shima Bai kalletaba ya amsa Kai tsaye yayi gaba ta bisa tana kallon hanyar kofar dakin umminta tana sake Jin tsanar Amal Idon Nera sbd akanta ne gashinan iyayenta sun samu matsalar da Basu taba samuba tun aurensu.

Gurinsu ummansa ya shiga Amma Babu wadda ta fito acikinsu dan Haka ya fito ya nufi motar dazasu fita da ita Kai tsaye.

Malam Rabiu ne yayi Masa barka da fitowa kafin suka fito.

A makaranta suka ajiye mufeeda kafin ya suka wuce gidan Maminsa Kai tsaye.

A harabar gidan suna shigowa suka tadda Haj Zainab zata fita itama tareda Siddi harma da Amal dake tsaye cikin kayan bacci yauma Riga da wando masu santsi ash.

Kallon mamin takeyi datace Mata kada ta fita koina umarnin Mijinta ne.

Mamaki da bacin Rai ne Mai tsanani a kan fuskarta musamman da mommyn ta nuna aminta da hakan..

Magana zatai motar AQEEL din tashigo harabar gidan.

Daga nesa yacewa malam Rabiu yayi parking ya fita yakoma waje gurin securities.

Fuskarsa a kame ya fito motar gabaki daya kwarjininsa da kame fuskar tasa yasa dukkaninsu yin shiru Banda Amal datake Jin kamar zata fasa kuka ta juya zuciyarta na ciwo tabar gurin kafin ya qaraso.

##MAMUH#

#HOTLOVE#AQEEL ASAD#AMAL IDON NERA.

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥

Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥

Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥

Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥

Safiya huguma

*KI KULANI*🔥

Miss xoxo

Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171

Maryam sani

Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*🔥
44

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

44

Yana qasarawo Siddi ce tafara gaidasa cikin kulawa kafin shikuma ya gaida Maminsa Yana dauke kallonsa daga hanyar da Amal tabi.

Yanayinsa yasa Haj Zainab Dan fara bayanin Fitowar Amal din akan tanason binsu ne wani Dan gurin dazasu tafi Mai mahummanci.

Dan shiru yayi Yana sauraronta kafin ya Mata kallon nutsuwa yana karanto kauna da sobon datayi na kasa takurawa 'yayanta.

Rufe Ido yayi ya bude sbd shikuma bayajin zaa samu yanda akeso din daga garesa ta wannan bangaren.

Wucewa sukai shikuma ya qarasa ciki sbd kamar Amal din Bata fahimci abinda ya fada Mata ba daga ita har Mamin.

Yana shigowa Palo su Bilkisu suka gaidasa cikin girmamawa kansu aqasa.

Amsawa yayi Kai tsaye tareda wucewa palon Mami baya yacewa Bilkisu ta Kira Masa Amal.

Da sauri Bilkisun ta nufi kofar dakin Amal tai knocking ahankali tareda bude kofar ta tura ahankali.

Amal dake tsaye tana amsa waya ranta a bace duk sbd zuwansa da maganar rashin fitarta datake ji bakin umman da safen.

Meyake nufi da nuna wannan ikon nasa akanta?,

Yaje can ya nuna akan mahaukaciyar matarsa data Gama mutuwa a sonsa Kamar yanda Siddi datakeda lokacin iya sanin labarinsa tafada.

Jefarda wayarta tayi kan gafo tana juyowa ta kalli Bilkisu kyakkwar fuskarta a hade ta zuba Mata ido tana jiran Jin abinda ya kawota.

Bata qarasa shogowa gabaki dayaba dakin ta Dan sassauta muryar sbd Yana palon Na sama zai iya jiyosu tace,

"Auntie Amal Maigidan ne yake kiranki....

Wani kallo ta jehowa Bilkisu tana kokarin danne fushinta sbd kada ta sauke akanta tunda batada laifi Amma Kuma maganarta tayi mugun tinzirata da mamaki tace,

"Waye maigidan?

Kuma na wane gidan?

"Maigidanki Auntie.

Rasa abin fadawa Bilkisun tayi sai kawai ta nuna Mata Kofa da idanuwanta dasuka Dan fara sauyawa tai Mata alamar ta fice daga dakin.

Juyawa Bilkisu tayi tana sake kallon Amal sbd Koda take Yar aiki me Kai sako bazata taba iya zuwa gabansaba tace Masa Amal din ta korota da sakon.

Tsayawa tasake bayan takai kofa ta waiwayo tana rasa abin fada ko yi da idan ta dawo Masa da rashin amsa ko bada tabbacin Amal din na zuwa,

"Idan naje me zance Auntie??

Rufe fararen idanuwanta tayi tana sakin qaramin numfashi Mai zafi sbd ciwon kai Bilkisun zata saka Mata da bacin ran zancenta akan Wanda yake cinta,

Toilet ta juya kawai ta wuce tana danne zuciyarta daga bugawa akan rashin hanata fita fa ake magana,.

Mommy datake cewa saiya bada izinin komai nata yanzu idan ta tambaya,

Ta hakura da duk abinda zaace saita tambayesa Dan Babu ranarda takejin zata iya zubar Masa da kanta tayi Masa hakan.

Bata bawa Bilkisu amasaba ta shige toilet tareda bugo kofar,

Bilkisu na ganin hakan jikinta yayi sanyi ta juyo tana Dan hada abinda zata fada akan sakon.

A natse cikin girmamawa ta Dan tsaya nesa dashi kadan zatai magana ya katseta da tausasshiyar muryarsa Mai nutsuwa da kamewa yace,

Kije kawai.

Juyawa tayi tabar gurin Babu Bata lokaci ta sauko kasa Takoma kitchen gurin aikinta.

Wayarsa da ake Kira yakalla yaga sunan Al-Amin Kai tsaye ya dauka a natse cikin rashin Jan zancen yace,

"Bazan shigo office da wuri ba akwai abinda zanyi ka rage schedules dina na yau.

Kashe wayar yayi tareda ajiyewa gefensa ya Dan rintse idanuwansa ya bude batareda ya waiwaya ko kadanba ya kalli hanyar dakin nata.

Wanka tayo tafito daureda towel blue tana kokarin zaunawa gaban madubi wayarta tayi ringing.

Kamar bazata dubaba sai Kuma ta juya ta dauko wayar a kan gadon

Sunan mommynta ne Dan Haka ta dauka Mai tsaye ahankali tana cewa,

"Naam mommy.

"Amal akwai takardunku da muka manta na process din ganin likitanku da zaayi,

Kiduba suna kan gaban mirror ki bawa Bilkisu takaiwa Taju yakawon yanzu Ina jiransa a office zaa karba.

"Ok mommy" tace ahankali tana nufar kofar dakinta da wayar ahannunta ta nufi bedroom din Mommyn dake kusa da nata.

Gabaki daya ta manta dashi takuma San Babu kowa agidan

Ko akwai Daman iya sune suke hawawo sama.

Dakin ta shiga tadauko takardun ta nufi stairs zata qwala Kiran Bilkisu hancinta ya shaqo qamshinta a bayansa da sauri tayi saurin juyowa sbd firgitar datayi Kuma Bata lura da mutum a palon ba data fito.

Saurin ja da baya tayi tana Masa wani irin kallon mamaki da bacin ran ganinsa gabanta a yanayin datake ciki.

Shi kansa baiyi marmarin sake yimata kallo na biyu ba bayan na farkon da yayi.,

Baya tasake ja tana kokarin kaucewa ta wucesa komawa bedroom dinta fuskarta a daure,

Dawo da ita yayi gabansa ya tsayar ya kalli fuskarta shima tasa Fuskar a matukar kame Wanda yasata Dan sake kokarin ja da baya Amma wani kallon daya jefata dashi yasata kasa daga qafafun nata tana sake daure fuska gashi ya tsaya gabanta ta yanda bazata iya wucewaba sai jikinsu ya Hadu kokuma idan ba turesa zatayi ba

Cikin biyun bazata kaunaci ko dayaba sbd data iya Kai hannu jikinsa harma ta turesa tafisan tayita tsayuwa a gurin idan ya gaji ya janye ta wuce.

Son yimata kallon tsaf yakeyi Amma bayason hakan sbd tabbatarda maganarsa akan tsayuwa idan yayi.

Muryarsa Mai tattareda nutsuwa da bayyanarda tsayuwa da rashin son mamaita magana yace,

Bana maimaita zance wa iyalina,

The 3rd time da Zaki Kuma fitowa daga dakinki da sleeping dress ko makamancinsu shine last time da Zaki kwana a gidan Nan....
Chapter 55 · 0% Book details