← Book details Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 95

Sashe 23

Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Turus ta tsaya batareda ta qarasaba tana kallon zainab din cikin shahararren mamaki da tsoro harma da wata irin qyama dake bayyane ganinta da sabon 'da a hannu dunkule Acikin zani.

Umma data fito motar tana tafiya ahankali sbd manyanci sosai daya kamata tsayawa tayi kallon abinda ke hannun Zainab din kafin a rude tace"

Ke,Meye haka?
Daga Ina?
Me kikeyi anan?
Bibiyarta kikeyi ne?
Meye wannan a hannunki?
Wata haihuwar Kika sake Yi kenan??
Shi Dan daudun naki bai fada Miki baa haihuwa a bariki ba???
Me kikeso da kikazo Nan da wannan abin naki?

Me Maryamah tai Miki da kikeson Bata sunanta agun dangin Mijinta da mutanen dake ganin girmanta matuqa......

Haj Maryamah da baqin ciki Mai tsanani da tashin hankali sukai Mata yawa kasa magana tai ta dauke kallonta daga kallon Zainab din da yaranta biyu dake tareda ita,

Wace qaddarar ce wannan ace ubanta daya da karuwa Mai 'da
Tabbacin ita Yar barikin ce kenan....

Muryarta kunshe da damuwa da zallan baqin ciki da damuwa tace"

Bayan kudin gadonki dake hannuna banajin akwai dalili ko alaqar dazata saka ki zo inda nake,
Me kikeso?
Kudin gadonki???

Mota ta juya ta dauko Jakarta tabude ta fiddo rafar 100k guda uku ta jefa Mata cikin tsananin bacin Rai da baqin cikin dake neman rufe zuciyarta tace"

Rayuwar da Kika zabarwa kanki da zuriarki kenan ko Zainab??
To kije kiyi rayuwar yanda kikeso saidai kada ki sake zuwa inda nake sbd har abada bazan taba iya kallon karuw.....

Kasa qarasa sunan tayi sbd baqin cikin fadarsa ma datakeyi...

Kije Zainab...
Kije...
Tashi kije....

Zainab data kasa dagowa ta kallesu sbd batasan ta ina suka diroba itama...

Sai alokacinda Haj Maryamah ta jefo Mata kudin ta dago ta kalleta idanuwanta na radadi da zafin kalaman 'yar uwarta.....

Magana zatayi umma ta katseta da cewa"

Idan kincika Yar halak dakiketa fada kotu to karki Kuma ambatar ko sunan Maryamah da 'danta bare zuwa inda suke sbd kin Riga kin lalata sunanki Dana zuriarki to karki lalata Mata nata....

Har abada babu abinda zai hada tsaftatacciyar rayuwarta da zuriarta da wainda suka qazanta rayuwarsu.......
Zainab kin zama tamkar rubabbiyar rayuwa wadda zata lalata suna da mutuncin duk Wanda ya rabeta...

Allah yasa kada ki lalata rayuwar wainnan yayan naki Kamar yanda Kika lalata taki.......

Hawayen dataketa nema tsawon lokacin ne yau Allah yabasu ikon saukowa daga idanuwanta dasukai jajir...

Haj Maryamah take kallo da dukkanin Idanuwanta dake tsayayar hawaye sbd ayanxu tana ganin ita kadaice takeda alaqa da ita Dan itace jinin,
Itace suka bada uba daya
Amma umma batada alaqar komai da ita tunda Bata haifetaba Kamar yanda ta fada....

Hawaye sosai takeyi masu radadi daga zuciya,
Kuka Mai qarfi ta fashe dashi agaban Haj Maryamah din wadda itama zuciyarta wani radadi da nauyin take Mata...

Share hawayenta tayi dukda sunkasa tsayawa ta dago takalli Yar uwarta Kuma yayarta Acikin wani irin sauti Mai bayyanarda tabbacin abinda zata fada tace,

"A yanda umma takira rayuwata da rubabbiyar rayuwar da zata lalata rayuwar Wanda ta raba
Ayau Ina Miki alkawarin har abada bazaki sake ganin Zainab ba,..
Alaqar da kuka yanke Dani ayau Nima na yafe na yanke alaqa ta jini data zahiri dake,
Kece jinina kece nakeda alaqa dake ba umma ba kema to ayau din na yanke kamar yanda Kika fada ba Ni bake har abada,
Bani ba jininki,
Bani ba zuriarki,
Ayau har sunan mahaifinmu na yafe Miki daga yau ko sunan mahaifi daya bazaa sake kiranmu dashiba...
Sunanki ma a bakina nayi alkawarin bazan sake fadarsaba har ranarda zan bar Miki duniyar na...

Wani mahaukacin Mari umma ta sakarwa Zainab din cikin tsananin fushi da takaici tareda bacin rai Mai tsanani tace,

"Basai kin nuna Mana cikarki Yar barikiba mun tabbatar tunda gashinan munga shaidar a hannunki,

Itace tafi kowa baqin ciki da takaicima idan kinkira sunanta ita da aka sakawa 'yarki sunanta........

Daga sakannin da nayi alqawarin yanke alaqar Nan a wannan lokacin na rufewa 'yata sunan.....
Baniba ko Wanda bai sanniba bazai sake Kiran sunan 'yata wannan sunanba.......

Kudinsu dake qasa ta kalla kafin ta Kama hannun MARYAMAH tace,

"Kudin gado na Kuma na barwa Allah tintini.

Jan hannun yarta tayi suka bar gurin zuciyarta na wata irin zafi da tafarfasa.

Asibiti Takoma ta tadda gawar siddi na jiran Azo a dauka Dan Haka ta Kuma fitowa ta nufi gidansu tarasa was zata sanarwa haka tadawo asibitin ta sanar musu basuda kowa ayi janaizarta anan.

Gida tadawo tayi kwanan zaune,
Zuciyarta zafi,qunci,radadi da hayaqi takeyi Mata..
Komai yasake juyawa Mata akaro na babu adadi..

Yaya zata fuskanci rayuwa da yara biyu bayan ita kanta haryanxu bata tsayarwa kantaba...

Washe gari acan asibitin akaiwa siddi komai aka Kai maqabarta saima data biya kudin mota dasu likafani.

Anan gidan take koina ya dauki labarin mutuwar siddi.

Madara ta siyo tana shayar da babyn wadda ta sakawa sunan mahaifiyarta wato siddiqa itama tana kiranta da siddi....

Sabuwar rayuwar jaruma Kuma tsayayyar mace ta budewa kanta sbd 'yayanta Wato MARYAMAH wadda ta sauyawa suna AMAL da Siddi..

Sanaoi da gwagwarmaya tafada gadan gadan Kuma Allah ya tallafa Mata sai gashi tanata tsayuwa da kanta.

Hausawa sukace zama da madaukin kwanwa.....
Rayuwarta ta sauya sosai Dan kuwa ta tashi daga Zainab mai sanyin jiki Dana zuciya zuwa Zainab mai zafi da rashin daukan Reni.

Zama cikin karuwai da Yan bariki kala kala yasa idanuwanta budewa fiyeda su dinma Amma duk da hakan Bata taba aikata Zina ba.

Babban matakin nasarar data fara samu na taka Wanda ya takasu shine sonta da Ds ya fito ya nuna yanayi har lokacin baya Yana sane da mutuwar siddi sanadin haihuwar cikinda yasan shine yayi.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma

*KI KULANI*🔥
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥

*_Arewabooks@Mamuhgee_*
19
Duk wata alamar kulawa Ds ya nunawa zainab sbd Zainab din yanzu daban take da zainab din dah kwata kwata,

Ta wanke tafito fes da ita duk da gwagwarmayar datakeyi Amma tana cikin rufin asiri sosai.,

AMAL da Siddi suna cikin lafiyayyar kulawa da kaunar mahaifiyar tasu,

Ta tsaya musu a komai babu abinda suka nema yafi karfinsu,
Komai nasu iri daya take siya musu babu wani bambamci saidai babbancin kala sbd fatarsu ba daya ba, AMAL tafi siddi haske itakuma siddi tafita kaurin jiki..

Zuwa wannan lokacin kusan kowa ya manta da siddi ba zainab ce ta haifeta ba wainda ma basusan asalin waye mahaifiyar siddin ba sunfi yawa..

AMAL tana primary ita Kuma siddi tana nursery akai rikicin wata yarinya Qarama a anguwa da aka lalata abun babu Dadin ji da gani,

Zainab taji hankalinta yayi matuqar tashi akan yayanta,

A duniya yanzu data bude Ido tasan kanta da yanci to mutuncin 'yayanta shine abinda kawai yake Bata tsoro da girgizata,
Bata kaunar ko sunan fyade taji sbd Su Amal dinta,
Sbd sune taji zama acikin gidan da anguwar yane neman ficewa a ranta sbd tako Ina anguwar 'yan duniya da mutanen banza ne aciki uwa uba gidan nasu dasuke ciki duk da dokar Lulu na Nan Bata Bari ta lalaceba saima qarfi jajircewa datayi ta qarawa dokar karfi sbd 'yaya matane da ita.

Alhaji Bulama wani Dan kasuwa Kuma Dan siyasa shine ya nacewa buqatarta amma Sam taqi basa damar suyi lalata shiyasa yake sakar Mata kudi sosai Dan kawai ya samu sauya raayinta ta bashi Dama su huta..

A yanda ta Gama karance Shi tsaf ba sonta yakeyiba shaawarta yakeyi Mai tsanani itama Bata taba jin alamar zata so kowane namijin ba saidai shima tsabar nacinsa taqi yarda saiya bullo Mata da maganar aure...

Batayi mamaki ba hakama Bata Musawa aurenba Dan tana buqatan dauke 'yayanta daga gidan.

Auren akayi ta tare Dan babban gidansa dake kusada anguwar tasu take ta bude sabuwar rayuwa,

Bude hannuwanta tayi ta ringa qwaqwalar kudi a gurin alhaji Bulaman ba sassauci sbd tagama sani da gano auren shaawa yayi Mata Kuma Yana Gama cire shaawarsa sallamarta zaiyi Dan Haka itama ta rufe idonta ta ringa amsar kudade a hannunsa kafin tabari yai yanda yakeso da ita din.

Mugun zama sukayi na tsawon wata hudu kafin ya sakota,

Tasan zaayi hakan tunda ta gane manufar aurensa Dan Haka Bata damuba ta tattaro yayanta suka dawo gida bayan tasa anyiwa gidan babban gyara tareda fadada shi yakoma tamkar sabo Dan Haka kudin gidan ta qaru ga kowa.

Aurenta gidan Alhaji Bulama yasa idanuwanta suka sake budewa tas,

Tasake wankewa tas itama,

Daga ita har yayanta sun canja sunyi kyau da qarin lafiya abunsu,

Jikinta Mai kyau ne sbd batada qiba ko sakakken jiki Dan Haka saitayi fes fes abinta Kamar ba itace da yayan gabantab.

Ana cikin hakan babban tsautsayin Datafi tsoro a rayuwarta yaso afkawa siddinta Wato 'dan DS daya kusa lalata Mata ita,..

Maigadin gidan ne yaja siddin yakaiwa Suraj din sai gashi Allah yasa anga shigar siddin gidan akazo aka sanar Mata
Hankali tashe jiki na rawa ta Isa.

Mummunan gani tayi alokacinda ta taradda siddinta tsaye gaban Suraj harya zare Mata wando....

Sumewa take neman Yi agurin saidai karfin da tafarfasar zuciyarta ya riqeta
Jikinta na wani irin rawa ta qarasa da gudu ta fizgota daga gabansa Bata tsaya komaiba ta sauke Masa wasu irin mugayen marirrika guda biyar a jere kafin ta fidda wayarta ta dauki hotunansa..

Jikinta babu inda Baya rawa tace,

"Wannan shine karo na qarshe da wani daga zuriar DS ma zai Kuma kullon mace bare lalata,
Alqawarine wannan nayi muku da yardar Allah.

Juyawa tai da yarta zata fito ya biyota da sauri shima jikinsa na rawa yafara rokonta akan zai Bata ko nawane kada zancen ya fita
Ko mahaifinsa bayason yaji sbd zai iya komai idan yaji ya aikata abinda zai taba Masa mutuncinsa da muqaminsa...
Chapter 23 · 0% Book details