← Book details Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 95

Sashe 29

Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adduoin fashin auren da gaggawa suka ringa jerowa cikeda tsana Mai tsanani ga sunan IDON NERA din gabaki daya..

Dan kusan kamar sunfi su tsanar lamarin gabaki daya sukeji... musamman Bilkees Jin takeyi kamar ta zama uwar SSG ta tsine Masa idan ya yarda yayi auren.

Ita Kuma mufeeda takaici da tsanar AMAL din tafi ji sbd irin Yanda ake kuranta kyau da ajinta tareda Basarwarta ga maza tana tinkahon Arzkin da suke dashi Wanda yake na qazantama...

Ta gogewa Allah takuma ta gode Masa da yasa daddy dinta kwata kwata baya sabgar da zata hadasa ko huldan business ko aiki da masu irin wannan qazantacciyar rayuwar mai abin qyama sbd batasan Yaya zatayi da rayuwartaba idan akace itace daddynta zai aura AMAL din wadda so daya ta taba ganinta Amma taji Sam Bata kaunarta sbd ta tarwatsa gidan uncle SSG dinsu.

*****AMAL tunda ta aminta da auren na SSG duk da ba lokacin zaayiba Amma tini momynsu tafara gyaranta ahankali ahankali shikuwa yasake bude musu kofar aljihunsa..

Har alokacin Amal Bata wani doguwar soyayya dashi Amma ba kamar dah ba yanzu Yana Dan samun kanta.

Siddi kuwa yafe komawa Abuja tayi Kiri Kiri saidai Sweetheart din nata yakoma shine yake zuwa akai akai sbd shima ba qaramar mutuwa yayi akan Yar babyn tasa ba bare Daman Acikin mugayen shaidar da akaiwa IDON NERA shin duk Wanda ya aura 'yayanta saidai iyalansa su yafesa.

Tako Ina gyara da tsimin yarta takeyi Haj Zainab sbd Koda lokacin auren zaizo basa buqatan wani dogon gyara
Koba komai tsimin ahankali ahankali yafi shigar mace maimakon na sai gabanin auren Sam wannan baya wani aikin dazai dauki lokaci mai Nisan tsayi ajiki.

Kasancewar AMAL din bamai son wainnan abubuwanba sai suka taqaita aka rage Amma dai still kullum sake rikida takeyi tana qara Kyau da kyan fata,

Dama AMAL komai nata Mai aji ne Koba yanzu ba fatarta lafiyayya ce sbd hutu da tsadaddun natural body products datake amfani dasu.

******Ta bangaren familyn SSG kuwa komai ya qarasa rikicewa matarsa da Aminiyarta Yar uwarta Bilkees wadda kusan ta fita shiga tashin hankali da damuwar wannan halin datake ciki,

Auren sai qara tabbata yakeyi sbd kudin auren da ake Shirin Kaiwa miliyoyan kudi uncle Lulu da baya qasar kawai ake jiran dawowarsa akawo kudin.

Tashin hankali akayi sosai tsakanin Nafee da SSG akan kudin dataji zaa kai na tambaya.

Da farko da Kansa ya Bata zabin kota zauna ta hakura kokuma ta tafiyarta Idan bazata iyaba yabata Dama.

Wannan kalmar tasa ta kawo mummunan tashin hankali a tsakaninsu sabo harta tattara kayanta da 'yayanta uku ta tafiyarta gidan iyayenta.

Hankali tashe Bilkees ya sameta gidan jikinta a mace.

Kamar zaman makoki ta tadda gidan sunayi sbd mahaifin Nafee din baya Nan yayi tafiya mahaifiyarta Kuma lamarin yafi karfinta sbd tasan bazasu taba iya Hana Hayat aureba to Amma Kuma abin baikai ya Koro nafeesat din gida ba.

Amrah kuwa tayi kuka sosai har idanuwanta sun kumbura sbd bazata taba kaunar iyayenta su rabu ba har abada,

AMAL IDON NERA ta zamar musu masifa da balain da zai tarwatsa gidansu su rabe tun iyayenta sunada sauran kuruciya a auren nasu.

Cikin tashin hankali da firgici Bilkees tace,

"Wannan balain tun Bata shigoba kenan,
Idan sun shigo sai Yaya kenan?
Ki dubi yanda ta rabo yara da gidan ubansu tana neman raba musu uwa da uba
Ji Amrah yanda duk ta fice hayyacinta sbd kukan baqin ciki.

Anya kuwa DR SHAYKH yasan wannan danyan hukuncin na SSG kuwa??

"Umme gaskia banajin Daddy ya sani da bazai Bari komai yayi nisa hakaba ki fada Masa Dan Allah yayi wani abin cikin gaggawa nidai wlh banason uncle din ya auri wannan AMAL din Sam Sam rayuwarsu babu abinda yake ciki sai qazanta da datti.

Nafee ce ta Hana a sanarwa Babban Aminin Hayat din wato DR SHAYKH mijin Bilkees sbd Bama zai iya shiga zancen wainnan qazaman karuwanba..

Ita kanta Bilkees Dama fadane kawai tayi Amma bazata taba barin ko sunan IDON NERA yashiga kunnensaba Mai tsafta bare ya saka bakinsa harma ya iya ambatar sunan.

Har kusan dare a gidan kafin su balkees suka tafi gida sbd Nafee na cikin mummunan halinda yasa duka jikinsu yayi sanyi Matika.

Bayan isarsu gida tsaban basa cikin dadin zuciya daga ita har Yar tata mufeeda babu Wanda ya iya shiga gurin umma ya gaidata Kai tsaye part dinsu suka nufa zuciya da Rai a cunkushe.

Washe gari hakama kota bangaren umman Basu bi ba suka fice gidan zuwa gidansu Nafee sbd Amrah data kwana da zazzabi Mai karfi hardasu amai so Acikin daren suka nufa asibiti fa ita.

Ayanda ta tadda Nafee da Amrah sun jangwame a asibiti kamar wainda sukayo hijira sbd damuwar dake zukatansu take Bilkees ta kwatanto hakan akanta da mafeeda take tafara jero istigfar tana girgiza kai da sauri tana cewa ba akainaba"cikin ranta.

Mufeeda ma Jin tayi Ina bazata iya dauka ba...

SSG din shima tunda safen ya iso asibitin cikeda kulawa da damuwa da Yana tsananin so da kaunar yayansa harma da ita kanta Nafee din Amma dai son Amal IDON NERA Yana Ransa daram guri na musamman.

Ya Jima a asibitin kafin yatafi sbd babu fuska ko kadan daga Nafee din,
Itama Bilkees kasa sake Masa tayi Kamar dah sbd harga Allah mutuncinsa ya zube Mata kwata kwata mutiqar ya auri wannan IDON NERA din.

Bayan tafiyarsa aka sallamesu suna kokarin shiga mota saiga motar gidan SSG din tashigo asibitin.

Shine da Kansa ya dawo asibitin batareda driver ba da Kansa yake Jan motar babu Wasa a fuskarsa yace Amrah ta shigo su tafi.

Cikowa idanuwan Amrah din sukayi da hawaye ta kalli mahaifiyarta zatayi magana Dad din ya sake cewa tashigo motar cikin Dan babban sauti Mai girma.

Motar ta nufa ta shiga jiki a mace tana hawaye Dan kamar rabata da mahaifiyarta ne zaayi tunda tasan gida zai tafi da ita.

Suna kallo ya dauki yarsa yabar asibitin yabarsu tsaye cikin zallar mamaki da sanyin jikin komai na sake daukan dumi kenan.

Gidansu Nafee suka Isa suka tadda acan dinma ya Aika driver ya dauki qannan Amrah din an tafi dasu gida..

Ta tabbata kenan auren Nafee da SSG rawa yakeyi a karo na biyu duk akan wannan lamarin.

Yau Kam ita kanta Bilkees din da wuri suka tafi sbd Nafeen dake cikin mummunan yanayi ayau din na 'yayanta da SSG ya karbe kenan baida niyar janyewa.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma

*KI KULANI*🔥
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥

*_Arewabooks@Mamuhgee_*
24
Su balkees duk yanda suke tunanin lamarin SSG Hayat ya wuce Nan akan maganar aurensa a ahalin IDON NERA,
Da fari bayan yakarbi yayansa ya Dan sauko sbd yanda yaran suka damu da rashin dawowar mahaifiyarsu Dan Haka ya Dan ringa lallabata tadawo Amma ta nuna bazata dawoba idan Bai fasa auren Amal Idon Nera ba,
Ta yarda ya aura duk wadda yakeso Amma Banda Amal..

Bilkees dayasan kusancinsu yaso yiwa magana sai itama ya lura da tsanarta akan lamarin Dan Haka saiya fasa ya tattarasu ya watsar yaci gaba da harkokin gabansa idan taga anyi auren zata hakura ta yarda har ita har yan uwanta dasu bilkees harma da Amrah wadda cikin 'yayan ita kadaice takeda girman datasan wani taya uwarta kishi.

****Ta dayan bangaren kuwa Haka su balkees da 'yarta suka ara suka yafawa kansu tsanar wannan auren na SSG sbd tsakanin Nafee da balkees Aminci da kaunar Yan uwantaka ce tun yarinta sai gashi Allah yasa suka auri Aminai duk da ita Bilkees aurenta da nata Mijin kamar na Hadi ne.,

Aurenta da Mijinta DR SHAYKH AQEEL ASAD Hadi ne daga mahaifiyarsa Haj Maryamah sbd yanda yaqi auren kwata kwata duk iliminsa da addininsa harma da wayewarsa da arzikinsa sai Allah ya cire Masa shaawar aure da wuri Wanda ta rasa gane ko meyasa hakan,

Ummansa tayi tayi Amma zuciyarsa a wannan bangaren kamar ta mutu ne gashi tako Ina samun tayin aure yake daga 'yayan manya Dana malamai amma Bai taba karba ba,

Rayuwarsa wata irin baudaddiyar rayuwace yakeyi Mara hayaniya da son takura Kansa ko wani,

Ummansa itace rayuwar kadaicinsa take damunta ta nema Masa auren Bilkees wadda take ganin tanada ilimin addini sosai Kuma Dama hakan shine raayinta.

Da farko baiyi naam da zancen aurenba sbd bayason duk wani Abu dazai takurasa kokuma shi ya takura koma wacece zai aura da halayensa na rashin ko inkula da yawan rashin zamansa Amma Haka umman ta Dage sbd tanason ya dawo qasarsa dayaqi dawowa tun bayan zuwansa daya daya koma Bai Kuma dawowaba acan yake ayyukansa da rayuwarsa,

A yanda ummansa ta sansa da magana daya akan Abu yasa tasan bazai dawo dinba tunda yace bazai dawo ba
Rashin dawowarsa Kuma tasan zai iya qin yin auren har abada tunda baida lokacin Kansa ya tattara rayuwarsa akan aikinsa da Kuma karatun addinin da Bai denaba har lokacin sai qara zufafa yakeyi.

Tana tsananin buqata da kaunar 'danta a tareda ita kusada da ita Dan Haka Dole ta nemar masa auren Bilkees Wanda ya aminta daqyar akai auren saidai Kuma ko bayan auren komawa yayi da matarsa UAE saidai ita umman sbd kadaicin rayuwa da rashin kowa sbd ga arzikin sun Tara Kuma kullum sai habbaka yakeyi Yana qaruwa Amma Bata cikin dadin rayuwa sbd rashin 'danta hakan yasa dole ta tattara ta bisa acan suka koma rayuwarsu gabaki daya.
Chapter 29 · 0% Book details