← Book details Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 95

Sashe 61

Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171

Maryam sani

Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*🔥

*_Arewabooks@Mamuhgee_*
49
Already anyi reserving lafiyayyan daki da sunan AQEEL ASAD din tun jiya a Echelon heights Dan Haka suna isa Id card dinta da akai amfanin dashi airport dashi Al-Amin yayi amfani aka isar da ita dakin dakin AQEEL ASAD din dake sama gabaki daya.

Sosai take cikin wani irin Hali dakuka period dinta dayake zuba sosai shiyasa ta Isa dakin Kai tsaye tareda Al-Amin da maaikatan gurin dake janye da qaramar luggage din AQEEL wadda take tunanin kayanta aciki Dan Haka suna Isa dakin aka bude Mata tareda shigar qaramar luggage din Al-Amin yayi Mata fatan hutawa lafiya yajuya.

Toilet ta qarasa kan tsaye tana takawa ahankali sbd duk motsinta azabar mararta datake Kamar a qulle takeji.

Babban toilet din dayake a tsare tashiga tafara zare kayan jikinta,

Tana gamawa ta shiga ruwan zafi wainda ke Dan sanyaya Mata wani lokacin.

Tana Shiga ta rufe idanuwanta hawaye na gangarowa daga cikin idanuwan jikinta na Dan rawa sbd azaba.

Ta Jima aciki kafin tayi wanka da suka products na kayan wankan dayake amfani dasu sune aka jere a toilet din sbd Al-Amin yayi order na komai da AQEEL ASAD yake amfani dasu an jera a dakin tun daga kan su toothpaste dayake amfani dashi da sabbin brushes na sonicare dasu shampoos da shaving kit,

daqyar a durqushe ta Gama wankan ta dauro qatuwar towel din dasuke jere ta fito a daddafe tana fitowa ta silale qasa tana tsananta hawayenta,

Mommynta take nema sbd wanna shine karo na farko data shiga Hali na ciwonta Amma babu mommy Babu ko siddi ko Anty Fareedah atareda ita,
Koyaushe idan Hakan ya taho suna tareda ita suna kulawa da ita tareda yawon asibiti da ita,
Yau Babu kowa atareda ita ga azaba tanaji kaman ranta zai barta.

Kuka takeyi sosai batareda tasan tanayiba
Gashi Daman bawani zuba takeyi sosaiba azabar ce takeda yawa kawai.

Kukanta Yana sake tsanantane tareda ciwon nata,
Rawa jikinta yakeyi sosai tafara Wani irin numfashi da juye juye....

Acan cikin rashin Bata lokacinsa ya gana sama sama dasu yana Dan kallon time a agogon hannunsa.

Baifi awa daya da rabi ba yagama ya fito Kai tsaye ya shiga motarda aka tanadar Masa Dan hidimar garin tareda Al-Amin suka bar gurin.

Tun kafin su Isa yasa aka Kira Masa likitan dazata duba Masa ita Dan haka Koda suka Isa likitar na Echelon din Dan Haka suka wuce Kai tsaye dakin.

Shine yafara amfani da card na dakin ya bude yashiga,

Kwance take a qasa tana numfashi daqyar dukkanin jikinta na kakkarwa Kamar zata shide.

Kai tsaye yayo kanta ya tallafota gabaki daya jikinsa Yana kallon fuskarta datayi ja cikin damuwa yakira sunanta ahankali Yana nufar makeken gadon dake dakin ya shimfidar da ita ya ja duvet ya rufe Mata jikinta ya budewa likitar kofa ta shigo Kai tsaye inda take suka nufa ya tsaya Yana kallon fuskarta dake hawayen Bata hayyacinta idanuwanta arufe.

Temperature dinta Dr tafara dubawa kafin taji pulse nata
Ta tambayesa Yana Dan tunanin abinda yake damun nata badan ya tabbatar da shi dinneba a Dan natse yace,

Inaga monthly pains ne na ummm,
Period I think..

Dawo da kallonta kan Amal din tayi cikeda mamaki tana miqewa tsaye ta bude jakarta datazo da ita ta fidda allurar pain reliever tayi Mata tana cewa,

"Amma sir Bai Kamata ace tana samun pains Haka sosai ba da wahala tunda tanada aure,
Mostly masu fama da wannan matsalar duk wata da sunyi aure kokuma sukai having first sex dinzu zuwa 3rd ko 5th Haka Marar na sakewa ciwon zai fara denawa ahankali shikenan,
Wasuma idan Basu denaba suna haihuwar fari kokuma samun miscarriage suna denawa.

Komawa yayi kan couch ya zauna tareda Dora kafa daya kan daya Yana sauraronta idanuwansa akan matarsa dake kwance kamar Babu Rai ajikinta.

Drip tasaka aka kawo daga asibitinta aka daurawa Amal din sbd qarfinta data rasa gabaki daya Dan tayi matuqar azabtuwa
Bakuma ta Dena azabtuwan ba.

Ana daura Mata drip din bacci Mai qarfi ya dauketa a jikinsa kwance ya rungumeta da hannunsa daya cikin kulawa sbd lokacinda suke kokarin neman jijiyarta da zaa saka cannula sai cakudata sukeyi duk da lallabawa sukeyi Amma ganin yakeyi kamar suna yamutsa da yawa Dan Haka ya taso ahankali ya zauna tareda janyota jikinsa ya kwantar ya miqa musu hannun nata da Kansa suka sake lallabawa aka saka Mata ka daura drip din.

Magani dasu tarin always dr din takawo da kanta Bayan ta tafi tadawo takuma nuna Masa yada zai cire Mata idan ruwan ya qare ta fice Al-Amin yabita yayi settling bills da payment dinta Dan babbar likita ce sosai.

Lokaci Mai tsayi ta dauka tana bacci har ruwan yaqare ya zare Mata ya gyara Mata kwanciya tareda rufeta dakyau yayi sallah tareda kashe wayoyinsa bayan yakira ummansa sai mufeeda.

Bata farka ba sai bayan sallar magrib shima ciwon ne yadan sake tada ita,

Idanuwanta ta bude ahankali Basu suka a koina ba sai akan kyakkwar fuskarsa datayi haske Yana zaune kan sofa cikin black Riga da wandon Calvin Klein dasuka fiddo sauran kuruciyarsa da asalin kyansa da nutsuwarsa Yana amsa waya ahankali cikin turanci.

Maida idanuwanta tayi ahankali ta rufe tana gangaro da hawayen kewar su mommynta.

Yana wayar idanuwansa suka sauka kan fuskarta da hawaye ke gangarowa ya fahimci ta farka..
A natse yayi sallama da Wanda yake wayar dashi ya kashe tareda ajiyewa gefensa ya miqe tsaye tareda nufar gadon ahankali ya tsaya akanta yasake kallon fuskarta yaga yanda hawayen ke gangarowa ya zare hannuwansa daga aljihunsa ya zauna bakin gadon ahankali tareda Kai hannu a wuyanta ya shafa yaji zafin jikinta yafara dawowa.

Hannuwansa ya zura cikin duvet din ya cirota daga cikin rufar gabaki daya tareda tada ita zaune Saida bazata iya zamanba ta zame zata kwanta ya tarota jikinsa Yana kallonta
Tayi fayau hasken fatarta yafito sosai
Jikinta ya saki Bata iya ko wani dogon motsi.

Tanaji tana ganin kanta ajikinsa kwance Amma Bata iya motsawa sai hawayenta dasuka tsananta gudu sbd gida datakeso.

Hawayen nata yake kalla Yana Jin wani iri sbd Bai Saba ganin matarsa na hawaye Haka agabansa ba idanma har tanayi din.

Dagota yayi Yana sake kallon fuskarta dakyau yanajin tausayinta.

Towel dinta yasake riqe Mata ya sauko da ita daga kan gadon tana jikinsa ya rakata har cikin toilet ya saka Mata toothpaste a brush ya miqa Mata Yana Mata wani kallo ahankali yace,

"Ko nine zanyi Miki brush din?

Hawaye ta sake gangarowa dasu tana janye jikinta daga nasa ahankali Dan Babata da karfin ko nuna bacin Rai bare fushi.

Fuskarta ya kamo da hannuwansa biyu Yana kallon wuyanta dake bayyane ya matso da fuskarsa gap da tata ya sakar Mata numfashinsa Mai dumi a fuska
Ta rintse Ido jiri na neman zubar da ita ta qanqanmesa
Ahankali yace,

"Zaki iya ne?

Sake janye kanta tayi tana dafa bango ahankali ta Kai hannunta dake rawa ta karbe brush din ta juya Masa baya tana dafa mirror.

Numfashi ya sauke a hankali kafin ya juya yabar toilet din.

Daqyar hannuwanta na rawa tai brush tasake wankan ruwan zafi taga pads da sabbin panties da aka kawo jere a toilet din cikeda kunya da takaicin yagama ganin panties din tareda sanin abinda yake damunta ta sako ta fito sanyeda farar bathrobe qatuwa ta maza wadda tayi Mata yawa.

Daqyar take iya daga qafa jiri na dibanta take qarasowa.

Daukota yayi yakawo kan kujera ya ajiye tareda miqa Mata cup na black tea Mai zafi sosai.

Qasa karba tayi sbd hannunta dake rawa idanuwanta na sake cikowa da hawaye.

Da Kansa ya gyara zama a gefenta ya ringa Bata tea din tanasha sbd batada zabi
Kuma tea Mai zafi Yana taimaka Mata ga yunwa da rashin qwari.

Tasha tea din sosai tana gamawa daqyar ta rigima Tasha maganin daya Bata Saida tun kafin tagama jikinta yasake daukan zafi Sosai wanda yasashi Jin duk Kansa na kuncewa da damuwa.

Maidata yayi ya kwantar a gadon ya rufe sbd rawar da jikinta keyi sosai.

Sallar ishai yayi yasake tambayar likita ko akwai wani abinda zaa Kuma yimata din tace Gaskia Babu indai ba maganin yakeson yayi Mata yawaba.

Qarfe goma Sha daya jikin nata yayi tsanani ya rungumeta jikinsa yanajin zafin jikinta na ratsa jikinsa Yana shigarsa ta cikin silk pyjamas din dake jikinsa na bacci.

Kuka takeyi Masa sosai tana Kiran sunan mommynta tana lafe jikinsa gabaki daya tagama fita hayyacinta.

Hankalinsa tashi yayi sosai ya sake shigar da ita jikinsa Yakai hannunsa daya cikin bathrobe din dake jikinta har lokacin Wanda hakan yasa kukanta sauya sauti Mai Dan karfi sbd sanyi da taushin hannunsa,

Shi kansa rufe idanuwansa dasuke a bude yayi Yana hade fuskarsa da tata ya Dora hannunsa kan mararta
Atare suka sauke shi numfashi Mai dumi itakuma wani irin sautin kuka mara qarfi.

Numfashinta yake shaqa da nasa numfashin Yana sauke Mata dumin nasa a fuskarta har lokacin hannunsa na Dan shafa mararta ahankali idanuwansa a rufe.

Sunan mommynta take Kira ahankali tana tsiyayar hawaye shikuma Yana sake shafa Mata marar tareda Dan dannawa ahankali
Numfashin junansu na sauka kan fuskar juna
Tafara Jin relief tun tana Kiran suna mommyn har bacci ya dauketa ahankali ta qarasa sakewa cikin jikinsa.

Ajiyar zuciya Mai sanyi ya sauke tareda gyara Mata kwanciya a jikin nasa Yana rufe idanuwansa sbd numfashinta Mai dumi dake sauka cikin wuyansa tana sakar Masa zazzabin tsakar Daren shima.

Bacci takeyi Mai tattareda gajiya da mutuwar jiki
Shikuma ya Jima a farke kafin baccin ya daukesa.

Tsakar dare ma Saida ta farka da sabuwar rigimar kuka da fadar yakaita gida daqyar yabita yayita shafa Yana matsewa jikinsa Takoma bacci
Asubar farin ma Saida takuma farkawa ahaka ya lallaba yayi sallar asuba yadawo gurinta Yana hawowa gadon yaji zufa ya feso Mata tako Ina alamar sai alokacin zazzabinta ya sauka..
Chapter 61 · 0% Book details