← Book details Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 95

Sashe 27

Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amal ce take driving din Siddi na Dan chat a wayarta har suka Isa asibitin Dr Inayah majeed.

Dr Inayah din sukaso gani amma Bata Nan so sai wata likitan ta dubasu Dr farhat...

Kamar ko yaushe wannan karon ma anduba batada komai Dan haka suka fito jiki a mace..

A daidai kofarsu ta fitowa asibitin motarsu takusan karo da wata motar wadda tasa AMAL din yiwa motar kallo daya ta dauke kai tana sakin qaramin tsoki ahankali tace,

"Wannan matar Wai bibiya takeyi ne ko me??

Da sauri siddi ta dago ta kalli motar tana cewa,

Kaman motar gidan SSG right??

Yamutsa fuska AMAL tayi tana cewa,

"Matarsa ce da wahala be qare Mata ba ko 'yarsa may be.

Karkatawa Amal din tayi ta wucewarta Saida suka wucesu Siddi tace,

"Ba matarsa bace 'yarsa ce tareda qawarta da akace kwana kin baya suka dawo Nigeria daga UAE..

Amal da babu ruwanta da koma su waye a motar ko matar ko 'yar ko wata qawar Yar koma Yar uwarsu ce

Dan Haka batai magana ba suka fice abitin zuwa inda Tai niyar zuwa tun farko wato makaranta.

Tare sukaje da siddi din suna Isa Sharif na isowa Dan sun Masa waya tun a hanya Dan haka juya da siddin zuwa wani gurin itama da zata.

A makaranta ta wuni sai kusan 4 ta fito nata nufi gida Kai tsayeba Saida ta biya ta dauki Fahat daga gidan iyayen anty Fareedah dake lekki tukana suka dawo gida...

Koda ta iso gida mommynsu ta dawo suna palon sama dukkaninsu harda uncle da Anty Fareedah da siddi suna fira da Haka itama wanka da sallah tayi ta nufi saman saidai Balkisu takai Mata abincinta can saman.

Kallonta Haj Zainab tayi lokacinda take zama gefen uncle dinta sanyesa milk Riga da wandon Calvin Klein masu Fadi sosai da kauri
Cikeda kulawa tace,

"Amal lafiya kuwa?
You look pale.

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon Uncle dinta dake kallonta cikin kulawa kafin ta kalli haj Zainab din tace,

"Mommy karatun Nan ne Yana neman juyar mun da Kai nafara gajiya fa.

Murmushi momyn tayi tana cewa,

"Kin shirya yin auren ne to sai abawa SSG daman fitowa...

Dariya siddi tayi tana cewa,

"Wane SSG din mommy?matarsa fa haukace take neman Yi ko sunan AMAL aka fada bare taji maganan aure mutuwa zatayi Kila..
And banajin Amal dinma zata aura SSG din da alama haryanxu Bai samu shiga agunta ba.

Uncle Lulu ne ya kalli AMAL data fara Shan Mango juice din da Balkisu da takawo Mata da abinci yace,

"Koda batasonsa ai tasan takusa aure tunda karatu zata gama,
Idanma ba SSG ba akwai wainda ke jira.

Itadai Amal batace komaiba sbd irin hakan Bata saka Baki tunda dai sai lokacinda tace tanaso tasan zaayi Mata.

Fira sukayi har zuwa magriba tukuna kowa ya tashi ya tafi sallah.

Bayan sunyi sallar magriba suka zauna dining cin abincin dare Banda momy da uncle Lulu wainda suke Palo suna tattauna maganar data taso musu haiqan na yanda malaman addini suka fara shiga cikin lamarinsu sosai abin yafara kawo musu illa da maganganu.
##MAMUH#
#AQEEL MUHAMMAD ASAD
#AMAL IDON NERA

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma

*KI KULANI*🔥
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥

*_Arewabooks@Mamuhgee_*
22
Duk da siddi tayi aure bedroom dinta tun ta budurci na gidan Yana Nan amatsayin nata Kuma koyaushe zaayi sabon gyara dashi akeyi tinda kusan tana nan abinta,motarta ce kawai babu a gidan saidai tayi amfani data mommynsu daya ko ta AMAL kokuma ta Anty Fareedah harta Uncle Lulu tana ja tunda komai nata na Abuja yanzu,

Masu aiki biyu suke dasu a gidan tareda securities na gate guda biyu dasuke canjin lokaci,

Masu aikinsu babbar mace da yarinya ne hakama yarinyar farkonta gida tabaro sbd cikin tsautsayi data samu bada aureba gurin cire cikin takusa mutuwa Allah dai ya kareta qarshe haj Zainab ta taimaka ta dauketa aiki sbd shekarunta sunyi qanana alokacin da zataje cikin manyan Yan bariki ta zauna rayuwarta qarasa lalacewa kawai zatayi tunda yarinya ce Qarama sosai Dan haka sai kawai ta daukota takawota gidan nasu Amma aiki takeyi musu Kuma rayuwarta ahakan saita gyaru sbd cima Mai kyau lafiyayya da muhalli Mai kyau ga Kuma ba takura ba tsangwama babu wahala ko cutatarwa, aikinta takeyi da gaskenta tareda zallar biyayya ga dukkanin ahalin gidan,
Gashi su biyune ba ita kadaiba kowa da aikin daya keyi Dan Haka ba wuya ba cuta saima Dadi da farin cikin kasancewarsu masu aikima acikin ahalin IDON NERA kowannensu harkar gabansa yakeyi babu Mai lokacin Yan aiki acikinsu bare ya takura su, Suma sunsan aikinsu basa jiran ace suyi sukeyin abinsu.

*****Washe gari da safe AMAL ta shirya ta fito ita kadai tayi breakfast sbd kowa Bai tashiba suna hutawa bare sai kusan 9 zuwa 10 suke breakfast a gidan.

Tana gamawa ta tashi ta fito ta shiga motarta ta fice gidan.

Makaranta ta nufa sbd lectures din safe ne takeda a ranar....

Lokacin period dinta ne Dan Haka a sama sama take yau batason doguwar motsi da hayaniya
Daqyar taga ta kammala da lectures dinta na ranar ta fito ta nufi gida,

Ahankali take driving din harta Isa gida Dama duk wata Haka take fama da MP Mai Dan tsanani.

Tana dawowa gida wanka tayi tareda shiga ruwan zafi Dan tasamu taji Dan sauki sauki cramps din Amma dai sai ahankali.

Riga da wando masu kauri ta saka tareda hula bayan ta Gama kintsawa ta Bata fitoba a dakin Bata Bilkisu ta kawo Mata black tea Mai zafi da plain doughnuts sbd bazata iya cin abinci a lokacin.

Momynta da Siddi ne suka shigo cikin kulawa Mai tsanani da kauna Dan sune sukasan yanda take fama duk wata da akan period dinta.

Zaunawa Haj Zainab tayi gefenta tareda rungumota jikinta tana cewa,

"Sorry Sweetie, ko Akira Dr tayo ne tunda Naga kaman harda stress a yanayin naki???

Girgiza Kai tayi ahankali tana Dan sake lafewa jikin momyn tana lumshe fararen idanuwanta sbd rashin son doguwar motsin dazaita Jin babu Dadi.

Siddi dake dayan gefen nata cikin kulawa ta taba wuyan Amal din tana cewa,

"Sweetie jikinki akwai dumi,zankira Dr tayo gaskia gwara ko pain relief ne yazo ya Baki kada jikin yayi tsanani.

Sake lumshe idanuwanta tayi tana Dan bude idanuwanta zatayi magana saiga uncle Lulu yayi knocking kofar dakin tareda shigowa Kai tsaye Fareedah na bayansa tareda Fahat idanuwansa akan AMAL din yace,

"Baby jikin ne???
Fahat ya daga Mana hankali yace Antinsa batada lafiya tanada kuka da amai.

Anty Fareedah ce ta qarasa gefen Amal din itama cikin kulawa ta taba wuyanta tace,

"Jikin da zafi,
Sweetie ki ragewa kanki wahalan karatu karki takura qwaqwalanki da yawa fa,
Idan karatun kinji ya Miki nauyi inaga ki aje sai a canja ki tafi wata qasan kiyi acan..

Cikin kulawa dukkaninsu suka zuba Mata ido suga yanda ta amsa zancen na Fareedah Dan idan tayi raayin hakan babu Wanda zai hanata acikinsu sai inda takeso zataje.

Ahankali ta bude baki cikin Dan rashin son magana tace,

"Babu damuwar karatu Menstrual pain ne kawai Kamar yanda kuka sani Koda akwai damuwar karatun kadan ne shima kaida kawo ne damuwar.

Shiru sukai dukkaninsu cikin damuwar yanayinta duk da koyaushe tana hakan Amma sbd kaunar dake tsakanin familyn sun kasa sabawa duk tashiga wannan halin Haka suke tarairayarta cikin kulawa.

Bacci tasamu ya Dan dauketa tukuna aka barta tasamu baccin cikin nutsuwa.

Sai yamma sosai ta farka ta sake yin wani wankan ta saka doguwar Riga Mara hannu da nauyi tafito sanyeda slippers qamshinta na Turaren Cartier carat na tashi jikinta a hankali.

Palon momynsu ta nufa acan ta tadda siddi tareda momyn suna magana akan likitan da siddi zata gani a India Jan matsalar rashin haihuwarta.

Zama tayi suna binta da kallo da tambayar ya jikinta.

Da Kai ta amsa Dan Daman kusan halinta ne daya zama dabiarta komai Bata Masa karauniya saidai duk rashin hayaniyarta magana a bakinta Bata wuya kowace irice Dan Haka ake ganinta Yar Kai tsaye Bata rufa rufa Bata bin bashin magana Koda waye.

Kallonta Haj Zainab tayi tace,

Sweetie ko zamu tafi dake ne kema kiga likita sbd wannan ciwon matar taki yayi yawa gashi yawanci sai anyi aure ake denawa ke Kuma kince aure ba yanxu ba,inaga gwara kiga likita may be da abinda zai iyayi akan hakan.

Kallon siddi tayi tana cewa,

"Baby fada Mata auren baida duk wani damuwar datake tunanin akwai ko takura ga karatunta.

Mommy tasani ai tunda gashinan tana gani nida nayi babu damuwar danake ciki..
Bare ita yanda SSG ya gama mutuwa akanta babu abinda zata takura dashi a aurensa bayan matarsa wadda itama zata gaji da haukanta ne ta Dena tunda dai aure kam ba fashi.

Wani kallo Amal din ta jefa Siddi dashi tana cewa,

"Kece Zaki auramun Hayat din kenan?

Nice Zan aura Miki shi,
Aure fa nakeson kiyi AMAL tayaya zan zauna Ina kallonki damammakin auren nata wuceki???
Kinfi kowa sanin ba karatunki kawaiba babu abinda zai sauya ko takura a rayuwarki Dan kinyi auren saima sake samun kwanciyar hankali da nutsuwa zakiyi a gidanki....

Mommy please""AMAL ta katse mommyn batason zancen kwata kwata musamman idan Ana maganar SSG Hayat Wanda tasan shine zaa aura Mata Koda cewa Tai auren zatayi sbd yagama samarwa kansa guri a zuciyar kaf ahalin nata Dan Haka kowa a gida shi yakeyi duk da akwai masu son auren nata dake sakarwa Haj Zainab da Lulu Nera Kamar Basu San zafinta suma Amma dai SSG Hayat yafi shiga ransu sbd shine matashin babba Bai Kai shekarun sauranba.
Chapter 27 · 0% Book details