← Book details Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 95

Sashe 42

Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baida abinda zai fadawa kowa ayanzu Dan Haka ya zabi yin shiru bazaice komaiba yanzu din.

Gida Kai tsaye ya wuce Dan daukan abubuwan dazai buqatan a kwana biyun dazaiyi Abujan ya dawo.

Yana Isa Kai tsaye Saida yaje ya hada karamar Louis Vuitton luggage ya miqawa malam Rabiu yasaka mota kafin ya nufi bangaren ummansa sbd yasan Bilkees na can.

Yana shiga yagansu hankalinsu kamar baa jikinsuba su dukan,

Qarasowa yayi cikin takun nutsuwa Yana kallon haj maryamah dake kallonsa cikin tashin hankali,tsoro,fargaba da babban tunanin Ina ya hadu Zainab,Kuma tun yaushe.

Kenan bayan tsawon shekaru yagano zainab din shine ya boye Mata?

Wace qaddarar ce wannan?
Zainab tazama masifar rayuwarta.

Innalillahi wainna ilayhirrajiuni
Tayaya zaace itace?

Rintse idanuwanta tayi tana cewa"

Ya Allah kada ka dawo da Zainab rayuwar tsaftataccen 'dana AQEEL,

Ya Allah ka hanasu sake haduwa sbd rayuwarsu ta bambamta,

Shi Mai tsaftane ya Allah,

Kowa yaje yayi rayuwarsa da abinda Allah yabasa
'dana mai tsarki itakuma 'yaya Masu daudar najazar uwa karuwa Wanda itama tanada tabbacin 'yar karuwace a yanzu...

IDON NERA??

Meya kawo sunan da ko tsarki da dadin ji da fada babu acikin rayuwarsu??

Da gaske

Shin Zainab dince ma idon nera kokuwa 'yarta data bar gida da ita kokuwa 'yar data haifa a karuwancin??

Mezaisa AQEEL ASAD dinta ya yarda ma ya kalli inda IDON NERA's din suke sbd tsananin taka tsantsan dinsa da kiyayewarsa ga kusantar qazanta??

Yasan Zainab itace idon neran shiyasa yaje kokuwa wata qaddarar ce takaisa har aka samu damar lalata mutuncinsa da sunansa..

Maganganunta dashine kadai yasan maanarsu yankar zuciyarsa sukeyi,
Bayason tayarda duk wani zancen ayanzu sbd bazaiso Jin mummunan sunan akan Maminsa ba daga bakin kowaba a gida.

Yanayinta dayake tsanani yasashi kasa cewa komai suka dauketa zuwa asibiti sbd numfashin nata neman tsayawa yakeyi.

Bilkees ma neman sumewar takeyi sbd numfashinta dayake neman toshewa Dan Haka da taimakon mufeeda itama ta Dan samun riqe numfashin suka Isa asibitin da umma.
##MAMUH#
#SISTERS#BLACK AND WHITE LOVE#
LOVE/ROMANCE
#HOTLOVE/MARRIAGE

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma

*KI KULANI*🔥
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥
*_ArewabooksMamuhgee_*
33
Suna Isa asibiti aka karbeta kasancewar tareda shine akazo asibitin take aka karbeta cikin gaggawa da kulawa..

Bp ne yayi sama sosai Dan Haka take suka fara Mata allurai da wasu daga cikin magunan dazai sauko dashi zuwa normal cikin gaggawa.

Zama yayi akan tattausan sofa kushin dake lafiyayyan Amenity room din tareda Dan rufe idanuwansa ya bude Yana sakin numfashi a ahankali.

Bilkees ce ta dawo gefensa ta tsaya idanuwanta gabaki daya sun canja
Masifa da tashin hankali ne kawai ke Mata tsalle da rumfa tako Ina,

Dr menene abinda yake faruwa Ni kwata kwata bana gane komai
A gurinka kawai zanji dalla dallah nagane me ake nufi??
Me Kuma yake faruwa??

Ni wlh halinda umma tashiga Wasa ne,
Zan iya haukacewa Dr idan kacemun Dagaske kaje IDON NERA's,

Gawurtattun kar.....

Cikin wani mummunan kallon dayasata rikicewa ya dago ya kalleta gabaki daya annurin fuskarsa ya tashi daga damuwan halinda umma take ciki zuwa mummunan bacin Rai da fushi..

Ahankali ya bude Baki tareda dauke idonsa akanta yace,

"Sunan Idon Nera ma karki sake ambata a bakinki bare wani sunan daban"
Dokace hade da umarnin..

Wani jiri ne ya dibeta sbd buguwar da zuciyarta tayi da karfi,

Muryarta na rawa ta qara matsowa gabansa sosai Wanda ya sashi sake kame fuskarsa batareda ya dago ya kalleta ba.,

"Banganeba,
Na Dena fadan sunan sbd qazantars......

Miqewa yayi tareda rabata ya wuce sbd akwai mutane tako Ina asibitin da ake tsakanin ganin girmansa da mutuncinsa tareda girmamasa bazaiso Ransa ya baci ba a irin gurin.

Bin bayansa tayi da kallo tana qarasa firgicewa,

"Menene yake faruwa Wai ma tukuna??

Wlh Bata yardaba ,
Takasa yarda da Mijinta AQEEL ASAD guda zai iya ko kallon gidan Wainnan karuwan bare ya iya kusantarsu ya shiga,

Neman auren Hayat yaje kokuwa?

Rawa qafafunta suka farayi da sauri mufeeda ta qaraso itama a rude take da abinda keta Shirin faruwa su sunkasa gane komai.

Abu daya suka sani shine Daga Idon Nera din har 'yarta sunyi kadan su lalata musu farin ciki,

Idanma da gaske angansa dasu suka lalata auren SSG da Idon Nera din  bare nata Mijin.

Motarsa ya Isa aka bude Masa yana shiga wayarsa tafara vibrating na baqin dake jiransa,

Dauka yayi yacewa Al-Amin baqin su wuce zai biyo flight din safiya da wuri insha Allah.

***Amal na Isa office din mommynta datake gudanar da harkokin businesses dinta apart from harkanta ta Daban da ake kira da karuwancin.

Ajiye jaridar tayi Kai tsaye gaban mommyn tana kallonta cikin Bata rai tace,

Mommy kina ganin alaqarki da wannan AQEEL ASAD din bazai kawo baci Rai da ninkin bacin sunaba akanki?

Mommy koma menene alaqarki dashi gabaki daya hakan Bai kwantamunba,
Shi kansa Bai kwantamunba,

Meyasa Zaki ringa tattala duk wani zancenza saikace shi din yafi sauran abokanan kasuwancinki,

Mommy idan akwai wani alaqar daba business ba a tsakaninku inason sani sbd Shi kansa dabiarsa akanki tayi hannun Riga kwata kwata da sauran kowace dabiar.

Mommy......

Katse Haj Zainab tayi cikin kulawa da kwantar Mata da hankali tace,

"Amal breath please,
Wannan rumours da bacin sunan ba yanzu aka fara ba,mun Saba,.ba komai bane,
Banajin komai akan hakan,
Damuwata dayace akaro nafarko akan irin wannan iskancin na Yan jarida shine sunan AQEEL ASAD dayake ciki,

Bantaba musantawa ko tankawa akan ire iren hakan sbd bana buqatan yiwa kowa bayanin halinda rayuwata take ciki Amma bazan iya Bari su Bata sunan AQEEL ba,

AQEEL ASAD shine Wanda raina zaiyi matukar baci idan suka lalata sunansa akan nawa sunan...

Mamakine ya sake shigar AMAL tana kallonta tace,

"Mommy?kinji abinda kike fada kuwa?
Mutuncinsa yafi naki ne?
Idanma sunansa ya baci shine ya kawo Kansa idan na tina,

Mommy please ki Dena fadan hakan kina sake sakamun zafinsa araina,
Tayaya shi din yasamu wannan mahummancin a gurinki?

Yanda ran Amal din yake a cakude yasa mommyn kokarin danne nata bacin ran akan lamarin Amma bawai Dan nata sunanba sai Dan mutuncin AQEEL dinta dakuma uwa uba babbar rigimar da hakan zata bullo sbd wanan jaridar zata tabbatarwa da duk inda uwarsa da kakarsa suke cewan itada AQEEL sun dawo rayuwar juna kenan,
Abinda Kuma ta guda din kenan sbd riqo da alqawarinta na cewan ta yanke duka wata alaqa dake tsakaninta dasu har abada Kuma tana Nan akan bakanta,

Idan Kuma suna Nan a yanda ta sansu to tabbas aduk inda suke zasu nemeta su sameta sbd isarda sakon zuciyarsu kaman Yanda suka Saba...
Hakan na na nufin Amal da siddi zasusan su din su wanene,.abinda Basu taba tambaya daga garetaba bakuma su damu da tambayarba Koda su din shegu ne Basu damuba tunda uwar data haifesu din tana taredasu kamar yayan sunna.

Shirunta tareda zurfi cikin tinani yasa Amal zuba Mata fararen idanuwanta tana kallonta cikin mamaki,

Amma koma menene batajin zata dauki cin fuska da sabon bacin suna ga mahaifiyarta sbd itace duniyarta gabaki daya.

*****Awar Haj Maryamah hudu a asibitin BP dinta ya dawo daidai saidai zuciyarta takasa Dena bugawa da sauri bp dinma tasan ba jimawa zaiyiba zai ringa hawane Yana sauka sbd ita kadai tasan yanda zuciyarta take bugawa tareda kasa Jan numfashin nutsuwa.

Daga ita harsu Bilkees Babu Wanda yake cikakken hayyacinsa,

Ita Bilkees da mufeeda hoto ne kawai a kawo umma asibitin Dan kusan Bilkees din tafi kowa ficewa hayyacinta a tsaye kawai take Amma Sam Bata gane komai sai an maimaita Mata abinda aka fada din.,

Kallo daya Haj Maryamah tayiwa AQEEL ASAD din alokacinda ya shigo ta fahimci Babu wata magana dazai iya saurara akan Zainab,

Kamewar da yayiwa fuskarsa ce ta tabbatar Mata da abinda taketa qin yarda dinne dai ya tabbata wato Zainab dai tadawo rayuwarsa Kuma yana sane da abinda ya sakata cikin wanna halin kenan shiyasa yaqi Bata fuskar yin maganar....

Innalillahi wainna ilayhi rajiun,

Wace sabuwar masifar ce wannan,

A bayan ma da Zainab takeda tsarki Bata barta da 'danta ba Dan haka babu ta yanda zata bari 'danta ya sake ko kallon inda qazantarsu takeba bare ya kwaso najasarsu,

Bazata taba yarda wannan karon 'danta Mai tsarki tsarkakakke ya kusanci inda sukeba,

Kome zatai zatayi Amma wlh Zainab bazata dawo rayuwar 'dantaba itada 'yarta,
Wannan karon kome na dukiyarta zata watsar akan 'danta ya tsaya gurinta bazai sake kallon zainab bama bare wata 'yarta wadda itama take baqin cikin fadar sunanta da aka sakawa 'yar gashinan ta qare a rayuwa irinta uwarta,

Sake kallon AQEEL din tayi idanuwanta da zuciyarta na sake daukan zafi da ciwo,

A natse cikin kamewa yagama tabbatarda Babu wata matsala zasu iya tafiya da umman gida.

Bilkees data gap da faduwa sbd tiririn da zuciyarta take ciki itada mufeeda,

Bata tafi gidaba itama saida aka duba bp dinta daya kusan haura 200 daqyar akai Mata controlling dinsa tayo gida a gigice saidai cikin rashin saa tana isowa akace AQEEL din yabi jirgin dare ya wuce Abuja.

Cikin tashin hankali ta kalli umma wadda itace ta matsa Masa akan ya tafi din taji sauki sbd tanada buqatan barinsa a garin na kwana biyu Dan tabbatarda abinda tasani,

Zainab tazama masifar rayuwarsu itada ummanta da 'danta,

Tayaya zata fuskanci wannan tashin hankalin dayake dawowa musu???

Bilkees data kasa gane kan umman ta qaraso gabanta hankali baa kwanceba tana jiran Jin ta bakin umman tukuna tasan ta inda zata fara da lamarin.

"Idon Nera" duk sunan ya fado a ransu sai anrasa tsakanin zuciyar haj Maryamah data Balkees wacce tafi girgiza dashiga mummunan yanayi,

Tashin hankali da rikicewar Balkees a zahirin bayyane yake ga duk Wanda ya ganta yasan tayi kololuwar fita hayyaci da tsananin kishi da tashin hankali akan lamarin tun lokacinda idonta ya kyallo jaridar,
Chapter 42 · 0% Book details