← Book details Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 95

Sashe 52

Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Batada wani sauran tunani daya wuce ta watsar da zancen itama tayita kanta da 'yarta sbd neman juyewa da kansu keyi Akan wannan sabon lamarin ba tsammani.

Tana buqatan nutsuwa itama tadawo kanta Dan tanaji hawan jini ma kawai ya Isa ya Gama da ita idan Bata koyi nutsar da kanta akan masifar su umma ba tinda qarfi da yaji sundawo rayuwar juna.

Shi kansa uncle Lulu ganin zasu dorawa kansu ciwo abanza suzo ayi biyu Babu gwara su nutsu subi komai ahankali kamar yanda Shi uban gayyar Babu ta inda ya damar da Kansa ya tattara kowa da wahalarsa ya zuba musu Ido,

To Suma zasu zuba Idon Amma dai Babu maganar wani tarewar Amal gidansa a ayanxu Koda yai magana shine maganar da Haj Zainab ta tsaya akai kawai.

Likita aka Kira Mata tazo gida ta dubata sbd kanta ya tsananta ciwo sosai.

Magani da drip aka daura Mata take bacci ya dauketa Mai qarfin gaske sbd shine kawai zai saukar da nauyin kanta da ciwonsa.

***Siddi da Anty Fareedah duk yanda sukaso Amal ta bari su zauna suyi magana da ita rufe dakinta tayi Bata buqatan kowa

Kadaicewa kawai take buqata sbd kukan datasha Mai tsananin gaske Wanda sai daga baya taji haushin kanta ma data tsaya rufe kanta a daki tana kuka akan Wanda ya nuna Babu abinda ya damesa da duk halinda kowa zai shiga akan lamarin.,

Tashi tayi ta nufi toilet ta tube Tai wankan da duk wunin ranar batayiba sbd yanda ranar tazo Mana a juye.

Wanka tayo tafito a nutsuwarta sanyeda bathrobe ash ta nufi gaban mirror ta zauna tareda qurawa fuskarta Acikin madubin Ido tana kallon yanda fuskarta tayi jajir sbd kuka gata fara Dan Haka sai tayi ja koina idanuwa Kuma sun kumbura kamar ba itaba data tsani kumburin fuska Koda na barci ne.

Ahankali ta sauke numfashi har lokacin idonta akan fuskarta datake Mata zafin kalla,

Yanzu itace ke yiwa namiji kuka Haka ta fita hayyacinta a wuni daya???

AQEEL ASAD duk zafin kanka da Jin kanka zaka iya mallakan Amal Idon Nera kake ganin?

Me kake daukan kanka?

Kanada komai da zaka mallaka macen da kaga Dama kake gani?.

Amal Sanda ba irin taka bace sbd nice nake juya namiji bashine ya Isa ya juyaniba da har zaka doramun aurenka batareda sanina ko yardataba.

Mai ta dauka ahankali tafara shafawa jikinta tana dauke kallonta daga kan fuskarta.

Tana gamawa Riga da wando ta saka ta Dora doguwar jilbaab akai tayi sallar azahar data wuceta tana idarwa bata bar gurinba akai sallar laasar ta miqe tayi.

Bayan tagama sallah jiki ba qwari ta zare jilbaab din ta maida tadawo ta zauna kan sofa tareda janyo wayarta data kashe ta kunna.

Sakonnin da Bata Gama budewaba dazun ta sake cin karo dasu Acikin notifications dinta.

Deleting nasu tayi gabaki daya batareda ta budesuba.

Kokarin Hana kanta shiga kowane gurinda zataci karo da zancen tayi ta shiga WhatsApp dinta inda acan tafara cin karo da sakonnin Taya murna da neman shiga daga yawan course mates nata maza da Mata daketa mamakin auren nata...

Sarai sunsan waye mahaifiyarta da sunanta akan harkarta Kuma sunsan kuma waye AQEEL ASAD Dan Haka suke mamakin yanda akai wannan hadin combination din duk da sunsan AQEEL ASAD Yana cikin wainda sune kawai zasu nema auren Amal Idon Nera Yar Zainab Idon Nera.

Babu Wanda ta amsa sakonsa sai kawai takuma kashe wayar tareda jefarwa akan gadonta ta zame ta lafe jikin sofar tana kokarin Hana kanta zubarda hawayen dake gangarowa kan fuskarta.

Bata fitoba har dare tana dakinta saidai Bilkisu takawo Mata abinci Mara nauyi Wanda shima Bataci ba Haka ta wuni tana yaqi da zuciyarta daketa karyewa da kuka Wanda take Hana kanta sbd qin yarda itace a qasan.

Haka ta kwanta batareda kowa yagantaba

Su siddi da Anty Fareedah sunyi magiya da rarrashi akan ta sauraresuma Amma Sam ta nuna Bata buqatan ko kalma daya data danganci auren Dole suka barta ta sauko tukuna.

Haj Zainab ma Bata farkaba sai dare zuwa lokacin Kuma kanta ya Dan sake sosai tadawo hayyacinta yanda ya Kamata Dan Haka itama wankan da bataiba a ranar tashiga tayi tareda alwala tafito tayi sallolinta

Siddi ce da kanta takawo Mata abinci cikin kulawa taci Tasha magani ta tambaya Amal ta sanar da ita Tana lafiya Amma dai tana buqatan space shiyasa kowa yabarta ta sauka tukana batareda an takura Mata.

Ajiyar zuciya Haj Zainab din ta sauke tana fatan kan Amal dinta ya sake kamar yanda nata ya sake Mata take jinsa yanzu Babu Wani 'daga hankali da tashin hankali,zasubi komai a tsanake Babu daga sakawa Kai ciwon kai tasan suna zaune su umma zasuyi abinda zasuyi su kashe maganar sai kowa ya huta shikenan.

****AQEEL ASAD daga asibiti very late ya Isa gidansa batareda yaje ya dubo umma ba yashigewarsa sbd kusan komai ummansa ke akai umman ce jagorar ko wace irin aikin rashin lurarta,

Securities din gabaki daya a Dan kame batareda zaqewaba sukai congratulating nasa akan auren da yayi sbd lura dasukai auren da alama Yana tafe da hargitsi duk da suna tunanin ko madam din tasa ba lallai tasaniba dan kila itama ta some kamarsu Haj Maryamah din kamar yanda labari yazo musu daga wasu daga securities din gidan da aka raba wasu ke gadin wancan gidan nasa inda akai daurin aure.

Bilkees dake zaman boyon Kai itada yarta sbd su umma datasan suna jiran samun lokacintane Dan sosai taga bacin rai da fushin dasukai akan abinda tayi hakan yasa ta kame kanta a guri daya tayi qaryar rashin lafiya itama ta lafe itada yarta suna jiran qurar ta lafa suji inda aka tsaya idan anyi watsi an rabu har abada tsakanin su umman da Idon Nera da 'yarta.

Mufeeda a ranar da safe kamar almara taga bayanin auren AQEEL ASAD din na yawo Amma Bata wani damuba sbd tinaninsu wancan zancen ne aketa yawo dashi har lokacin sbd sunsan Babu ta yanda zaayi Yayi auren da ake fadan batareda sanin familynsa.,

Bilkees da mufeeda ta fada Mata itama Bata wani damuba Kai tsaye tace,

"Yanzu bana buqatan wahalarda Kaina da damuwar komai sbd su umma suna yaqin ne amma nice Mai qaruwa da hakan,

Ban buqatan sakawa kaina rashin sukuni akan Idon Nera da duka kwashe kwashenta sbd nasan su umma har abada bazasu yarda da alaqarta 'yarta,

Dan Haka Ni hakan ma yamun ba damuwarsu gabana yanzu ta Mijina zanyi Dan ko sunan wata MARYAMAH bazan Bari aringa fada agabasaba tunda an yanke alaqar tasu.

Mufeeda ma cikin son komai da umminta tafada ya tabbata tace,

"Amal Idon Nera itace damuwata Ni,

Ko inda daddyna yake ban kaunar ace tasake bi bare,

Wlh umme da munsan Haka abin zai zama da zamewa kikai ta auri Uncle SSG ma can suda suka Saba da duka wannan tashin hankalin su qarata nidai wlh ko alaqa da akace mamanta nada da umman daddyna naji ciwo da zafinsa tareda baqin ciki Mai tsanani akan hakan,

Nayi takaici da baqin cikin hada jini da ita ko yayane.

Bilkees ambatar sunan gidan Nafee yasata hade fuska tana Jinjina Kai mamakin Nafeen nasake Kamata Dan kuwa duk wannan rigimar da akeyi takasa kiranta ko zuwar Mata bayan ita a lokacin nata yaqin itace ta tsaya mata,

Zatayi lokacinta daga Baya idan tasamu kanta yanda ya Kamata.

Rashin ganin AQEEL tunda safiyar ranar yasata Kiran wayarsa cikeda narke murya ta fara magana ya dakatar da ita ta hanyar cemata Yana asibiti umma ba lafiya.

Da mamaki sosai tace,

Meya samu umman?

Shine bansaniba har umma na asibiti,

Wane asibitin ne zanzo yanzu tareda mufeeda.

Cikin rashin son Jan zancen yace,

"Karki zo ba wani sabon ciwon bane hawan jinin ne dakuma zuwan Abu

Kimata addua kawai

Doctors ma since kada a dameta hutawa kawai take buqata

Nima ganinan dawowa gidan zuwan anjima.

Tana kashe wayar numfashi ta sauke tana mamakin ciwo har sosai Haka Amma Bata saniba.

Bangaren su umman ta shirya ta nufa cikeda sanyin jikin dake nuna batada lafiyar itama.

Gaida umma dake kwance ba lafiyar itama tayi zatayi magana umman ta daga Mata hannu

da hannun ta nuna Mata batason magana Dan Allah ta tafi tabari saita dawo daidai tukuna.

Da mamaki Bilkees din tasake kallon umman tana cewa,

"To lafiya dai kuwa?

Ni hankalina yatashi Kuma da rashin lafiyar tamu duka nima fama nakeyi da kaina daqyar na iya tasowa nazo.

Ko kallonta umma Bata sake yiba saima wani kallon Data Sakar Mata tanada tabbacin Bilkees din batada labarin auren mijin nata Dan Haka itama saitaqi fada tana ayyanawa da ba Yar Zainab ya auraba da wlh kyalesa zasuyi da auren suyi maganin Bilkees din,

Amma ko yanzu wlh sai tasan abinda tayi Bari dai su samu kansu sufara yakice Zainab da jininta ataredasu kafin suyi lokacin nata iskancin datayi musun.

Ganin ba fuska yasa Bilkees tashi ta tafiyarta,

Kai tsaye girki tasa akai na musamman da kanta ta jeresu a dining din babban palonsu daya raba samansa dasu.

Bayan sallar magrib ta fito fes cikin adon Riga da skirt na atampa dasukai Mata kyau ta fito babban palon suna fira da yarta hankali kwance.

Qarfe Tara da mintina hamsin da hudu ya dawo gidan daga asibitin da gobe insha Allah yakesa ran a sallamo umman.

Duk da akwai gajiya da ciwon kan yamutsin ranar ataredashi Amma nutsuwarsa da kamewarsa yasa kamar a lokacin aka Gama daurin auren

Yayi Mata kyau sosai Cikin shigar tasa ta daurin auren har lokacin.

Mufeeda sannu da zuwa Tai Masa kawai ta kyalesa ya wuce samansa ganin Yana buqatan hutawa.

Bilkees ce ta bisa cikin kulawa.

Koda ta hawo baya Palo Dan haka ta wuce bedroom dinsa Kai tsaye ta taddasa harya tube Yana daureda towel a qugunsa brown.

Fresh fatar jikinsa Mai hutu da lafiya ta kalla tareda Jin shaawarsa Mai qarfi sbd kakkarfar siffarsa dake sake daukan hankalinta da kwadaita dashi.

Qarasowa tayi ahankali tana murmushi ta tsaya gabansa tareda saka hannuwanta biyu akan towel dinsa tana Masa wani irin kallon tsananin so tace,

"Kwana biyun Nan baka zama meyasa ne?

Yau Ina kaje ne kayi irin wannan kyan?....

Sai alokacin ya kalli fuskarta ahankali Yana karantar fuskarta dake jiran amsarsa.
Chapter 52 · 0% Book details