← Book details Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 95

Sashe 48

Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har suka Isa Babu Mai magana Dan Haka suna Isa Amal takama hannun mommynta sukai ciki shima Uncle Lulu fitowa motar yayi yana sake shafa sadakin AQEEL ASAD a aljihunsa ya nufi bangarensa da matarsa ke jiransa.

Har bedroom Amal ta raka mommy Saida taga tayi Shirin komai ta kwanta take bacci ya dauketa sbd magunan da aka Bata akwai Mai saka bacci sosai batareda taso hakan ba Dan waya taso Yi da AQEEL ASAD adaren sbd goben nayi komai zai iya sauyawa batareda sun samu lokacin dakatar dashiba,

Fitowa Amal tayi ya nufi dakinta bayan taga baccin mommyn yayi nisa.

Tana shiga bedroom dinta tubewa tafara yi ta nufi toilet tayi wanka ta fito sanyeda bathrobe pink tana qamshin shower gel dinta na asalin original makari.

Sama sama ta Dan shafa Mai da body spray ta saka White silk Riga da wandon bacci ta kwanta bayan ta kashe wayarta gabaki daya.

Mintina kalilan bacci ya dauketa sbd itama kanta dake Dan ciwo.

AQEEL ASAD daga IDON NERA's Bai koma gidansa ba Kai tsaye gidansa daya na karatunsa ya wuce Wanda shima Babu abinda ya rasa na luxury life din dako wane attajiri yake buqata.

Koda ya Isa a Daren Al-Amin na gidan ya rigasa isowa Yana jiransa sbd Kiran da yayi Masa akan ya samesa yanzu.

Kallon Al-Amin yayi Bayan ya zauna ya kafin ya maida kallonsa kan shigogon hannunsa na patek Philippe ya kalli time kafin ya kalli date din ranar.

Maida kallonsa kan Al-Amin yayi cikin nutsuwa da yafada Masa daurin auren da zaayi goben da dauran bayanan abubuwan da zaiyi.

Dagowa Al-Amin yayi yana kallonsa da idanuwansa ba Dan fili sbd tsananin mamaki.

Cikin girmamawa yace,

"Ok sir zaa gudanar da komai kafin time din daurin auren inshallah.

Harya juya yadawo yace,

"Names na invitations din Sir???

Rufe idanuwansa yayi ahankali zuciyarsa sai alokacin take kokarin ambatar sunan MARYAMAH da wani sunan..

Ahankali yace,

"AQEEL ASAD and AMAL SANDA....

Subucewa iPad din hannun Al-Amin tayi sbd rikicewar dayayi lokaci daya.,

Saurin tarota yayi Yana riqewa dakyau murya na Dan rawa yace,

"IDON NERA???

Batareda AQEEL din yasoba ya dago idanuwansa dasukai laushi ya zuba Masa su.

Da sauri Al-Amin din Yakuma juyawa Ya nufi kofa Yana cewa,

"Sorry Sir,
Angama.

Ficewa yayi Yana daga wayarsa Dan Kiran inda zaa hada lafiyayyan invitation da zai watsawa manyan mutane da jamaar Dr AQEEL ASAD din kowa zai sama nasa kafin safe lokacin daurin auren.

Acikin Daren kwana Al-Amin yayi aikin hidimar daurin auren kafin safe komai ya kammala cikin qanqanin lokaci Dan haka Koda safiyar ranar ta waye da labarin auren AQEEL ASAD aka tashi wanda ya sama harda SSG Hayat da baya qasar.

Gidansa ya dawo da safiyar ranar anan yayi shirinsa tsaf cikin wani lafiyayyan tsadaddiyar luxury milk Cashmere.

Daga Bilkees harsu umma da Haj Maryamah dakowa yake fushi da kowa a gidan basusan dawowarsa ba da safen har shiryawarsa da ficewarsa kamar yanda basusan abinda yake faruwa basusa labarin komai sbd mufeeda ma dake harkan Social media sosai bata cikin kwanciyar hankalin kunna wayarta sbd zancen rikicin tun kwanaki daketa yawo Ana maganar shiyasa ta goge duk wani app dinta dazaisa tagani ta zauna ahakan sai baya kwana biyu komai yawuce.
#MAMUH#
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

Makarantar Lafiya dake garin Kazaure (Kazaure school of health technology) tana farincikin sanardaku cewa ta Kawo wani sabon tsarin karatu a saukake na part-time Degree da Diploma a wasu kwasakwasai domin ma'aikata masuson karin karatu da 'yan Kasuwa wanda basu da isasshen lokaci.

Kwasakwasan kamar haka:

DIPLOMA

1.Dental surgery Technician

2.Medical X-ray Technician

3.Health Information Technician

4.National Diploma in Biomedical Engineering

5.Public Health Technician

6. Community Health Extension Worker (Re-trainee)

7.Junior community Health Extension Worker (JCHEW)

DEGREE

1. Health Information Management

2.Public Health

3.English Language

4.Public Administration

5.Business Administration

6. Economics

7. Accounting

8.Computer Science

9.Mass Communication

10.Agricultural Economics

Domin karin bayani a tuntubi wannan Lambobin:08035298851, 07066542055 ko Azo haraban makaranta dake No 3 Emir's Palace road off Kano-Daura road Kazaure a jihar Jigawan Nijeriya

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma

*KI KULANI*🔥
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥

38

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

38

Tun sallar asuba uncle Lulu yake yawon son magana da zainab sbd tun tsakar dare shine mutum na farko da aka turowa iv din ta waya,

Kwana yayi Yana juya sadakin a hannunsa,

Ita kanta Anty Fareedah ba qaramin firgata tayiba da Jin maganar auren,

Amal da auren Dole?

Mai Mata Kuma?

Harma da budurwar 'ya,

Bayan duk wannan AQEEL ASAD 'dan Haj Maryamah...

Numfashi Mai zafi ta sauke Dan kuwa lamarin akwai rudani Mai girma Amma Kuma ta wani bangaren auren yayi Mata 100% sbd AQEEL ASAD shine Mijin nunawa duniya da Amal dinsu zata samu Kuma abin nunawa duniya Suma AQEEL ASAD ya zama sirikin ahalinsu na IDON NERA,

Zasu sake samun power da suna kamar yanda itadai takeso.

Har qarfe Tara saura uncle Lulu na yawon son magana da zainab Amma har lokacin maganin baccin Bai saketaba,

Bayason Amal tasan meyake faruwa shiyasa yaqi nacewa sai ya yada zainab din Kamar yanda ita ta rokesa aka Dan Allah abar mommyn tayi bacci tunda duk kwanakin Bata samun bacci sbd damuwa.

Ganin yanda Amal ta Dage aka abar mommyn tayi bacci isashe yasa Dole yabarwa Allah yaje ya shirya zuciyarsa na wani irin bugu da tsallen rashin sanin abinyi.

Lokacin daurin auren da aka saka yayi saura kadan,

Manyan mutane zasu taru shi zaa tsaya jira bayan yasan sadakin na hannunsa Kuma shine zai bada auren,

Koya je ko kar yaje yasan auren kamar an daura ne Dan Haka gwara yaje yabada auren Babynsa AMAL Kamar yanda ya basa na siddi

Dan wannan shine burinsa na ganin ya aurar dasu su dukan to Amma na Amal din yazo da babba rudani da firgici.

Dan Haka zuwan nasa kamar Dole ne baida zabi bayan na qarasa shiryawa yaja motarsa Kai tsaye ya nufi babban masallacin AQEEL ASAD din dake hade da gidan karatunsa cikin shigarsa ta alfarma.

Amal kuwa wanka tayi takoma bedroom dinta ta kwanta tana waya da Siddi akan a ranar zata zo jirgin yamma zata biyo.

******Bilkees da mufeeda na sashensu a kunshe suna zaman baqin ciki da tsinewa zuriarsu Haj Zainab gabaki daya hardatasu Haj Maryamah din Yan jarida suka zo gidan sbd labarin daurin auren AQEEL ASAD din.

Daga gate security suka Kira bangaren Haj Maryamah suka sanar da ita zuwan Yan jaridar da abinda suka fada.

Shiru tayi Dan kamar Bata fahimci abinda suka fada dinba ta katse wayar tareda ajewa gefe bayan ta sanar musu su koresu batason hayaniya.

Kamar an dawo Mata zancen a kunnenta tayi saurin daukan waya ta Kira gate din tace,

"Me kace sunzo Yi??

Ma'am rahoton daurin auren Sir sukazo dauka Amma min sanar musu a mosque na gidan karatunsa zaayi daurin auren.

Miqawa umma wayar dake zaune tareda ita tayi tace,

"Umma ji me suke fada nakasa ganewa.

Karban wayar umma tayi tareda sake tambayarsu suka maimaita Mata zancen daya sata Ciro wayar daga kunnenta ta kalla tasake maidawa kan kunnen tace,

"Waye ne zaa daurawa auren yau?

Wane Sir din?

AQEEL ASAD kokuwa sir dinku na can inda aka daukoku aiki??

Batareda damuwa ba Security din yace,

"Ma'am auren Sir AQEEL suke magana Wanda zaa daura ayau 10am da family na madam IDON NERA......

Tashi zaune umma Tai da kyau tana rike wayar dake neman subucewa daga hannunta ta kalli agogon palon da sauri a arikice take cewa,

"Wane AQEEL ASAD din zaa daura aurensa da gidan IDON NERA??

Wace Kuma karfe goman safen???

Haj Maryamah dake kokarin hadiye ruwan datake Sha dawo Mata sukai suna sarketa tareda shigar Mata kai.

A haukace ta kalli umman tana kallon agogo ta karbe wayar tana miqewa tsaye.

Bayanin da akaiwa umman Shi akai Mata.

Kashe Wayar tayi kafafunta na wata irin rawa Kamar Mai rawar disco ta Nemo lambar Al-Amin ta saka kiransa.

Umma ma miqewa tayi qafafun nata na rawar mazari makoshinsu su dukan Yana bushewa suna jiran daga wayar Al-Amin.

Yana daga wayar atare suka jefa Masa tambayar data sakashi Basu amsa atake sbd manyan baqin da akewa iso.

Baya Haj Maryamah tayi zata zube tayi saurin dafa bango tana neman tasa numfashinta.

Umma kuwa a rude cikin masifaffen tashin hankali da zafin zuciya Mai qarfi ta kwadawa ramatu Kira tace maza kice a fidda mota fita zanyi.

Hanyar waje ta nufa ko gani sosai batayi sbd matsanancin tashin hankali da wutar datake cin zuciyoyarta.

Data Bari a daura wannan auren yau gwara ciwon zuciya ya Kama AQEEL din suyi jinyarsa Amma badai ayi wannan aurenba da gwara asarar duniya dashi.

Haj Maryamah ma fizgo numfashinta dake riqewa da karfi tayi tana Jin bazata taba yarda ko a mugun mafarki ba wannan mugun labarin ya tabbata,

Da 'danta ya auri Yar Zainab gwara tayi ciwon sashe.

Umma takarminta daya Dana ramatu daya ta saka batareda tasan Ina kanta yakeba hakama rigar Haj Maryamah ta yafo akanta batareda shima tasan Meye akantaba,

Haj Maryamah kuwa gilashinta na medical upside down ta fito dashin da takarmin umma a kafarta dasukai Mata mugun kadan Amma Bata tasa takeba a rikice suka fada mota driver yajasu cikin mugun gudu suka nufi gidan karatunsa suna duba agogon dayake nuna karfe goma harda mintina Biyar zuciyoyinsu ma wani irin tsalle da rawar tashin hankalin da basu taba ba.

****Acikin barci Haj Zainab ta farka a firgici cikin wani mummunan yanayi na tashin hankali.

Agogo tafara kalla dukkanin jikinta na wata irin rawa.

Goma saura mintina qalilan.

Fitowa Tai daga gado tana istigfar da tashin hankali..

Sallah tayi qafafunwanta na rawa tana idarwa kasa tsayawa addua Tai sai istigfar data sake yi na tsautsayin rashin sallah akan lokacin daya Kamata.

Wayarta take kunnawa hannuwanta na wata irin rawa..

Uncle Lulu take Kira Amma sam baya dauka.,
Chapter 48 · 0% Book details