← Book details Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 95

Sashe 28

Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amal kuwa babban abinda yasa Bata kaunar auren babban mutum shine ta tsani zaman kishi,
Batada hakuri, Bata daukan reni, Bata iya qyalewa Dan Haka ta tsani auren duk Wanda yakeda Mata Dan tasan Koda ba guri daya sukeba Mijin ko waya yayi da matar a gabanta sai sunyi rigima ba Qarama ba uwa uba ta tsani auren mijinda wata ta Gama dashi shekara da shekaru ta bar mata Dan Haka ta zabi raayin auren saurayi Wanda Koda auren yayi a gaba itace dai tagama morarsa kafin wata din ta mora.

Daga mommy har siddi damunta sukai da zancen SSG Hayat duk sukaita korantasa tana saurarensu kawai saiga Anty Fareedah wadda itama takeyi SSG din take ta shiga suka ringa fadar qualities dinsa Amma Sam takasa jinsa cikin ranta.

Kamar jikinta ya lafa sai gashi da daddare ya dawo Mata sosai Wanda yasa Dole ko bayan zuwan Dr tayo Saida suka nufa asibiti da ita Acikin daren..

Acan suka kwana Ana qara Mata ruwa tareda allurai tasamu tayi bacci Mai nauyi Bata farka ba sai guraren 10 na safe.

Wanka tayi da ruwan dumi a toilet din dake Amenity room din dasuke ta saka free Riga da wando Tasha tea Mara sugar tana gamawa kenan saiga shigowar SSG Hayat dakin tareda uncle Lulu sai PA din Hayat din..

Qamshin tsadadden turarensa ne ya Dan gauraya dakin
Mayun idanuwansa gabaki daya akan AMAL din wadda tayi fresh da ita komai nata da class din dayake kashe maza takeyinsa batareda tasan illar da hakan ke musu ba.

Haj Zainab ce ta shigo dakin itama tareda Fahat da sbd Siddi da Fareedah ne suka kwana da AMAL din ita kanta Haj Zainab din sai tsakar dare sosai ta koma itada uncle Lulu.

Ganin Haj Zainab yasa SSG takaita kallonsa akan AMAL da itama kallo daya tayi Masa duk yabi Yana neman rasa nutsuwarsa.
Gashi batason doguwar magana Dole dasu Siddi da Fareedah da uncle suke fira cikin sakewa da wayeba babu ruwansu.

Shogowar Haj Zainab yagaidata cikin girmama a sake babu wani noke noken kunya sbd akwai sabo da wayewa so a sake suke dukkaninsu sunata fira Amma idanuwansa akai akai suna kan Classy Amal dinsa Dan kayan jikinta sun qara Mata kyau da aji harma da bayyanuwar sabon jini ce ita.

Ya Jima sosai a asibitin kafin ya baro tareda driver dinsa da securities dinsa da PA dinsa,

Koda ya Isa office dinsa kusan duka meetings dinsa na ranar kansilesu akayi sbd baida lokaci ko nutsuwar yinsu
Yau Amal da rashin lafiyarta ce kawai a Ransa
Ko gida daya dawo gabaki daya Hana kowa zuwa gurinsa yayi bayason damuwa Kansa na ciwo..

Da daddare a gidan IDON NERA Res yayi dinner sbd an sallamo AMAL din sun dawo gida Kuma sun saba sosai Dama Kuma duk ranar da SSG yazo gidan Nera ce zayi kuka Dan sake musu yake.

Ko aranar wasu irin siyayyar dimauta akayo aka kawosu Kaya guda na dukkanin abinda AMAL keso da buqata ne.

A main palour na gidan sukai dinner a makeken dining dinsu Anata fira cikin sakewa da kulawa har aka Gama suka koma palon Baqinsu na musamman shida AMAL din wadda taketa fizgar nutsuwarsa da Basarwarta da komai nata dayake sanyi.

Duk da Bata jinsa cikin ranta Bata wulaqanta sa saidai Kuma baya samun surunta sosai soyayyar sanyi da basarwa take Dan Yi Masa.

Sai after 10 yabar Gidan ya tafi bayan yayi musu abinda ya Saba wato barin Nera.

Bayan tafiyarsa Kai tsaye Bata tsaya komaiba tayi Shirin bacci ta kwanta.

Bayan isarsa gida Saida ya kirata yasake Jin jikin nata tareda Dan jimawa Yana tarairayarta a wayar tana basarwa sbd bacci datake ji.

Washe gari tafara samun sauki Amma SSG Bai samu nutsuwa ba Haka ya ringa yawon gidan duk da tarin schedules dinsa Amma Haka yake watsi dasu idan lokacin zuwa dubo AMAL dinsa yayi.

Ganin yanda SSG din duk yaqara mutuwa akan AMAL yasa familynta suka sake nacewa akan aurenta dashi duk da Bata sonsa Amma tanason abinda familynta ke so Dan Haka ta da fara saukowa akan maganar auren nasa Amma da sharadin duk abinda zaisa ta hadu da matarsa yayansa zai kiyaye bataso.

Familynta tsayawa sukai akan raayinta Suma sbd basuda niya ko nufin takurata tako Ina..

Shima SSG din babu musu ya amince sbd Daman yariga yasan raayi da halin Amal din Kuma shima matarsa yasan bazataso haduwa ko ganin Amal din ba.

****Maganar aurensa da Amal ta Amince Yana Isa kunnen matarsa hankalinta yayi mummunan tashi sbd Mijinta na auren AMAL tasan tagama yawo ita Dan Haka wlh bazata taba yardaba.
##MAMUH#
#HOTLOVE/AMAL/MARRIAGE
#IDON NERA

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma

*KI KULANI*🔥
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥

*_Arewabooks@Mamuhgee_*
23
Babbar 'yar SSG Yar kimanin shekaru goma Sha bakwai ce tashigo bedroom din mahaifiyarta riqeda wayarta a hannunta da alama kome nene yakawota dakin mahaifiyarta a Acikin wayar yake sbd yanda ranta yake bace.

Nafeesat dake zaune tana waya da babbar aminyarta Kuma Yar uwarta Bilkees wadda duka duka batafi wata ukuba zuwa hudu da dawowa kasar da Mijinta da yarta sai uwar Mijinta...

Dagowa tayi tana kallon 'Yar tata batareda ta Gama wayar datakeyiba tace,

"Amrah lafiya?
Menene ranki yake a bace haka?

Miqa Mata wayar hannunta dake daukeda kyakkyawan hoton AMAL da kyanta ke bayyanuwa sosai kamar wadda ta hada jini Arab.,tace,

Mummy duba kigani maganar auren daddy da wannan karuwar dangin karuwai da Yan daudu ya tabbata sai yadawa akeyi a social media
School ma kusan koina zancen suke tunda ansan AMAL din da zafin Kai da  ajin banza tana familyn karuwai.

Zubawa screen din wayar idanuwanta tayi zuciyrta na bugawa da qarfi,
Kyakkyawar fuskar Amal ta zubawa idanuwanta dake Neman qanqancewa da tashin hankali da baqin ciki tareda tafasar zuciya.

Ko tana so ko bataso kamai Hassada da baqin cikinta Akan Amal tasan kyakkyawace Wanda hakan yake qara mata baqin ciki da tsanarta harma da tashin hankali tunda tasan yanda mijinta ya gama Mutuwa akan kyan bayako duba da qazantar karuwanci dake tattareda zuriarsu

Jin shirun nafeesat din yasa bilkes da itama taji abinda Amrah ta fada ta cikin wayar,
A dan hasale tace,

“Nafee meyesa wai kinaji kina gani da ranki da lafiyarki zaki bar Mijinki ya auri karuwa? Karuwar ma wadda tayi Gadon abinta ta uwa da uba da dangin uwa Dana uba tunda kince yayan uwarta ma Dan daudu ne na musamman mai zaman Kansa.,

Wace masifa ce wannan Zaki zauna kina kallo ta shiga rayuwarki?

Kinkuwa San babbar masifar dakika shiga wasa ce idan har wannan Idon Nera da ake fada tashigo gidanki??

Gaskia nafee kinada sake a komai,

Ni Aminyarki karkiji yanda zuciyata ke shiga tashin hankali da tisishi tareda daukan zafi idan na kwantanta halinda kike ciki ma kawai,

Gaskia Nafee banbaki shawarar barin SSG ya auro Yar IDON NERA ba kamar yanda naji sunan koina aka fadesa dai shedar daya ce.

Cikin Jin zafi da qunci Mai tsuma nafee tace,

"Inda ma ace irin karuwan Nan ne qanana marasa galihu da suka tuba zaa rufa musu asiri a aura sai suzo suyita yimaka biyayya......

A qule Aminiyar tata ta katseta da cewa,

"Ba tubabbiyar karuwa ba ko Tubabbiyar malama ce Karki yadda a auro Miki Dan babu gwara fa a kishiya,

Nafee kinji abinda nakeji kuwa ko sunan kishiya aka ambatarwa wani bare ke da kike Taredani,
Nidai gaskia banaji Miki alkhairi a wannan lamarin gwara musan abinyi tunda har barazanar rabuwa dashi kinyi ko gwada yaqi fasawa.

Hawayen baqin ciki da radadin zuciya me suka gangarowa Nafee tana kasa riqesu tace,

"Bilkees Hayat fa ya Gama shallake duk wani tunanina,
Yariga yayi Nisan da sai Allah Amma na tabbatarda Idon Nera Basu barsa Haka ba Dole akwai abinda sukai Masa,
Qarin abin baqin cikin da takaici basa zaman auren fa,
Tana shigowa zata mallaki fiyeda Rabin arzikinsa ta rabu da auren taje ta auri wani Wanda ya fisa a kudi takuma aura,
Auren uwarta Dana 'yar uwarta baya kirguwa fa, yanzu gashi zaa hada da nawa Mijin gurin qirgan auren muguwar zuriar tasu.

Wani zazzafan numfashi Bilkees ta sauke tana sake jinjina lamarin,

Innalillahi wainna ilayhi rajiun,ita Kam duk ranarda nata Mijin yace zaiyi aure Kila bugawa zatayi uwa uba aure irin wannan na SSG din da dangin da kaf babu Mai kunya bare kawaici bariki sai wadda suka manta.....

Inaaaa,Astagfirllh, Astagfirllh, Allah yaci gaba da barmin mijina da kamewarsa da nisancinsa da Mata.

Hawayen Nafee dasuka koma sheshekan kuka yasa Dole suka katse wayar hankalin Bilkees a matuqar tashe da wannan masifar data fara isarta akan wannan Idon Nera din.

Ajiye wayarta tayi tana kokarin tunanin yanda zasu bullowa lamarin,
Dan tsananin kishinta akan nata mijin yasa ko Wanda tasani taji kishiya akansa ta ringa zullumi da damuwa kenan bare Aminyarta guda Kuma Yar uwarta uwanta zaayiwa wannan babban lamarin.

Hameeda dake gefenta zaune tana duba waya ta dakata da duba wayar ta kalli mamar tata cikin Jinjina lamarin itama tace,

"Umme idan Kikaga AMAL IDON NERA din sai hankalinki yafi tashi fa,
Gaskia mummyn dasu Amrah na cikin  babban tashin hankalinda su kadaine zasu iya fadar abinda sukeji,

Hameeda bana buqatan ko ganin hotonta wlh,
Idan bana son Abu to ko inda Zan gansa bana zuwa,
Karki nunan hotonta Dan ko ahakan karkiji tsana da qyanqyamin danake musu bare Nafee da zaa aurowa,
Tana zaman zamanta a kwaso musu jaraba da cutittika da komaima,
Tazo karshe ta haihu yayan Nafee sun hada jini da yayan gidan karuwai fa kenan...ya Salam,wlh Nafee na cikin mummunan Hali,.ya Allah ka lalata wannan auren ka hanasa ka wargaza zancen can taje ta samu wani ta aura badai SSG dinba.

Amin umme fatar kenan,
Can tasamu Wanda zai aureta..
Chapter 28 · 0% Book details