← Book details Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 95

Sashe 50

Idon Nera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bin bayan maigidan nasa yayi Yana satar kallon Amal da shigarta datafi komai basa mamaki duk da yasan agurinta da irin rayuwar gidansu wannan shigar ba komai bace tasaba fita da abarta Amma ai yau din auren DR SHAYKH AQEEL ASAD guda ne akanta.... gaskia Dole Haj Maryamah da umma su samu somewa Dan kuwa koshi sumar ne kawai baiyiba a jiyan da AQEEL ASAD ya sanar Masa AMAL Idon Nera zai aura ayau din gashi Kuma an daura din dai Dagaske shi din sirikin Idon Nera ne.

Yana fitowa aka sanar dashi farfadowar dukkaninsu gabaki daya Wanda Daman dukansu tsabar shock ne yasasu somewa.

Umma tinda ta farfadoba bayan ajiyar zuciya Babu abinda takeyi sbd bakinta wani abune Mai nauyin gaske ya toshesa ya danne Dan Haka takasa sai ajiyar zuci da kallon AQEEL din takeyi.

Haj Maryamah ma kuwa jininta yaqi sauka Dole aka mata allurai tareda wasu dubarun bacci ya dauketa na Dole Wanda acikinsa sai ajiyar numfashin takeyi itama..

Haj Zainab kuwa tunda ta farfado Bata iya cewa komaiba itama sbd ganin Amal agurin Dan Haka tace ita gida zata koma bazata zauna asibitin ba.

Sallamarta akai suka fito dukkaninsu harda AQEEL ASAD yasa Al-Amin ya wuce gida da umma shikuma a motarsa zai tafi da Maminsa yakaita gida tunda ummansa ita ba yanzu ba tana asibitin.

Amal Kai tsaye ta nuna itace zata tafi da mommyn Amma ko ta kan zancenta AQEEL ASAD Baima bi ba sbd lura da zafin datake ciki.

Uncle da Anty Fareedah suka lallabata baya AQEEL din ya wuce da mommynta yabarta agurin tsaye.

Uncle Lulu da Anty Fareedah ne sukabi bayansu mommy itakuma airport ta wuce sbd siddi datai Mata wayar ta iso.

Tana Isa airport din sun sauka already Dan Haka daukota kawai tayi suka nufo gida ranta har lokacin a bace yake da ikonda wani zai nuna Mata Akan mahaifiyarta bayan mommyn ta yanke duka wata alqarta dashi.

Har suka iso gida fuskarta a daure take ita kanta siddi hankalinta yayi mummunan tashi dajin mommynsu ba lafiya har a asibiti.

Suna shigowa parking kawai Amal tayi suka shigo ciki atare da siddi

Siddin ce a gaba AMAL tana bayanta taba kokarin duba wayarta da sakonni suka shigo Mata a jere Wanda ake tayaya murnar aurenta da AQEEL A....kasa qarasa karantawa tayi ta nufa palon mommynsu Kai tsaye a sama inda ta tadda siddi tsaye takasa qarasawa sbd abinda mommyn ke fadawa AQEEL da uncle Lulu.

Hawayene kwance kan fuskarta cikin matsanancin tashin hankali da fita hayyaci take kallon AQEEL ASAD Wanda yake tsaye gabanta ta riqe hannuwansa duka biyu tana cewa,

"AQEEL wallahi na yarda duk Wanda zaka aurawa Amal ka aura Mata kanada cikakken iko akai Amma Dan Allah ka warware aurenka da ita,

AQEEL bazan taba hanaka iko Akan Amal ba Amma Dan Allah ka warware aurenka dake kanta na rokeka........

Kallonta yakeyi da dukkanin idanuwansa masu kyau da Isa,

Baida niyar magana sbd Babu abinda zai iya Yi akan abubuwan datake fada,

Warware aure take magana nasa da MARYAMAH,.

Me zaice Mata?

Daga ita harsu ummansa ya shirya sakawa borinsu Ido kawai batareda tankawaba Dan kuwa sunyi nisanda basa gane komai idan ba na rabuwar ba.

Kallonsa uncle Lulu yayi Amma kwarjininsa ya hanasa yayi Masa magnar dayake son fada din.

Ahankali ya zare hannuwansa daga na Mamin Yana kallon fuskarta dake firgice gabaki daya ta fice hayyacinta.

Ahankali ya girgiza Mata Kai cikin nutsuwa da kamewa da muryarsa Mai aji acikinta yace,

Mami Babu saki ko warwara a wannan auren kinfi Kuma kowa sanin tsayuwata Akan zancen daya....

Siddi datai mutuwar tsaye ce da Jin abinda yake faruwa da matsanancin mamaki tajuyo tana kallon Amal wadda itama Tai mutuwar tsayen tana sauraron abinda yake faruwar tace,

"Wace Amal din ce aka daurawa aure dashi Mommy??

Haj Zainab da uncle Lulu ne suka waiwayo kofar a tare cikin firgici,

AQEEL ASAD din kuwa Babu wani damuwar data shigesa kai tsaye ya juyo ahankali ya zuba Mata idanuwansa dasuka saka gama rudar da Siddi da tsananin kwarjininsu.

#MAMUH#

#HOTLOVE#MARRIAGE#AQEEL ASAD.

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

Makarantar Lafiya dake garin Kazaure (Kazaure school of health technology) tana farincikin sanardaku cewa ta Kawo wani sabon tsarin karatu a saukake na part-time Degree da Diploma a wasu kwasakwasai domin ma'aikata masuson karin karatu da 'yan Kasuwa wanda basu da isasshen lokaci.

Kwasakwasan kamar haka:

DIPLOMA

1.Dental surgery Technician

2.Medical X-ray Technician

3.Health Information Technician

4.National Diploma in Biomedical Engineering

5.Public Health Technician

6. Community Health Extension Worker (Re-trainee)

7.Junior community Health Extension Worker (JCHEW)

DEGREE

1. Health Information Management

2.Public Health

3.English Language

4.Public Administration

5.Business Administration

6. Economics

7. Accounting

8.Computer Science

9.Mass Communication

10.Agricultural Economics

Domin karin bayani a tuntubi wannan Lambobin:08035298851, 07066542055 ko Azo haraban makaranta dake No 3 Emir's Palace road off Kano-Daura road Kazaure a jihar Jigawan Nijeriya

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥

Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥

Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥

Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥

Safiya huguma

*KI KULANI*🔥

Miss xoxo

Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171

Maryam sani

Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*🔥

40

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

40

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

Makarantar Lafiya dake garin Kazaure (Kazaure school of health technology) tana farincikin sanardaku cewa ta Kawo wani sabon tsarin karatu a saukake na part-time Degree da Diploma a wasu kwasakwasai domin ma'aikata masuson karin karatu da 'yan Kasuwa wanda basu da isasshen lokaci.

Kwasakwasan kamar haka:

DIPLOMA

1.Dental surgery Technician

2.Medical X-ray Technician

3.Health Information Technician

4.National Diploma in Biomedical Engineering

5.Public Health Technician

6. Community Health Extension Worker (Re-trainee)

7.Junior community Health Extension Worker (JCHEW)

DEGREE

1. Health Information Management

2.Public Health

3.English Language

4.Public Administration

5.Business Administration

6. Economics

7. Accounting

8.Computer Science

9.Mass Communication

10.Agricultural Economics

Domin karin bayani a tuntubi wannan Lambobin:08035298851, 07066542055 ko Azo haraban makaranta dake No 3 Emir's Palace road off Kano-Daura road Kazaure a jihar Jigawan Nijeriya

****************

Da mamaki Amal ke kallon mommynta da Uncle Lulu dasuma ita din suke kalla,

Zancen Bai razanata sosaiba sbd tasan bamai yiyuwa bane abinda take tunanin taji din?

Ba ita Amal din ba sbd abune da bazai taba yiyuwaba mommyn su aurar da ita bada sanintaba Kuma aurenma na Dole da Wanda sukasan kota Yaya bazata yarda ta taba aurensaba.

Qin kallonsa tayi ta qaraso ahankali gabansu mommyn tana sake kallonta da kyau kafin ta bude Baki tace,

Mommy wace Amal ake magana akai?

Wane auren Kuma aka daura?

Dakuma waye aka daura auren??

Siddi ma cikin mamakin ta qaraso tana kallon Mommyn tasu Amsarta suke jiran ji Dan itama tashiga rudani da mamaki Mai girma idan har Amal dinsu ake nufi,

Mezai hada Amal da auren bazata, auren Dole, auren rashin sani??

Rintse idanuwa Haj Zainab tayi hawayen dake ciki suka Kuma gangarowa kan fuskarta datake ta jiqewa da hawaye tunda suka dawo din.

Kasa kallon Amal tayi sbd tasan baa kyauta Mata Dan Koda zaayi Mata auren bazata da dolen yakamata a sanar Mata

To Amma ya zatayi AQEEL itama yasha gabanta ya zartar da wannan danyan hukuncin da batasan ya zatayi ba bare Amal,

Girman kaunarda takewa AQEEL wata halittace da Allah ya halitta Mata cikin ranta da bazata taba iya cirewaba ko fincikewa,

Tasan kaman yanda yafada tafi kowa saninsa a duniyarsa baya magana ya janye tun Bai kawo yanzu dinba bare yanzu daya sake zama mutum tsayayye,

Wlh tasan bazai saki wannan aurenba a yanzu gashi tayi rokon harta galabaita Babu alamar Wasa ko sauyin raayi a tattarre dashi,

Me zata cewa Amal?

Tayaya zata kalleta tace Mata aurenta aka daura ayau batareda saninta ko Jin raayinta ba.

Innalillahi wainna ilayhi rajiun"

Kan daya daga kujerun palon ta zube dabas tana dafe kanta hawayenta na tsananta gudu..

Siddi ce ta qaraso kusada ita da sauri ta zauna tana sake shiga mamaki da firgici Dan kuwa alamun sun nuna dai kila Amal dinsu ake magana akai..

Dafata tayi cikin kulawa Mai tsanani da damuwar ganin halinda take ciki sanyaye tace,

"Mommy Dan Allah ki kwantar da hankalinki ki dawo daidai bamason ganinki hakan

Koma menene matsalar zata wuce zamu fuskanceta mu maganceta kaman yanda muka Saba tsayawa da juna,Amma Kuma mommy wace Amal din aka daurawa auren ayau??

Dago jajayen idanuwanta tayi ta kalli inda Amal ke tsaye tana jiran amsar da zataji tabawa Siddin.

Ahankali ta iya bude Baki murya a shaqe tace,

"Amal wannan da muke da ita guda daya gatanan.....

Kaman siddi batasan wacece Amal din ba ta waiwayo cikeda dinbin mamaki ta kalli Amal din zatayi magana Amal ta katseta da cewa,

"Aure fa kuke magana Mommy¿

As in aure aure irin na kowa da ake Masa???

Maida kallonta kan uncle Lulu tayi cikeda mamaki tana sake kasa gasgata abinda aka fada din tace,

"Uncle meyasa kayi magana Dan Allah Mana.

AQEEL ASAD daga inda yake Bai waiwayo ba ya nufi kofa hankalinsa kwance ya fice yabarsu sbd bayajin akwai sauran bayanin da Bata ganeba idanma Bata gane dinba zasu Mata bayanin dazaisa ta gane din.

Bayansa uncle Lulu yabi da kallo fuska a Dan yamutse da tunanin Yaya Kuma zai tafi ya barsu da bayani baya shine yayi Aika aikar gabaki daya.

Dawo da kallonsa yayi kan Amal Yana Dan Jin tausayin abinda zai fada Matan, cikeda kulawa da tausasa harshe yace,

"Baby Aurenki AQEEL ASAD yayi ayau,

Kudin aljihunsa ya cire tareda kamo hannunta zai Dora Mata ta zame tana kallonsa da idanuwanta dake cikowa da hawayen tashin hankali,mamaki da baqin ciki tareda firgita.

"Wannan shine sadakinki Amal" uncle Lulu yafada Yana kallon idanuwanta dake kokarin cika da hawayen baqin ciki da zafi zai tsanani,

"Sweetie kiyi hakuri....

Uncle aure fa kace?

Auren Dole kukai mun?

Kallon Mommy tayi sai kawai takasa cewa komai ta juya ta fice dakin da sbd zuciyarta harbawa takeyi da qarfi da ciwo..

Kai tsaye dakinta ta nufa tana kokarin rufewa mommynta ta tare kofar tareda shigowa idanuwanta cikeda rauni da tausayin 'yarta takasa magana sai rungumeta datayi Tana cewa,

"Kiyi hakuri Amal,
Chapter 50 · 0% Book details