Sashe 9
Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kyau,sanye take da riga da skirt English wears,long skirt mai budewa tundaga kugu sai rigar iya kugu mai gajerar hannu kalar ruwan hoda,hula ne akanta black sai black din flat shoe wanda suka hade da fatarta kalar half-caste sukayi mata kyau sosai hannunta riqe da wayarta iPhone 8+ da ita da Nihal da Laila wayarsu iri daya. Amsa sallamar sukayi,nan tafara gaida kowa tare da jan kujera tazauna. Bodejo tace"kawai saboda bakin hali saikishige kurya kiqi fitowa?akan wane dalili? Turo mouth gaba tayi tace"Kai bodejo uhumm,awara ta zuba da egg source tare da tsiyayan kunun gida tafara sha. A lokacin su Daddy suka kammala harma da Galadima suka miqe. Suma su Sauban basu wani jimaba suka tashi, dama a takure take saboda irin kallon da Kareem ke mata a sace. A hankali kowa yadinga tashi duk aka watse yarage daga Zuhra,Laila,Nihal da maimoon. Wajejen 9:30 kowa yana apartment dinsa inda su Zuhra ke apartment din Ammi dakin Laila. Sauban ne ya shigo bedroom din Ammi,cike da girmamawa yace"Sweetheart kenan haryanxu baki baccin wurin ko?duk da kallo daya zakama fuskansa zaka fahimci yana cikin damuwa. Kura mishi idon Ammi tayi tare da aje hisnul muslim din hannunta akan side drower tace"Son lafiya?naga kacanza ne bakamar sanda kadawo cike da farin ciki ba? "Sweetheart Daddy p suka sameni akan wani magana wanda Allah yasani tun farko nace banason yarinyar amma sunce umarni suke bani kan na amince inhar sun isa dani,bama kaman Daddy sweetheart bakiga yanda yakeyi ba. Shikuma Galadima harda rokona wai yana gudun lalacewar zumuncin su day rigimammiyar tsohuwan nan hajiya Laure. "Wallahi muddin akamin haka ba'a kyauta min ba sweetheart don sam yarinyar batamin ba,yaqarasa maganar tare da murza forehead dinsa da babban yatsan hannunsa. Ajiyan zuciya Ammi tasauke tace"Amma basun fadamaka dalilinsu na umurtanka da auren ba? Sauban yace"A'ah sweetheart kawai sunce sunyimin mata sannan umarni suke bani wai inhar sun isa, Galadima hardamin kuka gabadaya sun daddaure ni,mema sanyi a ciki shine Abbie, yanzu yazanyi da rayuwata?wallahi sweetheart banason yarinyar nan please kisa Baki.Yayi maganar idanuwansa nasake jajazur. Ajiyan zuciya Ammi tasauke tare dayin murmushin da baiwuce iya labba ba don Allah yasani har zuciyarta bata aminta da aurensa da Akeela da akeso a hada ba amma bazata hanashi yima iyayensa biyayya ba,kuma bazatayi sanadin abinda zai bata zumunci ba. "Kaine kajawa kanka Sauban tun tuni ake maka maganar kafito da matan aure amma kaqi to ya kakeso ayima nibazan goyi bayan kaqi yima iyayenka biyayya ba kacigaba da addu'ah Allah yasa hakan shi yafi alkhairi. Shiru ya ratsa na wani lokaci,mikewa yayi yace"shikenan sweetheart nizan tafi na kwanta ina furar da kika mun magana? "Yananan a cikin karamin fridge dincan. Nufar fridge din yayi yabude yadauki furar sannan yamata sai da safe tare da jan kofar yabar bedroom din,girgiza kai kawai Ammi tayi tacigaba da duba hisnul muslim dinta. Washegari zuhra zaune take a qasa kusa da Abbie tana saurarensa,gefensa Ummie ce fuskanta kadaran kadahan sai ya Taufeeq da yake zaune kusa da Ummie. "Kinji mamana anan zaki cigaba da zama saboda munyanke hukunci dasu Daddyn ku kan zaki shiga University of maidugri ne tunda kindage bakison zarian koh?baki kewar mune? Dago dararan idanuwan ta tayi tadubeshi cikin cool voice nata tace"ina kewanku mana Abbie musamman ma kai dasu maimoon da mommy,amma nafison nandin,takarisa maganar muryanta na rawa. Sosai Abbie yaji wani irin tausayinta saboda yasan badason ranta zata zauna anan ba amma saboda mahaifiyar ta tazabi nisantar su. Cike da barkwanci ya Taufeeq yace"Ai Abbie tagaji da ganinmu ne musamman ma ni. Turo mouth tayi tace"Kai ya Taufeeq wallahi niba haka nake nufi ba kawai dai....tayi shiru batare da takarisa ba,kasa take duban Ummie wacce take lallatsa wayarta tamkar bata a wajen,ajiyar zuciya mai karfi ta sauke tare da rintse idanuwan ta. Dafa kanta Abbie yayi yace"shikenan Allah yayi miki albarka kinji Allah yabada sa'a akan KARATUN da zakiyi 'yar jarida,nan yashiga yimata nasiha masu shiga jiki,wanda har sai da zuhra jikinta yayi tsananin sanyi,duban Ummie yayi yace. "Ummien yara to kema kiyi naki nasihar mana. Barin lallatsa phone din tayi tace"Allah yabada sa'a ubangiji kuma yamiki albarka.Tana gama fadar haka tamike. Duk cikansu da kallo suka bita,sosai zuhra jikinta yayi sanyi. Shima ya Taufeeq 'yar nasihar yayi mata tare da dan zolayarta kamar yanda yasaba. Bayan kwana daya Abbie,Abba,Ummie,mommy,ya Taufeeq, Laila, Nihal suna shiga motoci inda Ummie, mommy,Abbie, Abba suka shiga mota guda Abba ne kejan motar sai dayar ya Taufeeq, Laila, Nihal dasu maimoon inda ya Taufeeq kejan motar sosai zuhra ke kuka na kewarsu don tunda take ko hutu bata taba zuwa ita kadai ba,inda Abbie yaturama da ya Sauban kudin shopping dinda za'a ma zuhra don before azumi zasu fara attending lectures,shiko ya Sauban yamaida masa yace ai za'ayi mata duk siyayyan daya kamata. Kowa haka ya watse cike da kewar mutanen kadunan. *_IDAN NAGA RUWAN COMMENTS ANJIMA NASAKI DAYAN PAGE DIN Xahratty CE Lallai Alqalami yafi takobi 19/2/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): *_GALADIMA FAMILY_* Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 10 _Bismillahir-rahmanir-raheem_ _____Ayau Saturday ne kuma su zuhra zasuyi jamb dinsu,tun wajen 7:30 tatashi tayi duk abinda yakamata. Don Daddy yace 8:00 zai dauketa su tafi wajen bodejo taje don mata sallama ita da galadima a parlon taciddasu su duka sanye da medical glass suna kallon tashan aljazeera. Amsa sallamar da tayi sukayi suna maida hankali akanta,duban tsanaki bodejo kemata sosai take mamakin girman zuhra don zakayi tunanin takai shekara 18 koma 20 saboda yanda Allah ya halicceta da diri sosai ko ina tubarkallah Masha Allah. Sanye take da Dubai gown Army Green sai white flatshoe duk da cewa face nata babu makeup sai dai tayi kyau sosai. Gaishesu tayi cike da kulawa suka amsa mata,bodejo tace"Har anfito za'a tafi? Daga kai zuhra tayi tace"Eah bodejo zanje wajen Daddy ne mutafi. Galadima yace"toh Allah yabada sa'a ubangiji yasa kifito da 300 score. Dariya suka sanya gabadaya zuhra tace"Ameen my Galadima na tafi. Fatan dawowa lafiya suka mata sannan suka fita, apartment Baba Hasheem tafara shiga, Mom tasamu a kitchen don haka tafara gaisheta tana tambayar Baba,cike da fari'a Mom ta amsa anan take sanar da ita baima tashi daga bacci ba. Sanar mata tayi da yanzu zata tafi wajen exam din jamb idan ya tashi ta gaisheshi. Fatan alheri Mom tamata. Koda tashiga apartment din Ammi a dinning ta taddasu itada Daddy,cikin shauki takarisa garesu face nata dauke da yalwataccen fari'a. "Good morning Ammi, good morning Daddy. Cikin fari'ah suke dubanta, Ammi tace"Morning my zuhra antashi lafiya? Daddy yadubeta yace"ah lallai mamana har anfito ne? Murmushi tayi tace"Ea. "To kizauna kiyi breakfast tare da Daddyn naku kafin shima Sauban yafito. Sosai kirjin zuhra yabuga saboda batason haduwa da Sauban din. Cikin sauri ta girgiza kai tace"A'ah Mom nayi breakfast Alhamdulillah bari naje dakin Aunty Mashahuda nayi mata bangajiyan jiya. Ammi tayi murmushi tace"ai bata tashi daga bacci takoma gashi ansamu hutun hadda. Cikin sanyin jiki zuhra tajuya don komawa parlon ta zauna, clashing sukayi da Sauban wanda fitowanshi kenan,suit ne a jikinsa blue black da covershoe black agogo kirara Gucci yake daura bakajin kamshin komai sai na perfume din da yasanya. Hada ido sukayi da zuhra wani harara ya gallamata,itakuwa cikin sauri ta dukar dakai tana murguda baki a hankali tace"Ina kwana. Ko amsawa beyi ba yasamu waje ya zauna,tare da gaisar da iyayen nasa. Cike da kulawa suka amsa,Ammi tace"Son kanwarka na gaisheka. Dan yamutsa face yayi sannan yace"Sweetheart banji bane hankali na na wani wajen,daganan sai ya cigaba dacin abincin sa. Daddy da Ammi kuwa murmushi kawai sukayi,a gurguje suka gama cin abincin,mikewa Daddy yayi Sauban ma yamike. kaitsaye parking space suka isa inda Daddy yashiga gidan baya zuhra kuwa gaba tashiga. Sauban ne yaja motan tare da sanya karatun alqur'ani na Abdullah Abba Zaria,zuhra kuwa a ranta tace"wannan mutumin mayen karatun Abdullahi Abba ne idan anbibiya ma baisan shi ba. "Idan ni bansanshi ba aike kinsanshi koh?taji muryan Sauban yajefeta da wannan tambayar a rikice zuhra tadago tana dubansa. Don sam batayi zaton karatun zucin da takeyi yafito fili ba,idanuwanta gabadaya ta diddilo waje tana duban Sauban. Shikuwa ko kallon inda take beyi ba yacigaba da driving dinsa. Koda suka kariso center da zatayi Jamba din Daddy dakanshi yashiga yakaita don har anfaffara shiga hall din. Nan Daddy yace tanatau tamaida hankali tayi exam din cikin nutsuwa,cike da girmamawa ta amsa masa da toh. Sai wajen karfe 11:30 su Zuhra suka fito daga wajen rubuta Jamb din,cike wajen yake da maza da mata,wasu sa'o'inta wasu sungirme mata wasu kuma ta girmesu sai hayaniya yake tashi a wajen cikin sanyin ta itakuwa take tafiya a kofan gate din center tatsaya tana tunanin ta inda zata koma gida gashi ita bawani sanin maidugri tayi ba. Hankalinta gabadaya yakoma gida saboda yanda taga anata zuwa daukan wasu daga gidajensu wasu kuma suna tsare adaidaita sahu,da yawansu zuwa daukansu akeyi. Samun gefen gate din tayi tatsaya. Duk wanda yazo wucewa sai yadubeta fuskar nan a hade wayanta taciro da niyyar kiran Ammi sai taji magana daga gefenta,cikin natsuwa ta dago don ganin me maganar. Wani saurayi tagani a tsaye yadubeta tare da nuna mata bakin titi yace"Wai kije inji brother naki,a hankali zuhra ta sauke wani gwauron ajiyar zuciya cikin nutsuwa tanufi motar. Sukuwa gabadaya student dinnan hankalinsu yakoma kan motar da ya Sauban ke ciki,'yan mata kuwa da dama ganinsa yasa sun susuce. Sallama tayi iya labba har tanufi gidan baya da niyyar shiga sai tatuno da maganar Aunty Mashahuda don haka sai tabude front seat tazauna,tare da gaidashi. Da kamar bazai amsa ba sai kuma zuwa can ya amsa. Sunyi tafiya babu wanda yayi koda tari sai zuwa can Sauban yadan dubeta, gyaran murya yayi tare da sake dan tsuke face yace"wannan Jamb din da kikayi tamkar aikin banza ne don basan karatun kike ba. Cike da rashin fahimta Zuhra ke dubansa,ta wutsiyar ido yake dubanta,gane bata fahimci abinda yake nufi ba yasashi cewa. "Zansamu Abbie nafada masa cewa keba karatu ne a gabanki ba aure kikeso tunda nakama ki sau biyu kenan. Da sauri tadago tana dubanshi tare da tsantsar mamaki da razana da kalamanshi mouth dinta har