Sashe 7
Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gidan kekiransa da Abbie sunan da Sauban yasa masa, Harun wanda suke cema Abba kuma yana lecturing a KASU ne,shima Hasheem wanda suke Kira da Baba yana lecturing ne a ABU zaria. Allah yarufama iyalensa Muhammad asiri da shi kansa dai gwargwado,sosai sunanshi yayi fice inda a wancan lokacin zamanin sarkin lokacin ya nada masa sarautar galadiman zazzau shikenan kuma sai sunan yabisa,an nada masa sarautar babu jimawa kuma don ba'a wuce shekaru uku ba yakoma MAIDUGRI gabadaya da iyalensa,banda Abba da Abbie inda Baba Hasheem yakoma University of maidugri yacigaba da lecturing dinsa. Zuhra kuwa sosai tasha wahala a hannun mahaifiyar ta bilkisou vwacce suke kira da Ummie,duk da kuwa tataso 'yar gatace Amma sam batajij dadi ta wajen Ummie yana daya daga cikin dalilan da yasa Abbie yake tsananin son ta kenan,tunda yayi fadar har yagaji yasama Ummie Ido,mommy ce a kaduna tamaye mata gurbin mahaifiyar ta. Inda sosai mommy ke tsananin tausaya ma zuhra tare da bata cikakkiyar kular da tadace komai tare take musu ita da Nihal har Allah yabata ciki tasake haihuwar junior yasir,takuma sake haihuwan mace maimoon. Dalilin dayasa zuhra tataso da tsoron Ummie kenan tare da shakkar ta,idan kuwa ace Abbie baya gari zama takeyi kamar mara lafiya. Wannan kenan. _Cigaban labarin._ Ji kake tassss! Jikinta babu inda baya shaking tsaban rudun da take ciki hawaye ne kawai ke tsiyayowa daga idanuwanta,dafe kuncinta tayi don sosai Marin ya shige ta. Lokaci daya parlon yadauki shiru sosai Taufeeq, Mashahuda, Laila, Nihal jikin su yayi sanyi ganin irin marin da Ummie ta zabga ma zuhra,cikin kakkausar murya tayi pointin dinta tare da cewa. "Karyan rashin hankali kikeyi zankoya miki natsuwa ne,stupid kawai. Takarisa maganar tare da jan tsaki cikin muryan tsawa tace"Get out !!! Da wani irin sassarfa zuhra tafita inda jikinta babu inda baya rawa, Taleeb kuwa sunkuyar dakanshi yayi idanuwan shi sunyi jajazur. Kaitsaye apartment din Ammi zuhra ta wuce,kicibus tayi da Ammi a kofar hawa stairs din Daddy, fadawa tayi jikin Ammi tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciyar duk wani mai sauraro,cikin rawar murya tace. "Ammi...Am...Ammi don Allah Ummie ne mama na? Ummie ne ta haifeni?meyasa Ummie tatsaneni?please kuje kubata hakuri kuce tasoniiii...taja kalmar saboda wani irin kuka da yazo mata. A hankali Ammi takai hannu tana shafa kan zuhra cikin tsananin tausayin ta wani kwalla taji ya taru mata a idanuwan ta,kama hannunta tayi tanufi hanyar wani corridor inda zai sadata da parlon ta,zaunar da zuhra tayi akan sofa. Facing dinta tayi tare da kakalo murmushi takira sunan zuhra, dago dara n idanuwan ta tayi wanda suka tasa saboda kuka ta zubawa Ammi. "Kiyahakuri kinji?kidauki duk wani abu da zaifaru dake a matsayin kaddara da kuma jarabawa kinji?Allah Yana sane dake Koda wasa kuma kada nasake ji kinkuma fadar maganar nan,watarana fah sai labari kinji zuhra na? Daga kai kawai tayi tare da amsawa Ammi,murmushi Ammi tayi tace"kinci abinci? Cikin sanyin muryan ta tace"A'ah yanzu zanje wajen Mommy na amsa alale na. Ammi tace"yawwa to taaji kije Allah yamiki albarka. Mikewa tayi cikin sanyin ta tafita,kaitsaye apartment din mommy tanufa dai dan lungun shuke shuke tsakanin apartment din Mom dana mommy taji anfisgo ta tafada jikin mutum. A tsananin gigice ta dago tare da kokarin sanya ihu,Ido biyu sukayi da Aseef inda yake binta da wani irin matsiyacin kallo Yana lashe lips. Jikin zuhra ne yatsananta kadawa,kirjinta na tsananin bugawa,baki yakai da zummar yimata sumba Allah kuwa yabata sa'a ta dunkule hannu takaimasa punch a hanci. Ai tuni yasaketa yana me dafe hancinsa,itakuwa zuhra dagudu ta falla bata tsaya ko inaba sai apartment din Mom banda nishi babu abinda takeyi,hawaye kuwa anan ya tsananta ambaliya. Gefe ta samu tafashe da kuka a fili ta furta"wa zankaiwa kuka na?wa zanfadama halinda nake ciki don ya magancemin? A hankali maganar wata 'yar ajinsu yafado mata inda suke fira dawasu can daban a cikin firar tace. _Fauziyya duk duniyar nan banda mahaifiyarka babu Wanda zaka fadama magana ya fahimceka sama da mahaifiyarka shiyasa Allah yakara ma iyayenmu mata lafiya da nisan kwana._ A fili tasake fashewa da kuka tace"banda nawa Ummien. Dafata taji anyi,da sauri tadago sai sukayi ido biyu da Taufeeq dan murmushi ya sakin mata yana kallon yanda hawayen idanunta kowanne yake rige n sauka,zama yayi a dan gefenta tare da daukan kanta yadora akan kafadarsa. Sai dai ko wannensu yakasa cewa komai,katse shirun da cewa. "Tashi muje mommy na nemanki,yayi maganar yana miqar da ita tsaye,a hankali ya miqar da ita. Apartment din mommy suka nufa. ******** "Daddyn Sauban bazaka gane abinda nake nufi bane wallahi bilkisou sam bata kyautawa rayuwar ta,ni kaina bacin agaban mu bilkisou ta haifi zuhra sai nace ba itace ta haifeta saboda wannan dan kankanin matsalar amma ace bilkisou tadauki tsanar duniya tadorawa zuhra,anyi anyi anyi?iyayenta sunyi rokon har sun gaji wannan wane irin musifa ne? Daddy yace"Aisha nikaina hankalina na tashi, muddin zamu hadu da Sadeeq to maganar da zaifara yimin kenan, yarinyar tana shiga tsananin damuwa,ni tsoro na kada wani larura ya kamata. Ammi tace"narasa meya shiga kan bilkisou,bilkisou meson yarane kaduba fa,kuma sanda tasamu cikin zuhra ta dauki son duniya ta dorawa cikin don ko cikin Taufeeq batanuna zumudi haka ba,ko a sanda tahaifeta kamar ta hadiye abarta sai daga baya zancen ya canza. Daddy yace"Allah ya kyauta,ita kuma Allah yakara mata hakuri da juriya ubangiji ya bata ikon cinye jarabawarta. *MALAYSIA* Sosai Sauban yake cike da farin ciki saboda kaitsaye anamasa interview akace za'a daukeshi aiki a company kuma hazaka da kokari nashi sun burgesu sosai,inda sauran goma sha biyar din akace zasuji bayani daga baya. Anan suke sanardashi nanda 2 weeks zaifara shiga office,sosai yayi godiya inda yafara shirye shiryen dawowa gida Nigeria. Kwananshi biyar a Malaysia yafara shirin dawowa. A MAIDUGRI kuwa gabadaya yaran 'yan matan gidan suna cikin din Ammi inda suke aiki,zuhra ce kehada couslow don aikin da aka bata kenan. Cike da sanyin ta take aikin sai dai sam fuskanta babu walwala ko kadan,cike da barkwanci Mashahuda tace"Aunty zuhra kiyi kigama hadamana couslow dinnanfa don nasan yau akwai santi akan dinning. Dariya duk sukayi muneefa tace"Ai sis shiyasa Ammi tabata hadin couslow din. Dan murmushin gefen baki zuhra tayi tace"kai Aunty's. Xahratty CE Lallai Alqalami yafi takobi 17/2/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): *_GALADIMA FAMILY_* Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 09 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ *This page is dedicated to my lovely son l,much love my rabin jiki* _____Wannan saurayin ne da suka hadu dashi a super market dazu,mirmushi ya sakar ma zuhra cikin sauri ta kawar dakai tare da basarwa. Maida dubansa yayi ga Aunty Mashahuda wacce batadena yimishi kallon mamaki ba,dan murmushi yamata yace"Auntymmu dama nan kukazo? Mashahuda tace"aiko nan mukazo sannu dai. Aunty Safeena tace"kunsan junane Shuraim?dan sosa kai yayi tare da murmushi yace"Ea Aunty munsan juna. Zuhra ce tadubi Abban inteey tace"Yaya Asheer sannu da zuwa, inayini? Fuskarshi cike da fari'a ya amsa da lafiya lou autan Abbie yaushe kuka shigo garin? Zuhra tace"yau sati daya. Yace"Masha Allah yasu Ummie da Abbie? Zuhra tace"duk suna nan lafiya lou harma sun koma yau kwana biyar da komawansu. Shiko wannan saurayin ke suna Shuraim tuni zuhra tatafi da imaninsa gabadaya hankalinsa yakoma kanta. Dubanshi Aunty Safeena tayi"Shuraim lafiya kuwa?firgigit yayi tare da maida dubansa wajen Aunty Safeena,daga Abban inteey har zuhra suma dubansu sukayi. Abincin Aunty Mashahuda tadauka tare da duban zuhra tace"Sis zo muje dinning muba su Yaya Asheer waje. Mikewa zuhra tayi don dama a takure take hannunta riqe da hannun inteey suka nufi dinning din zama sukayi inda zuhra tajuyama parlon baya. Cikin kasa kasa da murya Aunty Mashahuda tace"kinsan wancan mutumin ke yabiyo anya ba sonki yake ba zuhra? Sosai zuhra taji gabanta ya fadi amma sai ta basar tace"hmmm Aunty ni babu ruwa na dasu Daddy wallahi yaje can yaqarata,takarisa maganar tana kai lomar spaghetti din bakinta wanda yaji dakakken naman kaza. Itama bata sake magana ba mashahudan, can wayar Mashahuda yafara Ringing,hannu takai tare da dauka sunan ammi ne ya bayyana akan screen din wayar. "Assalamu alaikum ammi,bansan me akace mata daga can bangaren ba sai dai tazaro idanuwa gabadaya,ta marairace face tace"please ammi kice masa muna hanya yanzu zamu dawo,magana aka sake mata tacan bangaren. Sake marairaice face tayi"please ammi muna zuwa fah. Itakuwa zuhra tuni ta aje spoon din a cikin plate din taja tissue tagoge mouth dinta sannan tamike,itama Mashahuda mikewar tayi bayan ta aje wayar tadubi zuhra tace. "Wai Daddy ne yadawo yake tambayar inda muke,shine tace munje supermarket shine fa yafara fada. Tafiya zuhra tafara suka dawo parlon,mikewa Abban inteey yayi yace"Shuraim kamaidasu gida zanshiga inwatsa ruwa ne don yanzu za'a kira magrib,cike da girmamawa ya amsa key din yace"nima gida zan tafi yaya dagacan. Abban inteey yace"tohm shikenan ka gaida mutan gidan kacema Alhaji gobe zanshigo. Aunty Safeena tace"muje toh kutafi don nasan kuna wuce magrib sai sunyi fada musamman ma Baba Hasheem,fita sukayi suna yiwa Abban inteey sallama. Parking space suka isa nan suka shisshiga cikin motocin,shima Shuraim sallama yama Aunty Safeena sannan yashiga yatayar da motan,nan gate man yabude masa gate din yafita. Aunty Safeena kuwa sosai take farin ciki don idan harsashen ta ya tabbata to tabbas sai tafi kowa murna( _Ji wannan safeenan zaki hadu da bodejo ai_ ) Suna cikin motar babu wanda yace da wani qala sai dai time to time Shuraim na duban mirror kuma cikin rashin sa'a su hada idanu,itako zuhra ta galla masa harara tare da murguda baki. Sai dai kawai yayi murmushi don shi masifar burgesa tsiwan nata keyi,a haka dai suka kariso anguwan su,kwatance Aunty Mashahuda tashiga yimishi,nankuwa yakawosu kofar gidan yadanna horn,da sauri Aunty Mashahuda tace. "Kada kadamu Baba mudi ma bayanan suna cikin masallaci ka ajemu anan ma ya isa,bude murfin motar sukayi suka fito, shima fitowan yayi yadan tsaya a setin zuhra duk da suna da tazara face nasa dauke da smile yadubi Aunty Mashahuda cikin zolaya yace"shikenan Auntymmu gashi dai a bonus naga gida da alama kuma tafiyar tawa akwai nasara,yakarisa maganar yana duban zuhra. Tunda yashigo layin idanunsa ya sauka akan kofan gate dinsu don gidan Galadima yana daya daga cikin manyan gidajen da akeji dasu