← Book details Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 64

Sashe 48

Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yawo da hankali ne yasa aka fara wahalar da ita,don har farcen ta sai da aka cire mata,wuyan da taji ne yasa ta amsa lefin don cewa itace ta kashesu,ta barbada musu guba a abinci,dama abinda jami'an suke so kenan hakan yasa suka tattare duk wani takardun ta suka mika court inda gobe itama za'a wuce da ita,sai dai mummunan abinda yafaru da Adda Zainab shine a daren tayi mafarkin wasu irin halittu sunzo suna amfani da ita ta bayan ta,sai sai farkawar da zatayi ta farka da hauka tuburan,don tsirara tayi ma kanta haihuwar uwarta,wasu tsutsotsi suna fito mata ta bayan ta,hauka sosai Adda Zainab keyi tana sanar da abubuwan da suka dinga aikatawa da nemanta ta baya da matan nan da sukayi,nanfa hankalin jami'an yayi kololuwan tashi,a a dai-dai lokacin Kuma Ammar da Taufeeq sunzo state CID din a dalilin hujjan da suka samo na ba Adda Zainab bace tayi kisan hajiya kareema ce kanwar Alhaji iliyasu,sai suka cidda wannan tashin hankalin,tsaban kuka da Ammar keyi kamar yayi hauka yasa hankula yatashi a office din, komai ya tabbata a computer ba Adda Zainab bace tayi kisan,ga inda Hajiya kareema tashiga har palour yayanta Alhaji iliyasu tasa maganin 6era a lemon da hajiya Aliya ta hada musu,har inda suka fadi tasake dawowa tana cewa"Nasan dole wannan kisan ace Zainab ce tayi itama a kashe ta idan yaso naji da suma wadancan tsinannun yaran ko kwangilar kisan su na bada",lokaci guda aka dauki Adda Zainab sai hospital don duk a tunanin ma'aikatan rudewa ne yasata hakan don su basu farga da tsutsotsin dake fito mata ba,kaitsaye akaje aka dauko hajiya kareema da safe aka maka ta a kotu tare da gamsassun hujjoji,don da farko taso ta musa sai da aka Sanya videon kowa yagani itama tagani sannan ta yarda tafara kuka da cewa sharrin shedan ne,yaranta ma kuka sukeyi,mijin ta kuwa atake anan yasake ta tare da mata Allah wadai,don anyanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya tare da horo me tsanani. *_BAYAN KWANA UKU_* Ummie itace ke tare da Adda Zainab a asibiti tare da islaha,sai matan yayan Alhaji iliyasu,kuka sosai Ummie keyi tana sumbatu"Allah na yafewa Adda Zainab ya ubangiji ka bata lafiya ka yafe mata wallahi nidai kam na yafe mata,gabadaya sai ta koma ita ake ma lallashi domin zuciyar Ummie tayi ma kowa naganin ta mace me yafiya,kamar wasa Ummie haka abinta keta gaba don harta kaiga hannu take sawa a bayanta tana jawo tsutsotsi,su Amma da yayyen ta maza suma kuka kawai sukeyi,abu kamar wasa duburan ta yafara zazzagowa yana jini ga nama duk a waje,dararrakun ta kawai kakeji tana ambatan boka hatsabibi sunan shi ya zauna a bakin ta zam. Duk wanda yaga Adda Zainab sai ya tausaya mata, Ummie har hawan jininta sai da yatashi, Taufeeq yakira su Daddy ya sanar dasu halin da ake ciki don yau suka dawo da Galadima domin jikinsa Masha Allah,maganar ne dai ana ganewa ma amma bedawo dai-dai ba dama sai a hankali. Washegari su Daddy suka iso,ya zamana Bodejo kawai da Galadima aka bari don Zuhra ma ta biyosu,duk da bata tambaye sa, Ammi ce tace tashirya,daga Ammi, Mom har Zuhra kuka sukeyi, Mommy da Mashahuda kuwa har su Saba gani don tare suke da Ummie koda yaushe. Kamar wasa Adda Zainab tadinga wani irin rama,naman ta na zagwanye wa don bata cin abinci,kashi kuwa idan yana fita babu control,kowa yaki jinyar ta sai Ummie. A wannan halin ne kuma Allah yadauki rayuwar ta bata ambatar komai sai sunan boka hatsabibi har tabar gidan duniya babu kalmar shahada babu komai ( _Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un hasbunallahu wa ni'imal wakeel,shikenan fa duk abinnan antafi cikin babban lefi wanda mutum be Isa ya yanke hukuncin tsakanin bawa da mahaliccin sa ba,masu hali irin na Adda Zainab Allah ya shiryesu,ku duba duk abinda ya haddasa hakan "hassada" shine ya jefata cikin wannan bala'in, wallahi wallahi wallahi mukiyaye kanmu da hassada domin babu abinda be sawa, Allah ka mana tsari da ita Allah katsaremu da mugun ji mugun gani Ameen!_ ) Bayan sati daya,Yasmeen ta koma hannun Ummie inda islaha take gidan ta mijinta yarike ta hannu bibbiyu dashi da iyayen sa, Zuhra kuwa satin ta daya da kwana biyu yau a kaduna,gobe ne komawar ta maidugri hakan yasa ita dasu Laila suka shirya suka nufi saloon, sannan suka wuce gidan lalle,a hanyar su ta dawowa ne wani mutumi yadinga nacin suzo su shiga ya rage musu hanya,ga rashin abin hawa gashi tafiya ce me nisa tsakanin su da gida, babu abin hawa gabadaya,tunda layin da suke tadan shiga hakan yasa dole suka hau,sannan shi ba kowa yakeso ba da alama niyyar rage musu hanya kawai yayi,har JABI ROAD kofan gate dinsu ya kaisu, gaban Zuhra ne yayi wani irin mahaukacin yankewa ya fadi,a dalilin wanda tahango,ya Sauban ne ta hango jikin mota shida ya Taufeeq gabadaya shi hankalin sa nakan motar da tayi parking,cikin sauri Zuhra ta 6alle murfin motar ta fito,idanuwan su ya shige cikin na juna,wani irin kallo ya aika mata dashi mesa hanjin mutum kadawa,domin kuwa daka kallesa kasan ransa a 6ace yake duba da yanda lokaci guda face dinsa ya sauya da wani irin mahaukacin kishi,godiya su Laila suka ma me motar sannan suka nufota, Laila na cewa"tundazu ya isa ace kinshige har mun kariso...shiru tayi a dalilin wanda tagani,itama jikinta ne yayi sanyi da irin kallon da taga yayan nama Zuhra, Nihal kuwa gigita tayi da tsoro hakan yasa da wani irin azababben gudu tashige gate din. Laila ce ta kamo hannun Zuhra,sumumi-sumumi suka wuce suka shiga gidan,nannauyan ajiyar zuciya Laila ta sauke,itako Zuhra hakanan tanemi natsuwar ta tarasa,ko ada da sukafi 'yar tsama be ta6a mata irin wannan kallon na yau ba. Shiyasa suna shiga kaitsaye bedroom din Ummie ta shige tana sauke numfashi. Shikuwa suna shigowa yabiyo bayan su, tana cikin cire gyalen ta Laila tashigo tace tazo ya Sauban na neman ta,sannan daka kalle face din Laila kasan ba lafiya ba. Cikin sanyi suka fito sun cidda kowa cirko-cirko har mommy, Mashahuda, Taufeeq, Ummie,wani mugun kallo Sauban ke aika mata dashi,tsayawa tayi cak taki karasowa kanta a kasa, muryansa tajiyo kamar zai tsaga palour,idan kika bari nazo nan saina tattaka kanki,kirjinta ne ya cigaba da bugawa a hankali ta shiga takowa"Na hanaki shiga motan tsinannun mutanen nan bakiji ko?yayi maganar idanuwan shi na diddilowa cike da kishi"wallahi duk ranar da nasake ganin kin shiga motan wani da sunan lift sai naci uban shi,wallahi sai na dauresa ko dan gidan uban waye,ke kuma sai na baki mamaki tunda kunnen kashi ne dake,ku kuma"yayi maganar yana nuna su Laila"Duk sanda zaku fita wata tasake dauko min mata sai naci uban yarinya a gidannan"yasake maganar yana huci,duk tsit palour yayi don Sauban idan yana fada kamar mahaukacin Zaki yake komawa, Ummie da Mommy kuwa sunji matukar dadi don kishinta ne bayyane a idanunsa. Itakuwa Zuhra juyawa tayi tana turo baki sai da takai dai-dai stairs tajuyo sannan tace"Kai da baka so na sai kabar masu so na su soni,ai da wani irin firgita yake duban ta,sauran 'yan palour kuwa da wani tsananin mamaki suke dubanta,ganin hakan yasa da gudu ta haye stairs,aiko Sauban ya rufa mata baya,tana kokarin danno kofan bedroom dinne ya kuwa danno kofan yaturo,kamar mayun wacin zaki yayo kanta,fisgota yayi ya kifa mata mari,aiko Zuhra ta bude baki da niyyar ihu,ai babu zato taji mouth dinsa cikin nata,wani mugun cafka yama lips dinta wanda yasata kwakufosa saboda zafin da taji,aiko nan yashiga punishing dinta da mouth, sosoai Zuhra ke hawaye babu bakin ihu ita kadai tasan azabar da takeji juya kai kawai yakeji,don jitayi kamar ana yayanka mata lip to pieces,hawaye takeyi sosai. Acan downstairs kuwa Mashahuda ta dubi Mommy tace"Mommy please kije kinsan halin Yaya da zuciya kada yazo yana ta dukan ta ne kuma ya hanata ihu"Mommy tace"Sauban bazai ta6a dukan Zuhra ba sai dai punishing dinta"Ummie tace"ai baby sai ana maganin ta rashin kunyar ta yawa ne dashi, Allah ya kyau ta,tana gama fadar hakan tanufi kitchen, Taufeeq yaja hannun Mashahuda yana mata rada a kunne,aiko nan suka shiga dariya kasa ,su Laila suka bi Mommy apartment din ta,tsawon 4minutes Sauban ya dauka yana azabtar da ita,sai da ya tabbatar ta shiga taitayen ta sannan ya saketa,aiko ta daddage tasaki wani irin kuka Saboda yanda taji lip din kamar ba a bakinta ba,tsananin azaba,duk beyi jini ba sai dai yayi mugun komawa pink,kuka sosai Zuhra keyi,shiko Sauban ficewan shi yayi yabar ta nan yanajin kukan nata har ransa,sai dai yanda yakeji yasa ko tunanin tausaya mata bayaji. After sallan isha'i su Laila duk suna sashen Ummie harda Mashahuda da Taufeeq suna dinner, mommy nacan wajen Abba don yadawo, Ummie ta dubi Yasmeen wacce takoma silent sam batada hayaniya yanzu tace mata"Yasmeen jeki kicema Zuhra tasakko injini kafin nahayo stairs din, Yasmeen tace"tom Ummie"sannan tamike,babu jimawa tasakko tace ma Ummie gatanan zuwa,tuwon semo akayi miyar ugushi da yaji busasshen kifi,sai farfesun kayan ciki,wani zazza6i ne yayi mugun lullu6eta,da kyar take iya tafiya,tana sanye da night gown me dan kauri,kanta sanye da hula,kujerar da zata zauna tana gefen ta Sauban ne,yimusu Ammi da Taufeeq sannu da gida tayi sannan taja kujera ta zauna, serving dinta Laila tayi kokarin yi,cikin sanyin muryan ta wanda yadan dashe saboda kuka tace" bazanci ba banjin yunwa"Ummie tace"ba tun breakfast bane a cikin ki?Koda kuka fita taci wani abu ne"Ummie tayi maganar tana duban Laila, Laila tace"Babu abinda mukaci"Ummie tace"yi serving nata,cikin muryan jin jiki Zuhra tace"Ummie idan naci zanyi amai inajin fever p sosai"dagowa yayi ya kalleta,sosai yaga tayi wani irin yaushi,a hankali yakai hannu ya ta6a gefen neck dinta,cikin sauri ya janye hannun yana cewa"what's wrong with you? Zuhra tace"inajin fever me tsanani a jikina"Ummie tace"shine bazaki sauko kiyi magana ba?kenan da bance a kiraki ba sai nashigo kwanciya zan ganki a yanayin? Allah ya shiryeki"dariya Taufeeq yayi cike da tsokana yace"taji aikin manya,yau anyi punishing dinta"yakarisa maganar cikin dariya,hararar Sauban ya watsa masa,itako Zuhra shiru tayi kamar ruwa ya cita,ajiye spoon din hannunsa yayi yace"kije kisawo hijjab kizo muje hospital"yayi maganar ko a jikinsa, Zuhra kuwa wani irin nauyi taji ganin kowa a wajen shikam beda kunya,duban Ummie tayi wacce kamar ma batasan abinda ke faruwa ba,abincin ta takeci hankali kwance. "Magana
Chapter 48 · 0% Book details