Sashe 6
Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kanshi zaije yawa kanwar sa wannan albishir din. Tabe baki bodejo tayi tare da mikewa ta gyara zaninta tawuce ko sallama batayi musu ba. Abba ne yasauke ajiyar zuciya yace"Yaya taya zamu sanar da Sauban wannan batun?kaga yaron nan yanuna bayason wannan abin tunfarko. Daddy yace"yakuwa zaiyi auren biyayya shine abinda zaiyi ko kuwa Sadeeq? Abbie Wanda koda yaushe fuskansa baya rabo da murmushi yace"Allah yasa hakan shine abinda yafi alkhairi. Sunji dadin addu'ansa. Nan suka kammala tattaunawan su sannan suka miqe. Zuhra ce kwance akan kujeran Ammi ta lumshe idanuwanta saboda tsananin ciwon da kanta ke mata,sosai jikinta yadauki zafi alamar zazzabi nason saukar mata. Yaran gidan gabadaya suna wajen Ummie don Ummie macece meson yara sai dai tsakaninta da zuhra sai a hankali. Ammi ce tafito daga kitchen hannunta rike da wani plate tayo inda zuhra ke kwance,zama tayi a gefenta sannan tadauki kanta tadora akan cinyar zuhra. "Subhanallah zuhra ai ba ciwon kai kadaine ke damunki ba ga zazzabi nan a jikinki, tashi kisha wannan fruit salad din. Batare da tayi musu ba tamike,wani irin Sara mata kan yayi da qarfi,hannu takai tare da kama kan,jijiyoyin kan sun firfito. Sake rikicewa Ammi tayi domin sosai Allah yadora mata son zuhra tun sanda Ummie ta haifeta tare da wani burinta akan zuhran. Sanyayyan muryanta tabude a hankali,muryan inbanda rawa babu abinda yakeyi tace"Ammi ki Kama mun kaina inajin kamar zai fashe. Kama mata kan Ammi tayi tafara yimata addu'o'i a hankali wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita. Ajiyan zuciya Ammi ta sauke tare dajin wani tausayin zuhran a ranta. Samun gefen ta tayi ta zauna tana duban kofar parlo tare da amsa sallamar da akayi. Kareem ne yashigo fuskar sa dauke da murmushi dama shi mutum ne wanda baya rabo da murmushi. "Barka da gida Ammi,yafada tare da rissiniwa. Cike da fari'ah Ammi tace"A'ah Kareem har kadawo daga airport din? Kareem yace"Ea Ammi nadawo don sai da natsaya ma har jirginsu yatashi sannan nataho. "Allah sarki Allah YAKARA muku dankon zumuncin nan naku da kaunar juna Kareem anfa gode,angode sosai. Dariya Kareem yayi yace"Haba Ammi tsakani na da Sadauki ai babu haka, bari naje gida hajiya tanata kirana. Ammi tace"tohm Allah yayi albarka ka gaisheta,kace inanan zuwa,anfa gode. Fita yayi tare da satan kallon inda zuhra ke kwance,duk da yaso yaga fuskanta Amma Allah baibashi sa'a ba. Da daddare yaran gidan duk suna sashin bodejo harda zuhra. Bodejo tadubi zuhra tare da kyabe baki tace"waike yarinyar nan lafiyanki?tundazu kiketa yatsina ko bakijij dadi ne? Shiru zuhra tayi tare da sake lumshe idanuwanta. "Yarinyar nan haryanzu wannan shegen miskilancin naki yananan,nidai keda saudan bansan wanda yafi wani wajen miskilanci ba. Gabadaya yaran parlon suka sanya dariya,maimoon tace. "Bodejo bafa saudan ba, Yaya Sauban. Bodejo tace"Toh uwar feleke,ni ina ruwa na,haka na iya haka kuma zan fada. Murmushi Galadima yayi yace"zuhra zo nan kinji. Mikewa zuhra tayi a hankali kamar wacce kwai ya fashe ma a ciki ta nufi inda Galadima yake ta zauna a gefensa tace"granny mezaka bani na dadi. Duban Laila Galadima yayi. "Zonan Laila,jeki kitchen din bodejo saman fridge dinta zakiga bakar leda ki daukomin. Zuhra batasan sanda wani murmushi ya subuce mata ba jin amfani hakar leda. Daga murya Galadima yayi yace"ki kuma zo da plate guda biyu.Da toh Laila ta amsa. Tuni yaran parlon suka fara murna. Laila batajima ba tafito hannunta da wani dan leda baqa medan girma,tare da plates uku babba guda da madaidaita biyu,akan babban plates din tadora ledan. Galadima yace"hajiya bodejo azo akasa abawa kowa nashi. Bodejo takama baki tace"wa? Ai idan zuhra na waje bodejo bata tasiri ga tagaban goshi? Murmushi Galadima yayi yace"Toh ko nihal ta raba ne?nihal zoki raba mana. Tasowa nihal tayi aiko ta raba kashi uku kamar yanda Galadima yace tayi,shida bodejo kashi daya itada da Laila da zuhra Kashi daya sai su maimoon ma kashi daya. "Allah yasaka da alkhairi granny ubangiji yaqara budi, Allah yaqara daukaka GALADIMA FAMILY,zuhra tayi addu'an cikin muryanta mai sanyi. Da Ameen su Laila suka amsa. Sosai Galadima da bodejo sukaji dadin addu'an na zuhra,wanda a kullum suna yabawa da hankalinta. _SU WAYE GALADIMA FAMILY?_ Cikakken sunansa Muhammad Taleeb Muhammad haifaffen garin MAIDUGRI sai dai mahaifiyar sa ce 'yar nan wacce take shuwaarab,shi kuwa mahaifinsa buzaye ne irin masu tashin nan,adalilin haka Allah yakawo mahaifinsa da mahaifiyar sa garin MAIDUGRI inda wata rana suna kwance da daddare wata takama Wanda ba'asan daga inda wutar yafito ba. Mutane suka fara kawo dauki,a lokacin Muhammad nada shekara a duniya,atake anan Allah yayiwa mahaifinsa rasuwa garin ganin ya cece matansa da dansa maisuna Muhammad,don sosai yayi wani irin mummunan kuna,mahaifiyar Muhammad kuwa itama kokari take takare Muhammad tare da abinda ke cikinta. Asibiti aka kai mahaifiyar Muhammad,inda likitoci suka dukufa akanta,koda suka duba sai sukaga cikinta yana watan haihuwa ne babu bata lokaci suka yanke hukuncin ciro abinda ke cikinta,suna shirye n yimata aikin ne Allah yadau rayuwanta,ganin haka yasa suka hanzarta yimata aikin. Aiko suka Ciro yarinya kyakkyawa mace, Muhammad kuwa sai kuka yakeyi,nan suka tattara akayi abubuwan da za'ayi aka amsa gawar Muhammad. A lokacin hakimin garin shine kakan bodejo don haka shine yayi komai,suka koma suka sallaci gawa biyu,babu bata lokaci hakimi da sauran dattawan anguwa suka yanke hukuncin baiwa hakimi su Muhammad,inda shi kuma hakimi yadamqasu a hannun danshi tilo namiji Harun mahaifin bodejo. A lokacin bodejo nada shekara bakwai mahaifiyar ta daga kanta bata sake haihuwa ba Allah yamata rasuwa,a lokacin matan baban bodejo na aure da kanin bodejo yakub sai aka bata jaririyar ta hadasu tana shayar dasu. Kamar yanda al'ada yazo ranar suna aka radama yarinya suna Lauratu inda mutane ke kiranta da Laure,sosai mahaifin bodejo da kakanta suka bawa su Muhammad gata,hakimi yasa aka tattaro masa raquman su Muhammad guda goma Sha biyar yabawa wani abokinsa dake cikin gari ajiyansu ana cigaba da kula dasu. A haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya har akasa Muhammad a makaranta inda shakuwa mai karfi tashiga tsakaninshi da bodejo,a gefe guda kuma hakimi na cigaba da kula mishi da dukiyanshi shida mahaifin bodejo. Xahratty CE Lallai Alqalami yafi takobi 16/2/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): *_GALADIMA FAMILY_* Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 07 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ _____A lokacin da Muhammad yagama secondry school lokacin Allah yadauki rayuwan hakimi,inda anan harun mahaifin bodejo yatura Muhammad cikin garin MAIDUGRI gidan aminin mahaifinsa inda gadon su Muhammad yake anan yaciga ba da karatunsa na gaba da sakandiri,a gefe guda kuma shakuwa sosai tasake dinkewa tsakanin bodejo da Muhammad lokacin tagama aji uku na sakandiri sai aka cireta, Laure ma tana samun kula sai dai takasance tun tana karama take da wasu dabi'u sam marasa kyau. A kwana a tashi babu wuya Muhammad yasamu kwalin diploma dinshi,a lokacin ne Kuma harun ya aura masa bodejo inda suka tare anan gefen gidansu bodejo din, Muhammad yataso mutum ne mai tsananin hazaqa da kokari uwa uba kuma kyau,auren su da wata uku yakoma makaranta. Lokacin da yagama Digree dinshi na farko a lokacin harun yadamqa mishi gadon su wanda tuni ansai da raqumayen,anjuya musu kudadensu inda ya habaka sosai,lokacin bodejo ta haifi danta mai santalele namiji kyakkyawa aka sanya masa Taleeb sunan mahaifin Muhammad,sai dai kiri Muhammad ya hana a boye sunan,bayan bodejo tagama wanka Muhammad yadauke ta ya maidata cikin gari inda yayi musu gini, Laure Kuma tana zaune wajen harun da matarsa. Bayan shekaru 28 aiki ya maida Muhammad garin kaduna inda yake zaune a zaria akuma lokacin yaran Muhammad su shidda ne maza hudu mata biyu,Taleeb ne babba sai Sadeeq,Haroun,Labeeba, Maryam sai auta Hasheem. A lokacin anyi auren Taleeb da Sadeeq don rana daya akayi bikinsu. Taleeb ya aure matansa 'yar maidugri ne don shuwa ce itadin gaba da bayanta,inda Sadeeq ya aure 'yar zaria wajen fada,duk cikansu Allah ya hadasu da mata nagari. Matar Taleeb sunanta Aisha,matan Sadeeq kuma bilkisou. Shekarar da suka cika shekara guda da aure Allah yabaiwa Taleeb karuwar da namiji inda yaci sunan Muhammad Taleeb Muhammad,waton sunan kakansa inda ake cemasa Sauban,bayan cikin Sauban suka sake haihuwar mace inda aka sanya mata sunan mahaifiyar Aisha Safeena suna cemata falmata wacce take sa'a da Dan wajen Sadeeq wato Ahmad ake masa laqabi da Taufeeq. Wasa Wasa sai da Aisha tayi haihuwa hudu, Sauban,falmata, Mashahuda, Laila. Amma bilkisou tundaga kan Taufeeq bata sake haihuwa ba. A lokacin shima abba yayi aure sai dai matansa shima bata haihu da wuri ba 'yar kaduna mai suna hauwa'u. Hasheem yayi aure inda yake aure da 'yar wan mijin Guggo Laure, me suna Rabi.Yaransa uku,babban Bashir ana cemasa Aseef sai muneefa inda takeda ciki a lokacin itama bilkisou tasamu cikin nabiyu. Anyi bikin Labeeba da Maryam, Labeeba tana zaune a Canada tare da mijinta yaransu biyu muhsin da musaddiq.Inda Maryam ke Lagos sai dai ita bata haihu ba. Rabi ta haifi yaronta namiji Mai suna yassir tsakaninshi da Laila wata daya,inda itama hauwa'u ta haifi diyar ta mace akasanya mata Nihal. Alokacin da cikin jikin bilkisou itama ya bayyana sosai ahalin Muhammad suka shiga farin ciki kowa yaqosa ace tahaihu,sosai akayi zumudin cikin,lokacin haihuwa tayi ta haifi yarinyar ta kyakkyawa Masha Allah anan ne fa akashiga turka turka inda bilkisou tace sunan mahaifiyar ta za'a saka mata,shikuma Sadeeq yace sunan mahaifiyar sa zai saka Fatima. A lokacin rashin kawaicin bilkisou yafito muraratan inda tace to muddin yasa sunan bodejo to bazatayi farin cki ba,sosai ran Sadeeq yabaci dana ahalinsa sai dai su suka danne,bodejo kuwa duk bakinta haka tazuba ma bilkisou Ido, Guggo Laure kuwa tasamu bilkisou tayi mata tijara tundaga lokacin ta tsani bilkisou. Aiko aka sanya sunan bodejo wato fateematuz zahra'u suke cemata zuhra. Da farko bilkisou tace bazata shayar da jaririyar ba,sai da mahaifinta da mahaifiyar ta sukazo har gida sukayi mata tatas inda mahaifinta yace muddin Bata shayar da zuhra ba sai yayi mata baki,sannan yatasa ta taje tabaiwa bodejo hakuri da M uhammad da mijinta Sadeeq. MUHAMMAD kafin kace mene yayi fice saboda kudinsa da kuma ilimi irin na 'yayansa ga uwa uba kyau,don alokacin Taleeb Yana aiki a NNPC inda yaran gidan ke kiransa da Daddy,Sadeeq kuma yana aiki a wani company a Lagos inda yaran