Sashe 15
Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inna ilaihirraji'un!!! Kalmar da Bodejo take ta fada kenan,hankalin ta yayi kololuwan tashi ga tsufa ga rudu,sai da Ammi da Mom suka kamata suka zaunar da ita. GALADIMA wayansa yaciro yafara neman layin Daddy,sai dai ba'a daukan kiran,maida kiran yayi ga Baba Hashim ba'a dau lokaci ba tadauka,cikin kamewa Galadima yayi sallama. Daga can Baba Hashim yadauka saboda a rude yake don muryansa har neman disashewa tayi saboda kuka. "Hashim lafiya meke faruwa ne? "Galadima ga munan dawowa yanzu,yakarisa maganar muryanshi na rawa. "Mekefaruwa ne anan ina tamabayar ka meya same abubakar?fashewa da kuka Baba Hashim yayi yace"Allah yadauki rayuwansa wanda yafimu sonsa ya amshe abinsa Galadima.Runtse ido Galadima yayi batare da yasake magana ba yakashe wayan. Cikin daburcewa Bodejo tace"malam meyasame abubakar din? "Gasunan a hanyar dawowa gida,amsar da yabata kenan a takaice. Dai-dai nan Zuhra tashigo parlon sai dai babu wanda ya lura da ita. "Don Allah malam kamin bayanin meya same dana abubakar? Bodejo tafada tana me fashewa da kuka. Sukansu su Ammi hankalinsu a tashe yake. "Kuyi masa addu'ah Allah yakarbi rayuwarsa, Allah yamasa cikawa......wani irin kara da aka kwala ta bayansu yasasu gabadaya juyawa. Zuhra ce a take anan tafadi sumammiya. Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un!!!!shine kalmar da gabadaya 'yan parlon ke ambata cikin tsananin rudewa, Ammi dasu mashahuda suka nufo wajen zuhra. Mom da Galadima suka nufi Bodejo saboda wani jiri da yadauke ta tanemi faduwa. 9:11 Kafin kace me gida yacika tam da jama'a bakajin komai sai tashin koke-koke na mata don ankawo Abbie gida,daga Daddy har Baba Hashim a gigice suke,me dauriyan ma Galadima ne. Makota duk sun cika gidan,ana haka sai ga Abba dasu mommy tare dasu Laila duk sun iso saboda shima sanda sukayi accident din ankirashi kaitsaye asibitin yanufa yacidda ai dan uwanshi yarasu sun nufo gida. Duk Wanda yaga ahalin nan a daren nan sai yayi musu kuka saboda tausayi, Zuhra kuwa tana apartment din Ammi ankira family doctor dinsu yaduba ta tare da samata drip da alluran bacci,saboda wasu sunbatu da mimmikewa da tafara. Gawar Abbie kuwa a daren suka shiryashi tsaf sai gobe karfe tara na safe za'a kaisa(kwanan keso,ake cewa Koh? Bodejo fifita su Mom ke mata saboda ta rude. Su Daddy kwana sukayi suna ma Abbie karatun kur'ani, taufeeq shikan shi a gigice yake yafita daga hayyacinsa. Washegari zuwa karfe takwas Galadima family yacika tam da jama'a dangi da masoya da makota,don abokan Abbie nanan Mai din da kaduna da yawa suna wajen, Maryam na Lagos ma ta iso abinka da jirgi itada mijinta da yaranta,labeeba dai suna hanya 'yan Canada. Mahaifiyar Ummie da kannenta maza Suma sun iso da hajiya Zainab. Duk Wanda yaga Zuhra sai ya tausaya mata saboda yanda takoma a kwana daya kawai ta gigice fuskarnan tayi jaa idanuwanta sunyi luhu luhu,mommy ce da Aunty Maryam rike da hannunta suka nufi babban parlon Galadima inda gawan Abbie take,mutane ne cike a parlon ana masa addu'ah,sallama sukayi suka shiga da ita,kowa hankalinsa yadawo gareta,dukar da ita Aunty Maryam tayi gaban gawar,dai-dai kunnenta ta mata magana"Banda kuka kinji? addu'ah zaki masa. Hawaye ne masu zafi suke rige-rigen zubo mata,hannunta na rawa tadan bude fuskan Abbie. Fuskan nan banda sheqi babu abinda yakeyi don zaka zata murmushi ma yakeyi kamar kace masa ya tashi. "Allah yajikan ka Abbie, Allah yagafarta maka ubangiji yamaka rahama, Allah yasadaka da mala'ikun rahama Abbie,kaine uwana kaine ubana wanda yafini sonka yadauke ka a lokacin da nake tsananin bukatan ka, Allah ne gata na kaine gatanaa.....takarisa maganar tana fashewa da wani irin kuka. "Abbie halinka nagari yab.....numfashinta ne yafara seezing da sauri Mommy ta kamata suka fita,kowa cike da tausayin ta yabita da kallo,anan aka fito da gawar. Nan fa gida yasake haumutsewa da koke-koke na mata, Laila ma atake anan ta fadi ta Suma garau. Guggo Laure da shigowan ta kenan da jiniyar kuka tafara"wayyo Allah mutuwa me yasa zaki Mana haka?me zesa kidaukar mana yaron kirki?ga sauran can,sai kika tafi mana da mai hakuri. Takarisa maganar tana Jan majina. Allahu akhbar kullu nafsin za'ikatul maut,duk Mai rai sai ya dandani dacin mutuwa Allah yajikan Abbie Sai wajen la'asar ya taufeeq da Kareem da wani kanin Ummie suka daukota daga hospital sosai ta galabaita itama sannan mutuwan Abbie ba karamin girgiza ta yayi ba,takasa mance maganganunsa wadanda sosai su sukafi tasiri a zuciyar ta( _Bilkisou inaso kisani bana fatan na mutu banga kin daidaita da Zuhra ba._ ) sosai wannan maganar yake dawo mata a kai saboda sosai tafara tsorata da lamarin nata ita kanta hakan yasa hawayen idaniyar ta suka gaza tsayawa. Ammi ne da Mommy da Mom suka kariso tare da kama Ummie kaitsaye apartment din Abbie nanan suka nufa don su Amma da hajiya Zainab suna can zaune. Zazzabi ne me zafi ya saukar ma Zuhra saboda kukan da tasha gashi har muryanta ya dishe,mijin Aunty Safeena da mahaifiyar shi sai yayyen shi mata su biyu sunzo don Shuraim ma yajawo su a motar,su kansu sun tausaya ma ahalin musamman ma Zuhra don da alama Abbie irin mutanen nan ne masu tsayawa a rai. Koda Zuhra tafito don su gaisa da Shuraim kasawa tayi saboda kukan da yaci karfinta,ga abinci da sam ba cinsa take ba. Tabbas Galadima jarumin tsoho ne don kaf 'yayan sa yafisu dauriya kukan zuci kawai yakeyi wanda kowa yasan yafi na fili azaftarwa da radadi. A ranar Aunty Labeeba itama ta diro da mijinta sosai fa gida ya cika. *MALAYSIA* Sosai yashiga rudu da tashin hankali da rasuwar Abbie din,don har Saida zazzabi me zafi yanemi kwantar dashi,duk da a bayyane ba lallai ka fahimci hakan ba. Sosai Abba ya kwantar masa da hankali duk da yaso yazo kasar a ranar amma baisamu izinin haka a wajen na sama dashi ba dole ya hakura,sanar dashi halin da Ummie tashiga shima sai yasake gigitashi. A haka yadinga dai zuwa office din zazzabi nata cinsa a tsattsaye,duk da kullum cikin video call yake da Taufeeq ko Ammi akan jin halin da Ummie ke ciki. ****** Bayan kwana uku da rasuwar Abbie,anan ne wasu daga cikin dangi da 'yan uwa suka wawwatse sai dai na jikinsa suna nan. Anan Daddy yakira meeting parlon Galadima,sosai kowa ya halarta a cikin ahalin gidan,Banda Guggo Laure dai,'yayan Galadima kawai ake bukata. Nan Galadima ya bude taro da addu'ah yayi addu'o'i wa Abbie, Daddy kuma ya amshe. Nasiha maishiga jiki yafara yiwa Ummie,tare da sanar da ita abinda dan uwansa yamutu da burin ganin yacika shine shiryawan ta da diyar ta Daddy ya cigaba"Sadeeq yace muddin kika ja marainiyar Allah a jiki kingama masa komai,ga Hashim nan abinda yadinga maimaita wa kenan kafin Allah yadau rayuwansa yakuma CE shi yayafewa kowa don bashi da kullin kowa a ransa. "Bilkisou kiji tsoron Allah ki kula da diyarki ki cikama abubakar burinsa mudai a iya saninmu baki da matsala kuma Alhamdulillah a kullum abubakar cikin yabon kyawawan halayyarki yakeyi illa matsala guda shine wannan matsalar,Wai ko kin manta Zuhra nada ciwon zuciya ne?kinsan dalilin da yasa a koda yaushe abubakar ke debe mata kewa kenan?don Allah menene matsalar bilkisou? Cikin muryan kuka Ummie tace"inason ta amma narasa meyasa nakejin tsanar ta? wallahi ina kewanta da begenta sai dai sam banaso ta rabe inda nake. Gyararan murya Abba yayi yafara magana"Ina ganin Yaya kamar maganar Yaya Sadeeq gaskiya ne da koda yaushe yake cewa shi yana zargin sihiri a lamarin,nima kuma gaskiya na sake a minta,da sauri Aunty Maryam tace"wallahi kuwa Yaya nima haka nake gani. "Hmmm nidai nace saboda taya uwa zata ki danda ta duka ta haifesa?sannan ko son da aka haifi Zuhra Bilkisou na tsananin son ta daga baya ne komai ya canza,Ammi tayi maganar. Shidai Taufeeq kansa na duke don shikadai ne a yaran gida yake parlon. Baba Hashim yace"toh me zehana anemi malamai masana addinin islama aji ta bakinsu? "Wannan gaskiya ne Yaya, cewar Labeeba. GALADIMA ne yayi gyaran murya,gabadaya wajen yayi tsit magana yafara kamar haka. Xahratty CE Lallai Alqalami yafi takobi 14/03/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): *_GALADIMA FAMILY_* Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 21-22 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ ___Sosai GALADIMA yayi nasihohi masu shiga jikin duk wani wanda yake zaune a wajen,inda a ka tsaida magana za'a ma wani aminin GALADIMA magana dake wani kauye anan maidugrin don masanin harkan sihiri ne kuma yana bada magani sosai,nan aka sake yiwa juna gaisuwa kafin kowa ya watse. Bayan kwana daya,ana masu amsan gaisuwa suka cigaba da tururuwar zuwa,hajiya Biba ma tazo ganin yanda Galadima family yasake tsaruwa ne yasa tasake kudira a ranta cewa lallai yakamata Rammat ta shigo gidannan,sawa tayi aka kaita sashin ammi,anan fa tadinga fadanci a wajen Ammi tare da yabon halayyan Sauban. Ammi tacika da mamakin hajiya Biba amma sai sam bata nuna ba,itakuwa Mom ta cika tayi Damm saboda yanda taga hajiya Biba na neman kwanta ma Ammi tayi wuff tace. "Hajiya kizo muje kiyima iyalen Abbie gaisuwa mana. Mikewa hajiya Biba tayi Rammat tana bayanta itama cike da kissa ta rissinawa Ammi tana mata sallama. Kaitsaye apartment din Abbie nanan suka isa sosai hajiya Biba tanuna jimaminta,itakuwa zuhra tana rakube gefen Ummie jikin kafar Adda zainab. A haka rayuwa ta cigaba da tafiya har yau gashi bakwan rasuwar Abbie a ranar ne kuma Sauban yadiro garin babu zato bare tsammani,idan kallesa baka isa ka tantance a yanayin da yake ba sai dai fuskar sa da take a dinke,ta gabanshi tazo ta wuce cikin sanyinta long hijjab ne a jikinta brown colour yayi mata kyau sosai,fuskar ta daka kalla kasan mutuwar tana dukanta. Ta wutsiyar Ido yabita da kallo har tashiga wajen Ammi,kaitsaye shikuwa apartment din Ummie yashiga bakinsa dauke da siririyar sallama,da Ummie suka fara hada ido,ai tuni tasaki kuka mai tsuma zuciya,da sassarfa yakariso gareta da sauri ya kama mata hannu. "A'ah Ummie don Allah kada kiyi kuka Abbie insha Allah ya dace,ko nima so kike kisanya ni kukan Ummie?please. Girgiza masa kai Ummie tashiga yi tanajan gunjin kukan hawaye wani na riga wani muryanta na rawa tace"Sauban Abbien yara ya tafi ya tafi yabarni da nauyij zuhra ya zanyi please? "Kiyahakuri don rashi mungriga da munyi Allah yajikan Abbie ubangiji yasada sa da rahamarsa. Da Ameen 'yan dakin