Sashe 17
Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kai saboda wani irin kallo da Akeela ta aika mata dashi,cikin natsuwa tasamu kusa da Bodejo ta zauna tace"Bodejo barka da safiya Ina kwana? "Lafiya Lou Zuhra harkin gama matsa masa kafafuwan? "Ea nagama don har na hada masa ruwan wanka yashiga kema yanzu zanje na hadamiki. "Yawwa Allah yamiki albarka yabaki miji nagari mejin kanki da kaunar ki. "Ameen Bodejo na,tayi magana kaitsaye tare da mikewa tace"bari nashiga wanka saboda zanje school"duban Guggo Laure tayi tace. "Guggo kune da sammako haka?sai kace wacce ake koranki daga gida?tayi maganar cike da zolaya. Guggo Laure tace"nida gidan mu?ai babu maganar sammako anan Fatima kinsan da zafi-zafi ake bugun karfe. Murmushi Zuhra tayi tace"gaskiya ne to sannu da zuwa,tana gama fadar haka tanufi dakinta. Basu dade da zama ba Galadima yashigo inda Bodejo tashiga hada masa breakfast,duban Akeela tayi tace"tashi kihado muku abin kari. Dan yatsina tayi tana mikewa tanufi kitchen din Bodejo tana wani karairaya uwa zata balle tanufi kitchen din. "Laure kece da safennan haka? Allah yasa lafiya dai? Dan murmushi Guggo Laure tayi tace"Yaya muhammadu kenan kunata fadin sammako kamar wacce tayi asibanci?nikam maganar yaran nan yakawoni......au Wai kaji,tayi subul da baka. "Au Akeela nakawo nan ta zauna koda sati biyu ne zuwa uku tayi anan tafara sabawa da gidan duk da gidan su ne. Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Bodejo da Galadima. Sauke ajiyan zuciya Galadima yayi yace"toh ai Shikenan sai su zauna da Zuhra a dakin zuhran koh? Da sauri Guggo Laure tace"A'ah ba haka za'ayi ba,ni nace taje can,tanufi wajen Aisha ta zauna tadinga tayata ayyuka abubuwan bukata ko kuwa? Gwalo idanuwa Bodejo tayi cikin mamaki tace"a bangaren surukar tata zata zauna?tun kafin akawo ta gidan? Dan tabe baki Guggo Laure tayi tace"Toh menene aciki? Aisha fa uwarta ce koda kuwa ba maganarta da Sauban. Dan murmushi GALADIMA yayi yace"Laure kenan ninakan rasa a Ina kika samu wannan wayewar kamar jinin fulani baya yawo a jikinki,ita Aishan tanuna miki bukatan son akeela tazo ne?koko tace miki bata da maid's ne? Guggo Laure tatsuke fuska tare da kankantar da idanuwa tace"yanzu munkoma gida kenan?to ai shikenan babu komai takarisa maganar tana latso hawaye tare da mikewa. "Dakata!!! Inazaki a haka?Akeela dai kika kawo ta zauna koh?to Shikenan kidauke ta kikaita wajen Aishan. Guggo Laure tamike inda Akeela kuwa tuni taja trolley dinta tafice cikin jindadi. *******KADUNA******* Sosai Ummie taji dadin ganinsu ya Sauban tarasa inda zata Sanya kanta don murna,haka tasa me aikinta takawo musu breakfast don wajen 9:30 suka iso shikuwa Aseef kaitsaye BQ yanufa batare da yaje gaida Ummie ko Mommy ba,koda yashiga wanka yasakeyi yacanja kaya,don sunyi da wata yarinya zasu hadu zai kama mata daki daga adamawa. Gidan tsohon governor jahar kaduna sukaje shida Taufeeq wajen abokinsa Hamid anyi biki Sauban baisamu zuwa ba kuma sosai ran Hamid yabaci,don ko zuwan baisan dashi ba. Basu suka shigo gidan ba sai wajejen Tara nadare shiyasa Ummie tarufe ido yadinga yimusu fada sosai,abinci tace suje dinning suci ita tawuce bangaren Abbie don tunda tadawo acan take kwana. Sunji dadin hakan sosai,sai da suka jira dare yayi nisa sosai misalin karfe sha daya sannan suka nufi bedroom din Ummie kaitsaye, Taufeeq yamiko ma Sauban man da su Daddy suka bayar sukace wanda zai dakko da hannunshi a cikinsu yashafa. Ansa Sauban yayi ya shafa tare dayin wasu addu'o'i sosai kana yaduka yakai hannunshi. Jikinsa ne yakama rawa saboda damko tukunyar kasan da yayi,kokarin fadi takeyi daga hannunshi kuma tabbas idan tafadi da matsala,jikinsa kuwa jiyake tamkar anjona mishi shock kota ko ina. Taufeeq bakaramin tsorata yayi ba saboda yanda yaga Sauban nayi,gashi duk wata jijiya dake kansa tafito banda zufa babu abinda yakeyi. Sauban kuwa jikinsa jiyake kamar ana yankan naman sa,jiyake kamar yasaki tukunyar amma taurin zuciyar shi bazaisa yayi hakan ba. Cikin yardan Allah dai yajawo tukunyar yadaukota,wani irin hayaki ne ke fita daga tukunyar,cikin sauri Taufeeq ya watsa garin maganin da malama Baba yabada a watsa,zuwa can kuma hayakin yafara raguwa,haka rawar da jikin Sauban keyi shima yafara raguwa,a hankali kuma komai ya lafa. Da sauri Taufeeq ya nannade tukunyar da wata bakar kyalle da aka basu, Sauban kuwa kamar jira yake a amsa yazube kan gadon,kansa namasa wani azababben sarawa. Ruwa Taufeeq yadauko masa anan fridge din Ummie dake dakin,da qyar Sauban ya iya tashi hannunsa dafe da kansa,idanuwansa sun kada sunyi jazur,sai da Taufeeq yatsorata daganin idanuwan Sauban. A haka Taufeeq yakamasa suka nufi bq yakaishi dakinsa don kowa da nashi dakin,sannan yace zai kwana anan don bazai iya tafiya yabarshi a yanayin da yake ciki ba. A haka dai suka kwana jikin Sauban gabadaya babu dadi abin kama da jarumi don sosai yakeda dauriya acewar Taufeeq. Koda safiya tayi dakyar ya iya shiga toilet ya watsa ruwa yafito,wannan man shi yashafa a jikinsa tare da kundundunewa cikin duvet saboda zazzabin daya rufesa,shidai Taufeeq hankalinsa yayi kololuwan tashi don haka yafara neman layin Daddy. *OLD MAIDUGRI* "Lallaima yarinyar nan ni akeey babe zata yaudara?wallahi bata Isa tabar kunya ba kuma dole itadin mallakina ce ko tanaso ko bataso kubarni da ita dole nakira boka na yayimin aiki akanta ni zata ci amana?hajiya daharatu tayi maganar cikin fusata. Zuleey ta tabe mouth"hmm mommy kenan ai Akeela ta mutu akan gayen nan kumafa bason ta yakeyi ba da ita da wannan kwadayayyar kakan tatace suke wahalar da kawunan su. Murmushin jin dadi daharatu tasaki tace"kice akeey 'yar wahala ce,yo metake nema anjikin da namiji?me zata tsinta?wallahi saina bata mamaki saina hanata jindadin rayuwa. "Ai mommy saikinyi tsaye fa don bikin baiwuce saura six month ba,inji zuleey. "Hmm kisha kuruminki dani take zancen wallahi.Tayi maganar tare da sakin kwafan bacin Rai don sosai ranta yabaci. *GALADIMA HOUSE* Xahratty CE 20/3/23. [5/4, 14:36] Xahratty (OUM AJMAL): *_GALADIMA FAMILY_* Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page:- 25/26 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ Welcome Ramadan Wishing all our Muslim brothers and sisters good health, luck and wealth on its moon sighting tonight March 22, 2023 before fasting commences. Ramadan Kareem, may Allah bless you with happiness and grace your home with happiness & peace and may all your good deeds, prayers and devotions get acceptance by Allah Almighty during this blessed month of Ramadan. ______Sosai hankalinsu yatashi musamman Bodejo tunda taji halin da akace Sauban na ciki, Ammi ma yashiga sai dai sam bata bayyana damuwar da take ciki ba addu'ah tadinga yimasa a cikin ransa tare da rokon Allah yabashi nasara. Akeela na zaune a parlo kusa da Ammi don Mashahuda tunda taji ance wai tazo ta zauna ne tabar parlon takoma bedroom dinta. Wayarta ce tafara ringing ganin sunan mommy wato hjy daharatu yasa da sauri tamike tanufi kitchen,da kallo Ammi tabita batare da takawo komai a ranta ba. "Hello my sweet mommy.... "Dallah can rufemin baki munafuka,mukike kokari ki munafurta Akeela?to bari kiji wallahi Koda zanyi yawo tsirara baki isa kibar kungiya ba kuma baki isa kice zakiyi aure ba,sannan duk abinda kikeyi kizo inason ganin ki tana kare fadar hakan tadatse kiran. "Mtsewwww nikam wallahi babu wanda ya isa yace zai hanani aure kuma da mijin da nake burin aure mijin da kowace mace zataso kasance wa dashi haka kawai bazai yuwu ba. Komawa cikin parlon tayi fuskar ta cike da tsantsar damuwa ta isa ga Ammi cike da bariki tace"Ammi zantafi gidan su kawata Suby yanzu akakira ni wai tafadi tayi targade a hannu shine zanje naduba ta"takarisa maganar cikin marairaice fuska. "Subhanallah gaskiya ya kamata kuwa kije amma don Allah kiyi sauri don bayan la'asar kiyi maza kidawo don Daddyn ku kinsan baison fitan dare. Sake marairaice face Akeela tayi tace"Insha Allah Ammi nace please kibani number dear nakirashi na sanar dashi fitata. Ammi tace"wanene Kuma dear ni Aisha? "Oh ya Sauban nake nufi Ammi. Ammi tace ok to bari nabaki,daukan tsadaddiyar wayar ta tayi tabawa Akeela tasaka number,zuciyar ta cike da tsantsar farin cikin tasamu number mafarkinta,mikewa tayi babu jimawa tafito tare dama Ammi sallama tafita zuciyar ta cike da tsantsar farin ciki. Tazo dai-dai fita gate dinne kuma saiga muneefa da Rammat zasu shigo, wani banzan kallo duk cikansu su biyun suka watsama juna ,dogontsaki Rammat taja tana me tofar da miyau,da mamaki muneefa ke dubansu gabadaya. Akeela kwafa tayi tare da yima Rammat gargadi da yatsu taraba au tawuce tana karkada shafaffen boom boom dinta. "Useless kawai"Rammat tafada cike da bacin rai. "Aunty rahama meke faruwa ne tsakanin ki da Akeela?meyayi zafi haka? "Natsani wancan 'yar iskan yarinyar duk duniya bani da babban makiyiya sama da ita kuma wallahi sai nayi maganin ta ahankali. Muneefa tace"kiyahakuri mushiga daga ciki kawai banji dadin banzan kallon da tayi miki bane don ko babu komai wata kusan tafi wata mushiga ciki. ****** Daka kalleta kasan a fusace take zaune take akan wata dakakkiyar kujera banda karkada kafafuwa babu abinda takeyi tana huci,gefen daman ta matane masu irin shekarunta,daya gefen kuma 'yan mata ne ciki harda zuleey da Suby. Shigowa tayi parlon ganin fuskokin kowa yasa jikinta yin sanyi kaitsaye wajenta ta isa. "Mommy kiyahakuri nasan nayi lattin zuwa wallahi bansamu dan adaidaita bane da wuri,sorry my sweet mommy,tayi maganar tana shasshafa mata face. Da sauri hajiya daharatu tabige hannun tare da mikewa tadubi Akeela ido cikin ido tana huci tace. "Nizaki yaudara Akeela nizaki ci amana?to bari kiji wallahi baki isa kici amanata ba kisanni sarai kaf cikin wadannan,tayi maganar tana nuna mutanen dake wajen da yatsa tace"Babu wanda yasanni a cikinsu sama dake kinsan ni nasanki kinsan abinda zan iya da wanda bazan iyaba wallahi wallahi kinji na rantse muddin kika ce zaki bijirewa umarni na to saina illataki. Sosai gaban Akeela ke bugawa don tabbas tasan halinta matukar sani ta kuma San batada Imani ko kadan,muryan ta yana rawa tafara magana. "Mommy kiyahakuri walahi bazan taba barinki ba inanan tare dake babu abinda zai rabamu nida ke,inason ya Sauban amma son da nake masa baikai wanda nake Miki ba,idan babu damuwa zanso nayi magana ta sirri nidake. Banda harara babu abinda momy ke zubama Akeela,zuleey kuwa burinta kawai hajiya daharatu ta kore Akeela daga kungiya ita kuma tazaga tayi cuku-cukun rabata da Sauban din ita ta auresa. Daya daga cikin manyan matar ne tafara