Sashe 24
Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Hmm kannen mijinki da za'ayi bikin ku rada day.....ai Suby bata karisa magana ba Akeela ta datse wayar. Kaitsaye Instagram tahau,Nan ta watsa fiki-fikin idanuwan ta kan wayar,da sauri tamike tare da kama mouth"Ewwee!ai da gudu tafita bedroom dinta"Mom! Mom!! Tashiga kwalama mamanta Kira,da sauri tafito daga kitchen,"Akeela wane irin Kira ne haka? "Mom kallah,tayi maganar tana mika mata wayar,ansa tayi. Wannan lefen na waye haka?tayi mgnr ta diddilo idanuwa. "Hhhhhhhh! GALADIMA FAMILY Kenan ana fada miki, kayan lefen kannen bby Sauban ne. "Kai Masha Allah kaya sunyi kyau,Wai wai ko wacce gidan manya zata shiga kenan? "Ea daya zata aure Dan gidan maishanu family,dayan kuma dan Abbie daya rasu zata aura. "Kai Masha Allah kaya sunyi kyau,Allah yasanya alkhairi ya kade fitina,ubangiji ya basu zaman lafiya. "Mom saura nawa,amma ainima yaka mata ace ankawo nawa yanzu,tayi maganar tana bata fuska . Harara ta wugamata tare da shogewa kitchen din,da sauri itama Akeela tanufi kofan fita,kaitsaye sashin Guggo Laure ta nufa,itama nuna mata videon tayi,ai bata gama gani ba tafara sallallami"duk ankawo nasu amma ke basu kawo naki ba?to me mutanen nan suke nufi danine?sannan akasa kirana a amsa kayan dani?wallahi sai yau nasake tabbatar da Yaya Bodejo bata sona,bata son jinina,lallai ko yanzu zanje gidan. Caraf Akeela tayi"wallahi dani zaki Guggo don inason ganin lefen nan azahirance, shikenan maza ki shirya muje. Aiko cikin farin ciki Akeela ta fita, Guggo Laure bata jima ba tashirya tafito tana mitan har yanzu Akeela bata fito ba?Nan mujaheed dandan Baba sani yashigo gidan da mashin dinshi kirar jincheng roba -roba. "Guggo fita zakiyi ne haka? "Ea wallahi mujaheed zanje gidan Yaya muhammadu ne nadawo nida Akeela, murmushi kwance saman fuskansa yace"Au da amarya zaku fita?ni mumma dade bamu hadu da Akeela ba Guggo. Yatsine baki Guggo Laure tayi tace"to kunyar wa mujaheed?ai kunyarka,kuna gida daya bazaka shiga kaduba ta ba? "Guggo kenan,ko nashiga wataran mom zatace bata tashi ba ko batanan,to Yaya zanyi? Mere Guggo Laure tayi da baki tare da cewa"kaga bari nashiga naga dalilin da yasa ja'irar yarinyar nan shanya ni,takarisa maganar tana shiga sashen,nan tafara juyo fadar Mom. "Waike Akeela sai yaushe zakiyi hankali? meyasa baki da kunya?wallahi kika fita gidan nan nidake ne,bubbuga kafafuwa Akeela tafara. "To yayane meke faruwa ne?ni inacan waje inajiran ki ke kuma kinshanya ni. "To ba Mom bane wai bazani ba,haka kawai tace bazani ba,kafin Guggo tayi magana Mom ta cabe"fisabilillah Guggo taya za'a barta taje gidan surukai saura sati biyu biki?wallahi rashin kunyar Akeela kullum gaba yakeyi. "Maimuna kedai sai kayi bagidajiya ko mu tsofaffin da bazamu dinga wannan abinba bare ku yara,yanzu lefi ne don Akeela ta shirya munje gidan Yaya muhammadu da ita?ke don ma banyi niyya bane da wallahi ranar asabar mai zuwa zata koma can da zama,zo muje kinji",tana kare fadan hakan suka fita Akeela nabiye da ita tasha wani dan ziririn mayafi tana karkada shafaffen baya kamar andanne da iron. Mom din Akeela kuwa sakin baki tayi tana duban su har suka bar farlon,a fili ta furta"Wallahi sam abinda Guggo take bata dacewa,wannan ina mutum zai yarda yabata danshi?mtsewww taja tsaki tare da juyawa ta koma kitchen din. Su Guggo Laure kuwa koda suka isa gidan sun cidda ya sake kacamewa don Aunty Maryam ma ta iso,wasu daga cikin 'yan uwan Bodejo su uku suma sunzo,hannu bibbiyu aka tarbeta kamar yanda aka saba,nan aka shiga gaishe-gaishe Guggo Laure tace"Ashe kuma ankawo lefen yara banida labari don ba'a kirani a amsa kaya dani ba,shima a waya yanzu Akeela take nuna min shine nace bari nazo naga zahiri"tayi maganar tana dariya kasa-kasa. "To menene a amsan lefe Laure kinmanta shi taufeeq mune zamu hada mukawo? Harouna su suka kawo lefen Mashahuda shida hauwa'u daga kaduna,a ranar kuma aka kawo na muneefa,to ai ba wani abu bane,sannan yaranki duk maza ne ba mata ba balle ace suzo a amshe kayan dasu. "Amma Yaya Bodejo duk da maza ne ai naga suna da matayensu ko?ko babu komai ai ace ko su maimuna da uwar mujaheed ne a turo,ammaai babu komai dama idan ba'a dauke ka da muhimmanci ba babu abinda bazaka gani ba. "Guggo wallahi ko daya ba haka bane,kayan ma ba mata ne suka kawo ba mazane suka kawo kayan. Guggo Laure tace"Maryam to tunda mazane suka kawo,ba sai akira ko mansir bane? Aunty Maryam tace"To shikenan Guggo kiyahakuri ai akwai na wasu 'yan matan har guda uku bayan wadannan kibari idan za'ayi nasu zakiji komai mun amsa lefinmu dai wannan. Ture kaga tsiya Guggo Laure tayiwa dan kwalinta tare da hura hanci tace"da dai yafi kam. Bodejo kuwa tun sanda taji Guggo Laure tafara korafi ta yunkura tabar wajen. "To shi Sauban nashi lefen be isone kuwa ba? Dan murmushi Aunty Maryam tayi tace"Ea to ina tunanin sai next week zai iso dasu 'yan Dubai ba,kinsan shi acan yake hada lefensa"murmushi Guggo laure tayi cike da jindadi tace. "Ah Masha Allah, Allah dai ya iso mana dashi lafiya,da Ameen aka amsa gabadaya. Akeela sosai taji dadi a ranta,sai lokacin ta tuna bata gaishe da Aunty Maryam ba,cikin kissa tashiga gaisheta, Aunty Maryam itama ta amsa cike da kulawar don batasan itace Akeelan ba itadai taji ana cewa jikar Guggo Laure ce. A kwana atashi babu wuya yau biki yarage saura sati guda kuma ayau Sauban zai diro don taufeeq yatafi daukosa tare da wasu abokansa su hudu,don kayan kwana biyu kenan da isowar su yana hannun wata kawar Ammi an aje a gidan.Itama Aunty labeeba anjima zasu kariso,gida fa yacika yayi tam,a gefe daya kuma Guggo Laure ranta a jagule yake saboda rashin ganin ba'a kawo lefe ba don kuka Akeela ta tasata tafara mata,aiko ana cikin hakane baba sani yayi sallama yashigo farlon. Gaida Guggo yayi cikin kulawa face dinsa dauke da raha yafara magana"Guggo dama maganar kayan lefen Akeela ne ankawo sunzo bayan la'asar don yanzu suka taf......ai be karasa magana ba Guggo Laure tamike tare da sakin wani guda. "Ayyyiirirrrriiiii!Allah nagode ma,sani ina suke masu kawo kayan?. "Sun tafi tun dazu Guggo. Shigowa Alhaji mansir yayi, ya gaida Guggo,nanfa ta amsa baki a yage tsananin murna. "Sani to ina kayan suke yanzu? Baba sani yace"Suna farlona. Hade rai tayi tace"a sashen ka Wai kake nufi? Sake tsuke fuska tayi tare da dubansa tace"A'ah magana ta Allah niban yarda ba akan wane dalili za'a ajiye kaya a sashenka ga sashin uban 'ya?gaskiya ayi maza-maza adawo dashi sashin mansir,daga baba sani har baba mansir,mujaheed sakin baki sukayi suna duban Guggo laure,cikin bacin rai Baba mansir yadago zaiyi magana,katsesa Baba Sanj yayi ta hanyar daga masa hannu sannan yadubi mujaheed wanda ranshi yakai kololuwar baci yace"Mujaheed maza kaje parlo na ga key din ka kwaso kayan lefen kanwar ka kakawo dakin Guggo,cikin ladabi Mujaheed yasa hannu ya amsa key din tare da juyawa yatafi,da harara Guggo laure tabishi tana Jan tsaki kasa Baijima ba yafara zhigowa da akwatunan,aifa nan Guggo laure tashiga guda daga Mom din Akeela har hajiya zainab murna sukeyi baki har kunne,kafin kace me gida yafara cika da makota zuwa ganin kayan lefe,sosai kayan sukayi kyau Masha Allah don Sauban yakashe kudi musamman hand bag da shoes nd Dubai gowns,kaya dai sunyi kyau sai dai makiyi akwatuna takwas yayi. Nanfa kafin kace me kawayen Akeela sunfara watsawa a duniya. Washegari ya Sauban yaturo mata da message kan yananan shigowa,murna Akeela tayi saboda aganinta yafara son tane da kula da ita a fili ta furta"Lallai bokan Guggo yasan aikin shi, hehehehe ya Sauban kenan ai kashigo hannu na kagama,takare maganar tana mikewa tare da fadawa toilet,sabulan ta na dilka dana bleaching da ake hada mata tafara muttsike jikinta dshi before tashiga wanka. Aiko washegari su Suby da Zuleey suka zo gidan inda suka je wani restaurant suka siyo musu snack's lafiyayyu,tare da shiryawa ala dole zakace su ne suka hada. Sai wajen 5:30 su ya Sauban suka iso dashi da Taufeeq da Kareem duk cikan su sunyi kyau musamman Sauban da Taufeeq duk da cewa manyan kaya suka sanya,shadda ya Sauban yasanya me ruwan kanwa inda aka mata dinki half jamfa sai hannun ma gajere hulan kanshi ya murzata brown sai cover shoe da ya Sanya brown,agogon hannun shi kirar Gucci me ruwan kanwa,inda farin fatan shi yafito yayi masifan kyau,face dinshi sanye da shade fuskar nan babu annuri ko kadan,shima ya Taufeeq shaddar ya sanya dark blue shima half jamfa amma shi besa hula ba takalmin shi da agogon sa bakake shima yayi kyau duk da daka gansu shida Sauban zaka san jini daya ne, malam Kareem kuwa kananun kaya yasanya jeans da t shirt sai dai yayi kyau don duk cikansu badai iya wanka ba,gabadaya sun rude da ganin zaratan mazan,sosai Zuleey da Suby suka hadiye miyau don gabadaya sunyi mutuwan tsaye da ganinsu musamman Sauban. "Hello sannun ku da zuwa,please have a sit, zuleey tayi karfin fada tana nunawa Sauban inda zai zauna,cike da karairaya ita da Suby suka samu 2 seater suka zauna,inda su Sauban ke zaune a 3 seater,cikin kissa Suby tasa wayar s kunne tare da fara magana"hello kawata wai mekikeyi ne?kifito mana haka gasu angon namu fa yazo,takarisa maganar tana lankwasa muryan ka,ta wutsiyar ido Zuleey ta gallamata harara tana me mikewa. Yake tasaki tana saka idonta kan na Taufeeq don sam kwarjinin da Sauban ya mata yasa takasa hada Ido dashi tace"excuse me!tayi maganar tana watsa yatsu wadanda suka sha kunbunan kanti,sanye take da wani riga da skirt na atamfa sunyi bala'in matseta duk da ba bayan ne da itaba amma karfi da yaji ake jujjuya su. Ko kallonta Sauban beyi ba don shi hankalin sa Yana ma kan wayan dayake daddanawa ne, Taufeeq ne da Kareem sukayi karfin halin amsa mata, Suby tace"ya shirye-shirye guy's?munji ku shiru Ashe yau dinma kuna tafe?shiru kowannen su ya mata yana danna wayansa,da mamaki Suby ta dubesu amma sai wata zuciyar ta bata amsa da kila basu jita bane. "Oyoyo sweetheart"Akeela tashigo farlon da gudu tare da nufar Sauban sai dai ganin face dinsa da rayi yasa dole ta ajiye duk wani kissa da bariki da taso aiwatar wa,cikin rawar jiki tashiga gaishesu,cike da kulawa Taufeeq da Kareem suka amsata amma gogan ko dagowa beyi ba balle tasa ran ze amsata,"amarya kina lafiya?karem yayi maganar yana dan murmushi, Akeela ma murmushin tayi