← Book details Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 64

Sashe 47

Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sa da yaji dakakken nama yayi kyau da dadi,sannan ta dama masa kunun gyada, Ammi ma ta aiko da breakfast din kosai da custard sai wainan kwai,shiryawa tayi cikin riga straight gown,wanda ya fito mata da cikakken surar ta ko ina yacika Masha Allah, tayi kyau sosai,abinka da atamfa me dan duhu sai tayi kyau kwarai,daurin Aisha buhari ta murza mai kyau,kafarta sanye da high heel shoe brown, fitowan ta kenan daga kitchen hannunta dauke da plates taji alamun tafiyan sa,turaren sa me kamshi Arabian Oud ya buge hancin ta,dan lumshe ido tayi tanajin faduwar gaba,daurewa tayi ta cigaba da shirya dinning din. Karisowa yayi yaja kujera ya zauna,sanye yake da wata yadi me kyau tare da maiko brown colour,daka ganta kasan lallai anyi fitan nera wajen siyan ta,kansa murzazziyan kube ce,wacce kudinta zasukai dubu 35 face dinsa babu wani walwala kamar koda yaushe, Zuhra kuwa gabanta ne ya cigaba da faduwa,a hankali tayi karfin halin furta"Ina kwana Yaya"kura mata ido yayi babu ko kiftawa,almost 5 minutes sannan ya girgiza kai kawai,ajiyan zuciya Zuhra ta sauke kirjinta na cigaba da bugawa daurewa tayi tace"Yaya meza'a zuba maka?hannunsa dauke da wayar sa yana latsawa batare da yadago ba yace"meda menene akwai?Zuhra tace"akwai jallop din macaroni with kunun gyada nama nd custard wih kosai,sai wainan kwai.Dagowa Sauban yayi yana zuba idanuwan sa akan warmers din dake kan dinning din,duk da a rufe suke yace"kisamun macaroni nd kunun gyada kadan inci tukuna"yanada tabbacin itace tayi wannan, cikin nutsuwan ta take serving dinta,gabadaya ya tsareta da idanuwan sa jinta kawai take a takure, shikuwa Sauban baiki yaji Zuhra akan cinyar sa ba, wani irin shaukin son ta kawai yakeji,batare da ya ankare ba yaji maganar ta"bismillah Yaya"dan sake hade face yayi yana daukan spoon din tare da duban plate din,lumshe ido yayi yanajin wani sanyi da dadi a ransa don dakakken mama yaji a cikin macaronin Masha Allah,hadiye miyau yayi, bismillah yayi yafara cin abincin cikin mutsuwa,jiyayi wani dadi ya ratsa masa har kwakwalwan kansa,sosai yake daurewa gudun kada yayi santi,ganin ta zauna tatasa kosai da yaji tanaci yasa ya dubeta"bazaki kiyayi kanki da cin yaji haka ba?wallahi idan kikazo kina min complain din basir da ulcer ko?sai kawai yayi shiru ya cigaba da cin abincin, Zuhra kuwa dagowa tayi cikin marairaice face,tare da wata shagwa6a66iyan murya wanda ita kanta bata ta6a sanin tana da ita ba tace"kai Yaya kosai fa idan babu yaji babu dadi"wani tsam!yaji a dalilin yanda tayi maganar,batare da yayi magana ba yadaga mata kai kawai,atake anan ya cinye plate din,gyaran murya yayi mata, dagowa tayi ta kallesa,da ido yayi mata alamun akara,kara mishi tayi ba da yawa ba,itako kosan biyar taci ta basshi cuz takasa sakin jiki taci yana wajen,shiko ko a jikinsa sakin jiki yayi yaci abincin sa yayi katt,yana gamawa yadau kunun gyadan sa yafara sipping,lumshe ido yayi domin har ga Allah yaji dadin kudun sosai,be yadda yabiye ma dadin ba yadaka,don a haka ma jin cikinsa yake ya cika don dama shi ba ma'abocin cin abinci bane,tissue yadauka yafara goge bakin sa,ji sukayi anwani daka kofan palour. Da sauri suka mike, Akeela ce tashigo jikinta sanye da wata doguwar riga fitted sai dai ko kadan batayi mata kyau,sai taunar chwengum takeyi tana kare ma palour kallo,ganin canja wasu abubuwa da akayi tare da kara gyara sa,ta6e mouth tayi tana jan tsaki,nan tashiga takowa a gaban Sauban ta tsaya idanuwan ta cike tafff da hawaye tafara magana"Kaine na mijin dana fara so a rayuwa ta wanda akansa nasan menene so,amma munafukai sunyi nasarar rabani dakai a lokacin da muka kasance tare,inaso kasani wallahi bazan ta6a rabuwa dakai ba koda kuwa zanyi yawo tsirara ne sai na farauto soyayyar ka,sai nadawo cikin gidan nan matsayin mata"takarisa maganar hawayen na zubowa,duban ta ta maida ga Zuhra tana nuna ta,ke kuma inaso na Miki wata zazzafan gargani duk sanda kikasan mijina a matsayin miji wallahi babu ke babu kwanciyar hankali,banza kawai jak.....ai bata karisa ba taji saukar gigitaccen mari Sauban ya shimfida mata a fuska,sannan yana huci ya nufi wajen extension wear ya ciro cabel din caja,ai Akeela na ganin haka ta nufi kofan palour tana fita da gudu,aiko binta Sauban yayi cikin zafin nama, Zuhra kuwa da taga ma tsorata da kalaman Akeela binsa tayi jikinta na wani irin rawa.Wallahi babu macen da ta isa ta haifa maka yara saini,ke kuma kijira kiga abinda zai sameki"tana kare fadan haka tafice kamar wata zararriya, Zuhra kuwa kuka ta fashe dashi tana juyawa don ta tsorata da kalaman Akeela gani takeyi tabbas kamar wani zai farun,babu zato taji Sauban ya mata wani irin runguma,ai a haukace ta fisge jikinta tanaja baya,tsayawa kawai yayi yana kallon ta,jiyayi ta saki kuka tana hade hannayen ta waje guda,kuka yasa ta gaza furta komai,nufota Sauban yayi da mugun sauri ta kuma jan baya,tsayawa yayi kawai yana kallonta"Naroke ka da Allah yaya ka sakeni,ni bazan iya auren nan ba inajin tsoro please kasakeni nac..... batare da taji sanda yakariso ba kawai saukan mari taji a kuncin ta me azaban zugi,wani ihu tasa tana dafe kumatun tare da duban sa,jikinsa ne ke wani irin shaking,idanuwan nan nashi sunyi jajawur bakinsa na rawa"Du....dduk..duk ranar da kika sake cewa na saki wallahi sai nayi miki dukan mutuwa"yana kare fadar hakan yajuya yana maida kwallan dake kokarin zubo masa,tabbas a yanzu ya tabbatar da yarinyar nan bata son sa, kaitsaye palour yafice jikinsa na cigaba da rawa,ita kuwa Zuhra inda yabarta nan ta zube tana sake fashewa da wani irin kuka( _Nikaina Zuhra kinfara bani haushi akan kalmar sakin nan da kike fada,da mene zaiji?_ ). Tana bedroom tana sallah taji shigowan sa yahaye upstairs,har taji sanda yake sakkowa da alaman ana jan trolley bag,cikin sauri ta mike tafito,shi tagani sanye da kananun kaya, security dinsa na daukan akwatin yana fita,kafadun shi dauke da wani jakan, Zuhra lokaci guda zuciyar ta tatsinke taji kuka kawai yataho mata,a hankali ya tako har inda take,face dinsa kadaran kadahan,hannunta ya kamo duka biyun tare da sumbatan goshinta"Zan tafi insha Allah zandawo nan bada jimawa ba,Zaki koma wajen Ammi before nadawo,ina miki fatan alheri"yana kare fadar hakan yajuya yafice,sai a lokacin makalallen hawayen da Zuhra ke makalewa suka samu damar sirnano mata,tana me zama kan sofa din sharaf,tana fashewa da kuka. Shiko Sauban a tunanin sa Zuhra zata biyo sa a baya amma sai yaga akasin haka,girgiza kai yayi yana sake yarda da lallai Zuhra bata son shi,mota yashiga driver yaja,dama ya masu Ammi sallama kaitsaye sai airport, Zuhra kuwa tasha kukan ta ta koshi sannan ta mike tashiga tayi wanka sosai ta kwanta atake wahalallen bacci yayi awon gaba da ita,sai wajejen biyar ta farka tasake wanka ta shirya cikin turkey gown me yankakken hannu,tadau hijjab tasanya,abubuwan bukatan ta tadauka,dama ba komai aka kawo mata ba na kayanta,fita tayi ta kashe kowane socket nd switch na sashen har saman shi sai da tahau ta kashe komai sannan ta rufe ko ina tafito tanufi Galadima house. Cikin sanyi tashiga sashen Bodejo tafara nufa,suka gaisa nan Bodejo tafara mata tsiya tana cewa ta canza lokaci daya saboda mijinta yayi tafiya sam babu walwala tattare da ita, Zuhra kuwa da baki be iya shiru tace"Cab Allah ya kyauta,ni wannan har nayi irin wannan shakuwan dashi ne? Allah yatsare a gayas,dariya Bodejo tayi tace"hmmm yaro yaro ne koma me zakice ba yarda zanyi ba. Nan suka ta6a hira ta mike ta nufi sashen Mom,tagaishe ta aiko nan ta cidda Rammat ai zama sukayi suka sha hirarar su sosai,duk da Rammat sa'an su Aunty Mashahuda ce amma akwai saukin kai gashi nasu ya hadu da Zuhra,ba ita tashiga wajen Ammi ba sai after magrib,aiko nan Ammi tafara nan-nan da ita,duk kulawar da take bata ada sai yakaru, Ammi kuwa sai taga kamar Zuhra na cikin damuwa ne na tafiyan mijinta yasa tace"ki kwantar da hankalin ki Zuhra, yayan ki baze dade ba zaidawo kuma idan zaidawo dake zai koma gaskiya"Zuhra tace"a'ah Ammi nifa ba komai,kawai dama Akeela ne..sai kuma tayi shiru,kallon ta Ammi tayi tace"dama Akeela mene?me Akeelan tayi miki? Zuhra tayi raurau,hawaye na silalowa,nan taba Ammi labarin abinda yafaru dazu da safe,sannan cikin muryan kuka ta cigaba"ni Ammi inajin tsoron abinda zatayi mun ne,tace"idan nasan shi,duk da ban fahimci me kalmar take nufi ba,kuma ninasan shi,ba Yaya na bane? Ammi ta sauke ajiyar zuciya don ta fahimci tabbas Zuhra bata gane me hausar idan kika sanshi yake nufi ba hakan yasa taji natsuwa tace"ki kwantar da hankalinki,kinfa je islamiya Akeela ke saukakkiya ce,kinsan bawa baya wuce kaddarar sa, Akeela bata isa ta miki abinda Allah be miki ba,kisa hakan a ranki, sannan kuskure ne Wanda kema kinsa ni nacewa miji ya sakeki,kinsan zunubin hakan,sannan kinsan wani irin so Sauban ke miki? Zuhra tace"Ammi wallahi Yaya beso na kawai ya aure ni ne. Xahratty CE Lallai Alqalami yafi takobi [7/15, 10:35] *_GALADIMA FAMILY_* https://chat.whatsapp.com/Cz6pFHyd9N68OmqNx3Vpqs Page:75/76 ____Ammi murmushi kawai tayi tana jinjina ma yarintar Zuhra,haka Zuhra ta cigaba da zaman ta a apartment din Ammi tama mance da wani Sauban sai idan taji suna waya da Ammi take tunawa dashi,sannan tasake yarda da baya sonta tunda ko kiran ta yakasa yi yaji ya yabarta,sosai taji zafin hakan,da yake sun dan samu hutun sati biyu na school hakan yasa taji tanason zuwa wajen Ummie. GALADIMA kuwa jiki Alhamdulillah don sosai aka fara ganin sauyi don har mikewa yakeyi da kansa cikin yardan Allah kuma yana dan maganar sa,lokacin da yaji Zuhra ta tare da Sauban ba karamin farin ciki yayi ba shiyasa koda Sauban din yazo nasiha yadinga masa kan ya kula da Zuhra ya riketa amana,sannan dui abinda zai gani ya mata uzuri harda yarinta. Shi kanshi Sauban din yaji dadin ganin Galadima don jiki kam Masha Allah tunda maganar ba sosai yake fita kamar da ba,sai dai ana sa ran nanda 3 days za'a sallame su gabadaya, Bodejo ita kanta tayi farin cikin hakan don da sukayi video call da Galadima har kukan farin ciki tayi mara misaltuwa. ***** Bangaren su Adda Zainab bincike sosai akeyi,inda taki amsa lefin kisan,tadai ce taje sashen marigayi Alhaji iliyasu saboda tunda suka dawo kwana biyu be lekota ba sai taje taduba ko lafiya shine tana shiga ta cidda gawansu don har kumburi sun fara,ganin da sukayi kamar Adda Zainab tafara musu
Chapter 47 · 0% Book details