Sashe 31
Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A can gida kuwa duk da mamakin su Daddy suka dawo tare da tambayar kawunan su a zuciyoyi mezesa suyi haka?shi kanshi Taufeeq mamaki ne fal ransa,sai dai rashin samun me Basu amsa yasa kowa yakasa furta komai,koda su Aunty Maryam suka isa apartment din Galadima tambayan su me jiki sukayi tare da me kwana da ita,cikin alhini suka basu amsa da wai Sauban ne zaiyi jinyar ta,ganin fuskokin tsofaffin sukayi normal babu wani alhini, Galadima yace"Hakan ma yayi Allah yabata lafiya ya kuma tada kafadun ta,da Ameen suka amsa jikinsu nasake sanyi da lamarin ahalin nasu masu cike da abubuwan mamaki.A sashin Ummie kuwa sun tadda Amma har tayi bacci abinta don dama kafa ya matsa mata, Adda Zainab ne keta sababi akan mezesa su Daddy suyi hakan?ita kuma Ummie takasa magana kan abinda yake faruwa,ajiyar zuciya Ummie tayi tace"bazan iya tambaya ba Adda domin koni dana haife Zuhra bankai bayin Allah nan sonta da kaunar ta,ni ina tunanin suna da kwakkwaran dalilin su nayin haka don dai haka kawai bazasu yanke wannan hukuncin ba. Adda Zainab tace"Hmm to ai shikenan Allah ya kyauta meson dangin miji ke dama sam bakison a fadi lefinsu koma dai menene?ai hakan dai bedace haba jama'a sai kace ana garin ga6a ,shiru ita dai Ummie tayi bata tanka ba.Hajiya Aliya ce tadubi Adda Zainab tace"Niko aminiya yaushe Alhaji iliyasu zai dawo ne?saboda munada biki acan gombe inaso da muje tare da kene,kinsan hajara na zata aurar da 'ya next week,cikin mamaki Adda Zainab ke duban hajiya Aliya tana sakin dariya"Eyye aminiya kina nufin hajara har zata aurar mu muna zaune?lallai aiko ya kamata muje ma hajara biki ai komai zaizo da sauki nima gobe zan koma nafara tarban dawowar shi don jibi zai dawo yace jirgin 4:00 zai biyo, cikin farin ciki hajiya Aliya tace"Kai naji dadi ai nida kaina ma zan tambaye shi domin nasan zaiji dadin hakan sosai,dariya Adda Zainab tayi tace"gaskiya kam zaiji dadi sosai Allah yadawo min dashi dai lafiya kinsan yatafi yana fushi danine don naki binsa sai a waya muka shirya,hajiya Aliya tace"Ai tafiye n nan irin nasu ba kowace mace bace zata jura kinji kiyi zamanki anan wallahi, Adda Zainab tace"yanda kikajin nan. Ummie najinsu sai dai bata tanka ba don asanin kanta duk abinda za'a cema hajiya Zainab akan hajiya Aliya ba yarda zatayi ba saboda son da take mata,tasani yanda takeson hajiya Aliya bata mata irin wannan son tun suna secondry school,sabanin ita da take tsananin son yayar tata,mikewa tayi don nufan dayan sashin nata don duba sauran jama'ar nata nan tabarsu suna cigaba da hirar su,da wani irin mugun kallo Adda Zainab tabita dashi tanajin kamar tatashi ta makure ta tahuta. Bayan fitanta cikin dacin murya Adda Zainab tafara magana"Aminiya boka hatsabibi bai kyauta minba,ba haka kukayi dashi ba nidai duk aikin da yabani nayi nayi amma kina ganin ma idon ki babu abinda yayi aiki ni garas ma naga takari,gaskiya zan canza wani bokan ki samo min wani nikam bazan iyaba wallahi so ake ciwon zuciya da bakin ciki su kashe nine ko mene?Hajiya Aliya tace"Kash!Kash!! Dadina dake Aminiya gajin hakuri,munyi magana dashi nayi masa korafi sai dai yace lefin ki ne wallahi domin kuwa duk aikin da kikayi sun lalace sai dai besanar dani yanda akayi suka lalace ba,amma kinsan idan kika fadi wani magana mara dadi akan boka hatsabibi kema baki masa adalci ba,shekara nawa yana miki aiki kuma anga dacewa don kawai wannan anyi kuskuren da kecema kikaja sai kifada haka?wallahi banji dadi ba idan yajiki kuma babu ruwana.Adda Zainab tace"gaskiya ne idan nafada wani abu nayi butulci aikam zanje nane mesa da kaina domin magance matsala ta. Hajiya Aliya tace"Da dai yafi kam,haka suka cigaba da tattaunawa akan matsalolin su har suka raba dare. ********* Wajen karfe 2:40 ta farka a hankali tashiga bude ido still tanajin kan na mata ciwo sai dai baikai na farko ba,kwata babu karfi a jikinta ga wani masifaffen fitsari da takejin ya matseta,muryan ta da babu wani kwari ta bude tafara magana"Ummie! Ummie!! Ummie!!! Zanyi fitsari"kamar a mafarki yakejin muryan nata don shi mutum ne wanda beda nauyin bacci,bude ido yayi ya zubanya mata batare da yayi magana ba,magana tasake still"Ummie zan shiga toilet,mikewa yayi yana me kunna switch din,room din ya gauraye da haske,ido biyu tayi dashi wani irin kamewa tayi akan bed din duk da kuwa wani irin fitsari da takeji ga rashin karfin da bata dashi ko kadan jinta take kamar a wani duniyar,tamke fuska yayi ganin yanda ta kura masa ido alamun ta tsorata dashi,bata fuska yayi da kyar ya bude baki ya soma magana"Zaki tashi narakaki toilet dinne ko zakiyi a zaunenne?yayi maganar yana tsura mata dakwa-dakwan idanuwan nan nasa,cikin rawar jiki ta mike sai dai ko second biyu batayi ba tatafi luuu zata fadi,cikin hanzari yakarisa yana me tallabo ta jikinsa,duk cikansu sunjisu a yanayi na daban a dalilin hakan,kamata yayi suka nufi toilet din wanda yakejinsa fess kamar ba'a hospital ba sai kamshin Toilet freshener yake Dana hypo,kokarin sakinta yake amma sai yaga tatafi luuu,ita kuma ga azababben fitsari tanaji kuma yaki matsuwan mata,rasa yanda zaiyi da ita yayi a hankali yake jan kananun tsaki saboda takaici shi sam bema san yanda zai mata ba,ganin haka yasa Zuhra fashewa da kuka tanajin wani irin takaici don dai ba'a kyauta mata ba da aka barta a daki daga ita sai shi,tafada a cikin ranta,ita batasan tana hospital ba,karfin hali yayi ya jingina ta da bango tare da dukawa,doguwar gown din dake jikinta ya fara dagawa,jikinta babu inda baya rawa kafafuwan ta naneman gaza daukan ta don ita abune wanda be taba faruwa da ita ba,a hankali ya cire mata pant din face dinsa babu walwala yace" Oya yikiyi, am waiting for you. Ganin da tayi bata da wani mafita yasa tafara kokarin yin fitsari ai babu zato bare tsammani tafara sakin shi a tsayen,runtse idanuwa tayi da karfi tana mejin wani irin mahaukacin kunya tare da takaici,shima takaicin a gefensa yake ji don ma anci sa'a bata fallatso mai da fitsarin ba da ya kafa mata mari acewar sa,idanunta a rufe,bude tap taji yayi nan ya jinginar da ita daga jikin bangon sosai yana me matsawa tare da kauda kai yace"Yi tsarki mufita,duk kincika ma mutane toilet da zarnin fitsarin ki,mtsewwww! Yaja siririn tsaki. Zuhra kamar kuwa babu zato taji hawaye na sirnano mata,cikin rashin abin yi tayi tsarkin ta gama,kamata yayi suka fito yana zaunar da ita akan gadon,idanuwan ta arufe ta kwanta tana jin kanta na juya mata. Kashe switch din shima yayi yana me komawa yazauna kan plastic chair din,kowanne da abinda yake sakawa a ransa,babu jimawa bacci yayi awon gaba da ita saboda alluran da aka sa mata a drip din harda na bacci,jin yanda take sauke numfashi cikin natsuwa ya tabbatar mata da tayi bacci don haka yamike ya shiga toilet din don dauro alwala. *~DA ALAMA BA KARAMIN CAKWAKIYA BANE ZAI AFKU GABA,NINAGA LABARIN NATA TSAYINE ANYA KUWA ???~* Xahratty CE Lallai Alqalami yafi takobi 11/6/23. [6/14, 10:59] Xahratty (OUM AJMAL): *_GALADIMA FAMILY_* Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 49/50 *_KUYAHAKURI PLEASE DUK DANI NA TSARA LABARINA NAKE KUMA RUBUTA ABINA SAI DAI WANNAN KARAN LABARIN SHIKE TSARANI YAKE KUMA JANA FATAN KUN GANE ABINDA NAKE NUFI?INA KOKARIN INJA BURKI,SHI KUMA YANA WASKEWA *PLEASE FORGIVE ME MAKARANTA GABADAYA LABARIN SADAUKARWA NE GA MASOYA BOOK DIN GALADIMA FAMILY.* ______Shi mutum ne me kyankyami gashi babu abin sallah don haka yabude kawai app din complete Qur'an dake wayan sa na Alaramma Ahmad Sulieman yafara karatun,itakuwa bancin ta takeyi cike da natsuwa,haka Sauban ya cigaba da karatun sa har aka kira sallar asuba,toilet yakoma yadauro alwala yafita don neman masallacin asibitin ya gabatar da sallah. ******* A can kuwa washegari haka suka tashi jiki a sassalube sai dai hakan be hana hidiman na bikin kawatuwa ba,cikin sauri su Aunty Maryam ke hada abin breakfast din 'yan asibiti su Laila na tayasu don bada su za'a koma Zaria ba, Rammat ma said tayasu aikin takeyi ta saje a cikinsu sosa,'yan aikin Ammi kuma suna na amare Akeela,sai wajen tara suka gama hada breakfast din. Da mommy dasu Aunty Maryam su Nihal sune suka nufi asibitin,don Abba, Daddy, Baba Hashim tun safe sukaje asibitin amma bata farka ba,haka suka dawo akan anjima zasu sake lekowa,Koda suka isa baya dakin sun ciddata tana zaune bayan ta pillow ne an jingina mata,ganinsu ba karamin murna tayi ba sai dai kallo daya zaka mata kasan tanajin jiki, basket din duk suka aje suna Isa bakin gadon suna mata ya jiki,shimfina dan babban carpet din da sukazo dashi sukayi,nan wasu suka zazzauna,mommy dafa kanta tayi tace"Sannu my baby ciwon nan naki na jiya ya tsorata mu sosai,ke Kinga yanda kikayi zuru-zuru kwana daya kawai,dan lumshe ido tayi cikin karfin hali tace"mommy nama ji sauki fa,duban su Aunty Maryam tayi tace"Mommy Maryam,mommy labeeba ina kwana?amsa mata sukayi cikin sakin fuska tare da tambayar ta ya karfin jikin nata?amsa tabasu da Alhamdulillah.Cikin tsokana Nihal tace"mufa munzata shekawa zakiyi har munfara tanadin gumba,duka akasa dariya,cikin karfin hali Zuhra tace"ai idan na sheka ku kanku bazakuji dadin zama a family dinba wallahi,cikin Wasa Laila tace"injiwa ya gaya Miki?lallai mudai kinmana bakin cikin cin gumba,kwafa tayi"hahaha kubari na warke zakuga yanda ake rashin mutumci.Duka 'yan dakin dariya suka sanya,dai dai sukayi sallama suka shigo dakin,shida Taufeeq ne,kallo daya ta masa ta kauda kai da sauri don harga Allah batason hada ido dashi,hada ido sukayi da Taufeeq wanda Kai tsaye yanufo inda take,langabar dakai tayi cikin muryan shagwaba tace"Yayaaaa sai yanzu ko? Murmushi dauke a face din taufeeq yace"sorry kanwaty aike dince kin tadama kowa hankali jiya kowa ya rude,tana kokarin magana aka turo kofar aka shigo. Shuraim ne da wasu 'yan mata biyu sai wata 'yar dai babban mace kamar su Aunty Maryam sallama dauke a bakunan su,hanayen 'yan matan kuma rike da ledoji riki-riki sai basket,cikin mutumtawa da girmamawa mommy dasu Aunty Maryam suka tarbesu,nuna musu wajen zama sukayi. Koda suka zauna gaisawa suka farayi da juna,shiko kaitsaye wajenta ya nufa face dinsa dauke da damuwa,tsira mata idanuwa yayi kamar zai lasheta cikin tausayin