← Book details Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 64

Sashe 42

Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

****** Akeela kuwa ganin abinda yafaru ba karamin rudewa da tashin hankali ta shiga ba,kuka takeyi tana fadar ta shiga uku shikenan tasan ita auren ta yanzu ya gama yawo,itakuwa hajiyar ganin abinda yafaru yasa ta tattara yanata yanata tabar gidan gudun wani mummunan abu ya auko,aiko Akeela cikin tsananin rudu da damuwa tanufi gidansu tana kuka kaitsaye sasan Guggo Laure ta nufa,da tashin hankali Guggo Laure ta tareta tana kamata suka shiga daki,ananfa Akeela ta shirga ma Guggo Laure karya da gaskiya ita kuma tahau ta zauna, bala'i tafara zazzagawa,nan kuwa ta shirya ta nufi gidan Galadima,a dai-dai lokacin su kuma suka dawo daga hospital,da kuka Guggo Laure da taresu don su sam basu lura da ita bama,duk cikansu mamaki sukeyi,musamman Daddy da Baba Hasheem,kaitsaye Ammi ta tunkara tana nuna ta da yatsa tare da kumfar baki"Aisha baki isa ki yanke abinda Allah shi da kansa ya kulla ba,dama tunda akafara maganar auren Akeela da Sauban na lura da take n ki bakiso,taya za'ace tunda tazo gida kullum sai kinshiga gidan ta kin tayar mata da hankali?wai me ta tsare miki,kwanaki ma da tayi 6ari tace kece kika zuba mata abu a lemu tasha cikinta ya zub........bata karasa ba Baba Hashim ya katseta cikin 6acin rai,domin dai da alama yau Guggon nasu ta kure shi"Don Allah ya isa haka Guggo ya isa,ita shedaniyar jikan takice tafada miki wannan kanzon kuregen?wallahi da na kama yarinyar nan a gidan nan yau dukan mutuwa zan mata domin itadin annoba ce a cikin ahalinmu,ko makiyin mu bazamuyi fatan ya hada zuri'ah da me irin halayen yarinyar nan ba"cikin daga murya Galadima yace"Hasheem kana hauka ne? Guggon naka kake fadawa haka?gabadaya idon Baba Hashim ya juye da bala'i yace"Galadima kadena sauraren maganar Guggo,domin duk halin da Aisha tashiga Akeela ce sila,domin dai Akeela 'yar madigo CE!nan yashiga basu labarin abinda ke faruwa tundaga zuwan Zuhra da suman da tayi har zuwan su dasu Daddy da sumar da Ammi tayi,gabadaya Galadima, Bodejo, Guggo laure salati suka sanya Daddy na tayasu,cikin kuka Guggo Laure tace"Karya kukeyi hasheemu wallahi sharri kukeyi Allah ya isa tsakanina daku da yardan Allah sai Allah yasakama Akeela, Allah ya isa"tana fada tana kuka haka yafita tabar gidan. Taga Galadima yayi zai fadi,cikin sauri suka taresa,fadi yake nine Laure yau takema 'yayana Allah ya isa? innalillahi wa Inna ilaihirraji'un,gabadaya gida ya hargitse kamasa sukayi suka kaishi bedrooms dinsa suna masa fifita, Galadima kuwa sai maimaita magana guda daya yakeyi abinka da tsufa yafara riska,shekaru 82 ba wasa ba ai"Nine Laure kema yarana Allah ya isa?a ranar dai sai da jinin Galadima yahau, Sauban ma ammishi waya kan gobe zai iso, Abba ma haka. Gabadaya ahalin kwanan rashin dadi da natsuwa sukayi domin tsiya sosai Guggo Laure takeyi Alhaji mansir na tayata, Baba sani kuwa cewa yayi abari ayi bincike,nanfa Guggo Laure da Alhaji mansir suka dirar masa wai shima ya yarda da sharrin da akama Akeela. Da daddare kuwa Akeela ba gida ta kwana ba,can tatafi suka sake cin Karen su babu babbaka,domin gani takeyi yanda tahada wannan maganar komai zaizo da sauki. Washegari kuwa da wajen 1:30 babu abinda kakeji na tashi sai hayaniya gidan Galadima family wanda har yaja koke koke domin kuwa Guggo Laure ta dage kan wallahi muddin aka raba auren Akeela da Sauban itama ta rabu da Galadima bata bashi babu zuri'ar sa rabuwa kuma ta har abada,a'inda Bodejo itama ta rantse kan wallahi sai Sauban ya saki Akeela don bazasu zauna da annoba,Sauban idanuwan nan sunyi jajawur nan yashiga recalling din abubuwa da dama,sannan tabbas shima yasha zargin sa da haka,nan yashiga bayanin komai shima,sannan Ammi tasamu shedar tunda akayi bikin Sauban bata shiga sashin ba sai jiya,sosai rayuka suka 6aci hankula suka tashi,ita kuwa shedaniyar batasan meke wakana tana can suna madigon su,duk da a gefe guda na zuciyan ta tanajin bazata iya rabuwa da Sauban ba.Gida kuwa sai kuka da kuka domin Guggo Laure tace"anuna musu sheda na kama Akeela da akayi tana madigo"Bodejo tace"sheda ai Allah ne shaida kuma insha Allah sai Allah yatoni asirinta mudaije zuwa. Wata kalma da ya girgiza su ne yasa mutane biyu zuciyoyin su rawa lokaci guda wato Galadima da Guggo Laure domin kuwa a take anan Sauban yace"ni Muhammad Taleeb Muhammad nasaki matata Akeela saki daya,biyu.....baikarisa na ukun ba yaji wani gigitaccen mari,da hanzari yadago lokaci daya, Daddy ne ya maresa"Sauban ka gwammace ka yanke zumuncin 'yan uwa biyu?Ashe baka da hankai? Sauban yace"Daddy ko na cigaba da zama da Akeela babu aure domin zargin ta zan fara,kuma aure da zargi babu aure. Ihu Guggo Laure tasa kamar mahaukaciya tana fadar"Allah ya isa tsakanina da ahalinki Yaya Muhammadu bani bakai,insha Allah abinda kukamin sai Allah yayi muku"tana fadar hakan tabar gidan tana kuka, Alhaji mansir yabi bayanta. Atake anan Galadima ya yanke jiki yafadi,wanda yayi sanadiyar karkacewan mouth dinsa tashi daya. *_LALLAI WADANNAN AHALIN SUNA CIKIN CAKWALKWALIN TASHIN HANKALI,A GEFE GUDA GA ADDA ZAINAB WACCE BA'A MASAN INDA TAKEBA,KOMAIFA YA RINCA6E YA LALACE [7/9, 13:44] *_GALADIMA FAMILY_* Page:- 65/66 ____Hankulan su yayi kololuwan tashi a lokacin da sakamako yafito kan Galadima ya kamu da paralys daga 'yayan har jikokin hankulansu yayi kololuwan tashi,lokaci guda aka fara kokarin hadawa mishi Visa shida Daddy da Abba don zasu nufi Malaysia gidan Abbie nacan zasu sauka idan komai ya dai-dai ta,family kuwa sai kuka da kuka. Sauban yayi nadama matuka akan hukuncin da ya yanke domin Daddy lefinsa yake gani inda dashi kanshi ma yake ganin shine silar komai, Bodejo kuwa kuka take sosai cikin muryan kuka tace"Duk abinda ya samesa Laure ce sila babu ruwan saudan domin shidin ya kasance meson 'yar uwansa ne ganin su biyu kawai iyayen su suka haifa,sam baya son damuwan ta shiyasa yake mata abinda zai faranta mata duk da kuwa yasan halinta na rashin kirki amma haka yake shanye komai, Allah yasani wannan yarinyar ta cucemu. Basu tare da natsuwa, Taufeeq dasu ummie ma sun karaso,inda jibi zasu bi jirgin karfe 10:00. Duk an mayar da matan gidan mazan ne kawai suka kasance a asibitin da jikokin nasa,acan gida kuwa sai maida zancen akeyi, Mom nabawa Ummie da Mommy labarin duk abinda ya faru harda cin mutumcin da Guggo Laure tayi daya haddasa haka. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un wannan abu sam beyi dadi ba,mezesa son ya yanke hukunci cikin fushi?da anbari duk an shawo kan matsalar ko don yankewan zumuncin nasu"sai a sannan Ammi tayi magana"Wallahi kuwa Ummien yara yayanke hukunci cikin fushi,ni a tsarina Sauban bazai sake Akeela ba yabarta duniya ma ta isheta. Carab Mom tace"Ca6! Kazanta wallahi ko jini bazamu yarda muhada da 'yar madigo ba,wai Aunty Aisha kin mance illarsa ne?kin mance girman zunubin sa? Ai wannan abinda yayi shine dai-dai kuma beyi lefi ba da yake dai ita Guggo Laure a yanda na fahimce ta sam batason lefin wannan yarinyar,ni tun sanda nafara ganinta bata kwanta min ba bata burgeni ba yarinya ido a bude sai kace sandar snooker?ai gara da Allah ya tona mata asiri,ga matansa nan kawai asa tarewan su kowa ma ya huta"takarisa maganar tana nuna Zuhra wacce tayi tsuru dajin furucin Mommy na karshe. Mom tace"yanda kikajin nan Aunty Hauwa,ai mu munyi mummunan gani munshiga tashin hankali. "Nikaina a yanzu nafi bukatan asa kawai ranar tarewar su ko sati guda ma inda za'abi ta nawa kada ayi,shi kanshi ma ya samu natsuwa"Ummie tace. "Gaskiya ne idan aka gama wannan abin komai ya lafa sai ayi maganar"Ammi tafada,mikewa Zuhra tayi jikinta nayin bala'in sanyi don harga Allah ita tasan batajin san ya Sauban acikin ranta,zuciyar ta a dagule tashiga bedroom din Mashahuda nada inda tattada ta tana kwance tare dasu Laila da Nihal,da yake tanata fama da laulayin ciki shiyasa,kwalla ne ya taru mata a ido tanajin damuwa lokaci guda ya dirar mata. Muneefa ce ta shigo da 'yar dariyar ta tace"Amaryan mu gaskiya ya kamata ayi shagalin biki kafin ki tare, Mashahuda ta mike ta zauna itama dariyar take tace"anyi maganar tarewar ne? Muneefa tace"maganar dasu mommy suke kenan a palour"wani ihu Nihal da Laila suka sanya,cikin tsokana Nihal tace"ai wallahi kuwa gara kitare Yaya ya tafi dake can Canada kikarasa karatunki, Mashahuda tace"Ai banjin zai iya tafiya da ita yanzu kila nan zata fara zama"hawayen da take makalewa ne ya samu daman gangarowa,kamota Muneefa tayi ta zaunar da ita kan gadon tace"a'ah menene kuma abin kukan yanzu daga magana?dagowa Zuhra tayi cikin muryan kuka tace"Bazaku gane bane,ni ni bana son sa Allah yasani don Allah kusa baki yasakeni.....bata karisa taji Mashahuda ta buge mata baki,cikin 6acin rai tafara magana"kinada hankali kuwa Zuhra?kinsan abinda kike fada?to tun wuri kishiga taitayin ki domin wallahi idan su Abba sukaji kalmar nan daga bakin ki sai na lahira yafiki jin dadi,ke bama su ba ya Taufeeq naji sai kinsha mamaki,'yan mata nawa ne ke neman irin damar ki basu samu ba?kinsan yanda 'yan mata ke rushing kan Yaya?to wallahi kisan maganar da zaki na furtawa gudun kada ya koma kunnensu da Daddy, Muneefa tace"Hmmm Zuhra kenan duk wannan abin da kikeyi yarinta da wauta ne kawai yake damunki,Amma I know ko badade ko bajima keda kanki zakiyi alfahari da samun ya Sauban matsayin miji,don koni naso shi amma nasan ba lalai yasoni ba,gashi Allah yamin canji damafi alheri. Duk shiru dakin ya dauka banda shesshekan kukan Zuhra babu abinda ke tashi, Laila tace"Allah ya ganar dake,kuma ko mutum naso ko baiso dole ya tare"tayi maganar tana sakin ma Zuhra gwalo tare da ficewa da gudu tana dariya,kokarin binta Zuhra keyi tana karama kukan ta volume. Dayake asibitin su Dr Ahmad akwai kula don asibiti ne me masifar tsada nurse's ke kula da mutum,wannan dalilin yasa karfe 10 su Daddy duk suka baro asibitin. Taufeeq da Sauban apartment din Ummie suka wuce, Zuhra ce zaune a parloun kasa tana cin abinci,don Ummie tashiga ciki watsa ruwa,sallamar su ce yasata dagowa tana amsawa idanunsa akanta duk da yacce face dinsa yake a tamke hakan behanashi kashe ta dana mujiya ba kamar wacce ta masa lefi,cikin tsananin farin cikin ganin Taufeeq tataso tare da hugging dinsa"Yaya ur welcome,shafa kanta Taufeeq yayi yace"thank you little,hope kina lafiya? Zuhra tace"fine Yaya I think ma nafika cikakkiyar lafiya",dariya suka sanya itadashi,shikuwa Sauban remote ya dauka ya kunna Ball,wanda yau akwai wasa 10:30 tsakanin
Chapter 42 · 0% Book details