← Book details Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 64

Sashe 4

Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nasanku ku maza shiyasa tun yanzu ma nake gaggawan taka maka birki kada naji ko nagani Koda kuwa andace ne. "Shikenan sweetheart hakama sam bazai faru ba gobe nakeso naje gidan Aunty falmata. Ammi tace"Allah yakaimu!da ameen Sauban ya amsa nan suka cigaba da hirarsu. Washegari da safe wajejen goma saura sai ga Guggo Laure itada Akeela,tsayawa nayi naqare mata kallo tasss,kyakkyawa ce sai dai ko kusa bata kamo kafar yaran gidan ba duk da cewa a ciki akwai qalilan da tafi kyau,sanye take da lutfaya baki mai ratsin jan flowers sai kafanta sanye da halfcover ja,hannunta riqe da handbag shima ja fara ce tass wanda a farin ma akedan karawa da man bleaching daga gani zatayi sa'a dasu mashahuda. Baba mansir mahaifin Akeela shine Guggo Laure tasa ya kawo su don baisamu shigowa gidan bane saboda ana jiransa ujila. Kaitsaye bangaren su bodejo suka nufa, Akeela kuwa tamkar bazata take kasa ba,Koda suka shiga sun cidda bodejo da Galadima,bodejo tana hada masa brabusko da miyar kuka Wanda yaji nama zallan tsoka daga bangaren Daddy aka kawo. "Assalamu alaikum!ga bakin sassafe fa. Guggo Laure tana fada fuskanta dauke da tsananin fari'ah saboda ganin motocin yaran gidan da alamu ma basu fitaba hakan ne yasata sake fari'arta. Galadima yace"Laure!kece a gidan?lallai jiki yayi sauqi sosai tunda gashi kin iya fitowa yayi maganar fuskansa kadaran kadahan. A inda Akeela take tsaye ta gaishesu ko rissinawa babu qiqam ta gaidasu. Cike da mamaki su bodejo ke duban ta, Galadima yace"ke haka akace miki mata na gaida mijinta?duqawa akeyi har qasa bawai atsaya a tsaye kerere ba kinji? Akeela ta wayance ta hanyar cewa"toh ai saboda bana auren tsoho irinka yasa na gaisheka a haka saboda kada tsohuwar matanka ta huramin hanci. Bodejo kuwa Sarai ta ganeta sai cewa tayi"to ai tunda kikama wannan angon haka babu irin angon da bazakiyi wa ba. Guggo Laure tace"musake gaisawa kundawo lafiya?ya gajiya Yaya bodejo? Bodejo tace"ai gajiya tabi jiki Laure Kuma marasa lafiya kun fito balle kumamu? Guggo Laure tace"wallahi fah kedai Bari jiya najuya yafi sau nawa? narasa gabadaya abinda kemun dadi a gidan duniya naqosa gari ya waye nazo saboda nace da zafi zafi ake bugun karfe shiyasa,tadubi Galadima tace"kada dai agaji dani akan kokari na nason aikata alkhairi. "Maganace dai akan yaran nan Akeela da Sauban shiyasa ma nace Akeelar tashirya tazo muje ayi komai a gabanta. "Shima kuma Sauban din ayi komai a gabansa. Cike da mamaki duk suke duban ta. Galadima kuwa abin duniya ne ma ya isheshi yayi dan murmushi irin nasu na manya yace"Laure kenan kekam akwaiki da wutan ciki, gashi yaran ba dukansu ne suke nan ba don shi sadeeq yau ya koma kaduna,shikuma Hasheem yaje ta'aziyyar amininshi da yarasu. Guggo Laure tace"toh nidai Yaya hakanan za'ayi hakuri ayi maganar nan yau a wuce wajen. "Yarinyar nan tana tsananin son Sauban,duk cikin jikoki na babu mafi soyuwa agareni kamar Akeela. Galadima yace"toh shikenan bari nakira taleeb din,hannunsa yakai gefen lumtsememen leaderseat dinda yake zauna yadakko wayarsa kirar sumsung yafara nemo number,baiwani dau lokaci ba yakira har takatse ba'a daga ba,ko kafin yasake danna kiran,Kira yashigo wayan nasa. Dauka yayi tare da sallama,daga can bangaren Daddy yagaishe shi,amsawa yayi kaitsaye yace"inason ganinku kai da Aliyu idan anyi sallar azahar,daga can bangaren aka amsa da toh insha Allah,sannan Galadima yakatse wayan. Guggo Laure kuwa murna takeyi kamar yakasheta,dakin da take sauka wanda aka mata nan tanufa harzata shiga sai Kuma tajuyo tace"ke Akeela zo muje mugaisa da matan gidan tukuna koh? Akeela kuwa farin ciki takeyi kamar anmata kyautan hajji,aranta kuwa fadi take itace zata mallaki Sauban jinin GALADIMA FAMILY?tabbas tayi sa'a,don Sauban namiji ne wanda da dama mata ke bibiyan sa,don ko a yanar gizo maganar sa mata keyi namiji ne mai tsadan gaske. Kai tsaye apartment and Ammi Guggo Laure tashiga,sallama tayi itama Akeela tayi cike da kissa. Su mashahuda ne a farlon,hada idon da muneefa zatayi aiko tamike da gudu tanufi Akeela tace"Kai lallai ma Akeela yau kece a gidannan haka? Akeela ta watsa idanuwa tace"aiko gani ai muneefa bakida kirki ko Guggo bakizuwa gaishewa. Mashahuda ta dubi Guggo cike da mutumtawa ta gaisheta,inda kallo daya tama Akeela ta watsar don sam ita Akeela bata burgers barin yanda take ganin tanasa pic dinta a Instagram na shirme. Muneefa tace"Tabb yaushe zaki ganmu so kike ya Sauban ya babballamu?dariya sukayi. Kujera Guggo Laure tazauna, Akeela da muneefa kuwa daki suka shige inda mashahuda tashiga kitchen don kiran Ammi,Ammi bata zama duk da masu aiki suke aiki Amma girkin mijinta ita takeyi tunda yanada suger,masu aiki kuma suyi na gida gabadaya ko da ita bata dauki wata mai aiki tayiwa mijinta girki ba. Mashahuda bajima ba tafito kitchen hannunta dauke da tray inda ruwa kekai da lemo. Ammi ce tafito fuskanta dauke da murmushi tace"Guggo ce a gidan? Guggo ta amsa fuskar ta dai kadaran kadahan tace"yauwa sannu Aisha nice. Ammi tace"inayini Guggo,kunzo lafiya? Guggo Laure tace"lafiya lou,munsameku lafiya? Ammi tace"lafiya ALHAMDULILLAH ya karfin jiki?jiya zamuzo da Rabi sai mazan sukaci mubari suje mu mazo yau Ashe jikin ma yayi sauqi? Guggo tace"jiki Alhamdulillah sai dai tasowar na dole nayi saboda mahimmiyar maganar dake tafe dani. Ammi tace"Allah sarki sannu da zuwa. "Yawwa Aisha,inasu Yaya na muhammadu? Murmushi Ammi tayi tace"Sauban yana dakinsa anata shirye n tafiya Malaysia. Guggo cike dason jin Karin bayani tace"mekuma zaije yi can? Mumushi ammi tayi tace"zaije interview ne idan da rabon yasamu aiki a wani company a can ne toh. Cike da farin ciki har zuciyar Guggo Laure ta yashe baki tace"Alhamdulillah Allah mungode maka,a zuciya Guggo Laure tace"(ya ubangiji Allah yakai damu ga harawa,lallai Akeela duniya sabuwa,duniya nakine.) Allah yabada sa'a ubangiji yadorashi bisa kawunansu. Da Ameen Ammi ta amsa. Nan Guggo tamike tamata sallama kai tsaye sasan Mom tanufa. Mom taji dadin ganin Guggo don ko babu komai da mijin Guggo da baban Mom uwa daya uban daya,anan suka gaisa Guggo tace"gaskiya Rabi bakida kirki yanzu kiri dan naman nan ma kindena aikomin dashi sai dai kikaiwa hajiya habi?haka amana yace? Dama ana saka alheri da mugunta?a fakaice mom ta watsama Guggo Laure harara,a zabiri kuwa dan marairaice fuska tayi tace"toh yazanyi Guggo?kiri baban Aseef ba siyowa yakeyi ba sai lokaci zuwa lokaci,nima kaina baya isata balle nabaiwa wani. Guggo Laure ta kama baki tace"Oh a haka Hasheem sumumi sumumi Amma duk Wanda yaganku yaganku cikin hutu don ke tunda kika shugo cikin a halinmu zaka sheda. Mom tayi dariya tace"gaskiya ne Guggo,amma bajiya akace bakijin dadi ba? Guggo Laure tace"hmmm aikedai bari ai tafiyar nan ta dole nakeyinta,nan Guggo Laure tazauna tabawa Mom labarin duk wani qudurinta kaf nason hada auren Sauban da Akeela. Kirjin Mom ne yayi wani irin mummunan bugawa hankalinta yayi qololuwan tashi,a diririce Mom tace"Guggo wani Sauban din? Harara Guggo Laure ta maka mata tace"Sauban nawa ne a gidannan?to dan uwanta mana nake nufi. Guggo tace"Bari naje rabi yanzu zakiji ankira azahar. Gabadaya har Guggo Laure tagama maganarta tabar farlon Mom bataji ba sai da taji karar rufe kofa tajuyo a hautsine. Mikewa tayi cikin gigita da rudewa tace"Inah? Sauban da Akeela?wallahi bazai yuwuba bazan taba bari Sauban ya auri Akeela ba. Duk irin son da Rammat takeyi masa ana nufin zaitashi abanza ne?wallahi bazai yuwu ba,qanwata Ina ganin yanda takeson Sauban kamar zata rasa ransa,Rana tsaka azo da maganar wata shegiya Akeela?wallahi bazai yuwu ba,Ina wayata? Tayi maganar tare da nufan hanyar wani corridor cikin gigita. _TIRQASHI ANA WATA GA WATA._ _MEKE SHIRIN FARUWA NE?ME MOM TAKE NUFI?DUK WANNAN ABINDA AKEYI SHI ME GAYYA ME AIKIN MA BESAN ANAYI BA,KUDAI KU KASANCE DA ALQALAMIN Xahratty Ce Lallai Alqalami yafi takobi 12/2/2023. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): *_GALADIMA FAMILY_* Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 05 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ _______A tsananin rikice mom take shiyasa koda tashiga cikin bedroom dinta sam hankalin ta baikai wajen phone nata ba,fita tayi daga bedroom din tanufi wani corridor wanda kaitsaye ya sadata da parlon Abba,neman wayar tashiga yi sai dai duk iya neman da tayi bata gani ba ( _Nikoh nace su hajiya mom manya tsaban rudewa a bedroom dinki kika bar wayan _ ). Dan siririn tsaki taja tare da fita tanufi bedroom dinta dai,gabadaya ta hargitsa dakin bata gani ba,banda numfarfashi babu abinda takeyi cikin sa'a kuwa idanuwanta suka sauka akan bedside drower dinta,sake watso idanuwa tayi cike da tsananin mamaki,mikewa tayi ta dakko wayar tare da komawa tazauna a bakin gadon hannunta har rawa yakeyi wajen dialing number Rammat,ganin andauka ne yasa Mom kara wayar a kunne bakinta na rawa tace"Hello Rammat kina jina ne?kina gida? Daga can bangaren akace Eah, Mom ta cigaba da cewa"kiyi maza maza kizo inason ganinki yanzu fah,still dai da toh aka amsa mata. Katse kirar tayi inda tafara safa da marwa a cikin dakin. A bangaren su Guggo Laure kuwa bayan sallar azahar duk suka hallara a parlon na Galadima, Galadima,bodejo, Daddy,baba hasheem. Guggo Laure tace"Yaya ayi maganar da za'ayi don Allah saboda nisam bansan sharrin shedanu. Dan murmushi Galadima yayi yace"Laure kenan bari akira yaran duk aji ta bakunan su. Duban Daddy yayi yace"taleeb lalubomin Sauban a wayarsa daganan kace masa su taho da mashahuda.Da toh Daddy ya amsa sannan yafara neman Sauban a wayarsa. Cikin kankanin lokaci kuwa ya dauka inda Daddy yasanar masa da saqon Galadima. Ba'a dau lokaci ba yayi sallama mashahuda na biye da ita,duqawa sukayi cike da mutumtawa suna sake gaishesu,nan Baba Hasheem yadubi mashahuda yace"takira masa Akeela daganan tawuce,amsawa tayi da toh tare da miqewa. Basu wani jima ba itama tashigo sai wani sake karairaya take tamkar iccen da yake gaf da karyewa,samun gefen kafar Guggo Laure tayi ta zauna sannan tafara gaida su Daddy. Gyaran murya Galadima yayi yafara magana. "Toh Alhamdulillah Muhammad wannan taron da akayi akanku kune kai da kanwar ka Akeela gatanan!yayi maganar yana pointing din Akeela,yaci gaba"Toh 'yar uwata Kuma kanwata kakanka Laure gatanan tanaso musake danqon zumuncin mu ta hanyar hada auratayya tsakaninka da Akeela. Da sauri Sauban yadago tare da duban Galadima. "Ita kuma yarinya tana sonka shine nace kaima munason muji ta bakinka kana sonta kokuwa? Sauban mutum ne wanda sam baida boye kaitsaye yake magana don watarana
Chapter 4 · 0% Book details