Sashe 13
Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Aunty nifa bansan shiba bansan koshi wanene ba akan me zan fitan masa?shiyasa ma ban fitaba,takarisa maganar tana dan babbata fuska. Itama Mashahudan bata fuska tayi tace"Lallai ma yarinyar nan kinci uwar rainin wayo to Shuraim ne yazo kitashi kuje ku gaisa mana. "Shuraim! Zuhra ta maimaita sunan alamun bata ganesa ba tace"Aunty ni bansanshi ba. Mikewa Mashahuda tayi tare da fita tace"idan kinje wajen ai zaki gane wanda nake nufi,takarisa mgnr tana barin dakin. Tsuru tayi tana bin kofan da kallo tadau kusan 6 minute's a zaune kamar wacce aka dasa,zuwa can tasauke ajiyar zuciya tare da mikewa,closet din ta tabude taciro wata Dubai gown mai taushi wanda yaji wasu irin flower's maroon colour,sannan tasaka viel din tayane kanta dashi,flat shoe baqi tasaka batare da tamurza ma kyakkyawan face dinta komai ba tafito parlon, Bodejo ta taras a zaune tana kallon Africa TV 3 dan sunkuyar dakai tayi like munafuka sum sum tafice. Cikin sanyin jiki take tafiya kamar mejin tausayin kasa acan gefen apartment din Ammi ta hango Mashahuda da wani don bata ganesa ba saboda ya juya mata baya,a hankali take tafiyar har ta isa inda suke zaune,sallama tayi cikin zazzaqar muryanta mai sanyi da dadi,da sauri yadago don jin muryanta. Da mamaki Zuhra take dubansa a hankali tace"Yaya dama kaine? murmushi kwance akan fuskar Shuraim yace"Ea nine Zuhra. Dan tsamm tayi tare da duban Mashahuda,mikewa Mashahuda tayi tare da duban Shuraim tace"bari nashiga na fito kafin ku gama gaisawa,sake fadada fara'a Shuraim yayi tare da cewa"Allah yafito dake lafiya Auntymmu,zuhr kuwa sakato tayi tana duban Mashahuda har tashiga parlon su,ajiyan zuciya ta sauke saboda muryan Shuraim da taji yana cemata ta zauna. Karasawa tayi kujeran da Mashahuda ta tashi ta zauna,dukar da kanta tayi kasa tafara wasa da yatsun hannunta. "Babu gaisawa ne Zuhra?Shuraim yace. Cike dajin nauyi da kunya cikin sanyin muryanta tace"eyya ba haka bane wallahi yaya don Allah kayahakuri, inayini? "Sai dana roka?yayi maganar still murmushi kwance saman fuskansa. "Kayahakuri,tasake maimaitawa cikin sanyin muryanta. "Lafiya lau Alhamdulillah ya kwana biyu? "Lafiya lau wallahi. "Ashe anata shirye-shiryen school ne?to Allah yabada sa'a Aunty Mashahuda take fadamun. Zuhra tace"Ea anata shiri munkusa fara zuwa school tafada cike da murna da zumudi murmushi kwance saman fuskanta,daidai nan Baba mudi yafara wangale gate,hancin mota ne ta shigo kirar Corolla ( _da take bansan kan motoci ba amma motar daga gani medan tsada ce._ ) duk cikansu maida dubansu sukayi kan motar,shikuwa tun sanda yashigo gidan idanuwan sa ke kafe a inda suke zaune,sosai yaji zafin ganinta da wani,balle murfin motar yayi ya fito,dole idan zai shiga apartment din Ammi ta gabansu zai wuce,koda yakariso fuskar sa a sake yake dubansu,mikawa Shuraim hannu yayi sukayi musabaha tare da cewa"Barka da warhaka.Duk da cewa ya girmi Shuraim din sosai ma don Shuraim ai sa'an kaninsa ne na biyu kuma akwai tazarar shekaru tsakanin su. Duban Zuhra yayi face dinnan cike da fara'a yace"kanwar mu bako akayi ne haka?dan rissinar da kai tayi tace"sannu da zuwa ya Kareem,cikin fara'a yace"yawwa mun sameku lafiya?ya shirye-shiryen school Kuma? Zuhra tace"Alhamd ulillah. "To Allah yabada sa'a! A takaice ya fada. Da Ameen duk suka amsa. Wucewa yayi. Duban Zuhra Shuraim yayi yace"Ina me neman gafarar ki akan maganar da nazo miki dashi bansani ba dai ko zaki iya amincewa dashi? Zuhra tace"me kenan ya Shuraim? "Idan babu komai inaso kibani wani matsayi da wajen zama a jerin masu kula dake,cikin rashin fahimta take dubansa. Gane bata fahimci abinda yake nufi ba yasa yace"kibani matsayi na yayanki muzama Yaya da qanwa nidake don Allah. Murmushi tayi tace"Kai Ya Shuraim nina dauka wata magana ce,haba ai babu komai nabaka wannan matsayin Yaya. "Masha Allah kanwata godiya nake Allah yasaka da alkhairi. "Ai babu komai Yaya ta fada cikin sanyin murya,nan suka cigaba da hirarsu don Zuhra sosai ta sake da Shuraim. ** *MALAYSIA* ** Yauma kamar kullum shirinsa yayi yafito cikin suit blue black,takalminsa kamfanin Gucci ne dai cover shoe black colour sai agogon hannunsa Rolex,Kai tsaye driver yaje yabude masa back seat yashige shikuma yaja motar, gaisheshi gateman yayi sannan suka fice, laptop dinsa yafara daddanawa yana duba saqonni ta email daga wasu kasashe da dama nason takalman company nasu, wayar sace tafara neman agaji. Sai da yadau lokaci yana ringing kafin yakai hanny yadau wayar,sunan Kareem ne ya bayyana akan screen din,cikin kamewa ya dauki wayan batare da yayi magana ba,sallama Kareem yayi. Amsawa Sauban yayi nan suka fara gaisawa inda Kareem keta masa shikiyanci zuwa can yace"yawwa dama kira nayi na sanar dakai wani abu don kaine babban Yaya, kuma babban wa uba. "Malam katafi maganar ka kaitsaye, yafada cikin kamewa. "Dama akan kanwar ka nakira muyi magana don naga iri ina nema don alamu sun nuna idan banyi da gaske ba za'a mun shigo ba zurfi,kai nifa idan na so samune ma a hada bikin mu tare. "Akan wa kake magana kenan? Sauban yayi maganar wanda ko driver din ba lallai yaji abinda yake cewa ba. Kareem yace"Akan zuhra mana nake magana gaskiya ni nagani inaso asan yanda za'ayi dani dazu na ganta da wani karamin yaro sa'an kabeer dinmu ne ma dagani wannan yaron wai yazo zance,so please ga dan gida nan. Lumshe idanuwana Sauban yayi tare da kwantar dakai dakai a jikin seat din motar wanda duk kwakwanka bazaka gane yanayin da yake ciki ba yace"menene haka Kareem?so kake ka zubar mana da mutumci yarinya karama tanemi ta raina mu?look gaskiya kada ma kafara wannan tunanin,guda nawa take wannan yarinyar neman zubda mana da mutumci gaskiya ban goyon bayanka",yayi maganar cikin kwanciyar hankali. Daga can bangaren Kareem kuwa baki da hanci yasaki yana sauraran Sauban sai da yabari yakai aya sannan yace"Nikam Sauban gaskiya bazan iya da wadannan halayyan naka ba menene aciki? "Komaima! Sauban yafada a takaice,a zafafe ya kuma cewa"inbanda jawo raini ina kai ina kula wannan kwailar yarinyar?yana gama fadar haka ya yanke kirar. Cigaba da danne dannensa yake a laptop din wanda sam baka isa ka karanci yanayinsa ba. Ta bangaren Kareem kuwa mamaki sosai ya gama rufeshi da halayyan aminin nasa shisam yafiye son girma da rashin son raini. ( _A daiji maganar babban Yaya Kareem don shine madaurin auren zuhra._ ) A haka suka isa babban company wanda gabadaya ma aikatan wajen sai girma suke bashi. **** *KADUNA JABI ROAD* Ummie ce zaune akan lumtsememen leaderseat din dake parlon ta kafa daya kan daya tana duban tashar aljazeera, Abbie ne yayi sallama tare da shigowa a hankali tadago tadubesa dan murmushi tayi tace"Sannu da zuwa yallabai. Murmushi Abbie yayi cike da zolaya yace"Yauwa yallabiya,zama yayi kusa da ita da yake cushion din two seater ne cike da gajiya yace"Am tired Madam. Dan dariya tayi tace"Toh bari naje na hada maka ruwa kayi wanka zakaji dan dama then sai kaci abinci kadan kwanta stressed ne kwana biyu baka zauna ba yallabai gashi jibi zaka tafi Indonesia. "Wallahi kuwa akan furnitures din su Mashahuda nakeso naje kinsan bikinsu 6 month akasa su ita da muneefa, shiyasa ma nakeso muje tare nida ke mu zabo musu kaya masu kyau,harda kayan kitchen. Ummie tace"iyye lallai Abbien yara ya shirya to shikenan Allah ya kaimu amma bazamu kawo komai gida yanzu ba ko? Abbie yace"to me za'a tsaya jira Bilkisou ai gwanda a kawo komai nasan kilama kayan su rigamu isowa. Kafin kuma na auta na yazo Allah yanuna min auren ta. Da Ameen Ummie ta amsa a maqoshi. Dan girgiza kai Abbie yayi yace"Bilkisou kenan Allah ya karkato da hankalin ki kan diyar ki. Cike da kwarin gwiwa Ummie ta amsa da Ameen,da mamaki sosai Abbie yadube ta saboda jin ta amsa cike da confidence. Ummie ta dubeshi murmushi kwance a fuskanta mai Kama da yaqe tace"kana mamaki koh?hmmm nima inason Zuhra sai dai tsanar da nake mata ya ninka son da nake mata,ina tsananin jin tausayin ta amma ya zanyi narasa meke damuna,takarisa maganar cikin raunin murya. "Huhhhh!Abbie yasauke ajiyar zuciya yana dubanta,zuwa can yace"Bilkisou bana fatan zagin da yakeyi yazama gaskiya. Cikin rashin fahimta Ummie ke dubansa. "Ea ina zargi,alamu suna nuna kamar akwai sihiri tsakanin ki da Zuhra. "Koh? Ummie tayi tambayar. "Kwarai da gaske, bilkisou inaso kisani bana fatan na mutu banga kin daidaita da Zuhra ba. Sosai gaban Ummie ya buga hankalinta yayi kololuwan tashi. ( _Duk da kin kasance Mai biyayya akan wannan abin kinkasa wa mahaifinki biyayyaaaaa._ _To bari kiji wallahi wallahi Ina sake jaddada miki muddin baki shiga hankalinki ba Bilkisou bazan taba yafemiki ba._ ) Kalaman Amma ne suka fara dawo mata a kwakwanta hankalin ta yasake tsananin tashi duban Abbie tayi idanuwan sa a rufe tace"Don Allah kadena fadamin haka kana tayar min da hankali na insha Allahu everything will be fine. Mikewa yayi jikinsa sam babu kuzari yanufi stairs,hawaye ne masu dumi suka tsiyayo ma Ummie. *_ADDU'AN DAI SHINAKE BUKATA NAGODE SOSAI MASOYA DA WADANDA SUKA KIRA DAMA WADANDA BASU KIRANI BA SON SO FISABILILLAH Happy birthday to you my rabin jiki baby Yusuf ( l) Allah yaraya ka ya shiryaka yabaka ilimi Mai amfani da albarka ubangiji Allah ya albarkaci rayuwar ka Yusuf Imran Muhammad bature Xahratty CE Lallai Alqalami yafi takobi 07/3/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): *_GALADIMA FAMILY_* Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 17-18 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ ______A kwana a tashi babu wuya after 1 month da satittika gashi zuhra jibi zata fara zuwa school(UNIMAID) sosai take jin dadi da annashuwa gashi gefe guda kuma suna tsananin mutumci ita da Shuraim da yake shi mutum ne mai barkwanci sosai duk da haka ZUHRA takasa sakemai ssai. A bangaren Kareem kuwa hakan ba karamin sosa mai rai yake ba don yanason ZUHRA tun randa yayi tozali da ita suna zaune da Shuraim yaji yana tsananin kaunar ta,wannan kenan! "Hajiya kefa kika ce zakiyi wani abu gashi wasa anci 2months da saka ranar auren su yanzu saura fa 6 months, Rammat tayi maganar tana latso hawayen da suke gangaro mata. Itakuwa banda girgiza kafa hajiya Biba babu abinda takeyi, Mom tadan mere baki tana duban Hjy Biba"Ni kam hajiya anya aikin malamin nan naki kuwa yanay........ "Ke...k..kke ke...keke kul! Meye haka rabi nema kike kidebomin tafasashen ruwa