Sashe 8
Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a layin,a hankali yarage speed din motar,idanuwansa ne yafara sauka akan na wannan saurayin dayake wani irin murmushi,da sauri yaduba don ganin wanda yake ma murmushin,nandanan yaji kirjinsa yabuga ransa yayi kololuwan baci yamaida dubansa ga Mashahuda wacce take ta murnushi. Kara speed din motar yayi gefen su yafaka motar yaballe murfin motar yafito,daga Zuhra har Mashahuda gwalo idanuwa sukayi waje,ai kamar hadin baki su biyun da sassarfa duka shige cikin gate din. Da mamaki Shuraim yadubi inda yaga sun kalla har yasasu wannan razanar sai dai abin mamaki baiga kowa ba awajen. Abinda Shuraim baisani ba kuwa shine koda Sauban yafito daga motan ko kallon inda suke beyi ba ya shige cikin masjid din,amma su da take sun ganshi shine fah. Yadade sosai a bakin gate din daga karshe yashiga motan ya gyara parking din agefe yanufi masjid din yayi alwala yashiga ciki. Su kuwa daga Mashahuda har zuhra kowacce takanta tayi don kaitsaye apartment din bodejo zuhra tashige,koda tashigo bodejo bataji shigowanta ba tana kitchen itada nana mai aikinta itama dattijuwa ce suna abincinsu ita da Galadima don suna da diabetes. Shiyasa bataji shigowar zuhran ba,can bedroom dinta tashige tare da sanya key tafada kan bed tana dafe kirji,gabanta banda dukan uku uku babu abinda yakeyi,tadade anan kwance zuwa can tamike tashiga toilet don dauro alwala. Bata jimaba tafito koda tafito kunna dum light tayi ta shimfida praymat ta tada sallah. Koda ta idar zama tayi har akakira sallahn isha'i tayi sanna tabude bedside drower dinta tafito da cake da doughnut wanda mommy tamata kafin su koma,cake uku ta dauka doughnut biyo,tabude dan fridge dinda ke cikin dakin ta dauko lemon mountain dew. Kan bed din takoma tahau tare da dauko phone dinta tashiga tiktok,da videon wannan yarinyar da ta shahara a duniyar tiktok tafara cin karo,wato Aakeelah Mancy don tashi take amfani,bude videon zuhra tayi nan taciddata taci kitson attached,tana sanye da riga da wando murna takeyi tayi tanama fans dinta albishir din cewa ankusa samata rana,sai ihu da tsalle take . Dan siririn tsaki zuhra taja kasa kasa a ranta tace"Kai wannan yarinyar ta cika rawar kan tsiya. Bodejo kuwa sai da sunacin abinci hankalinta yadawo jikinta cewa su Zuhra fa basu dawo ba tun wajen biyar da suka fita,dai dai Sauban yayi sallama. Galadima da bodejo suka amsa masa idanuwansu na kansa cike da tsantsar soyayyan sa a zuciyoyinsu, cike da zolaya yace"Don Allah tsofaffin nan kada kucinye ni batare da nima naga 'yayana da jikoki na ba,ku gwara daku don da alama har tattaba kune zaku gani. Dariya suka sanya bodejo tace"Ungo nan,tayi maganar tana aika masa da daquwa,murmushi yayi tare da jan kujerar Galadima ya zauna,bude warmer din yayi yazuba lafiyayyen dambun accan Wanda yaji kayan ciki tare da vegetables. Duban shi Galadima yayi yace"ai shiyasa kaji muka damu dakayi auren kaima shiyasa muka zaba maka mata. Dan hade face yayi yana Kai lomar dambun bakinsa. Murmushi kawai Galadima yayi yana girgiza kansa don tabbas yasan cewa Sauban biyayya kawai yake kokarin yimusu amma batare da yanason yarinyar ba. Galadima yace"munyi magana da mahaifinka kan zasuje gidan Laure wajen Sani a tsaida ranar aurenku....cikin sauri Sauban yadago tare da sauke ajiyar zuciya. Dan yatsine face yayi cike da aji da natsuwa don kowata macen albarka yadubi Galadima yace"please Galadima kada asa ranar nan kusa nida so samune ma asa nan da two year's. Wani kallo Galadima yayi masa irin na yhu re not serious dinnnan,budejo kuwa dariya tayi. Sauban yace"bakace komai ba Galadima. Galadima yace"kabari anjima sai kaje wajen mahaifinka ka tuntubeshi abinda yace shikenan. Wani wawan ajiyar zuciya Sauban ya sauke yace"ai idan nayi magana kamar nayi rashin kunya ne inhar nayari Daddy da zancen. Murmushi Galadima yakuma saukewa a karo nabiyu yasake cewa"Kaje kasamu Hasheem kayi maganar dashi. "Huhhhhhh wannan tsohon sam bazai ganeba, Sauban yafada a ransa yana share gumin dake keto masa duk da kuwa AC dake a wajen. Koda suka kammala cin abincin mikewa Sauban yayi yamusu sai da safe, bodejo tace"kabiya sashin Aisha katuromin Zuhra. "Hmmmm kawai Sauban yace yafita kai tsaye apartment din Ammi yanufa,da 'yar siririyar muryansa yashiga parlon da sallama,babu kowa sai Mashahuda tana waya,ganin shi yasa takatse wayar tafara tsilla-tsilla da idanuwa,sake hade face yayi don yana sane dasu. "Ke ina yarinyar nan?sosai Mashahuda cikin rudewa tace"Tatafi apartment din bodejo,don tagani wanda yake nufi. Harara ya zabga mata tare dayin kwafa yace"zanyi maganin ki soon,yana gama fadar haka yanufi corrridor dinda zai sadashi da parlon Daddy don yasan Ammi nacan. *******^^^^^^^****** Cikin muryan kuka take magana"wallahi hajiya ina sonshi nidai gaskiya ayi duk yanda za'ayi aga wannan auren baiyuwu ba tsakanin shi da wannan yarinyar,don ni natsaneta kodan fans dinda takedashi a tiktok. Wacce aka kira da hajiya na duba sai karkade kafa takeyi,face dinta murmushi kwance daga ganinta kasan idanuwan ta kyar suke. "Haba Rammat to meye kuma abin kuka?nimafa inaso ki aure Sauban don yanzu shine tauraron sa ke haskawa, Mom tayi maganar tana dafa kafadar Rammat. "Hajiya gaskiya duk yanda za'ayi ayi don ganin Rammat tashigo cikin GALADIMA FAMILY,yanda kika shiga kika fita harnima nashiga to itama tashiga,kinsan kuwa nan da 1week Sauban zai koma Malaysia akan sun daukeshi aiki,Mom tayi maganar. Ai dasauri wacce suka Kira da hajiya tadubi Mom tace"Wai Rabi dagaske kikeyi?kinfasan burina baiwuce Koda yaushe ku aure manyan mutane ba kushiga dangina dana ubanku ana girmamaku,tuntuni nayiwa Rammat sha'awar auren yaron nan,Ashe makirar Laure tarigani hada nata tuggun?hmmm nasan Laure farin sani sai dai ita batasanni ba batasan koni wacece ba,amma muje zuwa a sannu zanyi maganinta. Ki kwantar da hankalinki Rammat,insha Allahu sai kin aure yaron nan Koda kuwa zakiyi kishi da wancan kodaddiyar yarinyar ne,tuni zamuyi waje da ita bayan auren. Rammat tace"A'ah hajiya ni gaskiya bazan iya zama da wannan munanan yarinyar ba,natsaneta. Mom tace"muma bamu fata insha Allahu bazakiyi zaman kishi da ita ba aikinfi karfinta wallahi. Hajiya tace"hmmm ku yarane bazaku gane me nake nufi ba amma a hankali zanyi muku bayani, Rammat ki kwantar da hankalinki indai Sauban ne kisa aranki kinsame ahi kingama. Dariya Rammat da Mom suka sanya cike da farin ciki. _TAB CAKWALKWALIN CAKWAKIYA KENAN SAUBAN KAIKAM KAGA TAKANKA_ _YANZU FA WASAN ZAIFARA KUDAI KUCIGABA DABIN ALQALAMIN OUM Xahratty CE Lallai Alqalami yafi takobi 22/2/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): *_GALADIMA FAMILY_* Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 08 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ ____Sai bayan sallar la'asar Taufeeq da Kareem sukaje daukoshi a airport yadawo gida cike da nasara inda gabadaya farfajiyan gidan GALADIMA FAMILY cike yake da yara da jikoki don taryan Sauban. A hankali motan tashigo cikin farfajiyan gidan bata tsaya ko inaba sai parcking space,su duka ukun suka fito daga motan kowanne dariya ne kwance akan fuskar sa. Yaran gidan ne suka fara tsalle da muryan dawowan sa inda suketa tururuwan yimasa barka da zuwa. Yassir babba ne yajawo trolly bag din. Uban gayyar kuwa direct wajen Ammi yanufa kaitsaye murmushi kwance akan fuskar sa ya furta "Oyoyo sweetheart yayi,yayi maganar tare dayin hugging nata. Murmushi kwance akan fuskanta tadan bubbuga bayansa tace"Oyoyo son hope kadawo lafiya? "Alhamdulillah sweetheart ! Ya ambata. Nufar bodejo yayi da niyyar yin hugging dinta itama,da sauri taja baya tare da mere baki tace"Allah yatsareni da wannan dabi'ar yahudawan inazan iya wannan shedancin saudan?boko yagama lalataka gabadaya Murmushi su Ammi suka sanya. Nufar Ummie yayi fuskar sa cike da fari'ah ya miqamata hannu don musabaha,itama miqamasa tayi don gaisuwan su kenan muddin zasu hadu. "Ummie na yaushe kuka shigo Mai din?ainazata sai gab azumi zaku iso? dariya Ummie tayi tace"aikuwa wannan zuwan munzo da wuri amma jibi zamu koma saboda school dinsu Laila da Nihal. Gyadakai yayi tare da murmushi yanufi Mom tare da rissinawa ya gaisheta itama ciki da fari'ah ta amsa yanufi mommy,hannu ta miqa masa suka tafa duk dashi a kunyace yake. Bodejo tace"Uhm uhumm lalacewa yakai lalacewa yanzu ke hauwa ko kunya bakiji ba?kika miqama kusan danki hannu kuka kashe? Gabadaya wajen dariya aka sanya,a zahiri kuwa Aunty hauwa bata wuce shekaru uku zatabawa ya Sauban ba,Yan matan gidannan suka fara gaida cike da girmamawa. Zuhra kuwa tana gamai gaisheshi ta sunkuyar dakai tamkar wata munafuka,akanta ya tsaida idanuwan sa sai dai kallo daya yamata yakauda kai. Dunguma sukayi suka shiga cikin parlon Galadima don da alama yau anan za'ayi dinner akuma taba hira. "Sweetheart Inasu Daddy da Galadima? Ammi tace"Basunan sunje masallaci kuma daga can zasu wuce jana'izar ladan don Allah yamasa rasuwa dazu wajen 3:30. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un yarasu? Ah muma zama baikama muba yakamata ayi jana'izar damu ko friend? Kareem da Taufeeq suka mike, Ummie tace. "Haka zaka kuma fita babu abinda zakasa abakin ka? Bodejo ya alhamis ina azumi ko kin manta ina azumin litinin da alhamis?yaqarisa maganar yana fita. A kaikace bodejo ta makama bayansa harara tace"Oho maka nina manta ma kanayin wani azumi. Bayan sallar isha'i gabadaya ahalin sun hallara a hall din cin abincin wanda yatsaru iya tsaruwa fada kuwa bata bakine sai dai kai maikaratu ka kiyasta irin tsaruwar Galadima family. Bayan Sauban yagama gaida iyayen nasa maza sun taba 'yar barkwanci da hausa shida Galadima anan akafara cin abinci harda matayen. Babu wanda yasake magana sai zuwa can ne mommy talura babu zuhra awajen cin abincin,gyaran murya tayi tare da duban nihal tace"Nihal ina zuhra ne?gashi anacin abinci batanan,tashi kije ki kirata. Miqewa tayi zata tafi Mashahuda tace"Bari nakirata a waya muji mommy,Kiran wayar zuhran tayi ba'a dau wani lokaci ba akayi picking. Da yake a handsfree wayar take cikin sanyin muryan ta maicike da natsuwa tare da shagwaba tace"Hello Aunty Mashahuda inayini? Mashahuda ta amsa tana me cewa"kizo dinning cin abinci anata jiranki fah,cikin shagwababbiyar muryan ta tace"Aunty Mashahuda na qoshi nikam shiyasa ma banzo cin abinci ba. Har Mashahuda zatayi magana Ammi ta amsa wayar,cikin muryan rashin wasa tace"Me kikaci?kiyi maza kizo kici abinci ina jiranki ne. Tana gama fadar hakan ta datse wayar. Mommy tayi murmushi tace"Zuhra hmmm batason cin abinci kwana biyu ina lura da ita. Cin abincin suka cigaba dayi. Ko 5minute ba'ayi ba tashigo tare da sallama cikin sanyinta,duk dagowa sukayi suna dubanta, Sauban kallo daya yamata sai dai kayan jikinta sun mata