← Book details Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 64

Sashe 21

Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nan bata dace da Yaya ba,kuma wallahi bataji fa"wani mugun kallo Ammi ta watsa mata wanda yasata Jan bakinta ta dinke. A bangaren Ummie kuwa sai nan nan sukeyi da Zuhra ita da Amma har ma dama-dama Amma tana sakin mata amma sam takasa sakin jiki da Ummie duk da kuwa yanda Ummien ke nuna kukawar ta agareta,mikewa tayi tare da cewa"Ummie bari naje na amso abincin ku wajen Bodejo wai tasa ayi muku faten alkama takarisa maganar batare da tajira abinda ko wannensu zaice ba,da kallo duk suka bita dashi. Ummie ta sauke wani nannauyan ajiyar zuciya tare da goge 'yar kwallan da ta taru mata tace"kingani ko Amma? Zuhra bazata taba sakin Jikinta dani ba sam,duk wanda ya shiga tsakanina da diyata haka tsawon shekarun nan bazan taba yafemasa ba ko wanene. "Kiyahakuri bilkisou aikomai a hankali ake binsa kuma a hankali zata saki jikin nata dake,inace ba yau bane aka warware komai?to komai zai dawo dai-dai yanda baki tunani ki kwantar da hankali,insha Allah ninarasa meyasa mu number addanku duk idan nakira baya shiga. Tayi maganar tana me latsa layin Adda Zainab din,cikin sa'a kuwa taji tashiga. "Kinga kuma tashiga bari muji lafiya kuwa. Daga can bangaren akayi picking call din,nan suka shiga gaisuwa anan Amma ke sanar da ita abinda ke faruwa sannan tafada mata tana maidugrin. Sosai tanuna jajantawar ta tare da alhini ta Kuma ce insha Allah Alhaji yau idan yadawo zata taho gobe da sassafe. Anan sukayi sallama da junan su inda Adda Zainab tacika da tsananin farin ciki don ko babu komai burinta na gabda cika koma tace yacika,landanan ta latsa kiran aminiyarta hajiya Aliya anan ta sanar da ita yanda sukayi da Amma. Itama taji dadi ta Kuma ce lallai tafiyar da ita za'ayi don aiwatar da aikin yanda ya kamata,sallama suakyi cike da kosawa ma garin ya waye. *WASHEGARI* Su Adda Zainab tun 7:00 suka fita amma basu suka isa ba sai wajen 6:30 sosai suka wahala don motar haya suka bi inda suka samu tarba na girma da kulawa. Sai da aka bari sukayi wanka suka ci abinci sannan aka fara gaishe-gaishe har sashen Galadima sukaje don mika gaisuwan su agareshi,cike da dattaku ya amsa sannan suka koma sashen Ummie nan aka dasa hirar yaushe gamo inda Zuhra tadan saki jikinta sosai don hajiya Aliya macece mai barkwanci da ban dariya,itadai Ummie na kwance akan hadadden gadon ta, Zuhra ne tashiga toilet din Ummien. Tadan bata lokaci kafin tafito tare da duban Ummie tace"Ummie ga ruwan wankan can nahada miki da komai da komai a ciki",cikin jin dadi ta dubeta tace"tnx my lovely daughter Allah yama rayuwar ki albarka. Da ameen duk 'yan farlon suka amsa. Ammi tace"kawa muje sashen Bodejo na dan taba hira nadawo",Zuhra tace"to muje. Ummie ma mikewa tayi don shiga wankan,kallon juna Adda Zainab da hajiya Aliya sukayi tare da sakin murmushin jin dadi,bayan tashiga toilet din dama maganin na jikin zanin Adda Zainab da sauri ta kwantoshi tare da mikewa dai-dai inda suka ga Ummie nasa kai nan suka daga pillow din tare da dan yaye gefen bedshit suka cidda duvet still akasan bedshit din,suka sake daga duvet din sannan suka tarda matress din,cikin sauri suka barbade maganin tass tare da barbajeshi. Nan sukq maida komai normal tare da duban juna duka saki dariyar jin dadi,cikin sauri suka fita dakin tare da nufar masaukin su. ********** "Barki kiji hajiya Laure nibazan lamunci cin zarafin ki ba akan yara,ni ina ruwana da abinda yashiga tsakanin Rammat da Akeela?da Akeela da Rammat duk abu daya ne a wajena...... "Karya kike Biba ba haka kika daukesu ba,me kike nufi ko kiso ko kada kiso Akeela jinin Sauban ne kuma aure kamar anyi angama. "Hhhhhhhhh casss! Auren da auren manufa zaki hada?ai Yaya Laure duk wanda yayi hulda dake yasan halinki ciki da bai,dadin abin ragowa zai sama don nasan duk rashin jin diyata bata aikata munanan lefukan da jikanki ke aikata wanda ko karya sai haka. Bude baki Guggo Laure cike da mamakin irin kalaman hajiya Biba"Biba nizakiwa sharri kiyiwa jinina?wallahi sai nabaki mamaki sai na nuna miki dani kike zance. "Ina sauraren ki nidake kafasa,kuma niba sharri nake mata ba gaskiya nafada amma kijira lokaci komai zai bayyana kansa"! Tana gama fadar haka tajuya tashige daki tare da rufe kofar. Nanfa Guggo Laure tashiga zage-zage sai tsinewa Rammat albarka takeyi ta kuma ce tajira taga abinda zai faru sai ta bata mamaki. Hartana kwallan ta tsaban takaici haka tajuya gida. ******* Banda nishi babu abinda kakeji natashi a dakin hajiya daharatu,da ita da Akeela ne suke aikata masha'arsu cikin kwanciyar hankali. Hajiya dahara sai sumbatu take"please baby kada kibar ni koda kinyi,don nima inason abinda kikeso don Allah ki kara rikeni gam"nan ta cigaba da shirmenta Akeela nataya ta gabadayansu haihuwar uwayeensu da ubayensu( _wa'iyazubillah! Allah yakawo mu zamanin da aikata sabo yazoma ba abin komai ba,don Allah 'yan uwa me muke nema da wannan rayuwar?meyasa muka mance cewa duniya bafa ma tabbata bace? meyasa muke mance banda wannan rayuwar akwai wata da zamuyi anan gaba?Wai mun mance wancan rayuwar ba'a ciwo ne?ba tsufa ne?haka zalika ba'a mutuwa ne?duka ba'ayi,in wuta wutane idan aljanna aljanna ne straight babu kwana......don Allah 'yan uwa muji tsoron Allah mufa dunga tuna duk rintsi akwai mutuwa kuma dole ko wane mai rai yadandani nacinta.Yau ina annabi Adam AS?Ina annabi Ibrahim AS ina annabi Yusuf AS ina shugaban annabi Muhammad SAW? Duk cikansu sun koma ga Allah,to shin kai waye da bazaka koma ga Allah ba?ya Allah kajikan magabatan mu,kajikan iyayen mu,kajikan mu ya ubangiji kayima na karshe mekyau._ ) ++++ *MALAYSIA* ++++ Zaune yake a office dinsa kunnensa makale da waya sai dariya yakeyi"ah haba Galadima sai kace wani ragon namiji?wai me kadaukeni ne tsohon nan?nafa fika jarumta wallahi kaima kasan haka,dariya yasakeyi kana ya cigaba "To ya jikin Ummien?Masha Allah,aidama ita sai a hankali zata sakewa da ita Allah dai yakara lafiya da tsarewa,yanzu zan shiga meeting ne Galadima I will call yhu back,katse Kiran yayi yana mikewa tare da gyara suit din dake jikinsa. 03/5/23. [5/7, 14:18] Xahratty (OUM AJMAL): *_GALADIMA FAMILY_* Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page:- 33/34 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ _____'Yan mata da dama sun mutu akan soyayyan Sauban a kasar sai dai wasu masu aji basu iya tunkararsa,wasu ko tsoro da shakkan sa ne yasa basu iya yimasa magana,wasu ko da kansu suke kai kansu office dinsa har sai da yahana sakatariyan shi bari ashigo saboda rashin hankalin 'yan matan yakoma bashi tsoro matuka,ya maida hankali sosai akan aikinshi daga can bangaren kuma yaron mai company din na shirye-shiryen dawowa zai amsa mukamin Sauban,dama can nashi ne rashin kammala master's din nasa ne ya hana abashi kujerun yana America karatu. **** *NIGERIA* **** Ummie kuwa a natse tafito daga bayin bayan ta kammala wankan,cikin nutsuwa tashirya tasanya wata Dubai gown fara tass tare da mayafinsa mai Kama da hijjab don har hannayenta ya rufe mata, gadon ta nufa tafara dube-dube sai dai da alama bataga abinda take nema ba, dai-dai lokacin Zuhra tayi sallama tashigo hannunta dauke da basket din kayan abinci,ajiyewa tayi tare da nufo inda take saboda ganin yanda taketa bincike. "Ummie lafiya?ko wani abun kike nema ne? dagowa Ummie tayi fuskar ta dauke da alhini tare da mamaki tace"Wai casbaha na nake nema amma ko sama ko kasa babu shi kuma akan bed din na ajiye don ko sanda nayi sallan magrib anan na aje gefen pillow dinnan amma kinga babu,gashi na kaku dana tada sallar,tayi maganar tana cilla pillow din gefe guda. "Ummie please kije kiyi sallan bari naduba kafin ki idar angani. "Ok my baby! Ummie ta ambata tare da tayar da sallan,nanfa Zuhra tayi dai- dai da gadon harda su yaye bedsheet da duvet din sai can gefen saqon tsakanin matress din da gadon tagani aiko tajawo tare da kokarin maida duvet din,fasawa tayi tare da sake yaye kayan shimfidan ta kakkabe kan katifar sosai tayi mai tatas sannan tadau bedsheets din da duvet din taje can corridor dinda zai sadaka da toilet tabude laundry basket ta saka su,adai dai nan Ummie ta idar da sallan. Ikon Allah Zuhra daga neman casbaha sai Kuma a bige da gyaran gado? murmushi kwance akan fuskar ta tace"Ummie wallahi sunyi datti ne naga sosai ga kuma datti harda kasa-kasa akan katifar shiyasa nacire"takarisa maganar tana bude closet,wanda bangare guda yake shake da bedsheets colours mabanbanta,duvets nd etc. Jawo wani tayi colour daya da wancan sai dai zane ne ya bambanta shima sai kalura ne zaka gane,wannan karan bata dauko duvet ba dama akwai wanda take lulluba dashi still a gefen bed din,shinfidawa tayi takuwa liliye gadon tsaf tare da sake gyaggyara pillows din,bayan ta kammala tajawo stool gaban kujeran da Ummie ke zaune ta ajiye,tana kokarin dauko basket dinne takatseta"Kinga ai kan carpet zan sauka naji kafata nayimin tsami,kije kikira addan ku kice nace suzo ga abincin idan kuma a kawo musu ne to.Zuhra tace. "Ok bari nasanar dasu,tayi maganar tare da fita,jingina ummie tayi da jikin gadon tare da rufe ido a haka taji sallamar zuhra. "Ummie sunce gasunan zuwa,babu kuwa jumawa da shigowan ta sai gasu suma sun shigo,da sauri Adda zainab tanufo ummie fuskanta cike da murmushi tace"bilkisou har kin fito wankan ne?Ummie tace"aiko nafito Adda ai ko kafin nafito naga kuntafi. "Ea muma munje muyi sallan ne,hajiya Aliya tace"sannu hajiya bilkisou ya jikin naki? Ummie tace"Alhamdulillah ai naji sauki wallahi. "To Masha Allah Allah dai yakaro mana lafiya dai,ubangji yabarki da diyarki"tayi maganar tana me shafa kan zuhra tana dariya. "Hajiya Aliya kenan Amin nagode. Nan Zuhra ta shiga zuzzuba musu abincin kowa na zabar abinda zaici, kallonta Ummie tayi tace"baby ke kinsa abincin kinci? "Ea Ummie naci tare dasu Bodejo da Amma aimu faten alkaman Bodejo mukasha,Kinga kuma itama Amma tanada diabetes in so sai yau akayi danan yawa,kuma fa nasa musu wadataccen kayan ciki. Adda zainab tace"ah lallai diyar albarka kinaji da wadannan kakannin naki,nikuwa bilkisou yanzu kindena cin dan gauda ne?dariya Ummie tayi"mekika gani Adda? "A'ah tambayace kawai naga kwana biyu banjin labarin dan gaudan. "Uhummm Adda kenan shekarun da yawa inaji rabona da cin dan gauda tun
Chapter 21 · 0% Book details